NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 11

???? *WA ZAI FURTA?*????
              1⃣1⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

        ****************
*KADUNA RIGASA*

Ranta a bace amma Sam hankalinsa baya kanta sauri sauri yakeyi daman tun da ya iso an shigo Mata da tsarabun da yayo.
Gabanta ya fadi, wannan rawar kafar ta mecece?
   Ta daure ta dan boye fushin ta, kafin tace : Wai lafiyar ka kuwa?
Yau ka dawo sai Yanzu ka shigo nan Kuma kana ta wani sauri sauri…….. Nan da Nan guiltiness ya kamashi, ya Fara Yan kame kame….. Nan da nan ta gano bakin zaren tayi murmushi ko hada gajiya halan?….. Ya kakaro murmushi gajiyar ma ce gaskiya.
Gaskiya ne.
Ta Mike , mu kwana lafiya kaje ka huta……wuf Shima ya Mike Daman jira yakeyi yayi waje Yana fadin Allah ya tashe mu lafiya.
 Ta bishi da ido kawai, lallai namiji akala ne, ta kuta zaka gane kirenka ka gama kwanakin ka dawo…amma zanje in ga kalar wainar da ake toyawa.
  Ummi nada tsawo Kuma doguwa ce tafi Amira .
Ita kuwa Amira irin Dan jikin Nan gareta Mai kyau da tsari, kallo daya Kai kace ummi keda Yara biyu ba ita ba.
Tana gyara jikin ta don ko tsakanin Ahmad da almustapha shekara biyar ne.
  Ta bashi kamar mintuna arba’in kafin ta saka bakar jallabiya matsattsa tabi jikinta da turaren da ya fi so ta nufi sashen sa don ta San Yanzu suna can.
Ta danna karaurawa, ummin ce ta zo ta Dan leka…..ta kalleshi tare da yin Yar dariya *Yaya Amira* ce.
Oya bude ya fada Yana kishingide Yana Shan kankana.
Ummi na sanye da dogon wando jeans ya matse ta da Yar matsattsar Riga kanta ba kallabi ta yi kitso shuku Wanda ta daure da katon ribom saboda karancin gashi .
   Ta kalli ummin sama da kasa sannan ta danyi murmushi sorry for disturbance please…..laaa ba komi karaso ciki.
Ya tashi zaune Yana Yar dariya Amira Yaya?
 Tayi Yar dariya…..zuwa nayi in ji ka siyo mun book din nan kuwa dazun na mance in tambayeka……ohhh yes, Yana mota Bari na dauko Miki……..ya yunkura..
A’a barshi kawo key din na dauko Yana ta wajen Ina?
Wurin Mai tuki jikin kofa Yana Nan….Ummi dauko key din.
Ta Mike.
Ya Kura Mata ido, Yana son tayi shigar doguwar Riga, wannan kamshin zuwa akayi ayi mun kwalele?
Good and fine, ta ce cikin zuciya, sannan tayi murmushi ta ce hmm kawai.
  Kinji?
Gobe zanje kasuwa Dan Allah da safe ba dadewa zanyi ba, Zan biya gidan Salma…..me akeyi gidan salmar?
Ta dan mishi warrrr da ido, zumunci……duk sai ya diririce, Ni Zan kaiki ko?
Ta Dan Kara farrr da ido tare da Yar dariya, lokacin da Zan fita bana tunanin ka tashi cos by 8 nake son zuwa kasuwa Kuma Kai ba ma’abocin son zuwa kasuwa bane…..Zan biki please.
Saura kadan ta tuntsure da dariya yanayin yanda yayi maganar. Ta danyi murmushi…..Ummi ce ta fito da key.
Ta mike Bari na dauko book na.
Ya bita da ido Ummi ta dankara mishi harara Amma Sam bai lura ba.
Bude tabar kofar tana dawowa Bata shigo ba ta tsaya bakin kofa….ga key din Ummi, ….wuf ya Mike Bari na karbo.
Tana daga waje ya hada da key din da hannun ya rike in fito goben muje?
Nooo, kaga Ummi zata ji haushi kayi hakuri ka bata full time dinta don nima turn Dina…..ya murza hannun da karfi.
Tayi Yar Kara, ya dawo Yana dariya…… Ummi kamar zata fashe amma ta daure ta cije duk da haka sai da ya danga chanji amma sai kawai ya share.
Butique ta tafi, ta siyo rantsattsun English wear sabbi hada three quarters wando da skirt da crazy jeans.
Har ta dawo wajen Sha daya bai fito ba.
Ta fada wanka Yara sun tafi islamiya tahfeez, ta kulle kofar ciki tabar Mai aikin ta kitchen tana fita ta kofar baya.
   Amira nada gashi sosai, kanta kananan kalaba ne duk sun zuba bisa bayanta wani sky blue crazy ta saka da wata crazy riga Mai hannu daya nononta kawai rigar ta rufe kasan ta Kuma bazace, ta cikin Bazar kana hango cibinta.
Kamshi kawai ke tashi gidan.
Sha biyu saura ya fito, motar ta kawai ya gani yasan ta dawo.
Ya nufi bangaren nata don agaisa.
Tana Jin motsin sa ta ruga daki ta dawo rike da littafi kamar me karatu ita a dole bataji shigowar sa ba.
 Mutuwar tsaye yayi ya kusa sarkewa da miyau sai kawai taji Yana tari…..ta dago Kai da sauri irin ta razana din nan…….

