NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 21

???? *WA ZAI FURTA?*????
              2⃣1⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

????????????????????  *RUKAYYA BAKO DAN  BATTA I love you so much, remember this always*????????????.

    
        **************
*ABUJA NIGERIA*

 Ya kyalkyace da dariya, ya kalli sadeeq she was shocked….. Ai dole ta razana wannan babban surprise ne. Ya Kara dariya.
Yeah I like surprise

 …… Da gaske Anwar ne mommy????
 Tayi Yar dariya shina halan bai hwada Miki zai zo ba?
Bai hwada min ba mommy muje ki raka Ni….. Walla Baki da hankali ni Zan kaiki inda Anwar?
Ta Fara dire diren shagwaba.
  Walla bani rakaki keji min ja’ira….. Ki kaisu can Fallon daddyn ki na baki zasu fi sakewa naga Anwar duk ya takura…. Mommy Dan Allah muje ki raka Ni…..
Ta kyalkyace da dariya yau naga ikon Allah….
To Wai ya ankayi yasan gidan mu?
Idan kinje Kya tambayeshi.
Ta tura ta waje daya ta fito da sauri….. Ta biyota da gudu mommy jirani….
 Ta boye bayan ta, Koda yaga mommy ce ta fito yayi saurin yin kasa da Kai…. ta wuce abinta tana dariya.
 Tayi tsaye tana Yar kyarma tana murmushi kanta kasa.
Sadeeq ya tsura Mata ido kinyi tsaye ki karaso Mana Bilkisu.
  Tayi Yar dariya sannun ku da zuwa ya hanya…..
Sadeeq ya ce qalau.
Ta bi bayan kujeru kuzo muje tayi gaba kadan duk suka Mike….. Tana zuwa saitin kujerar sa ya yi charaf da hannun ta ya kalli sadeeq Dan ubanka shiga gaba…. Ya tuntsure da dariya, idan na shiga gaba in kaimu Ina?
Kwatanta mishi Bilkisu…… ta fizge hannun ta lokacin ne ta Sami damar kallonsa don ta bashi harara…..kyaleshi sadeeq muje….. Ya dawo da ita da sauri jeki sanyo hijab…… Ta kalleshi zaka Fara ko? Gidan namu ban tsira ba? Yasha mur jeki sanyo hijab wallahi kada mu sayar da Hali anan…… Dole ta juya tayi daki ya bita da kallo har ta shige ya hadiye wani tsinkakken miyau ya dawo Kan sadeeq ya Kai mishi uban duka Allah ya Isa Dan ubanka ka ga harammmm….. 
 Wata muguwar dariya sadeeq din ya saki …. Kayi a hankali fa…
  Ashe duk dramar nan mommy na kitchen na hangen su….. Ta Kama dariya ita kadai….lallai Bilkisu tana da aiki.
   Ta fito da doguwar hijab har kasa ta banka mishi harara muje….. Suka bi bayanta..
   Ba sadeeq ba, Anwar kansa falon ya tafi da imanin sa, ya zauna bisa two sitter sadeeq Kuma ya zauna kujerar dake can karshe Shi kadai ya ma t.v kuriiiii ganin ana best film dinsa *mortal combat*
   Ta zauna bisa three sitter tana facing sadeeq ta Kara gaishesu
Sadeeq ya kalleta Yana dariya sai Kika ganmu ko?
Tayi murmushi hmm,
  Hakuri muka zo badawa….. Ke ki dawo Nan kin mun nisa… Ya fada Yana kallonta.
   Tayi kamar Bata ji ba, sai kawai taga ya Mike tayi saurin kallonsa… Yana tasowa ya figo hannun ta Yana fadin ke wallahi wata bagidajiya kike wancen Dan iskan ba dashi zakiyi fira ba ni ne bakon…… Ta fizge hannunta… Akwai CCTV ta nuna mishi da hannu…. And then?
  Ta zaro ido…. Kai Wai baka da tsoro?
Mtsew yaja guntun tsoki tare da figarta da karfi ya zaunar da ita kusa dashi, just sit down here.
  Kaii Allah ya raba ka da rigima….. Allah ya rabaki da gardama kema.
  Rahina ta shigo da tray cike da kayan marmari da lemuka masu sanyi ta Fara jerawa a dining table sannan ta fita tana kawo kuloli kala kala….. 
  Baza mu ci abinci ba fa saboda bamu sanar ba kada a takura ayi Mana.
   Har an gama ai, idan baku ci ba mommy zataji babu dadi?
 Me yasa Kika kashe wayar ki?
Tayi shiru tana murmushi.
Kinji?
Duk kin rame kinyi rashin lafiya ne?
Um, ta ce.
Ko dai tunani na ne?
Ta galla mishi harara , ya kyalkyace da dariya ni ma na rame ko?
Um, ta ce.
To ki tambayeni dalili Mana …… Ta danyi murmushi kaiiiiiii Anwar.
