NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 12

???? *WA ZAI FURTA?*????
             1⃣2⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

???????? *Godiya ta musamman ga :*
*Mowa ( maimuna Nasir )*
*Hauwa’u, ( mum khady nima Ina kaunarki matuka*
*Da masu mun waya, text da kirana direct ku sani cewa zainab wowo Bata Raina masoya wlhi Ina kaunar ku sosai*
???????? *Unex*????


         ***************
*KADUNA RIGASA*
  
  Ta dan rike kugu tana Yar rangwada…. Mura kakeyi haka?
Wuffff…. Ya riko kugunta, kece Zaki Sanya mun ita Yanzu, Ina Kika Sami kananan Kaya haka?
Sai faman shinshinarta yakeyi ya nutsar da kansa cikin wuyanta.
Tayi wani juyi tare da mayar da fuskar ta gab da tasa saboda ya sunkuyo tayi warrrr…… Kawai taji ya hada bakin sa da nata…… Fittt… ta fizge. Ta danyi baya tare da buga wani makirin tsalle rigar tayi sama cikinta ya fito fili….. Kanka qalau kuwa?
Ya yunkura zai Kara chafko ta tayi baya tana Yar dariya idanunsa sun kada sunyi jawur…. Ya kalleta kamar Mai Shirin yin kuka *Dan Allah ki tsaya bani da karfin binki ko’ina*…….
Amma kasan ba anan kake ba ko?
Ya langwabar da Kai, please one kiss…. Tabbb wlhi Haram. Ta fada tana wata karairaya. 
Ya kura Mata ido duk hankalin sa ya tashi…. Amira kada ki hadu da fushin Allah ki tsaya….
To Yanzu……. Charaf! Taji ya damke ta cikin taku daya. Yana riketa ana dukan kofa da karfi.
Kafin yayi wani motsi ya jiyo muryar hajia ( mahaifiyar sa ) tana fadin Amira ko Bata ciki ne?.
Ya buga wani uban tsoki ya ingijeta ya wuce bedroom dinta da sauri………


