NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 24

???? *WA ZAI FURTA?*????
              2⃣4⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

????????????????????  *RUKAYYA  BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*????????????.

       ****************
*KADUNA RIGASA*

Wannan doka da tsari ya Kara taimaka wa zaman su sosai da sosai, gidan ya zauna qalau ba sauran tashin hankali idan Yana gari ko wace zata kama tsaginta har ya gama kwanakin sa ya koma sannan zasu ci gaba da ziyarar juna, Koda yaushe Ummi na sashen Amira musamman da ta Fara laulayi………..

       ***************
*ABUJA NIGERIA*

…… Juyowar da zaiyi suka hada ido da Anwar din cikin wani irin yanayi…..ya razana ya firgita, sannan yayi baya da sauri tare da fadin *You scared me*…… Meye naji kana fada?….idanun sa sun kada sunyi jawur kamar garwashin wuta….. Ya daka mishi tsawa nace meye naji kana fada??????
  Look please understand…… Ya shako wuyan rigarsa Kai munafuki na ne ba Amini ba sadeeq?????
Ya girgiza Shi ya tura baya da karfi… Yayi taga taga zai Fadi…. *What the hell are you doing*….. Shima ya daka mishi tsawa…. Sai kawai ya dafe Kai ya duke wurin Yana fadin *Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un*….. Hankalin sadeeq ya tashi ya kamo sa Anwar please…. Ya ingije Shi.. kyaleni sadeeq…kyaleni bana so… Zan maka bayani Anwar please calm down..ya Mike a hargitse ni za’a daura ma Aure ba tare da na sani ba??? Ya nuna kirjinsa Yana zaro mishi idanu…. Please…. Ya tura Shi baya I don’t want to hear it….. Ya yi gida da gudu… Shima ya rufa mishi baya ya biyo shi….tare suka shiga daki Yana kokarin turo kofa ya rufe sadeeq din ya banka da karfi …. *Get out*…. Ya daka mishi tsawa… Ya maida kofar ya rufe , mutanen gida kowa ya fito yayi jugun , jigumm ……
   Cikin bacin Rai sadeeq din ya Fara magana; Kana ganin laifi nane??
Ko kana tunanin Ina da laifi ko hannu aciki????……. Ya akayi ka sani ni ban sani ba???
   Sadeeq wane laifi nayi da za a dauran Aure ba tare da na sani ba??
   Ya bude fridge ya dauko ruwa Mai sanyi ya Mika mishi a cup ungo kasha let’s talk peacefully please….. Bana Sha ka fada mun  waye ya dauran Aure Kuma meye hujja???
  Ita Bilkisun ta sani???? Ya Kara zaro mishi idanu…
Daddyn Bilkisu ya ce a daura…. Dalili????? Ya Kara tsareshi da ido….
  Wallahi itama Bilkisun bata da masaniya, Kai waye ya fada ma???
   Ban sani ba ya daka mishi tsawa….. Ya Mike tsaye bari kaji Anwar bana tsoron ka bana shakkar ka, ka saurara Zan fada ma abinda na sani akan wannan daurin auren idan kaga dama ka yarda idan Kuma ka ga dama ka Sanya a daureni sannan kaje ka dauki duk matakin da ka dauka…… Ya kura mishi ido, yau sadeeq ke mishi tsawa haka?
   Lokacin da aka Kai kayan daddyn nasu ne yace a daura Aure saboda yanayin rawar kanka musamman yanda kake kakkama mishi ‘ya…. Ko kasan cewa ya bada labarin duk bidirin da akeyi school???? Musamman Yana da wadanda suke bin yarsa suna monitoring?? Kasan gidan akwai CCTV wacce yake ganin duk zancen da kakeyi da Bilkisu???? Kaga laifin sa don ya kubutar daku daga halaka?
Muharramar ka ce da zaka na irin wadannan abubuwan?
  To Alhaji Hassan ya sanar dani dalili kuwa saboda sun san nine shakikin ka ni kuma na shaida wa mahaifina akara samun shedu kasan duk duniya maganar nan bazata taba fita ba daga bakunan mu bacin da ka jiye ma kunnen ka.
