BidiyoLabarai

Bidiyo:; Ba Laifinta Bane: Sani Mai Iska Ya Bayyana Gaskiyar Abun Da Ya Raba Aurensa Da Fati Muhammad

A hirar da aka yi da shi a wani shiri na sashin Hausa na BBC mai suna ‘Daga bakin mai ita’, an jiyo Sani Mai Iska yana cewa:

“Tana da gaskiya ina da gaskiya. Uzurinta a wancan lokacin mahaifiyarta da mahaifinta musamman ma mahaifiyarta Allah ya ji kansu dukkansu sun rasu.

Ni kuma uzurina dama ban kammala babban sakandare ba toh kuma ga dama ta samu, ina ga ya kamata na tsaya na samu dan wani abu.

Toh wannan shine babban abun, ya zamana ni ba zan janye karatuna ba kuma na yi nisa, ita kuma tana matukar kaunar mahaifiyarta.

Saboda haka sai muka je muka sami su hukumomi muka ce masu toh gashi gashi, sai su Uk suka bamu zabi cewa tana da zama za mu iya mu raba aurenmu amma za ta iya tafiya inda take so ta je ni kuma zan iya zama a inda nake so na zauna har sai na kammala abun da nake so.

“Amma akwai rudani a cikin lamarin saboda shi abu idan aka ce maka musamman ita a lokacin nan wato tauraruwarta tana haskawa sosai, Allah ya daukake ta sosai ta kowani bangare don ko a can UK din ta samu soyayya daga bangare daban-daban.

Ta sanadiyarta ne ma nima na san wasu manyan wurare daban-daban.

Gadai cikekken bidiyon ku kalla kuji da kunnen ku:;

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button