NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 19

???? *WA ZAI FURTA?*????
              1⃣9⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

????????????????????  *RUKAYYA DAN BATTA I love you so much, remember this always*????????????.

         ***************
*Federal University dutsinma*

  …….. Bani da wani feelings akan Anwar he always telling me we are just friends….just friends, so Ina tunanin all this is because he likes me as that shine kawai……. Kada ki yaudari zuciyar ki wallahi……. Kada ki rantse Anwar bashi da alkibla. 
Idan Yana Sona let him say it idan Kuma bai *FURTA* ba I cannot waste my time and wait for unknown….. Anwar din ne unknown…yes to me he is.
Abinda na tabbatar wa kaina shine ko naji Ina sonsa bazan taba yarda ya gane ba bare har nace Zan fada mishi..nooo! Bana iya hakan.
 Dai dai sunzo kofar gida, suka sauka Aisha ta biyota da sauri ganin ta yi saurin shigewa……. Amma saboda Allah bakya jin  kin Fara son sa?
Tayi murmushi.
  Um?
Aisha forget about this…. Dan Allah ki amsa ni. Ko kadan bakya jin kina sonsa?…
So!, So!…. Ta maimaita.
  Suka bude daki ta fada bisa katifa….. To Wai ya zanji idan na Fara sonsa?
  Yawan tunanin sa, son ganinsa ko Jin muryar sa, komeye zai yi zakiga baya Baki haushi…. Koda kin fusata zakiji azuciya Baki Jin haushinsa, kishin sa…… Tayi Yar dariya…. Please Aisha fita Kija mun daki barcin nan ya dameni.
  Anya Bilkisu????
Anya meye?
To nidai Kisha oat din kada ki haddasa mun fitina anjima don Anwar sai ke wallahi…. Abeg go.!!
Zan fita but please Kisha…. Zan Sha Yanzu.
   ……….ya dafa kafadar sadeeq, kaji menstrual pain ke damun Bilkisu…. Ka dubi girman Allah kada ka nuna Mata kasan haka zaka Bata kunya Anwar.
   Ya tuntsure da dariya, to me yasa Bata boyewa Dr ba sai …..
 Sai ubanwa? Shi ba Dr bane? Idan bata fada mishi rashin lafiyar ta ba zai San wane magani zai bata ne?…. Ikon Allah, sadeeq akan Bilkisu wata Rana kilan ka dakan ko?
Tabbas, saboda ka takura Mata da yawa fa…… Meye abin takura anan.
Na dai fada ma, wallahi kada ka nuna kasan me ke damunta zata ji babu dadi… Kai nafi so ta Saba da Hali na tun Yanz…. Maganar ta makale da alama yayi *Subul da baka*.
Hahahahahahahaha, finally….. Ya galla mishi harara finally what?
Nothing forget…ya fada Yana dariya.
*Sixtus* ya shigo kunji anyi closing school till further notice?????
Sadeeq ya kalleshi saboda me?
Corona virus…… Anwar yace hazbunallah are you serious?
Of course. Ya fada.
Anwar yayi saurin daukar waya ya Kira academic secretary…. Ya tabbatar mishi….
Ya kalleshi sadeeq is true.
Ya zaro ido Nawaoooo….. ya zanyi da yarinyar nan sadeeq??
Kamar ya?
Sai yayi shiru….. Ya kura mishi ido huh?
Mtsew ya buga tsoki ya fita waje…. Ya bishi da ido Yana murmushi, saboda ya gano inda zancen sa ya dosa.
   Abinda ya tayar mishi da hankali ganin student nata parking ana buga ma wadanda Basu dawo ba akan su yi zamansu…..
Ya Kira number Bilkisu gashi tana ringing Amma Bata dauka ba, saboda barci ta sanyata silent mode da alama ta sami yin barci.
   Aisha ta Kyaleta har kusan karfe shidda ta wuni zungur tana barci… Ko da ta tashi wata azababbiyar yunwa ce ta tashe ta, ga mamakin ta taga Yar cooler kusa da katifar, tana budawa taga kuskus da miyar Dankalin turawa, tayi murmushi Allah sarki Aisha.
Sai da taci nayi nat! Sannan ta shiga wanka ….. Tana cikin saka riga Aisha ta shigo, kin tashi?