  …… Ya juya zai bar dakin cikin bacin Rai Anwar din ya riko hannun sa da sauri, sadeeq din yace good cikin zuciya saboda yayi hargagin ne don ya nutsar dashi.
  Ya dawo dashi a hankali duk jikin sa ya mutu ya ce zo zauna sadeeq…. Bazan zauna ba Ina ce ni munafukin ka ne ba Amini ba ….. Kayi hakuri I regret it…. Kayi hakuri…. Shima sadeeq din duk jikin sa yayi sanyi ya dawo ya zauna.
  Sadeeq meye shawara?
Ya kalleshi kamar zaiyi kuka…. Kayi hakuri Anwar I know how you feel about this…… Forget about my feelings please what shall I do????
  Shawara daya ce Anwar pretend as you don’t know. Ka nuna Sam baka sani ba….. Zanyi haka saboda Zan tayar ma Bilkisu da hankali…. Ai anyi shawarar ita a sanar da ita saboda ta kiyaye sharuddan Aure…… Ya dafe Kai tare da runtse ido to ni me yasa basa so na sani?????? …… Saboda rawar kanka. Sadeeq ya fada Kai tsaye….. Zan basu mamaki sadeeq…. Wallahi Zan nuna masu how true I love ‘yarsu…….. Alhamdulillah sadeeq ya fada tare da janyo Shi ya rungume Shi….. Anwar wannan ba karamin gata akayi maku ba wallahi hakan da akayi ya faranta zukatan dangin ka….. Ina ka taba ganin anyi Haka? Ka tabbatar gida kamar na su Bilkisu ba za su taba hakan don kwadayi ….. Mtseww please I don’t suspect that.
Ya tashi zaune sadeeq an dauran Aure da Bilkisu????? 
Ya kara runtse ido yayi baya ya kwanta bisa gado har lokacin bai bude ido ba…. Sadeeq Ina son Bilkisu, wallahi duk abinda nakeyi ina sane am just testing her , Ina jaraba ta ne sadeeq Kuma yarinyar taci jarabawa ta, tana Sona sosai I knew it amma kullum tana kokari ta danne don ta tsira da mutuncin ta Ina son Mata Mai Hali irin nata *she’s exactly the wife am praying for*…….. Ka Basu mamaki Anwar….. Ya bude ido ya dago da sauri….. *I will* wallahi zasu Sha mamaki *trust me*
…… *How I wish ita ma su Kyaleta bazasu fada Mata ba?*
No, is better su fada Mata Anwar kasan Mata da wauta……. Yes ni Kuma ga kishi…. Duk sukayi dariya… Ya Mike tsaye ya buga wata Kara… Wuuuu *Mrs Bushara* wawwwwww!
  Sadeeq ya bishi da dariya.
Ko su Hajiya baza su san na sani ba. Sadeeq Zan ba guys din nan mamaki….. Dan ubanka su daddyn ne guys…. Duk suka kwashe da dariya sadeeq yace *Yaro da kudi*…… Ya Kara sa da *Abokin tafiyar manya* suka tafa.
  Ya zuki iska ya hurar  *Honestly I can’t believe we are now husband and wife*….. Kai zanje na kwanta I’m feeling sleepy. Sadeeq ya fada tare da mikewa….. Sadeeq Ina zamu je hado lefe?
Ya banka mishi harara sai Corona tayi sauki Dan ubanka……. Ya kyalkyace da dariya, Shi Kuma ya fice yaja mishi kofa.
 Ya fada bisa gado….. Wai ni nake da rawar Kai, zasu karyata hakan da kansu lallai Basu San waye *Bushara* ba.
  Ya dauko waya lemme call her idan sun fada Mata nasan she’s awake now, idan Kuma basu fada ba tayi barci….
Taci kuka har ta bani tayi lamoo bisa gado, wayar ta Fara Kara a hankali…… Kamar kada ta dauka sai Kuma ta tuna da nasihar daddy cewar Yanzu duk abinda tayi mishi na rashin Jin dadi Allah zaiyi fushi da ita.
  Hello…. Ta fada cikin dusasshiyar muryar da Tasha kuka…… *What are you crying for?*……. Gabanta yayi mummunan faduwa Taya akayi yasan kuka tayi?
Um? Ya Kara fada.
Tayi shiru kwallan suka shatato Mata.
Bilkisu? Ya kirata a hankali.
Gabanta ya Kara faduwa tsoron ta daya Anwar ya San ita matar sa Yanzu tasan kawai *Ta mutu* Yanzu ma ya ta Kare dashi bare yasan matar sa ce……. Bazakiyi magana ba?
Ba komi, ta fada a hankali.
*Is that because you missed me?*
