NOVELSUncategorized

DIYAM 47

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Seven : The Messages

Sai dana gama sannan na zauna akan toilet seat na dafe kaina, ina jin jiri yana juyani duk da cewa a zaunE nake. Nayi iyakacin kokari na gurin ganin cewa ban yi tunanin maganar da Sadauki ya fada a palo ba sannan na mike na wanke bakina da fuskata na fita, ina tunanin ya riga ya tafi
amma ina fita sai na ganshi a tsaye yana kallona yace “ba kya jin dadi ashe? Allah ya sawake” na sunkuyar da kaina ciki ciki nace “ameen” sannan na wuce shi zan shiga cikin daki Inna tace “ba kiji Sadauki yana miki sannu ba? Shine kika wuce ba zaki amsa shi ba?” Na juyo nace “Inna nace masa ameen, ameen, ameen summa ameen,me kuma yake so ince masa” sai kawai yayi murmushi ya juya ya fita, inna kuma ta rufe ni da fada Mama tana taya ta, na zauna kawai nayi tagumi da hannu bibbiyu ina jinsu har suka gama sannan na zame na kwanta a gurin ina jin jikina kamar mai zazzaɓi har Mama tayi mana sallama ta tafi. 

Kwana biyun haka na kare su babu lafiya sosai, na so inki komawa saboda bana jin dadi amma Inna ta matsa Saghir ma kuma yace in ma zan zauna sai dai ya dauki Subay’a saboda makaranta ni kuma bana jin zan iya barin ta tare da Fauziyya dan nasan ba kunya ce ta ishe ta ba. Dan haka dole na shirya Saghir yazo muka tafi. A hanya ya kalleni yace “kin kara kiba, baki da lafiya amma kinyi kiba kin kara fari. What’s the secret?” Na bata rai nace “what secret kuma?” Yayi murmushi “wai cewa nayi ko Subay’a ce zata yi kani? It is about time, tayi girma da yawa” na juya kai ina kallon titi” I missed my period wannan watan, a lokacin bikin nan ya kamata inyi kuma banyi ba but that doesn’t mean anything tunda dama ina missing sometimes. Ina ganinsa yayi packing a bakery suka shiga shida Subay’a suka lodo kayan ciye ciye sannan muka tafi. 

A toilet da zan shiga wanka na tsaya ina kallon kaina a mirror, da gaske nayi girma na ciko ta koina musamman hips, abinda da bani dasu sai yanzu suke zuwa kuma. A raina nace “sai yanzu makerin budurci ya tuna dani” after I lost mine long time ago.

Na fito daga wanka kenan ina shiryawa text ya shigo wayata. Na daga sai naga number din Sadauki, a raina nace “really? Ko dai batan kai yayi?” Sai kawai na ajiye wayar nayi shiryawa ta. Saghir ya shigo da magunguna a leda ya bani yana taba wuyana yace “gobe asibiti ya kamata muje in zazzabin nan bai tafi ba, test nake so ayi miki ma dan ni jikina yana bani ciki ne” nace “no fa ba wani ciki” amma a raina sai naji ina son ma ace cikin ne, I was really in need of love, kuma ina ganin haihuwa zata taimaka min sosai” na kwanta na dauki wayata yace “za’a fara karatun ko? Bana hana ba?” Nace “to me zanyi? Babu wani abin yi sai dai mutum yayi bacci ya tashi ya gyara gida yayi girki ya kuma komawa tayi bacci” ya danyi shiru yana kallona kamar mai tunani sai yace “kina son komawa school?” Nayi saurin kallonsa, ban taba tambaya ba saboda banyi tunanin zai bari ba amma raina yana so, ina son in zama abinda baffana ya ke kwadayi, nace “da gaske?” Ya daga kafada yace “why not? In dai zai faranta miki that’s what I will do” sai na kama tsalle ina murna shi kuma yana dariya sannan ya jawo ni yace “so? Me zaki karanta?” Nayi shiru ina tunani. Na tuna wani visiting da Sadauk yaje min school shida wani abokinsa and we talked about carrier, a lokaci nace musu bani da choice sai Sadauki yace later in life zan fahimci role din daya kamata inyi playing a rayuwa, but yet still, bani da choice a raina. 