        ***************
*Federal University dutsinma*

It seems like baki da gaskiya fa!. Ya fada tare da tsareta da ido.
Ta dake ta kalleshi Yanzu dai Wayata ce zaka tafi da ita ko?
In shaa Allah, ya fada Yana murmushi.
Wai meye zakayi da wayata ne Anwar?, Bincike……., Ya fada Kai tsaye Yana kallonta, tayi shiruuuuu…….
Naji Zan baka, kawo na goge abu daya shikenan….menene?
Wallahi dana goge Zan baka hoto ne…..hoton Suleiman?
Ta doka tsoki Wai Kai komai Suleiman??????
Eh, ai kema komai shine….mtsewww to ba nashi bane nawa ne.
Kiyi hakuri bazan Baki ba don Ina son ganin hoton.
Ta Sha mur bani da Riga ne, Shi yasa da best Aisha ta daukemu muna cin abinci akwai hotuna da yawa nawa sai ka gaji da gani amma wannan bana son ka ganshi…….Ni Kuma naji Shi kadai nake son gani ma …..ta zaro ido. What?
Cikin fushi ta juya gara ta nade tabarmar kunya da hauka… shikenan sai da safe ka cinye wayar ko kaje wurin Yan gyaran waya su bude…..dawo dawo….zo …zo..zo please. Gashi zo ki goge ya fada da sauri Yana fiddo wayar daga aljihu.
Ta kusa sakin dariya Amma ta daure ta Mika hannu okay bani.
Ya rike wayar yaki saki…..ki rantse da Allah ba text ko hoton wani Zaki goge ba…… Wai me ka daukeni ne?
Ya langwabar da kai hoton nawa Zaki goge?…. Ikon Allah ta fada duk ta Fara kosawa, guda daya ne ko?
Ta sakar mishi wayar ganin baida niyyar Bata….. Ya Kara mikowa ungo amma kiji tsoron Allah kada ki gudu da ita Kinga na rantse.
Wallahi Zan baka Yanzu.
Ya sakar Mata ta Dan ja baya ta fidda key din sannan ta shiga setting ta chanza password din, tana dannawa zata Kara confirming yayi fit!!…. Da wayar, Wai meye kikeyi?.
  Kawo na karasa please baka zanyi…… Password kike canzawa??????? Ya fada Yana Mata wani kallo. 
Tayi murmushi, Yanzu dai Kara confirming ka Sanya *Balky02* shikenan…….
Dirowa yayi bisa mashin din saura kadan ya fada Mata tayi saurin ja da baya, kawai ya Fara binta Yana magana cikin daga murya…. password Kika chanza? Hankalin sa duk ya Fara tashi cikin bacin Rai……. Ai …ai ….tanayi tana ja da baya Yana binta.
Gama korar awakin na rantse da Allah sai kin sanar Dani tsohon password dinki da dalilin da ya Sanya Kika canza….au ni Kika mayar photo?
Bayanta ya daki bango ta daga hannuwa sama Dan girman Allah ka ja baya Anwar……waye password dinki?
Ta runtse ido…… Dan Allah kaja baya Zan fada maka…… Kina fadawa Zan koma inda nake meye tsohon password dinki?
Dabara ta fado Mata, sunan da ake kirana gidan mu ne Kuma bana so ka …… *Balky* shine abinda ake kiranki saboda har daddy da mommy suka tafi banji sun kiraki da wani suna ba bayan haka wane password ne Kika goge Wanda bakya so na sani?
Ka koma yanda kake kada wani ya ganmu a…… Suleiman kike gudu da samarinki ko? Ya Kai hannu daya a bango.
Ta runtse ido na shiga uku…..sai kwalla sharrrr……. Ya kura Mata ido jikinsa yayi sanyi sosai, ya sauke hannun a hankali ya Dan ja baya tare da saka hannuwan sa duka ga aljihu ya kura Mata ido.
A hankali ta bude ido, ita kanta Bata iya fadin ga dalilin kukan, saboda wani yanayi ne ta fada Mai rikitarwa.
Ke shagwababbiya ce?
Kamar ta shako wuyansa,
Tayi mishi banza.
Meye tsohon password dinki?……woohoho, Anwar idan maye ne ya Kama mutum tabbas sai mutuwa.
Kina so kiga irin tawa rigimar ko?……. *Yar Fara* ta fada a hankali, kakata ce kafin ta rassu take kirana da haka shine na saka……..ta karasa maganar tana addu’a a zuciya ya Allah ya ceceta ya yarda da hakan.
Yayi jimmm, sannan yayi murmushi me yasa baki so nasan haka?
Ta galla mishi harara ban sani ba …..Nima meye zakayi da wayata?.
…….yayi Yar dariya, bincike….ai Ni ban boye Miki ba.
Karfe nawa?
Ina ruwanki da ko karfe nawa keda kike bakin kofar gida fadawa kawai zakiyi?.
Ina binki bashin abinci Wanda aka mun kwalele lokacin da mufeeda tasa nayi laifi……ta doka uban tsoki, kaje ta dafa maka mana.
Saboda me?
Saboda yarinyar ka ce.
A’a na kawata nake so my best friend Bilkisu…. Hmmm.
Ko ni ba babban abokin ki bane?
Shine, ta fada a gajarce.
Kika ce mun bakya fitar dare ya akayi yau Kika fito ??? Wannan karon Yar dariya tayi Wai haka kake da masifar tambaya?
Ya bi kumatunta da kallo, yau Kika San haka?
Tayi hamma , 
Barci yazo?
Da sauri ta daga Kai.
Yayi murmushi, to jeki kwanta…… Ta juya da sauri daman kafafunta duk sunyi dayi saboda tsayuwa.
Tace sai da safe…….ya bita da kallo Jin bai amsa ba ta Dan waigo….ya tsareta da ido ta dalla mishi harara…..wallahi  ka fiye kallo da yawa. Ya matso da sauri me?
Ta kwasa da gudu ta fada gida tana fadin Wai yau meke damunka ni Bilkisu??????
   Ya Kama dariya kawai ya juya ya haye mashin. Tana jinsa ya tada ya tafi sannan ta shige daki.
Ta cire kayan ta mayar Dana barcin da ta cire ta kwanta…….akwai tambayoyin da nake son yiwa Anwar amma inajin nauyi.
Ta lumshe ido…..yau dole ta kwana karatu kada gobe taci kaniyarta, abubuwan da suka faru suna dawo Mata a hankali.
Ya Allah kasa Anwar mijina ne….ta fada a hankali.
 Tayi tagumi, nasan Yana Sona…..Amma Ina son ji daga bakin sa, ya Allah yasa da gaske abinda nake gani a idanun sa har cikin zuciya ne ya bashi ikon *FURTAWA*…….. Ta lumshe ido……..