Ta buga tsoki….. Ya kyalkyace da dariya to kukan na meye daddy ya dake ki?
Tayi shiru, 
Ki jirani karfe takwas da safe Zan zo inji dalilin…..
 Ba sai ka zo ba….
 Ta fada kamar zata Kara rushewa da kuka.
Saboda me?
Huh?,
Sai da safe Ina son nayi barci…. Karya kikeyi ba Zaki iya barci ba yau….. Gabanta ya fadi. 
Bazan iya barci yau ba?
Eh,
Me yasa?
Saboda na tafi na barki…. Ta buga tsoki ya kyalkyace da dariya.
Kilibabba Allah ya kamaki Ashe kullum nabarki sai kinyi kuka ko?
Wallahi a’a .
To kukan meye kikeyi?
Ba komai.
Na Jin dadi kenan?
Eh. Ta fada cikin tsawa ya Kara dariya….. Ko dai ni nayi laifin?
Ta ce hmmm,
Ya lumshe ido, kiyi hakuri toh.
Tayi shiru….
Kinji?
Um, 
Ba um Zaki ce ba toh ake cewa, ko inzo nan mu kwana……. Kamm, ta fada tare da latse wayar….. Ya Kama kyalkyatar dariya Yana mirgina bisa gado, dukkan su babu Wanda ya samu yayi barci, Shi Murna ita zullumi.
  Yana gama sallar asubah barci Mai bauyi ya daukeshi, sai Sha biyu ya tashi,
    Ita kuwa ta tashi idanu kumbure saboda kuka, karfe Sha daya mommy ta tafi airport, daddy Kuma ya na gida saboda hutun Corona virus.
  Karfe biyu ya karaso, Rahina ta shigo Aunty ga Uncle Anwar……. Gabanta ya Fadi.
   Daman tayi wanka ta Dan gyara fuskar ta har lokacin ana gane tayi kuka.
   Yauma da kananan kaya, ya mayar da facing cap din gefe ya rufe idanun sa da bakin goggle.
 Jiki ba kwari ta shigo ya kura Mata ido har ta zauna sai kawai ta bashi tausayi.
Ina kwana…… Wuni dai ko?
Yanzu Kika tashi barci ne?
Yana maganar a dake,
Tayi shiru.
Kin dafa mun abinci?
Ta girgiza Kai, 
Saboda me?
Yanzu meye zanci toh?
Tayi shiru,
Ke me Kika ci?
Nan ma tayi shiru.
Jeki kawo mun abinda Zan karya….. Ta Mike sim sim….ya bita da kallo.
Ya zuki iska ya fesar tare da Dan zamewa ya kwantar da bayansa a kujera.
Wayoyi kawai yake amsawa har ta shigo da tray a hannu…..kawo nan bazan hau ba table ba…. Okay Zan Kira anjima kaci gaba da lissafi ka turon brake down…
 Ya ajiye wayar Yana Mai saukowa bisa carpet.
Indomie da kwai ta kawo mishi da oat.
   Ya hada oat din da kansa ya cika Madara yasa sugar kadan ya tura Mata bowl din wallahi tallahi sai kin shanye duka ni zanci indomie din……. Ya Sha mur,.
Zatayi magana ya harareta Zan hada Miki da indomie din Kuma itama nayi rantsuwa… Ai yamun yawa… Ba abinda ya dameni ko zakiyi amai sai kin shanye.
    Yaci gaba da cin indomie din yanayi Yana satar kallonta, tana tsakura, tana tsakura har ta daga bowl din ta kafa Kai…. Da kyar ta shanye.
  Ya mike zanje Kano anjima sai next week Zan dawo kinji ko?
Toh,
Ya kalleta kinyi zaune ba rakiya ko cikin ya cika da yawa?… Ya karasa maganar Yana dariya….. Ta banka mishi harara ta mike.
Yana tafiya ta koma daki, ashe hada yunwa ta hanata barci ko mintuna 3 batayi ba barcin yayi awon gaba da ita.
  ……. Kwana biyu ta warware, kullum basa yin waya sai cikin dare.
    Hankalinta ya Fara kwanciya saboda sam da alama bai San an daura masu auren ba.
   Hajiya ta kasa boye farin cikin ta Koda yaushe maganar ta Bilkisu….. 
Ja’iri ashe mace kabi Shi yasa ka dage Kai anan zakayi karatu…. Ya yi dariya Wai waye ya fada miki mace nabi? 
Coincidence ne ya hada mu, amma ni ba ita nabi ba…..yaki nuna ma kowa yasan wainar da ake toyawa.
  Har suka je sokoto suka dawo bai nemeta a waya ba. Hakan ya Bata mamaki, ta Fara tunani ko daman rashin sanin inda alakar su ta dosa yasa yake yawan takura Mata Yanzu da ya tabbatar magana taje ga iyaye yasa ya Sami natsuwa?.