     *****************
*Federal University dutsinma*

 …..Ta kasa dagowa ta amsa, jikinta ya Fara Yar kyarma.
Helen ta kalleta, Anwar na Miki magana…
 A hankali ta juya kamar Mai ciwon wuya , idanun sa cikin glass Yana Dan murmushi…….. Minti biyu. Ya fada kafin ya juya ya Fara tafiya can nesa wurin parking motoci.
 Ta Mike  jikinta duk ya mutu tabi bayansa.
Jingina yayi da mota hannuwan sa duka cikin aljihu ya kura Mata ido.
  Kanta a kasa ta karaso fuskar ta babu yabo ba fallasa. Ta kasa magana…. Ya Kara nutsar da idanun sa gareta yace: Ranki ya dade ya exam din?
 Ta danyi murmushi kadan Alhamdulillah…Ina kwana.
Lafiya Lau, na Aiko a Baki hakuri kina ta ba mutane wahala kince dole sai nazo da kaina to gani nazo.
Ta Kara kasa da Kai tana murmushi…… ban taba tunanin zakiyi fushi haka dani ba ko kadan.  
 Tayi shiru dai,
Har kiranki nayi da sallah without knowing u deleted my number……. Shikenan dai ya wuce. Ta fada a hankali.
Kin tabbatar ya wuce? 
Eh,
Mun shirya?
Sai kawai tayi Yar dariya saboda yanda yayi tambayar kamar wani karamin yaro.
 Yabi fuskar da kallo……  Ji yakeyi kamar ya kamota ya rungume… Yayi murmushi kinji mun shirya Yanzu ko?
Eh, 
To na gode, Zan kiyaye daga yau Allah ya Kara Baki hakuri shikenan ko?
Um, tace a takaice.
Ina zakije yanzu?
Gida Zan tafi.
To muje na rakaki ….. A’a barshi kawai na gode, ta katse shi tare da yin gaba abinta.
Ya bita da kallo baya so ta tafi ko kadan.
 Ya hura iska…. nawaoooo yarinyar nan miskila ce ta karshe.
  Wani sanyi zuciyar ta keyi mata, tana zuwa daki ta fada bisa katifa ta rungume filo ta maida idanu ta rufe a hankali.
Su Anas suka bushe da dariya, ya cire glass Yana hararar su , Helen na bayansu, tana so taji yanda akayi.
 Munafuki sai kace yau neman shiri zakayi Shi yasa tun karfe biyar ka yo wanka kana faman shiri.
Mtsew yaja guntun tsaki, suka jera suna tafiya.
Ya kalli Helen din dake kokarin jerawa da su yace ke kuma lafiya kike faman binmu?
Kamar za ta nutse dan kunya, ta juya kawai ta koma…… Sadeeq ya harareshi wallahi ka daina dizga mutane haka Anwar. 
Ya maida glass din a idon sa, inba gulma ba ubanwa zatayi cikin mu?
Kasan tun dazun ina tsaye da Bilkisu hankalin ta na nan?
Kayi mamaki ne? Inji Anas.
Waye bai San ta mutu kanka ba…… Ban san abinda kuka mayar dani school din nan ba. Ko wace jik and jak Sona takeyi? Mtseww kada kusanya inci ubanta da kyau fa. Mufeeda ma ta gama haukanta ta shafan lafiya bare wata arniya……. Kada ka taba yarinyar mutane arnan can sun fika hauka….. Ko in gwada? Muga cikin mu wa ya darar ma wani?