 Sha biyu saura ya shiga daki.
Dakin a cike ana jiransa.
 Ganin hada Yan 100level yasa bai saki fuska ba kada su Anas su kawo mishi wasa( …..Kai Anwar case ne ).
Kowa jinin sa akan akaifa don karamin aikin sa ne ya fatattaki kowa yace barci zaiyi.
  A hankali yake kallon kowa daman duk dudumar za’ayi dakin Babu Mai hawan gadon sa,
Ya zauna bakin gado yace to bisimillah……. Duk suka zaburo.
Bai Sami kansa ba sai uku saura.
Tuni su Anas sunyi barci.
Ya kwanta daga Shi da best Daman akwai wuta ya janyo laptop dinsa yayi connecting da wayar Bilkisu ta nuna mishi option ya shiga *transfer file*…
Gallery din ya shiga, a screen din system din yake kallon pictures din……ba karamin tashin hankali ya shiga ba ganin hotunan ta da yayi ba Wanda ta dauka babu hijab.
Duk duniya ba abinda yake son gani a kullum irin ya kalleta ba tare da hijabi ba.
Tsikar jikinsa sai tashi takeyi yayi ma wani hotonta kuri da ido Yana kallon kirjinta……..hazbunallah ya fada.
Ya zaro ido ganin wani hoton Shi Kuma ba kallabi gashin ya zubo Mata a kafada ya zarce kirjin ta…… Attachment ne ko nata? Ya fada Yana rike Baki……
Wannan yarinyar anya Bata fi karfina ba?
Zumbur yayi ganin ta cikin kanan Kaya riga da wando tana rungume jikin daddyn ta, gefe mommy ce da kannen ta biyu maza. daganin pic din kasan ba Nigeria bane……yayi Mata kuri da ido Yana kallon kugunta….. Ya fadada murmushi *this is Dubai*……. Nawaoooo.
 A hankali yake ingiza hotunan a system din sa.  yarinyar nan gaskiya ta gama haduwa…….kutt!!! Ya Kara rike Baki.
Duk wani hotonta dake cikin wayar sai da yasa a system dinsa.
Ya shiga videos, mafi yawa Indian music ne.
Ya shiga text nan yayi karo da text din Suleiman Yana kyarma ya Buda.
“`Aslm, Dan Allah lecture din yau karfe nawa ne ?“`

