NOVELSUncategorized

DIYAM 46

DIYAM Chapter 45
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
New Saghir

Jin yayi shiru kuma bai fita ba yasa na bude idona, na
ganshi still a tsaye yana kallona, muna hada ido yace “me
nayi miki me zafi haka Diyam? Still akan wannan dan

iskan yaron ne ko? Saboda kina sonsa ne yasa kika tsane
ni irin haka ko?” Na yaye abin rufar nace “don’t bring
Sadauki into this, babu ruwan Sadauki da tsakanin mu”
yace “saboda an miki auren dole ne dani? It that it? Nima
in kika tuna ba son auren nake yi ba lokacin da aka yishi”
na girgiza kaina nace “ba dan an tilasta min aurenka bane
ba Saghir. Su kansu wadanda suka tilasta min auren naka
Inna da Alhaji ai ban rike su a zuciyata ba, babu komai a
yanzu tsakanin mu sai kyautatawa da tausayi” yace “ni
kuma fa Diyam? Menene nawa a ciki? Nasan ba kya sona
but me yasa ba zaki bani dama ba?”
Na mike tsaye ina jin zuciyata tana karyewa nace
“you……raped……me” sai jikinsa yayi sanyi, nace “in ka
manta da dakin nan yana magana zai tuna maka, na nuna
gado na nace “here, anan ka dasa irin kiyayyar ka a
zuciyata. I was only 14 years then, ranar baffana
kwanansa 47 a kasa and you raped me”.
Hawayene kawai suke bin fuskata, ya diririce “Diyam na
baki hakuri ai, I was drunk, I wasn’t…..” Nace “shine
excuse dinka? Giya ce excuse dinka? Bayan kuma har yau
shanta kake yi? How can you raped me and then expect
me to enjoy sexual relationships da kai? Tun ranar gini ai
tun ranar zane. Ka dasa tsiron ƙinka a raina sannan kazo
ka zuba masa taki when you killed my babies” sai kuka ya
kwace min “you killed my babies and you left me to die a
asibiti”.
Sai ya taho da sauri ya jawo ni ya rungume ni, na fara ture
shi amma yaki sakina har na hakura nayi ta kuka na a
jikinsa. Yayi kissing forehead dina yace “Diyam ba zan iya
dawo da baya ba, amma nayi alkawarin gyara gaba. Kome
kike so zan yi miki Diyam in dai zan goge baya, banda
saki because I can’t. I love you”.
Knocking kofa akayi “Darling?” Fauziyya ta fada daga
waje, na ture shi na hau kan gado na lulluba har kaina. Ina
jinsa ya hawo yayi kissing Subay’a sannan ya fita gun
darling din tasa.
Da safe tun dan tashi da assuba ban koma ba, fuskata
duk ta kumbura tayi min nauyi saboda kukan da nasha jiya
da dare na tausayin kaina da rayuwata. Yaushe zanji dadin
aure ne ni? Na gabatar da adduoi na kamar kullum, ina
rokon Allah ya bani ikon cin wannan jarabawar da nake
ciki ta auren Saghir, idan har zama da Saghir shine mafi
alkhairi abu a rayuwata Allah ya rage min kiyayyar sa daga
zuciyata. Sannan kuma nayi addu’ar Allah ya bamu zaman
lafiya da amarya. Dalilin da yasa na yarda da auren Saghir
shine, ina ganin yin auren nasa wata hanya ce ta rage wa
ksina tarin zunubin da nake dauka na gudunsa da nake yi,
at least in da wata matar nasan wannan responsibility din
ya ragu daga kaina.
Ina gamawa na sauka kitchen na fara fere dankali, sai ga
murja nan ta shigo mu ka gaisa ta dauka ta fara tayani
muna hirar mu, har muka gama na fara soyawa ita kuma
tana soya kwai sai ga Saghir nan ya shigo, har yayi wanka
yayi kwalliya, murja ta gaishe shi ta fita sai ya jawo stool
ya zauna yana kallona “barka da assuba” nace ina kallon
sa, yayi murmushi “good morning. Ina jin yunwa a bani
abinci” nace “wai da so nake in hada muku kai da Fa’iza
sai akai muku sama” yace “Fauziyya ba Fa’iza ba” na dafe
kai “sorry. Fauziyya” ya girgiza kai “bacci take, ni kuma
yinwa nake ji. Zubo min inci anan kawai” na zuba masa a
plate na dora fork na mika masa, ya karba yace “naga
Subay’a yau bacci take tayi” na hado masa tea na kawo
masa na koma na cigaba da aikina shi kuma yana ci. Sai
daya gama ya mike yazo bayana ya rungume ni yana
shanshana gashina yace “am sorry Diyam kinji? I promise
insha Allah zan saka ki murmushi more than yadda na
saka ki kuka” ya juyo dani yace “da ace ina da dama da
sai na bude nan” ya dora hannunsa a kirjina “na saka
soyayya ta a ciki na rufe da kwado” na ture hannunsa
ganin yana neman wuce gona da iri nace “stop it. Amarya
tana sama tana jiranka” sai yayi murmushi kawai yace
“zan fita. Sai na dawo”.