  …….Anas ya zaburo Kar ka Soma wallahi. Babu ruwanka da ita baka San tana yi ba kawai ka ci gaba da nuna Mata baka ganeba.
    Naji! Ya fada a takaice.
Yaushe zaka Mana bayanin Economic of production?
4, yace a takaice.
4, Kuma? 
Eh, saboda zanje wani wuri da daddare…….duk suka kalleshi.
Yanzu barci zanyi, 4 Kuma sai muyi zuwa magrib ko bai muku ba?
   Amma ai yau ba ball ina zakaje ne?…. Murmushi kawai yayi.
Suka Kara binsa da ido.
Wai lafiya? Ya bukata Yana Yar dariya.
Ina zaka je muka ce?
Wanda zai bini ya shirya ban hanaku ba….. 
Duk sukayi shiru, suna kallon kallo.
Ya kyalkyace da dariya wallahi ku munafukai ne…… sadeeq ya Kai mishi duka wallahi baka da gaskiya.
Ya kyalkyace da dariya.
Mashin daya suka hau.
Dakin acike bai samu ya yi barcin ba daga wannan sai wannan, ya gaji matuka. Shi ba koyawa ko bayani ke baya son yi ba, cin lokacin sa da akeyi ke sanya Shi kosawa.
  Sai da yayi wanka sannan ya Fara shiri cikin farin boyel ya dauko hudaddun takalma ya saka na fata *masarati*, yana cikin sharce gashi suka shigo.
Duk suka zaro ido….. Ya fiddo turaruka ya shiga fesawa kusurwa kusurwa, lungu lungu.
Sadeeq ya kalleshi *Anwar Ina zaka je?*
Bai ma kowa magana ba ya Mike, har ya Kai bakin kofa ya waigo ku bakwa ganin karuwa da danta baku tambayi ubansa ba.
*Zance Zan je*……. Ya fice da sauri suka Fara surma mishi zagi.
Yana tafe Yana tunanin Yanzu kuwa Yana zuwa ya tarar tana tare da wani to ya zai yi?
Ya tofar da miyau, Wai kada abin ya Zama gaskiya.
Mashin din Salim, roba roba ya karba.
 A bakin gidan yayi farking ya kafe mashin din tare da Zama saman Shi kamar kujera sannan ya Kira wayar ta, tana kwance da Yar shimi ta barci rike da littafi tana karatu wayar tayi Kara…….. Tunanin ta mommy ce.
Ta muskuta, Ba tare da ta kalli screen din ba tace.
Mommy…..
Mommy Kuma? Ya bukata.
Ta zaro ido tare da kallon fuskar wayar sai akwai ta mayar a kunne….still Baki mayar da no. Ta ba ko?
Ya hakuri Ina wuni?
Gani waje Ina jiranki……. Waje Ina?
Kofar gidan ku.
Na shiga uku…..Bata San a fili ta fada ba sai da taji yace…..zuwan nawa ke da shiga uku?
Ta zaro ido. Duk ta diriri ce. 
Ko baki maraba dani na juya?
Ina zuwa… Ta fada a hankali.
Jikinta yana ta Yar kyarma. Ohh ni Bilkisu ko lafiya?
 Sauri sauri ta shirya ta zumbula hijabi har kasa ta fita.
Kallo daya tayi mishi tsikar jikinta ta tashi Yarrrr….
 Anwar a manyan Kaya????
Tayi murmushi kunyar duniya ta kamata gabanta ya dunga faduwa tana zullumin me ya kawo Shi?
  Ya tsareta da ido, yaki magana.
Ta dago Kai sai ta zumbure baki ta maida Shi kasa.
Yayi murmushi, haushi kikeji nazo saboda ba Suleiman bane ko?