Ansa: “`Four“`

Na biyun

“`Bilkisu ya murar? Allah ya Kara lafiya?“`

Ansa:
“`Amin thank“`

Ya buga tsoki…… Dan iska uban chusu….. I hate this idiot.
Ya bincika ba wani sauran text daga na kawayenta Mata sai nasu Daddy da mommy.
Ya tafi dialing calls, mafi yawan Kiran Suleiman shine yake Kira kusan idanun sa Kira biyu ya gani tayi mishi.
Ya Kara doka tsoki.
  Ya Kara komawa message baiga text din da ta mishi na birthday ba.
Ya doka tsoki watan ni ta goge ni ko?
Ya Fara dialing number sa Nan da nan sunansa ya bayyana “`ANWAR“`
Ya saki ajiyar zuciya ya Danna sunan ya bi ta message sai kawai yaga text din ya fito, Nan da nan ya gane ta saka Shi secret conversation ne.
Yayi tsammmmm! To me take nufi da hakan?
Bana son Mata yawan tambayoyi ko don munyi fada tayi hiding?…
Ya kada Kai kawai…..hmm.
Ya hada xender ya tura Mata GB WhatsApp ya Mata installing…..
Ya rubuta Mata a wall status din ta *You can hide what is on your mind not eyes…*
Profile picture din Kuma ya saka Mata hoton Mommy da daddy Wanda suka dauka tare cikin jirgi……
Kiran sallah yaji an Fara ….. Ya zaro ido….yau akwai chakwakiya fa…..ya rufe da sauri, ya kashe wayar ta sannan ya dauko littafi saboda 8 suke da exam.
Rutsum , itama bata runtsa ba, Rabi karatu Rabi tunani.
Shi ya tayar dasu sadeeq sallah.
Daga masallaci Basu Kara ganin sa ba ashe school ya gudu ya boye Yana karatu.
   Babu abinda idanun ta keyi sai zafi. Tana zaune can baya ana shirya su har an Fara raba question paper babu Anwar.
Hankalinta a tashe ga sadeeq ya Mata nisa bare ta tambayeshi.
Tana Shirin mikewa ta dauki excuse ta ari waya ta kirashi ya shigo, Yana ta mazurai Yana Bata rai…… Malamin ya bashi question dinsa da booklet ya ce biyoni….. Sukayi baya.
Yana zuwa dai dai inda take zaune ya sa biro ya zunguri hancin ta malama kalli paper karki sa in Fadi…..ta rasa inda zata sa kanta saboda kunya saboda hatta malaman kowa yaga abinda yayi Kuma Harga Allah ita ba Shi take kallo ba. Tayi sauri ta sunkuyar da Kai bisa table.
Kowa addu’a yakeyi Allah yasa akawo Shi kusa dashi amma malamin nan ya kaishi can karshe last.
Jarabawar tayi zafi, matuka.
Tunda yaga questions din Shima hankalin sa ya tashi yasan sunyi wahala though Shi ba wacce bazai amsa ba.
Bilkisu kawai yake tunani saboda jiya yayi obstructing karatunta.
  Yana rubutu Yana dago Kai. Sai ya hango ta tayi zugummm.
Addu’a kawai yakeyi Mata Allah yasa ta Sami mafita…… Da kyar ta iya amsa tambaya daya *b* part din ma da kame kame ta karasa…… Na shiga uku ta fada.
Na kusa da ita kowa yayi zugummm.
Wadanda ke gaban Anwar suka Fara juyawa Nan ya Fara fada musu kwatsam….. invigilator ya hango su…..hey…..hey….yayo baya.
Come….come…..come….ya nuna Anwar taso daga Nan zonan….
 Ya tashi a hasale Yana jiyawa na kusa da Bilkisu na Mata magana ko ta gane question 2? Ya hangoshi yace Shima ya taso…….saura kadan Anwar ya taka rawa yace Alhamdulillah a hankali…..suka hada ido da sadeeq ya daga mishi gira sadeeq din ya mishi dakuwa kasa kasa……ya danyi dariya. Ya fiddo wurin yace ma Bilkisu matsa ciki ya ce Kai Kuma zauna.
