NOVELSUncategorized

DIYAM 61

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Sixty One: The Decision

Nayi kokarin dago kaina in kalleshi amma na kasa, tun daya fara magana nake hawayen tausayin rayuwata da tasa, wani gurin kuma inyi murmushi ina jin soyayyar sa tana kara ninkuwa 9a zuciyata. A karshe sai na samu
kaina da tambayar kaina. Shin tsakanin ni da Sadauki waye yafi son dan’uwansa? 

But can I tell him that? Anya zan iya gaya masa cewa babu abinda ya ragu a zuciyata dangane da soyayyar sa sai ma karuwa da yayi. Sai jin murtarsa nayi a hankali yace “should I start crying? Ko kuma in durkusa a kan guiwa ta?” Na yi murmushi ina karasa goge sauran hawayen ido na, na bude baki sai maganar ta makale, sai kawai nasa hannayena na rufe fuskata. Ya kama dariya yana cewa “you must be kidding me. Yanzu ni in zauna in gama bude miki zuciyata amma ke sai ki rufe fuska? In ba zaki gaya min bama at least let me look at your eyes in karanto amsa ta a can” na girgiza kaina nace “I can’t” yace “wait, wai kunya ta kike ji?” Na bude fuskata nasan “mu fulani kunya ce damu” yayi dariya yace “maybe kin manta, nima bafulatani ne” nace “half ba. Mun bar musu kuma” yace “ni ban yarda ba, ko bani da jinin fulani my heart is fulani. Zuciya kuma itace rayuwa” nayi murmushi ina tuna ranar daya fara fada min nice zuciyarsa a Taura. Yace “I still need to hear it. I need to hear you say you love me. In kika fada then I have tukuici for you. Happiness insha Allah, till eternity. Through thick and thin”.

Ina sunkuyar da kaina kasa, murmushi a lips dina, ruwan hawaye a idona, nace “kalmar love can’t even begin to describe yadda nake jinka a zuciyata. Sometimes ina jin soyayyar ka kamar tayi waya a kirjina Kamar zuciyata ta cika har tana zuba da sonka. Da sonka aka haife ni Sadauki kuma nasan da shi zan koma fa mahalicci na. Bana jin kalmomi zasu iya bayyana soyayya ta gare ka dan duk abinda na fada ji nake yi kamar yayi kadan” sai yayi sauri yace “okay, will you marry me? Please? Sai a nuna min soyayyar a aikace ko zan fi fahimta sosai” sai nayi saurin jan hijab dina na rufe fuskata saboda nauyin maganar sa da naji. Ban san me yasa yanzu nake jin tsananin kunyar Sadauki ba bayan kuma sanda nake karama bana ji kamar haka. Ina jinsa ya sake jawo kujerar sa kusa dani yace “Please say something Diyam. Am dying here”.

Hayaniyar su Asma’u ce tasa na bude fuskata amma ban kalli inda yake ba sai na juya inda na jiyo muryoyinsu. Murjanatu tazo da sauri tana cewa “yaya, wallahi naga irin motar da kayi min alkawari as my birthday gift. Please, please yaya ka bar min ita” sai ya dafe kansa da hannu daya yace “zaki saka min ciwon kai Fanna. Please go and make the noice somewhere else” sai na mike tsaye nace “yauwa an kawo abinci, dama yunwa nake ji”.

An jera mana abinci iri iri akan shimfidar da akayi mana akan grass carpet din gurin. Muka tafi mu uku muka fara saving kan mu muna ci muna hirarrakin mu amma hankali na tana kansa yana zaune har yanzu a inda muka zauna da waya a hannunsa. Naji shigowar text cikin waya ta sai na duba naga “Please ki ajiye abincin nan kizo mu karasa maganar mu” sai na juya na kalle shi nace “me za’a zubo maka?” Ya bata rai yace “am not hungry”. 

