NOVELSUncategorized

DIYAM 44

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Four : Sweet Sixteen

Nabi bayansa da kallo ina jin kamar ya ciro tawa zuciyar ne ya tafi da ita. My chest felt empty kamar babu komai a cikinsa, ji nake kamar in bishi a baya O
da gudu in rungume shi kamar yadda naje yi sanda ina karama, ina son ya rungume ni nima kamar yadda ya taba yi min a gidan Alhaji Babba, but I couldn’t saboda akwai wata igiya data ke rataye a wuya na, igiyar auren Saghir. 

Bazan iya komawa palon ba saboda duk bana son kallon fuskokin su. Yes, Alhaji Babba ya cuce ni iyakacin karshen cuta amma kuma still yayan Baffa na ne, kuma va’a taba chanjawa tuwo suna, komai suka yi bazan taba cewa su ba iyayena bane ba. And there is wani satisfaction da ake samu a cikin forgiveness, wannan satisfaction din shi nake yi wa Sadauki kwadayin samu.

Sai na juya na tafi gurin Maman Iman duk da dai ita kuma surutu ne da ita ni kuma a lokacin bana son magana. So nake inyi shiru inyi jinyar zuciya ta. Dan haka ina zuwa sai nace mata bana jin dadi ne ina so zan kwanta, sai kuwa ta bude min dakin yaranta, dakin mu ni da Asma’u a da. Na shiga na kwanta, but sai dakin ya cigaba da dawo min da memories din da. Sadauki’s memories, na sake gwada kiran wayarsa still bata shiga. Dai na kifa kaina a pillow na fara kuka. It really hurt to love someone so deep while you are married to another, another din kuma wanda ba ka so.

Sai da akayi magrib Maman Iman ta shigo ta tashe ni in yi sallah. Ayi alwala nayi sallah sannan na koma part din Inna, ina shiga na tarar sun tafi, Inna ta bini da kallo tace “kuka kikayi ko?” Na girgiza mata kai amma sai hawaye suka fito. Tace “me yasa kika masa magana dazu? Ba nace miki ki fita daga maganar ba? Tunda ke kince kin yafe shi ki barsa ya karbi abinsa. Na gaya musu nace Asma’u ma tace bata bari ba”. 

Ranar sunday, da safe muna shirye shiryen komawa gida ni da Subay’a kamar daga sama sai jin sallamar Sadauki nayi a tsakar gida. Na dakata da folding kayan da nake yi naji Inna tana amsa masa da yake tana tsakar gida ni ina palo, naji ya gaishe ta ta amsa tana tayi masa sannu da zuwa tace ya shigo palo, yana daga labule muka hada ido sai yayi sauri ya saki labulen ya koma yana cewa “basai na shiga ba Inna, dama zan dan shiga dakin Ummah ne” sai Inna ta kira saka mayafinta da kanta ta shiga gurin Maman iman ta gaya mata za’a wuce, saboda sai an bi ta nan za’a karasa dakin Ummah. Subay’a dake kusa dani ta tashi ta leka tsakar gida, sai naji yace mata “Subis, come here” sai ta makale a bayan kofa taki fita, yace “ba zaki zo ba? Dan kin ganni baki babanki kuma fari ko?” Sai inna ta dawo ta tarar dasu tayi dariya tace “Subay’a kizo ki gaishe da babanki mana?” Subay’a ta tura baki tace “ba baba na bane ba” inna tace “ji fitsararriya?” Yayi dariya yace “gado tayi ai” sai Asma’u ta shigo, tana ganinsa ta kama murna tana gaishe shi, yace “yar asama yammata” a raina nace “wato yana iya yiwa kowa magana faran faran, ni ce dai na koma aljana a gurin sa”. 

Asma’u ce ta raka shi ya bude dakin Ummah ya shiga, sannan ta dawo. Inna ta shigo tana kallona tace “kina jin Sadauki ba zaki fita ki gaishe shi ba?” Nace “baya son ganina inna. ganina a dakin ne fa yasa ya fasa shigowa”. Inna tayi shiru kawai bata ce min komai ba ni kuwa zafin da nake ji a raina yasa na dauki kayan na koma cikin daki, amma sai na kasa cigaba da gyarawa na kwanta kawai. Ina kwancen ya dawo, ya leko yayi wa Inna sallama sai ta ce yazo tana son magana dashi. Ya shigo palon ya zauna tace “Sadauki. Ni dai kam bansan wanne kalamai wanda yayi laifi irin wanda nayi maka zai yi amfani dashi gurin rokon gafarar wanda yayi wa lafin ba. Na cutar da kai Sadauki iyakacin cutarwa kuma duk a bisa son zuciyata ba wai dan kayi min wani laifi ba. Amma a karshe sai ya kasance ni din dai nice a wahale. In kace ma ba zaka yafe min ba Sadauki bazan ji haushi ba saboda na cancanci koma menene zakayi min. Amma abinda na sani shine nayi nadama, Sadauki dan Allah….” Sai ya dakatar da ita yace “Inna na yafe miki ai, da ban yafe miki ba Inna ba zaki ganni a dakin nan ba. Maganar ta wuce tsakanin mu har abada” sai Inna ta kama yi masa godiya, har ya sake mikewa zai fita sai ta kira Asma’u, sai kawai zuciyata ta raya min in leka su, naje ta jikin labule ina lekawa sai naga ta kamo hannun Asma’u ta saka a cikin na Sadauki tace 