Yana juyawa Anwar din kafin ya zauna ya ajiye Mata booklet dinsa Shi Kuma ya dauki nata sannan ya zauna kawai ya Buda .
Ya Fara karanta shirmen da ta rubuta kawai ya soke ya bude sabon shafi…..
 Tsoro gareta….jikinta ya Fara karkarwa, ta bude tana karantawa…. Ya cika booklet din tabbb…kaiii Anwar *guru* ne wallahi. Ta fada cikin zuciya.
Ya iya bada amsa ga turanci Shi yasa kullum cikin photocopy din C.A din sa akeyi Yan aji.
Tunani kawai takeyi ta Yaya zai karbi tashi ya Bata nata?. Tayi sukutiiiii…….. Chinyere ta hango zata you submitting…… Ya daga kai, idan kin gaji go and submit….. Bata San ta mishi wata uwar harara ba……shin nashin zata bayar amatsayin tata?
Dukewa yayi Yana Yar dariya yaci gaba da rubutu.
Sit biyu ne tsakanin ta da Suleiman tana son daga mishi na Anwar Amma sunyi nisa.
A hankali aka Fara submitting…… invigilator din nan yazo yayi tsayi tagar kusa da su.
Anwar na gamawa kawai ya Mike yaje yayi submitting yayi signing out ya fice…..
Kaiii Anwar karshe ne.
Ta kasa tashi. Har sai da akace time out….stop writing, aka bi ana karba…… Ta saki ajiyar zuciya a hankali sannan ta mike taje tayi signing out.
  Yana can zaune bisa taga….. Ya kura ma kofar fitowar ido. Tare suka jero da Suleiman…. Bilkisu yau Nasha wahala Allah dai ya kyauta….. Bilkisu kinyi duka ko? Naga Anwar aka maido miki…..Helen ta dafa kafadarta.
Tayi murmushi eh.
Suleiman yayi karaf, da kyar na amsa question one *b* da question three *a*.
Sai na tafi question 4 na buga mishi kame kame ya Allah kasa ko *e* mu Samu na gaji da carry over wallahi….ai Bata da dadi ta fada tana Mai jajanta mishi.
Wallahi Suleiman *Anwar* dan rigima ne Wai kasan Shi yamun jarabawa yayi submitting Ni kuwa yaban tashi na bayar?
Ya zaro ido ban gane ba.
Ta bashi labari…yayi dariya yace *Hmmm* kawai.
Yana ta kallonsu…ji yakeyi kamar ya je ya Shakure Shi.
Na Miki Barka wallahi Allah ne ya duba Miki.
Wallahi kuwa Alhamdulillah ai jiya na kwana du’a’i wallahi saboda daman na tabbatar Ina ruwa……. Karaf suka hada ido dashi.
Ya bata rai,….Ina zuwa Bari na karbo wayata wurin Anwar……. Okay sai gobe Nima zanje waje wani ke jirana.
Ya wuce, saboda yasan ba dawowa zatayi ba dan Yanzu.
  Kun gama? Idan baku gama ba kije gashi can zai tafi…..Anya ba kishin Suleiman Anwar keyi ba?
Ta fada a zuciya. Shiru kawai tayi.
Baki da lokaci na?
Ta kalleshi, wallahi duk ka sauya Mani, Yanzu Abu kadan sai ka Fara fada kana sako Suleiman, Yana fada mun yanda yasha wahalar exam ne shine fa ka ganmu……. Bana sonji.
Kina son fada mun cewa kowa baisan Shi din saurayinki bane.?
Zatayi magana ya Mika Mata wayarta, ungo idan daddy ya tambayeki kice wayar ba chargy ta kwana saboda na kasheta b4 ya Kira don’t know what to tell him.
Fishi kayi?, Ta ce ba tare da ta karbi wayar ba.