Tare da murja muka gama aiyukan mu kamar kullum,
sannan naje nayi wanka nayi wa Subay’a muka sauko
muka fara cin abinci sai ga amarya ta sauko. Tana ta wani
yayyatsina fuska, sai kawai na tsaya ina kallonta. Babu
makeup din jiya, wannan ya sake fito da kamanninta
sosai, sai nayi realizing ai na santa ma, tana daya daga
cikin matan da suke zuwa har gida neman Saghir shi kuma
yana ce min abokan aikin sa ne. Tazo ta zauna murja ta
gaishe ta sai naga tana kallona irin kamar tana jira in
gaisheta din nan tunda tana ganin ta girme ni. Nace
“Subay’a ki gaishe da auntyn ki. Fa’iza ga Subay’a, koda
yake nasan kin santa ma ai tun sanda kike zuwa” sai ta
bini da kallo kawai. Na tashi na barta a dining nace “ga
abinci nan Bismillah”
Na koma sama ina mamakin wannan rayuwar. Ni in nice
Saghir ya zanyi in auri saura na, ai sabuwa zanso wadda
ban taba testing ba, no wonder yazo yana shashshafa ni
da sassafe.
Rayuwa ta cigaba da tafiya, har Fauziyya tayi sati a gidan.
A ranar ne kuma Saghir ya tubure. “Babu wata shekara,
ban yarda na. Eh an baku dama kuyi kyautar kwana amma
sai da amincewar mijin ni kuma nace ban amince ba” na
daga gira ina kallonsa a raina ina cewa ‘zakayi saki reshe
kama ganye kuwa’ a dole na na hakura na karbi kwana na.
Dokin da yake sai daya sa naji tausayin Fauziyya. Ni kuma
kamar an saukar min da bacin rai haka naji nayi zamana a
dakina amma sai gashi ya taho. Ina game a waya ya karba
ya ajiye yace “me kike so inyi miki ne Diyam? Kuka zanyi
ne ko tsallen kwado?” Na juya masa baya nace “duk
wanda ranka yafi so” sai ya hawo gadon ya fara yi min
tausa. Yace “da gaske fa nake. Say it, anything, yanzu zaki
ga anyi miki” na tashi na zauna yace “kudi kike so?” Sai ya
dauko bandir din 500 notes ya ajiye min akan cinyata yace
“ki shirya gobe in kaiki shopping ki sayi kayayyakin ku na
mata, kayan kwalliya, jaka, takalmi anything” na mayar
masa da kudin sa nace “ka sayi kayan abinci ka kai gidan
Alhaji” ya dawo min da kudin yace “angama. Can we
please go to my room? Kinga Subay’a tana nan”.
Washegari kuwa ya fita dani, yayi ta lodo min kaya komai
ya gani na mata sai ya dauka, “wannan zaiyi miki kyau,
wannan ma yana da kyau, wannan zai dace dake” haka
dai yayi ta fama. Muna dawowa gida muka tarar babu
abinci, bata yi ba tunda girkina ne dan haka na shiga
kitchen na dora da yake weekend ne Subay’a tana sama
tare da Saghir suna kallo. Riga da wando ne a jikina kaina
babu dankwali na daga gashina sama ina ta aiki na ina jin
kida a waya ta sai naji kawai wani strange kamshi da ban
sani ba, ina juyo wa sai naga wani mutum a tsaye a palo
yana kallona muna hada ido sai cewa yayi “Fauziyya tana
nan?” Ni kuwa na zunduma ihu ina kiran Saghir, sai kuwa
gashi nan a guje ya sauko kafin mutumin ya fita. Ya
damko shi yana tambayarsa lfy sai cewa yayi wai shi gurin
Fauziyya yazo shi dan uwanta ne kuma ita tace mishi ya
shigo. Ranar naga bala’i a gurin Saghir, daga Fauziyyan har
bakon nata ya haɗa ya balbale su da fada daga baya ma
ya haɗa har da maigadi wanda yayi ta faman rantsuwa a
kan cewa shi bai san mutumin ya shigo ba. Ni dai na
dauki yata muka koma sama nace ku kare kalau.