Anan mukayi sallolin mu, Murjanatu tana ta yi masa nacin mota sai yace ta bari sai birthday din nata. “Ke ba iya motar ma kika yi ba. In na baki me zaki yi da ita?” Tace “koya min zakayi ai” yace “ni bani da lokacin koya miki mota akwai driving schools ki shiga ki koya a can”. Sai da magrib ta gabato sannan muka tafi gida. A hanya Asma’u da Murjanatu ne kawai suke ta hirarrakin su amma ni da Sadauki kowa yana hira ne da zuciyarsa. Ni ina rarrashin tawa ne akan ta yarda da hukuncina a kan Sadauki, ina gaya mata cewa hakan shine abinda ya kamata gare ni, gare shi ga Subay’a, ga kuma zuriar dazamu haifa in muna da rabo. But my heart was weeping tana ganin banyi mata adalci ba. Tana gaya min hukuncina ni zaifi affecting ba wai shi wanda nayi wa ba.

Muna zuwa gida yayi packing a kofar gida su Asma’u sukayi masa sallama suka fita, ina hango Subay’a ta fito da gudu sai kuma ta tsaya tana kallonsa sai ta juya ta koma gida. Ya juyo yana kallona, nasan maganar da zaiyi min kuma kirjina bugawa yake da karfi ina tattaro courage din amsa masa, yace “baki bani amsa ta ba Diyam. In kin amince min ina son zanje gurin Kawu Isa” na juyo ina kallonsa, ina tunanin irin smartness ne Sadauki. Gurin Kawu Isa. Yasan a yanzu in ya nemi aurena a gurin Kawu Isa da gudu zai bashi ko dan ya kara bakantawa Alhaji Babba rai tunda har yanzu basu shirya ba. Sai kuma nayi tunanin hakan da Kawu Isa zaiyi shi zai kara rusa yar guntuwar zumuntar da take tsakanin uncles dina guda biyu. Sai nace “ina son aurenka Sadauki. Zan iya cewa shine greatest burina a yanzu. But, ina son muyi shi akan dai dai. Ina son muyi shi ta yadda nan gaba ba zamu zo muna nadama ba” yace “nadama kuma? Akan me zamuyi nadama?” Nace “have you thought about maganar da mukayi ranar nan? Akan forgiveness?” Sai ya dauke kansa gefe yana kallon waje nace “nima da akayi wa laifin nan na yafe musu. And I felt good lokacin da na yafe din ji nayi tamkar na dauke wani abu ne mai nauyi daga zuciyata. Wannan feeling din shi nake yi maka kwadayi. And Subay’a, ƴata ce at the same time ƴar Saghir ce duk yadda bana son Saghir bazan taba cewa ba shine ya haife ta ba. She will come in between us ko da munyi auren ma she will never forget cewa kai ka rufe mata mahaifinta and that may affect me nima a gurinta zata iya tunanin da sani na akayi komai” yace cikin dacin murya “I didn’t lock up her father. Shi yayi signing takarda da hannunsa babu wanda ya tilasta masa” nace “but intentionally ka bar masa ai. Kuma kudin ka ne. You can just walk to the court a yanzu kace ka yafe masa a d that will be all” ya girgiza kansa yace “you seem to be forgetting something. Ba kudina ne kadai yake rike da your precious Saghir a prison ba. Ko drygs din ma ni na daka masa a dakin sa?” Naji zafin kalmar ‘precious Saghir’ din daya fada amma nasan kishi ne yake yi, sai nace “ba kai ka saka masa ba. Abokinsa ne yayi framing dinsa amma yayi framing dinsa ne saboda ya samu damar guduwa da kudinka da Saghir ya dauka, so it circles back to you. Please Sadauki, you have the power, you can set him free. Saghir yayi nadama. I saw it in his eyes sanda naje gurinsa a prison” yace “nadama? Baki san hausawa sunce kowa ya tuba dan yuwa babu lada ba? Ko zaiyi nadama Saghir ba yanzu ba” nace “Sadauki, Saghir fa…..” Sai ya daga min hannu yace “stop, Please stop mentioning his name” sai na fahimci wani abu. Duk maganar da nake Sadauki ba jina yake yi ba, kishi ya rufe masa ido gani yake yi kamar saboda ina son Saghir ne nake so ya fito da shi. Ban kuma cewa komai ba sai na dauki purse dina na bude kofa na fita. Ina jin yana kirana amma ban juyo ba duk kuwa da cewa ji nake tamkar tawa zuciyar tafi tashi jin zafin hakan.