Akan meye zanyi fushi, Ina abinda ya dameni, na Isa in rabaki da Suleiman ne while Nima albarkacin sa nakeci na…….. *Anwar*….. Ta Kira sunan sa.
Ya kalleta,
Wallahi ka canza, bana Jin dadin abubuwan nan har ga Allah.
Magana takeyi kamar me Shirin yin kuka.
Yayi shiru kawai, 
Amma kayi hakuri idan na bata maka Rai shikenan ko?
Naji karbi wayar ……
Ta danyi murmushi ta Kai hannu.
Kina Sanya attachment?
Da sauri ta kalleshi, ya kura Mata ido….
Ta sunkuyar da Kai Allah ya sawake ban taba ba…… Gashin ki ne haka?
Haka me?…. Daman ka karbi wayar ne don ka man kwakkwafi kazo ka addabeni da tambaya?
Ya bushe da dariya…… Me yasa anan bakya sa ko gyale bare ki kwatanta saka wando mu gani…….. Juyawa tayi ta Fara tafiya, ya dirko da sauri ya bita….Ina zakije?
  Yasha gabanta…. Dan Allah kiyi hakuri na daina.
Hmmm, ta ce.
Na ce na daina ko?
Shikenan, bani wayar.
Tafiya zakiyi?
Eh, tace, 
Suka jera suna tafiya,
gobe ne last paper kuma morning ana fitowa Zan gudu……… Nima gobe Zan tafi. Ta fada mishi.
Haba, Abuja ko sokoto.
Tayi Yar dariya Abuja….. Shikenan na Sami lift har gida ke zanbi ko? Ance Kano kike kawa jirgi Yar gayu ……… Tayi Yar dariya…..inji wane magulmacin.?
Ke fada mun Zaki tafi dani na shirya ko….. Shatar mota zanyi fa ba zuwa akeyi daukana ba……. Shatar mota?
Eh, 
To kawai ki Bari mubi motar gidan su sadeeq idan anzo……Kai nifa bana son rabe rabe….. Ba damuwa nida sadeeq daya ne kada ki damu we are now family.
Shikenan Zan fadawa mommy yanda tace ……. Ya watsa hannu fine.
Ta harareshi Kai wallahi Anwar din Nan ka fiye yanga kamar mace……
Ya tuntsure da dariya a’a kin manta nine Bilkisu.
Barci kawai kowannen su keji. Koda suka suka rabu gado kowa yabi lafiya……….
   Shako wuyansa yayi suka yi bayan daki…..Kai lafiya ….Wai Anwar kana da hankali kuwa?????
Warning Zan maka wallahi tallahi idan kayi kuskure *you are dead* ya mishi nuni da yanda a wuya.
Da Bilkisu zamu tafi gobe na fada Mata Kai zamubi idan ka saki ka nuna Mata inada alaka da tafiyar you are sorry Dan ubanka.
Zan ma Umar waya in mishi bayanin komai…… Kaji ko?
Naji banza….sakarni toh.
Yayi murmushi. Good and fine.
Wace karyar ka shirga Mata?
Ya tabe baki wallahi bance Mata komai ba Kuma nasan bazata tambayeni ba…..
    To kaja ma Umar kunne wallahi……bai da matsala. Kuma wannan karon Shi kadai zaizo ba wani security saboda Kai zaka zauna gaba nida Bilkisu a baya …… Dan ubanka ni oga Kuma a gaba? Eh, Kai zakayi arranging hakan…….mtsew naji.
Cikin kwanciyar hankali tayi wa mommy bayani. Tayi Mata nasiha da addu’a , ganin Bata boye Mata hakan ba, (munafunci ga yaro Shi keda ciwo).
  Umar yasan dakin su, can ya biya aka Sanya musu kayansu kafin ya karaso cikin makarantar.
Suna fitowa ya tareta Yaya?
Ta ce ta shirya.
Haka suka biya ta dauki jakar ta suka wuce.
Sadeeq ne oga ya kame a gaba.
Shida ita baya….. Ya kalleta. Kinga WhatsApp???? Tayi murmushi eh,
Zamu ringa chatting kinji?
Toh, 
Ko Baki da time?
Me zai hana……
Good, ya fada.
Kinyi break?