   Me yasa Kika koma da gudu bayan kin ganni?
Tayi Yar dariya….
Murna CE?
Ta Kara galla mishi harara.
Bacin wancen Dan iskan da Baki sako hijab din nan ba kayan sun Miki kyau kin San Haka?
Ta ce hmmm, kawai.
Gobe Zan dawo ni kadai kada ki Sanya hijab kinji ko?
Ta harareshi kammmm.
   Yayi murmushi Dan Allah kisa irin gyalen dazun…. Bafa Zan saka ba dazun ma na manta ne….. Zan cireta idan Kika saka wallahi…… Anwar Nan fa gidan mu ne nidai ka rufa mun asiri. Ni Yanzu ka janyo mun anjima dole in amsa tambayoyi wurin daddy?
Na mene?
Dalilin zuwan ka ko?
Kice fada mukayi gashi kin kashe wayarki nazo bayar da hakuri…… Nidai Dan Allah da baka zo ba saboda zai…… Ya tsareta da ido. Tayi shiru.
Uhum, Ina jinki saboda zai ce meye?
Nidai shikenan.
   Ya kalli sadeeq jeka ci abinci fa, okay ya Mike ya nufi wurin
….ke Kuma kawon nawa anan inci.
   Saboda me?
Saboda bana son kimun nisa Kuma bazan yarda gani ga ki ga sadeeq a wuri daya ba muna ci…… Wai Kai meke damunka….????
  Yayi dariya kawai.
Suleiman ya kiraki?
Gabanta ya Fadi, wace amsa zata bashi kada Kuma ya Kara hasala saboda ta lura tabbas baya kaunar Shi.
  Bari kawai na fada mishi gaskiya….. Ya yi ta Kira Amma ban dauka ba wallahi…au haba?
Allah kuwa.
Ko shine dalilin da yasa Kika kashe wayarki?
A’a ba Shi bane.
To nine?
Tayi shiru.
Saboda me Kika ki daukar wayarsa?
Anwar ka daina kawo maganar Suleiman tunda ita ke kawo Mana sabani….. Dole ki canza layi….. Ta zaro ido dole fa kace .
Yasha mur tabbatas and I mean it.
   Ta Mike kawai tana hararar sa, ya Kai hannu zai kamata tayi baya da sauri tana fadin Zan kawo ma abinci ne…. Sadeeq ya banka mishi harara kaidai wallahi bakayi ba….. Yayi murmushi ka Gama kazo ka bar Falon nan ka isheni haka Nan …. Babu inda zaije. Ta fada tana zuba mishi farfesun Koda da dankalin turawa….
  Ki hanashi din ki janyo ma kanki Yanzu in ci ubansa anan har su daddy suji…. Gabanta ya Fadi tasan karamin aikin sa ne.
 Ta kawo Masa ta Dan janyo stool ta ajiye ta koma ta dauko mishi juice exotic Mai sanyi na kwakwa da abarba.
   Ke ce kikayi?
Ya kalleta lokacin da yayi lomar farko…… Mommy ce.
Yayi dadi amma gobe komeye za’ayi kiyi mun kinji ko?
  Ta galla mishi harara kawaiyayi murmushi Ina dai Shan harara Ni Anwar.
   In tambayeki???
Ya tsareta da ido.
Um,
Tsakanin ki da Allah kinji dadin zuwa na?
 Tayi Yar dariya kawai….. Kinji?
Wai ya akayi kasan address din nan gidan?
Yayi murmushi sirri ne.
Ta Dan harareshi ka Sanya mun ido da yawa me yasa ka damu dani haka?
 Saboda……. Yayi shiru Yana Yar dariya.
Ta tsareshi da ido, saboda me?
Saboda kawata ce ke my best friend…. Ta buga tsoki…. Ya kyalkyace da dariya. Yana ci gaba da Shan pepper soup din.
    Sadeeq ya Mike Bilkisu bude mun kofar can naga exit ce ko?
  Eh, amma ya zaka fita zaka biye maganar  sa ne?
Yayi murmushi a’a Zan dawo ne shidin banza ya hanani Zama anan?
  Ya bisu da kallo kawai Yana Shan lemu.
   Tana budewa ta hango iyayen motoci da katti sai gewaye gewaye sukeyi suna mazurai….. Ta dawo da sauri, Wai Kaine kazo da waccen bataliyar?
   Ta tsaya gabansa tare da rike kugu, ya daga ido Yana murmushi tsiwar ce ta tashi?
  Anwar waye baban ka?…… Ya fesar da lemun bakin sa saboda dariya. Ta tsuke fuska, ya fizgo hijab dinta tayo kansa zata fada yayi saurin mayar da ita gefensa ta zauna….. Innalillahi, Kai Wai wane irin mutum ne?
  Idan za ‘ayi tambaya Zama akeyi ba tsayuwa ba bakauya…. Nice bakauya ? Eh ya fada Yana hararar ta,
  Ka amsani …….. Maganar ta makale ganin ana shigowa da jikkuna set/set….. Ta zaro ido ko yazo neman auren ta ne?????
Ta kalleshi da sauri meye ake shigowa dashi kamar wani lefe?????? Ya kyalkyace da dariya lefe Kuma an fada Miki na Isa Aure ne?