Ta fada tana murmushi, ta mayar mata da murmushin ta nuna Mata cooler da Baki tace Kinga alama can….. Sai duk sukayi dariya.
Yunwa ta tasheni, wallahi kin taimaka….. Ai kin shaa barci, Ni kuwa nasan haka na farka naga 23 missed calls….. Tabbb.
Kin kirasu ko?
Mommy kadai na Kira sauran sa nemeni idan ya damesuuu……wayar ta Fara kugi duk suka kalli juna.
Ta nufi wayar, ta Dan kalli Aisha *Anwar* ne…. Tayi Yar dariya Ina zuwa , ta juya tabar dakin….
Assalamu alaikum,
Kin tashi kenann….
Amsa sallama wajibi ne malam….. Wa’alaiki assalam. Sai me Kuma? Tayi Yar dariya, Ina wuni?
Ya kike ya jiki?
Alhamdulillah.
Cikin ya daina ciwo ko kina ji har Yanzu?
Bana ji da sauki sosai.
Zan kawo Miki maganin anjima kinji ko?
Ka bada akawo mun Mana ….. Saboda bakya son ganina?
Ba haka bane.
Haka ne Mana . Ba maganin kadai Zan kawo ba ai Ina son duba jikin ki ne…
Shikenan sai kazo.
Zaki iya dafan indomie din????
Innalillahi kaii Anwar fitina ne wallahi…. Nine fitina Bilkisu.???? 
Ta zaro ido kayi hakuri  wallahi maganar zuci ce ta fito……. Da kyau Ashe a fili kike nunan ba wani abu kina can kina zagina cikin Rai ko?
A’a wallahi….eh Mana. Gashi kin kirani da fitina….Dan Allah kayi hakuri.
Bazanyi ba…. Ya Fara fada kamar da gaske Yana son yaga how much she care about him … Kina da fuska biyu kenan Bilkisu? Watau a fuska kike nuna mun …..Anwar kayi hakuri…. Bazanyi ba nace.
Ba zakayi hakurin ba?
Gabansa ya Fadi ya tuna fadan su na baya….. Yayi saurin cewa zanyi amma ba Yanzu ba .
Sai yaushe?
Sai nazo anjima kin kalleni kin bani hakurin da gaske….. Tayi Yar dariya wannan na karya ne?
Da alama. Ya fada.
Shikenan sai kazo. Ya kake son indomie din?
Ki barshi kawai bana ci.
Dan Allah kayi hakuri….. Na ce ban hakura ba?
To ka fada mun yanda kake son indomie din kasan kowa da yanda yake son dahuwar indomie…..kiyi mun yarda ki ke dafawa idan zakici… Karfe nawa zaka zo?
Eight, ya fada Yana Yar dariya ko nayi latti?
Ta Dan harari wayar kamar Yana kallonta kawai tayi shiru..
  Kinyi shiru kina ta Duran zagi a zuciya ko?….. Kaiii Anwar.
Eh Mana.
A’a wallahi. 
To fadan da kikayi shiru me zuciyarki ta saka Miki?
Ta kyalkyace da dariya kaiii nikam na bani ….. Yayi murmushi.
Ke Kam kin bani zuciyar ta saka Miki?
Ta zaro ido… A’a.
To fadan me ta ayyano Miki.?
Cewa tayi eight din is okay….. Yayi Yar dariya are you sure???
Yes. Ta fada tana ci gaba da murmushi.
Shikenan sai nazo. Kin hada kayanki ko?
Sai anjima.
Ya zaro ido kinji labarin Coronan ne?
Eh, mommy ta fada mun da mukayi waya.
Yaushe Zaki tafi?
To gani dai…. Ban gane gaki dai ba.
Ka bari idan kazo anjima zamuyi magana…. Shikenan sai nazo.
  Ashe yayi waya yace a kawo mishi mota da maganin. Ko da aka kawo sai driver ya juya gata haya yabar musu motar.
   Katuwar mota kirar Jeep Amma Honda baka, Kai da kaga motar kasan lallai Mai ita *Don* ne.
  Ta Sami Aisha daki, sai na jiki shiru.
Eh, wallahi Ina parking ne.
To Wai strike din ne ko Corona?
Duka fa, Anwar ya fada Miki?