….tambayo. Ta fada a zuci. A zahiri tace Nasha tea.
Tea?
Umar akwai abinci motar nan?
Eh, yalla……. Yayi saurin datse maganar ya canza da cewa, Yana daga Nan baya…..
Sadeeq ya juyo Kai bana son hauka abincin nawa zaka cinye?
Bilkisu zata ci ko zaka Mata rowa ne……Ni na koshi ma ta fada tana Yar dariya……. Au Bilkisu waa nakeyi I tot koshine keson ci.
Ya yunkura ya dauko cooler sadeeq ya Miko mishi spoons biyu, yabude…..kamshi ya buge motar… Gasassun kaji ne da soyayyen dankali da kwai.
Ya kalleta kici ….
Tayi murmushi…..na gode.
Wani kallo yayi Mata….bakici?
Ta tabe baki Alhamdulillah.
Ya daga kafada, kufa wadannan an Saba haduwa ko? Wurin mu ne sabbin zuwa ya waxgi kaza ya Fara ci.
A hankali a hankali yaci ya koshi tana kallonsa ……..Kai namiji baida kunya ita Ina zata iya Shan ko ruwa a nan?.
Ya Mika ma sadeeq ungo…… Miko mun maltina Mai sanyi gaban ban……Ashe Yar cooler ce ta ruwan sanyi dankare da lemuka …….
Ya kalleta me zai Miko Miki?
Ta girgiza Kai na koshi…… Ke kuwa Dan Allah hajiya Kisha ko Mai sanyin ne…….Kyaleta umar tana tsoron kada mu saka Mata baliyan……. Ta zaro ido….yasha mur…… sadeeq bani maltinar Nima…… Ungo wannan Kisha Ni ta isheni. …..ya Miko mata tasa.   
Kurba biyu tayi da kyar, ya tsareta da ido…..ko kadan baijin kunya ko nauyin kallonta, taci gaba da rikon ta………tana jujjuyawa.
……… Kina tunanin Suleiman ne?…
Wohohoho Kai kuwa a Rana sau nawa kake ambaton Suleiman a rayuwar ka Wai meye ya tsare maka?.
Inba tunanin sa kikeyi ba Kisha…..na koshi ne kaima ka kasa shanyewa bare Ni?
Kuna da Yan uwa a Kano?
Um, um…. Ni ban ma taba zuwa Kano ba sai ta dalilin karatun nan.
Da gaske?
Allah kuwa…..
Kai Dan asalain Kano ne?
Yayi murmushi ciki da bai kuwa…..ya bangan ka da tsagen kanawa ba?
Yayi Yar dariya, daga kaina aka daina gidan mu kinsan nine auta gidan mu muna da yawa….. Ya sunan anguwar ku?.
Keda Baki San Kano ba Ina ruwan ki da sunan anguwar mu kuma?.
Eh, Ina son sani.
Yayi Yar dariya ni ba cikin garin Kano nake ba kauyen Kano karkashin karamar hukumar *Rano* kin San wani gari *Dagama*? 
Nope, ta fada.
Yayi Yar dariya.
Suna shiga Kano ya ce a tsaya ya sauka.
  Ya Dan fita can gefen hanya…..ya Kira Alhaji Mubarak a airport.
Hello an Gama komai?
Ya rusuna, angama Allah Shi taimakeka.
Yawwah.
  Ya shigo motar da sauri, Umar airport muje Airport da sauri please……. Ta kalleshi zakewa????? Shi Dan karo sai instruction yake badawa tun dazun.
  Tun daga bakin gate ake Basu girma. Ko kadan Bata kawo wani Abu a ranta ba.
 Ya tokare bakin kofa zan koma mota, sadeeq sune Yan gari zasu raka ki har ciki……
Toh, na gode sai munyi. Sai Yan waige waige kamar marar gaskiya……zamuyi chat kinji?
Tayi murmushi ba damuwa……. Manyan mutane biyu ta gani sun zube gabansa Allah Shi taimakeka Barka da sauka………
Ya zaro ido ita Kuma tabi fuskar sa da kallo……..✍????????????????

Alawiyya ma na gefe…????

*ZAINAB WOWO* ????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button