 Ta daka mishi tsawa to na menene?
Calm down ya fada a hankali ganin tana neman tayar da hankali…… Na kawo Miki tsaraba…. Tsaraba ta mecece?
Anwar wanene baban ka a Kano? ….Kai Ina son in San waye Kai ayau… Dai dai sun gama ajiye jakunkunan set hudu ta daka musu tsawa ku mayar dasu mota bazamu karbi kayan Nan Haka ba fa…. Sadeeq zaiyi magana ya daga mishi hannu yace jeka kawai Zan Mata bayani…… Anwar ko hakan zai Zama batawar mu ta har abada…… Ki dubi girman Allah ki daina janyo mun tashin hankali ki jira na amsa Miki duk wata tambaya da Kika rasa amsar ta.
  Zan amsa Miki wanene baba na a Kano….
  Ta tsareshi da ido, ya yi Yar dariya.
  Baba na ya rassu Ni maraya ne…… Jikinta yayi mugun sanyi.
Tayi saurin kallon sa kamar zatayi kuka…kayi hakuri Anwar ban San Haka ba.
Ta Fara magana a hankali Allah ya jikansa da rahama yasa mutuwa hutu ce, yayi murmushi cike da Jin dadi Amin ya Rabbi.
   Sai kuma me?
Waye Kai? Ko Kuma wanene marikin ka?
  Yayi Yar dariya nine *Hamza bushara*….. Ta dago Kai da sauri taja baya ta koma karshen kujera kamar wacce taga abin tsoro….
Ya Kara Yar dariya…. Bilkisu nine *Bushara* Wanda Kika ji ana fada a *Nigeria*…. Na shiga uku ta fada da karfi…. Ke kwantar da hanka… Ta Mike da sauri shima yayi saurin mikewa…… Idan Kika gudu Zan biki har gaban mommy wallahi…. Dan Allah me kake nema wurina Anwar?…. Na shiga uku. Ta Kara fada duk jikinta ya tsinke da rawa…… Zauna in Baki amsa ta Kara ja baya….
Ka kwashi kayan can kabar gidan nan tun kafin ma….. Ke Wai ya akayi ne ya daka Mata tsawa.
….. Ta daga hannuwa kayi hakuri na tuba *Bushara* ta Kara maimaitawa a hankali….. Ya buga tsoki ke bana son gidadanci zo Nan ya Mika hannu..ta ja baya .
Ya fiddo ido…ke me yasa kin cika kawo matsala? Yasha mur kina son in kamaki ko?
A’a, ta fada tana girgiza Kai, oya come and sit down let’s sort out where the problem is…… Ta zauna a dosane….. Ya kyalkyace da dariya ji yanda Kika canza lokaci daya….. Kin taba ganina a TV? 
Ta ce a’a.
Jarida fa?
Ban gani ba.
To Kuma.
Kika sani ko Ina zolayar ki ne?
Ta Dan kalleshi.
Yayi murmushi eh Mana .
To ko da wasan kakeyi?
Ya kyalkyace da dariya kawai.
Ta bishi da kallo.
Ke Ina Kika San *Bushara*?
Ta harareshi a Nigeria waye bai San wadannan sunayen guda biyu ba *Dan gote da Bushara*?
Ya Kara yin dariya….. Yayi saurin matsawa kusa da ita ya chafki hannuwanta…. Yawwa ya fada Yana murmushi….nine *Bushara* ki kwantar da hankalin ki nothing will happen sai alheri…… Kwallah suka shatato Mata ita kanta Bata San ko na menene ba…… Kuka again?
Ke bakya da wahalar kuka?
  Bana son kayan can daddy zai tambayeni na menene Kuma zai mun tambayoyi akanka……Yanzu kukan na menen ciki? Kayan ko kuwa sanin da kikayi nidin waye?
  Kai nidai gaskiya ka kyaleni…. In kyaleki? Kin Kara maimaita wannan kalmar Dana fi komai tsana ko?
Ta kalleshi Anwar me yasa ka mun waccen hidimar?
Ya saketa tare da watsa hannuwa kawai I feel to….. Ba yiwuwa ka fada mun me yasa kake wannan over acting din?
  Na ce Miki kawai na siyo miki tsaraba ne bana son zuwa hannu biyu….. Ta Mike bazan karba ba ka mayar dasu gida idan ka Isa Aure ka hada wa matarka….. Ya Mike ta nemi kwasawa da gudu ya yi saurin  rike hijab dinta.
Wallahi sai ka sakeni haka kawai daga muna course mate zaka jibgo irin wannan hidimar ka kawo mun….. Kawai ne Bilkisu?
Ya fada Yana matsawa kusa da ita…. Kawai ne wallahi, I don’t value friends lemme tell you.
Kina son ki kunyata ni ne?
Ta galla mishi harara Ni ma ai kunyata ni zakayi idan daddy ya tambayeni sai kawai ince abokai….. Kice *INA SON KI* ne…. Ta zaro ido jiri ya nemi daukar ta………✍????
*Zainab wowo ce*
     