Kallon sa tayi da sauri , ya Sha mur!
Kin tsaya kina ja mun class kamar irin nazo zancen nan.
Dariya tayi.
Yanzu dai Ina wuni, me ya kawo ka cikin tsohon Daren nan?
Yayi murmushi, zance nazo can baya na biyo mu gaisa ko ban kyauta ba?
Gabanta ya fadi, ta dan tsuke fuska. Hmm.
Ko ban kyauta ba?
Kayi daidai.
Ke baki iya tarar bako?  Ko haka kikeyi wa Suleiman idan yazo?
Suleiman again? Ta ce cikin zuciya. Wai meye kake ta fadin Suleiman…… Ba Kya so long sunan sa na fada kada gabansa yayi ta faduwa?.
Ikon Allah ta fada.
Eh Mana. Gashi kin kasa sauraron kowa sai shine ya shirya mu……. Baka ji dadin hakan ba?
Ya Dan harareta meye tsakaninki dashi? Ki fada mun sirrin….. Anwar rigima kazo muyi ko kuwa zuwa kayi mu gaisa da gaske?
Duka biyun nazo yi.
Karatu nakeyi.  Nasan kayi covering gobe ka Fara ansar extra sheet ina page 2 ina zare ido…… Suleiman zai Baki amsa…. Na shiga uku. Ta fada tare da kallon sa. Yasha mur, ko ruwa bazaki bani ba da gaske……juyawa tayi kawai.
Ya bita da kallo. Kwalin fresh milk ta fito da Shi da cup a hannu, gashi amma ba sanyi.
Ya karbi kofin ya Mika Mata alamar ta zubo mishi.
Ya tsareta da ido sai Yar kyakkyarwa takeyi. 
Nayi kyau da manyan Kaya?
Ta tuntsure da dariya…… Yau naga ta kaina. 
Shima dariyar yayi, to naji kin ki yabawa ….. Ta dalla mishi harara ita wacce kaje gurinta Bata yaba bane?.
Ya Kai kofin bakinsa yasha kafin yace, ta yaba tayi comments kema kiyi naki.
Har zata ce ni budurwar ka ce sai Kuma tayi shiru kada yace *Eh* tafi so *YA FURTA* Da bakin sa.
  Me yasa baki WhatsApp?
Hakanan.
Bai yiwuwa , saboda duk Mai hankali baya abu babu dalili. Me yasa bakya yi?
Allah kawai bana son abun da zai daukar mun hankali daga karatun nan.
 Muga wayar…….ta kalleshi.
Ya nutsar da idon sa cikin nata tayi saurin kawar da Kai.
Kada Inga text din Suleiman? Bazan shiga can ba……ta Mika mishi da sauri, yayi murmushi. Zan dawo Miki da ita gobe ya saka aljihu. Meye password din?
Ta zaro ido, Daddy na kirana every asubah….. don’t worry I’ll talk to him meye password din?.
Dan Allah ka bani saboda……. Saboda Suleiman bazaiji dadi ba? Sau nawa nake ganin ta a hannun sa?
Wai lafiyar Anwar kuwa meye Yanzu magana daya sai ya ambaci Suleiman???? 
Na rantse da Allah sau biyu ne, Kuma duk chargy ya kaimu ya Kuma karbo…….
Yasha mur meye password dinki?.
Gabanta ya Fadi duk ta rikice saboda ANWAR ne password din. Ya kalleta wallahi wurina wayar Nan yau zata kwana Kuma sai kin fada mun password din……….✍????????

Zainab wowo ce ????

Ayi hakuri da kadan. An dameni da cigiya ????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button