Mommy, Ina tashi naga ta kira nabi Kiran,shine take fada mun, kema gobe Zaki wuce?
In shaa Allah, sai gida….Kare yasha taba. Duk suka bushe da dariya.
Ke sai jibi ko goben zaku wuce?…… Har na ma driver waya gobe in shaa Allah na fada mishi ana gama sallar asubah zamu bar garin nan six da izinin Allah….. Anwar din fa, ba dashi zaku tafi this Time ba????
Noooo, bama zai sani ba….. Gaskiya bazai ji dadi ba….kada Allah yasa yaji so what?
Ta kura Mata ido, wannan Jan ajin naki fa ya Fara yawa ki zauna idan zaren ya tsinke zakiyi wa kanki.
   Tayi murmushi, sai dai ya tsinke Amma ko Zan rasa Anwar bazan taba binsa kamar rakumi da akala…… Yanzu me Zaki fada mishi? Ko kunyi maganar?
Bamuyi ba, sai anjima ya ce zaizo kawai Zan nuna mishi banyi deciding ba…. Bilkisu….
Aisha please mubar maganar Nan.
  Dan Allah idan ya kawo Miki maganin ki dibar mun saboda Hafsa ( kanwarta ) ita ma the same problem with you.
In shaa Allah…..ohhh Wai carton, komai Shi sai yayi hauka….. Ba hauka bane kulawa ce.
Gasu mufeeda can time dinsa kawai suke so Amma sun kasa samu….. Haka ne .
Ai shu’umi ne wallahi. Nake ga kamar duk abun Nan Yana Axergurating ne don ya Sami sauki Yan mata…. Yanayi bil hakki da gaskiya.
Ko?
Allah kuwa.
Ta ce hmmm. Kawai.
Suleiman ya kirata, da sauri ta daga hello, Suleiman Ina wuni.
Bilkisu ya karfin jiki?
Na zo dazun har Kun fita da Anwar halan asibiti kuka je.
Eh wallahi. Jikin ma Alhamdulillah.
Mashaa Allah, sai Kika ji Kuma hutu ko?
Bari Kai dai.
Wallahi naji haushi da na Kara jinkirtawa Kinga da ban wahala a banza ba.
Ai kuwa. Ta fada.
Shikenan Allah ya say ya zamo alkhairi garemu duka ya kawo Mana karshen wannan fitina.
Amin ya Allah.
Sai nazo Allah ya Kara lafuya…..ta ce Ai…. Amma tuni ya latse Kiran Sam bai ji cewar zatayi wata magana ba.
Ta kalli Aisha naji Yana sai yazo kada yazo gobe na tafi ko in Kuma kiransa Kinga babu dadi.
Kyaleshi goben sai ki Kira. Yanzu kada ya zargi wani abu kin San maza….. Eh Kuma fa. Ta fada.
   Ta dafa mishi indomie da kifin gwangwani, ta Sanya tarugu da albasa Mai lawashi sai kuwa spices dinta.
  Tayi masifar dadi sai kamshi ke tashi….. Kafin ta sauke ya kirata.
Ta dauka hello…
Ina waje. Yana fadin haka ya kashe.
Gabanta ya Fadi,jikinta ya Dan dauki rawa, ( Wai me yasa Yanzu ko waya sukeyi takejin wannan yanayin? ).
Doguwar Riga ce jikinta blue, tana da duwatsu yayyabe jikinta.
Ta dauko hijab maroon har kasa ta saka, ko kwalliya batayi ba turaren da ya siyo Mata ne ta fesa kawai ta juye indomie a plate ta rufe ta dauki robar ruwa da maltina ta fita.
Yana hangota da Kaya ya fito daga motar….. Gabanta ya Fadi. Anwar a irin motar uncle? ( Wani kanin mommy ne Mai masifar kudi ) wurin Shi suka Fara ganin motar Shi bama Nigeria yake zaune ba Soja ne a America.
  ……. Ya karbi plate din Yana Yar dariya, kawo na taimaka Miki.
Ya shiga motar ya zauna wurin Mai tuki ita Kuma tana tsaye ta rike murfin kofar tana son ya karbi ruwan da maltina.
Ya Dan kalleta zagayo Mana ki zauna….um um Nan ma ya Isa.
Ya Kara kafa Mata ido , sai Kuma yaki cewa komai ya Mika hannu ya karbi ruwan.