*Assalamu alaikum*
Masoyana Ina alfahari daku.

Nazo da wata tsaraba, hausawa na cewa kula da Kaya…….

1. Ina wacce ke fama da karancin ni’ima?
2. Wacce ke fama da budewa tana son jinta a matse da ni’ima sosai?
3. Ko kinsan yawan zubar da ruwa wani lokacin matsala ne? Wacece keson taji ta adai adai?
4. Wacece mijinta baya gamsar da ita?
5. Suwa ke fama da infection?
6. Akwai matan da har yau Basu San dadin Aure ba sam Basu Jin sha’awa ko kin San dalili? 
7. Wacece keson ta gyara nonon ta da jikinta yayi luwai luwai?
8. Ina wadanda mijinsu baya gamsuwa dasu?
9. Wacece kullum sai tayi amfani da lubricant saboda karancin ni’ima?
10. Ina wadanda miji ke musu gani gani da hargagi kullum?
    Akwai supplement masu kyau na dukkannin matsalolin aure daga zainab wowo, direct order ne muna turawa ko wane gari Amma Kano, Abuja da katsina zaku sameshi free delivery in shaa Allah. Masu bukata su tuntube Ni. Darajar annabi da alqur’ani serious buyer nake bukata Dan girman Allah na rokeku. Ga number ta 08089973394 in shaa Allah.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button