Nace “me kake ganin ya kamata?” Yace “anything. Nasan ku mata da son harkar health, zaki iya yin nursing ko midwifery. In ma kuma medicine din kike so sai inyi wa Mr Abatcha magana ya hada ni da wani a samo miki admission” na ture shi ina jin raina ya baci nace “forget Mr Abatcha din nan” yace “why? Shi ya bani wannan shawarar ma fa, ya tambaye ni kina makaranta nace a’a sai yace ya kamata in saka ki. Kinga ai he will be willing to help” na girgiza kaina nace “na fasa karatun” sai kawai ya tsaya yana kallona da mamaki.

Sai da zan kwanta na bude message din Sadauki “ya jikin? Allah ya kara afuwa ameen” nayi tsaki na ajiye wayar na kwanta, sai kuma na tashi na sake karantawa sai kawai na kashe wayar na jawo drawer na saka ta nayi kwanciya ta.

Da safe muna breakfast gabaki dayan mu har Fauziyya, ya ajiye ledar drugs din daya siyo min jiya yace “kina gama cin abinci zaki sha magani, dan naga ashe jiya baki sha ba kwata kwata” nace ” in tambaye ka mana Please” ya ajiye spoon din hannunsa yace “ina jin ki” nace “ya sunan ogan ku na office” ya bata rai yace “Mr Abatcha mana” na girgiza kai nace “sunan shi na gaskiya nake nufi. Like sunan da yake rubuta wa in an bukaci sunansa” ya danyi tunani yace “Engineer Aliyu Umar Abatcha” na gyada kai nace “ohh okay” yace “me yasa kika tambaya?” Nace “a bikin nan ne naji ana zancen wani, I tot shine ashe bashi bane ba” yayi murmushi ya fara praising Mr Abatcha “yana da kirki sosai, na girme shi amma mi gaskiya he is my role model. He is very smart and intelligent. Kuma yana sona. Kunga yadda yake korar mutane kuwa duk wanda yaga wasa yake yi ba aiki ba yanzu zai tura maka quiry amma ni ko sau daya bai taba bani ba. Diyam kin tuna sanda ya tura ni Germany? Sai da naje na fahimci ya tura ni ne kawai dan in huta ashe already ya riga yayi sighing contract din. Sai dan workshop dana ringa zuwa kawai” na girgiza kaina a raina nace ‘ya tura ka ne dan ya samu damar zuba kaji a gidan ku’.

Munje asibiti anyi min pt and it came back positive. Sai naji dadi, maybe wannan haihuwar ta zamo min silar gyaruwar lamura na. Saghir kam doki har a gaban Fauziyya, ya bawa Subay’a labarin zata yi sister ko brother ita ma tayi ta murna. And yana fita sai gashi da sabuwar waya, yace “wannan tsohuwar wayar taki dai ya kamata ki ajiye ta haka” na karba nayi masa godiya sai kuma ya tambaye ni in akwai abinda nake so. Na zauna kusa dashi nace “so nake kayi wa su Murja aure” ya bata rai, nace “Please, auren suke so wallahi kuma Alhaji bashi da halin yi musu to waye zaiyi musu in ba kai ba? Su ba karatu ba, su ba aure ba me kake tunanin xasu yi?” Yana kallona yace “sai in kinyi min alkawarin kema zaki koma school” nace “sai in kayi min alkawarin zaka daina shan giya” ya daga kafada “na daina fa” na tsare shi da ido sai yace “na kusa dainawa. Seriously na kwana biyu rabo na da ita” nace “mata fa?” Yace “na daina wannan tunda na kara aure ai” sai kuma ya jawo ni yace “tell me, kishi kike yi?” Nace “Saghir ko bana sonka, kai mijina ne, kuma uban yayana, ba zan so kuma yayana su tashi suga babansu da wadannan halayyar ba”. Yayi murmushi yace “am getting there”.