“na hana ka auren Diyam a lokacin da kiyayyar ka ta rufe min ido, amma yanzu ga Asma’u na baka, duk abinda yayi Diyam shi yayi Asma’u har kamanninsu iri daya ne, ina fatan zaka karba kuma wannan zai wanke maka zuciyarka” 

Na juya ina dafe kirjina kamar mai kokarin gana zuciyata fadowa kasa. Idanuwana kamar zasu baro mazauninsu ina girgiza kaina a hankali ina cewa “no, no, no” amma sai naga Sadauki yayi murmushi, sai ya cire hannun Asma’u daga nasa ya mayar wa da inna yace “Inna na gode da wannan babbar kyauta da kika yi min, kuma da gaske wannan kyautar ta wanke min zuciyata sosai amma kiyi hakuri bazan iya karba ba. Zuciyata Diyam take so ba kamannin Diyam ko asalinta ba, in na karbi Asma’u banyi mata adalci ba saboda zan tilasta mata zama dani alhalin zuciyata bata tare da ita. Kiyi hakuri idan ban kyauta miki ba amma hakan shine zaifi mana alkhairi a gani na”.

Na saki labulen na zauna a gurin ina juya lamarin a kaina. He refused Asma’u, sweet teenage Asma’u, yana claiming that his heart belongs to me, how can that be? Bayan ni kuma I belong to someone else?

Sai yamma muka koma gida, daga nan kuma muka cigaba da lonely rayuwar mu nida Subay’a. Duk da ina kokarin ganin na rage tunanin Sadauki amma kullum tamkar kara min shi akeyi. 

Two weeks after that akazo aka raba gidan Alhaji Babba. Aka ja katanga tun daga part dinsa har zuwa bakin gate, sai ya kasance part din nasa da filin compound din dayake gaban part din har zuwa dakin maigadi da gate din gidan duk na sadauki ne. Main house din kuma da sauran abinda ya rage na compound shi kuma na Alhaji Babba, amma ko gate basu dashi dan haka sai katanga suka fasa ake shiga gidan, ko kudin da za’a sayi kofa a saka babu.

Ba’ayi sati dayin haka ba dakunan Alhaji Babba suka zama dakunan kaji, Sadauki ya cika katon palon Alhaji da kuma two bedrooms dinsa da kajin gidan gona, broilers da layers. Compound din kuma akayi katuwar rumfa aka zuba raguna da tinkiyoyi, dakin maigadi kuma ya saka masu kular masa dasu.

Alhaji Babba kuma ya koma cikin gida, dakin da Inna ta zauna nan ya dawo da zama. Washegarin da aka zuba dabbobin da sassafe murja ta kira ni “Diyam wallahi yau bamuyi bacci ba a gidan nan. Yadda muka ga rana haka muka ga dare wallahi, ragunan nan tun magrib suka fara koke koke har garin Allah ya waye sannan kuma kaji suka dauki nasu suma. Ni dai gidan ki zan taho in taya ki zama kafin hamma ya dawo ya kore ni” nace ta taho babu komai. Sai kuma naji babu dadi a raina. Murya, Hajiya Yalwati da sauran yayan Alhaji Babba basuyi wa Sadauki komai ba amma har dasu ake paying. Isn’t Sadauki taking this too far? Bayan gudun daukan alhakin wanda baiji ba bai kuma gani ba?

Da dare Sadauki yaje gidan mu. Ya gaishe da Inna sai yace da Asma’u. “Yar Asama kina son gidan gona?” Tace “gidan gona kuma hamma?” Sai ya ajiye mata takardu yace “gashi nan na baki kyauta. Duk karshen wata za’ake kayo miki kudin da aka samu a ciki” Asma’u sai murna da tsalle, yayinda Inna ta saki baki ta kasa magana.

Yana tafiya Asma’u ta kira ni tana son bani labari amma maganar ta kasa fitowa dan murna. Nace “kinga ki nutsu ki fada min, me ya faru?” Tace “hamma Sadauki ya bani kyautar gidan gonar sa da yayi a gidan Alhaji Babba” cikin mamaki nace “what?” Sai ta mikawa Inna tayi min confirming maganar. Har da sunan ta da komai a jikin takardun. 

Na kira shi da niyyar yi masa godiya amma shiru wayar bata shiga kamar kullum. Nayi tsaki na yar da wayar feeling very frustrated sai kuma na dawo na sake dauka na tura masa message “ina yiwa Asma’u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka” na tura sannan na zauna rike da wayar a hannu ina jiran reply. Can sai gashi ya shigo. Three words

“You are welcome”.

Nayi tsaki ina jin haushin sa, amma bansan dalilin da yasa nake jin haushin nasa ba.

Bayawa ko? Sorry, busy weekend

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button