Sai da daddare kuma Saghir yayi ta bani hakuri. Nace “duk
wanda ya sayi rariya dama ai yasan zata zubar da ruwa.
Tun da har ka auri yarinyar daka gama nema a waje ai
kasan dole zata kawo maka maxa gida kaima. Duk abinda
kayi ai kaima dole za’ayi maka. Haka rayuwa take” ya
fahimci magana nake fada masa sai yace “kin san ai
dalilin da yasa nayi auren nan ko? So nake kike kula dani
yadda ya kamata sai nayi tunanin idan nayi aure kika ga
wata tana kula dani kema zaki koya. Wannan shi yasa na
auri Fauziyya saboda bana son in auri wata wadda itama
bata iya din ba” a raina nace “oh, ita wannan ta iya din
kenan”
Rayuwa ta cigaba da tafiya. Saghir har mamaki yake bani
yadda yake yi min, gabadayansa ya chanja kuma duk
abinda nace to kuwa zaiyi shi sai dai in bance din ba. Na
saka shi ya ke kai kayan abinci gidan su, sannan kuma na
daina jin warin giya a tare dashi duk da ban tabbatar ko ya
daina sha ba. Fauziyya bata da problem, tana dai da daga
kai da nuna irin ta fini dinnan amma tunda ta fahimci
yadda Saghir yake ji dani sai ta ja baya. Bamu fiya zama
muyi hira ba kowa harkar gabansa yake yi. In ranar girkin
tane tayi ta iyayi da rawar kai ni kuma in ranar girkina ne
Saghir yayi ta rawar kafa, duk da dai ba koda yaushe yake
samun abinda yake so din ba dan wani lokacin rufe kofa
ta nake in kashe waya, watarana kuma in naje in bata rai
har sai ya hakura ya rabu dani. A lokacin ne kuma bikin
Rumaisa ya tashi, za’a hada ayi tare dana yaya Mukhtar.
Lokacin muna 22 years, tana kuma final year dinta a
jami’a.
Bikin yana matsowa na tambayi Saghir sati biyu. Ya rike
baki “sati biyu kuma Diyam? Kwana nawa za’ayi ana bikin
da har zakiyi sati biyu?” Nace “nice fa babbar kawar
amarya. In ina nan ta yaya zanyi shirye shirye?” Babu
yadda zaiyi yace “shikenan” amma ina kira Mama na gaya
mata zan taho tace “baki da hankali dama? Babu wani
sati biyu da zaki zo kiyi, sati daya zakiyi shima kuma dan
kina da abokiyar zama ne da ba zan barki ki taho ki barshi
shi kadai ba” ranar har kuka nayi, I just needed a break
from the house and from Saghir.
Sai satin bikin sannan Saghir ya kaini gidan Mama. Ya
kuma buga min warning “saura kuma ki shiga cikin
yammata kuyi ta shiririta. Kinsan dai ke mai aure ce ko?”
Nace “uhm” a raina ina mamakin wai yau Saghir ne yake
kishi na. Ko yaushe zan fara nasa ni?
Munsha bikin mu lafiya mun gama lafiya. Da muka je
dinner naga yadda Rumaisa take nishadi da mijinta sai naji
wani longing a zuciyata. I missed all this, ni banyi
yammatanci ba kuma babu abinda zan adar na bikina.
Ranar Lahadi muka kai amarya dakin ta. Litinin kuma na
biyo su Inna muka dawo gida tunda satin da aka bani bai
kare ba sai nan da kwana biyu. Muna zuwa naji Maman
Iman tana soya wainar fulawa sai na aika Asma’u ta karbo
min na zauna ina ci.
Ina tsaka da ci sai kawai jin sallamar Sadauki mukayi wai
ashe duk mondays yake zuwa ya gaishe da Inna. Na
sunkuyar da kaina ina jin wainar ta fita daga raina har ya
shigo ya gaishe da Inna da Mama sannan na dago na
gaishe shi. Ya amsa yace “ya family?” Sai na kasa reply.
Ya mike zai tafi Mama tace “oh Sadauki kaki aure har
yanzu? Ko so kake ayi maka kidan tuzuru ne?” Ta tsaya
yana shafa kansa, muka hada ido yace “an kusa ai mama
insha Allah” Inna tace “alhamdulillah, ai gwara ayi din,
aure ai shine cikar kamala da kimar mutum. An sami
matar kenan” yace “eh, a can gida ne. A Maiduguri ne” sai
naji wainar dana ci duk ta tattaro ta dawo makogwaro na,
da sauri na mike na shiga toilet sai da na amayo duk
wainar da naci.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button