And two days after that. Ina ta aiyukan gyaran gidana, da yake ni ban damu ba ko aikina ne ko na Fauziyya ni in dai na tashi zan gyara gida saboda bana son kazanta, it irritates me, ina mopping kasa Saghir ya leko ta stairs yace min “ina tsohuwar wayar kine? Naga har yau baki kunna sabuwar ba” nace “tana bedside drawer ta” na cigaba da aikina. 

Na gama naje na wanke mop, na dawo ina saka turaren wuta Fauziyya ta sauko ta kunna tv ta kwanta tana kallo. Sai Saghir ya sauko da wayata a hannunsa, I looked at his face and I felt something knot in my stomach. Ya nuna min wayar “waye wannan?” Fauziyya ta mike zaune tana kallon mu. Message na gani a jikin wayar “ya jikin? Allah ya kara afuwa ameen” na girgiza kaina nace “duba ni ake yi, what’s there?” Sai yayi scrolling sama, tun message din farko. 

“Third option. Kazo a baka hakurin da kake so” 
“tomorrow evening. Gidan Baffa”
“ina yiwa Asma’u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka” 
“You are welcome”.

Na daga kafada, ni banga abin tayar da hankali a cikin maganganun mu ba. Ya sake cewa “waye wannan Diyam? Sadauki ne ko? Amana ta kike ci ko Diyam? Wato abinda yasa kike guduna saboda kina samu a wani wajen ko? I always tot, yarinyar nan sai kace dutse, ashe kina da tap din da kike karbar rabonki a gurinsa”.

Na zaro ido “wanne irin magana kake yi? How can You even accuse me of that. Menene a cikin messages din nan da zasu saka har ka fadi haka? Yes, munyi magana sanda suke case da Alhaji Babba kuma yayi wa Asma’u kyauta na yi mata godiya. Menene a ciki?” Yace “to uban wanene ya gaya masa baki da lafiya har yake duba ki?” Nace “a gida ya same ni yaje gaida Inna yaga bani da lafiya. I don’t even know me yasa nake defending kaina. Dan kana yin abu sai ka dauka kowa ma yi yake yi?”.

A girgiza kai idonsa jawur yace “am going to trace him. Am going to enter his number into my phone and call him. In na gano inda yake kuma wallahi sai na daure shi. Sai yasan matata ya taba” ya juya da sauri zai koma sama sai nayi saurin rike rigarsa “Saghir ka tsaya ka saurare ni. Wallahi ba abinda kake tunani bane ba” ya juyo a fusace ya sauke min mari a fuskata, kafin inyi wani abu ya sake sauke min wani a same side. Na rine fuskata ina jin jini yana bin hancina, ganina yayi dusu dusu. Amma still na rike rigarsa i a girgiza masa kaina, ta gefen idona na hango Fauziyya tana dariya, sai ya warce rigarsa ya hankada ni da karfi na fadi, unluckily sai cikina ya bugu da kafar bene, na mirgina gefe ina rike marata da hannun bibbiyu shi kuma yayi sama da sauri ba tare daya kalli inda nake ba.

Na sake kokarin mikewa amma marata ta rike kam sai da kyar na daddafa stairs na mike, tunani na daya shine in Saghir yayi dialing number din Sadauki a wayarsa zaiga Mr Abatcha. And that can destroy Sadauki’s reputation a gurin aikinsa. Na juya na kalli Fauziyya da take zaune tana kallo na da murmushi a fuskarta nace “get up from my chair. Munafuka” 

Sai na kama bene ina tafiya a hankali nabi Saghir a baya. Ina hawa sama yana fitowa daga dakinsa hannayensa da waya ta da kuma tashi. Nace “ka saurare ni Saghir” bai ce komai ba ya fara daddanna wayar sa. A lokacin mara ta tayi wata irin murdawar da sai da na kai kan guiwowina na runtse idona, sai ji nayi yace 

“Mr Abatcha? Menene hadin Sadauki da Mr Abatcha?”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button