Zaman kujera yayi ya sako kafafunsa waje duka biyun Yan facing dinta. Ta Dan ja baya ,yayi kamar bai lura ba .
  Riga round neck navy blue ya saka da jeans dark blue. Kansa yau ba hula, ya kwantar da gashin sa inda ya bada kusurwa kusurwa ( waves ).
Yayi kyau matuka.
Ya bude plate din sama, kamshi ya daki hancin sa ya Dan lumshe ido waww…. Daga ji zatayi dadi fa.
Tayi murmushi kawai.
Ina folk din ko hannu Zan saka????
Ta Dan bude idanu innalillahi…Bari na dauko na manta….. Ta juya da sauri.
Kinga dawo ga wani Nan …
Ya fada .
Ta dawo ya gyara fuska alamar seriousness yace duba aljihun kujera a baya akwai spoons dauko mun ciki.
Ba gardama ta ce toh…. Ta bude ta shiga lalube takeyi sosai tun kafar ta na waje har ta shiga motar ciki tana tura hannu kawai taji kofa ta rufe wani Abu yayi Kara Nan da Nan ta gane locking yayi.
Ta dago Kai da sauri sai taga Yana ta cin indomie din a hankali….. Au dama da spoon dinka a aljihu kana son na shigo motar ne…… Kina baya Ina gaba hakan ai ba matsala bane unless Zaki takura na dawo bayan….. Karka dawo ta fada da sauri.
Motar ta dau sanyi da wani da dadden kamshi….. Kamshin ya Mata dadi Amma hankalin ta duk ba a kwance yake ba.
…….. Amma indomie din nan tamun dadi kin ci?
Eh, ta fada da sauri.
Kice wallahi na ci…. Ba sai na rantse ba.
To idan ma bakici ba nidai na cinye tas!
Ta ce hmm.
Ya bude maltinar ya kafa Kai…. Yana shanyewa ya kalleta kina da fridge ne?
A’a.
Yanaji da sanyi ko siyo mun kikayi?
Ina ruwanka Kai dai kasha maltina.
Ya kyalkyace da dariya. Wallahi ke Bilkisun nan kin iya gwasale mutum….. Ta harareshi kawai.
Ya dafa kujerar say ta baya ya juyo sosai Yana kallonta….. Dan Allah in dawo Nan….a’a wallahi ta fada da sauri. Yayi murmushi shikenan.
Yanzu yaushe Zamu tafi gida?
Kai da wa?
Da ke!
Tayi murmushi, tare muka zo?
A’a Amma tare zamu koma.
Shikenan mu jira gobe muga abinda Hali ya bada ko?
Ya rungumi kujera okay as you wish…
Ya Miko Mata ballin magani ungo Kisha ga ragowar can a boot ance kullum daya zakisha har kwana hudu.
Sannan every month da kin Fara expecting Zaki Sha sau biyu a Rana safe da yamma har ki ganshi …… Ta mishi banza.
Kin fahimta. Eh. Ta ce a kagare.
Ya sumke dariya ganin tana ta faman kasa da Kai.
…..Wayarta tayi Kara, Suleiman ne. Ta Dan zaro ido a hankali ta daga tare da kangawa a kunne yayi fit! Ya fizge. *Suleiman eco* yaga an Sanya.
  Nan da Nan annurin fuskarsa ya bace ya sa handsfree hello kana magana da Anwar….. Kawai sai Suleiman din ya latse wayar…… Ya kalleta kutumar uba ni zaima hanging phone??? 
Ta mishi banza. 
Ya daka Mata tsawa meke tsakanin ki da Dan iskan yaron nan?
Akan me zaka Kira Shi Dan iska???
Ya zaro ido.
What?
Ai kaji abinda nace. Kai ya Kira? Akan meye zaka dauki wayar da ba taka…… Ya wurga Mata wayar ta daki kirjin ta yace get out of my car…..
Ta dago da sauri ta kalleshi … Ke kurma ce? I said get out ya Kara daka Mata tsawa……✍????✍????✍????✍????

Ayi hakuri da kadan yau ban zauna ba wlh
*Zainab wowo ce*????*ALAWIYYA NASIR MY FAVORITE THANK YOU SO MUCH TAWAJENA*????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button