  Har iyayen nata sai da suka fahimci hakan.
 Shi kuwa yayi amfani da wannan Dan hutun ya Fara zirga zirgan nemar Mata transfer zuwa University of Abuja. Ko sadeeq bai fadawa ba yasa aka had a mishi transcript dinta cikin sati biyu ya kammala komai. Hatta kayan ta kafff yasa an balle dakin an kwashe sannan ya gyra kofar ya rufe.
 Yana jira akoma ya Mata registration……
Ranar da aka koma, ya aika da komai washe gari yazo da takardun gidan su.
  Tana ta shiryen komawa, bai Mata waya zai zo ba sai dai suka ganshi kwatsam, ta gama kulewa fushi sosai takeyi dashi saboda kusan sati daya kenan basuyi waya ba.
   Yanayinta kawai ya kalla yasan fushi takeyi.
Yana zaune bisa hannun kujera alamar kamar sauri sauri yakeyi, ta Kara daure fuska….. Wai fushin na menene?
Ta mishi banza.
Yayi Yar dariya, kiyi hakuri abubuwa sun mun yawa ne, bana zaune….. Kuma shine baka da lokacin kirana???
Ya Dan yi murmushi to ke ba sai ki Kira ba?
Ko laifi ne Mata ta Kira mijinta……….dammmm gabanta ya Fadi ta kalleshi da sauri yayi murmushi yes tunda na Aiko gidan ku ai kin Zama matata ko wani ya Isa ya shigo Yanzu neman aurenki?
Ta Dan saki ajiyar zuciya, ya kusa sakin dariya….. Nayi missing dinki sosai Bilkisu, Ina ma ciki amma nasan komai na Dan lokaci ne daga ranar da aka mikon ke nasan komai ya Zama labari……. Gobe Zan koma school. Ta fada a hankali.
Keda waye Zaki koma?
Ban sani ba daddy yace na Fara sanar dakai tukun.
Da banzo yau Kuma fa?
Zan maka text.
Saboda me bakya son kirana?
Tayi shiru,
Ya kamata ki rage kunyar nan fa.
Tunda na Aiko gidan nan Bilkisu duk kin canza kinyi sukuku Anya kina Sona?
Ko baki son kiyi rayuwa Dani?
Baki magana?
Kina damuwa ne akan rabuwa dasu mommy??…… Sai kwallah suka zubo mata sharrrr…… Ya Salam ya tashi yaso gabanta , tunanin ta zai kamata kamar yanda ya Saba sai taga ya zauna gabanta ya harde kafa…….
      Kinga ki kwantar da hankalinki wallahi Bilkisu bazakiyi dana sanin Aure na ba, bazan taba Bari ki tozarta ba.
Ke shaida ce, duk kudi na da commitment nawa bai hana na baki time din kanki ba, Ina son kula Shi yasa Nima nake kulawa dake, Ina son ki fiye da  dukiya ta, wallahi tallahi ko Yanzu da Kika ga na Dan kaurace Miki I wanted to prove your parents how good I am, and how I truly loved you.
   Kin San cewar nasan an daura Mana Aure?…….. Ta Mike tsaye ta zaro ido, ya Kara Yar dariya yes I knew it and I promised my self I’ll never touch you again, tunda an ce *Ina da rawar Kai*
Ta Kara kallon sa da sauri, ya Kara dariya.
Ya Mika Mata takarda ga Shi gobe gobe Zaki je kiga registration officer na nan University of Abuja akwai abinda Zaki karasa, ta Kara zaro ido.
Me kake nufi?
Ya Dan Sha mur, Ina nufin na mayar da ke can anan Zaki gama…. Kai kuma fa?
Ni Zan karasa a dutsinma….. Wallahi ban yarda ba ta Mike tsaye…. Shima ya Mike, wannan shine umurnin da na Baki Kuma abinda na zartar a matsayina na mijinki……. Akan meye zakayi haka?
Saboda na nunawa kowa cewar ba sha’awar ki nake ba sonki nakeyi saboda Allah……Anwar…. Bilkisu kada Kija maganar nan, kada kuma ki sanar wa iyayen ki cewar nasan an daura Mana Aure kawai Ina son ke ki amince da *Ni Anwar son da nake Miki na Aure ne ba na sha’awa ba*………….????✍????

*Zainab wowo maman Abdallah*????
Masu kirana waya kuyi hakuri ku aiko da sako ta whatsapp????????????????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button