Ina shiga na tarar Asma’u da Murjanatu sun saka Inna a gaba suna ta bata labarin guraren da muka je. Sai na wuce su na shiga daki da niyyar rage marata a toilet sai kawai naga Subay’a a kwance a kan gado, na karasa kisa da ita sai naga kuka take yi a hankali hawayenta yana zuba kan katifa. Naji hankalina ya tashi sai na durkusa na jawo ta jikina nace “Subay’a? Kuka? Me ya faru?” Sai taki magana ta cigaba da kukanta ni kuma nayi ta rarrashinta har tayi shiru Sannan na sake tambayar ta sai tace “Daddy na nake son gani” sai nayi murmushi nace “dan kina son ganin Daddy sai kiyi kuka? Kiyi hakuri kinji? Da weekend zan kaiki ki ganshi” ta gyada kai kawai. Har zan tashi sai kuma na dawo na zauna nace “Subay’a, ranar nan da kika ce min kinji su Inna suna magana akan uncle Sadauki shi ya rufe Daddy ba haka bane ba, bakiji dai dai ba, uncle Sadauki shi yake kokarin fito da Daddy daga prison. Dazu ma maganar da muke yi dashi kenan” sai ta sake gyada kai kawai but she didn’t looked convinced. Sai naji babu dadi saboda nayi mata karya amma kuma hakan ina ganin shine zai rage kiyayyar ta ga Sadauki. Ina kuma fatan komai ya dai-dai ta kafin tayi girman da zata gane komai.

Sai da nazo kwanciya naga text din Sadauki “am sorry Diyam, but I can’t”.

Sai nayi ta juya wayar a hannuna na rasa amsar da zan bashi. A karshe kawai na kasheta na ajiye. Cikin dare na tashi na gayawa Allah bukatu na. I want everything to turn out alright a gurin kowa da kowa. Ina kuma son zumuncin mu da yanuwan mu ya koma kamar yadda yake kafin a hada auren karfafa zumunci tsakani na da Saghir (ko auren bata zumunci ba), sai na roki Allah ya duba zuciyata yayi min zabi mafi alkhairi. Kafin safiya nayi making decision. Makaranta zan koma in cigaba da karatu. 

Da safe na samu inna da bukata ta. “Inna maganar makarantar da nayi miki ranar nan. In kin amince ina so in nemi makarantar in sayi form in fara kafin shekara ta zagayo in tafi jami’a” ta tsaya rana kallona, daga dukkan alama maganata bata yi mata dadi ba amma sai tace “Allah yasa hakan shi yafi alkhairi” nace “ameen”.

Da yamma sai ga Sadauki yazo gidan. Ya zauna kowa ya gaishe shi sai yake yiwa Murjanatu magana “Papa ya kira. Yace ki shirya ki koma saboda shirin tafiyarki school” ta bata rai, ya daga hannu yace “babu ruwana. Kinsan in baki tafi makaranta ba this year ba aure za’ayi miki” ta turo baki “Sa’adatu ma ba’ayi mata aure ba sai ni?” Yace “okay try me ki gani. Kin dauka wasa nake ko. Su Sa’adatu ai duk karatu suke yi ke kuma zaman banza kike yi zaman kula samari” sai tayi shiru fuskarta kamar an aiko mata mutuwa. Inna tana jin su tace “gwara kije karatun ki. Diyam ma tace makaranta zata koma” ya juyo yana kallona naki yarda mu hada ido sai yace “school? Very good. Ina zaki je?” Nace “computer school zan yi, kafin in samu admission. Tunda kaga yanzu an gama registration har an fara karatu sai next year kuma” ya daga kafada yace “ba duk universities bane suka rufe admission” nace “wacce ce ba’a rufe ba? Kasan kuma banyi jamb ba, so ko ba’a rufe ba bani da hope” yace a hankali “you can go to Oxford. Can nake nemawa Murjanatu, zaku iya tafiya tare” sai Murjanatu ta mike da sauri ta fara tsallen murna. “Haa, har naji dadi wallahi. Please Diyam say yes kinji? Please, please, please”.

Sai nayi shiru ina kallon Sadauki wanda shima ni yake kallo, with so many unspoken words a cikin kallon namu ni ina jin haushin wato akan ya yafe wa Saghir ya gwammace ya tura ni wata uwa duniya karatu shi kuma yana jin haushin dan yaki yafewa Saghir na yi choosing in koma makaranta akan in aure shi. 

Ba yawa, kuyi manage.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button