NOVELSUncategorized

DIYAM 62 & 63

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Sixty Two & Three : The Bet

Inna ce ta yi magana “au biye mata zakayi? Wani irin karatu zata tafi har wata kasa tayi? Ba gwara ayi auren ba in yaso in ma alhuda huda zata zama sai tayi ta zama ba?” Na kalleta nace “Akwai wanda yazo yace yana son
aure na ne Inna?” Sai tayi min dakuwa tace “ku raba ke da yan gidan ku, yanzu zama kike so yayi tayi yana jiranki har ki gama wani karatu? Ko wanne karatu ne ai za’a iya yinsa a gidan miji” sai ya mike yana kallon Inna, ban kalle shi ba but I sensed cewa ransa a bace yake, yace “in karatu take so Inna ki barta tayi karatun ta, in zata je Oxford din ta fada and I will take her there. In kuma bata son ta ta fadi duk wadda take so in dai ina da dama zan kaita” sai ya juya ya fita. 

Na mike da sauri nabi bayansa kamar wadda ake fusga ta zuwa gare shi na same shi a gareji nace “Aliyu” ya juyo da sauri yace “what?” Ina kallon yadda idonsa yayi ja nace “kar kayi fushi dani please” ya dawo gabana ya tsaya yace “nasan abinda kike trying to do, kinsan ina sonki da yawa ina son aurenki shi yasa kika yi shawarar tafiya karatu a tunanin ki hakan zai saka na fito miki da Saghir dinki, which I will never do. Na gaya miki kuma nace bazanyi ba, the more you keep mentioning him and showing that you care about him, the more zuciyata take gaya min in barshi yayi rotting there. In da kinsan kina son sa sanda na tambaye ki ko kina son komawa gidan sa sai ki gaya min, I would have supported you, kamar yadda a yanzu zanyi supporting dinki through karatun da kika ce zaki yi. You know why? Because I love you, and to me that’s what true love is. In kana son mutum soyayya ta gaskiya shine you care about him and support him, you put his happiness a saman naka, you sacrifice everything just for him” 

Naji bacin rai nace “how can you accuse me of that? I don’t love Saghir kuma ka sani, ka sani kai nake so, kuma…” Yace “ni kike so? Na dai ji a baki kin fada kin ce kina sona. But am not so sure about that. Saboda duk abinda kike yi is total opposite of abinda na fahimta a matsayin so. Yes, kin soni a da na sani, but yanzu ban sani ba because a yanzu Saghir dinki shine a gabanki, dashi kadai kika damu” nace “ka daina cewa Saghir dina, ba nawa bane ba, bana son Saghir kuma ban taba son Saghir ba kuma bana jin zan taba sonsa tunda har na zauna dashi a matsayin mijina for years amma ban so shi ba. Kai na so, kai nake so kuma kai zan cigaba da so. Son da nake maka ne kuma ya saka nake so ka fito dashi din for your own good, for peace a cikin rayuwar da nake mana burin shinfida wa dani da kai har mutuwa, and that’s my version of true love. In jawo ka kan gaskiya even if that will hurt you and me”.

Sai naga idanunsa sunyi softening, yana girgiza kansa yace “I can’t, na gaya miki I can’t”.

Raina a bace na koma cikin gida. Why is he so stubborn? Amma ina zuwa gida na tarar inna ta na tsarawa Murjanatu dalilin rigimar mu ni da Sadauki, sai ta juyo tana kallona tace “why are you so stubborn?” Nace “ni? Au nice ma mai taurin kan bashi ba?” Inna tace “ke ce fa. Kuma ke zakiyi wa kanki, dan ni bazan goyi bayan yayi ta zama yana jiranki ba har zuwa sanda zaku gama rigingimun ku wadanda babu rana. Ke fa kece baki da gaskiya, shi waye yace ya daukar masa kudi? Ita kuma Subay’a ai ba’a kanta aka fara rufe uba ba, wasu ma uban nasu mutuwa yake yi ya bar su kuma haka suke hakura. Wadansu ma basu san iyayen nasu ba uwa da uba gabaki daya. Kowa da kaddarar sa”. 

Ni dai bance mata komai ba saboda nasan ba fahimta ta zata yi ba. Sai naga ta saka mayafin ta tace mana ta tafi unguwa. Sai bayan ta tafi sai sannan na zauna nayi wa Murjanatu bayanin irin yadda Sadauki intentionally ya shirya wa Saghir trap din daya kai shi prison. Maimakon inga ta fahimce ni sai naga tayi dariya tace “kadan da aikin yaya na wallahi, Aliyu Haidar sadaukin sadaukai” na bude baki ina kallonta da mamaki “wato ke burge ki yayi ko?” Tace “waye yace ya daukar masa kudi? Ai kamar yadda ya fada ne shi ba shi yayi forcing hannunsa ba, ba kuma bindiga ya saka masa a kai ba, ya dai haka masa rami amma shi yayi deciding ya dauka dan haka shi ya jefa kansa cikin ramin”.

Sai dare sannan Inna ta dawo daga unguwar tata. Lokacin kwanciya bacci yayi muka je muka kwanta ni da Murjanatu dan tun zuwanta na mayar da Subay’a dakin su Inna. Muna kwance Murjanatu tana ta chatting da sisters dinta da samarinta. Na dauki wayata ina ta jujjuyawa a hannu na. Sam bana jin dadin rabuwar da mukayi da Sadauki dazu, amma kuma banji dadin abinda ya gaya min ba akan wai ina son fito da Saghir ne saboda ina so sa. Zuciyata tana son in kira shi in ji muryarsa kuma in bashi hakuri amma kuma wani barin yana nuna min cewa shi me yasa ba zai kira ni ba? Na ajiye wayar nayi tsaki na kwanta na juya bayana, kusan awa daya ina kwance babu bacci babu dalilinsa, har Murjanatu ta gama yin wayoyinta da chatting dinta naji tayi addu’a ta kwanta. Sai na kuma dauko wayata na nemo number dinsa nayi dialing a raina ina cewa ba lallai ne ta shiga ba, amma sai ta shiga din, bugu dayakuma ya dauka sai kuma muka yi shiru gabaki daga muna sauraron numfashin juna. 

Nace “I tot ba zaka dauka ba” yayi ajjiya zuciya yace “ni na isa. Bayan kin hana ni bacci” nace “ta yaya zan hana ka bacci ina miles away from you” yace “yes, miles away but so close” sai na lumshe ido na ina jin dadi a raina, naji duk bacin raina yana gushe wa zuciyata tayi fes. Nayi murmushi nace “ko?” Yace “ke ma kin sani ai, ko sai na maimaita miki. Haliman nan dai ita ce a kirjin Aliyu. Itace a jininsa ita ce a tsokar jikinsa. Bana jin akwai abinda zakiyi min in ki daukan wayarki” a hankali nace “kayi hakuri. Na bata maka rai na sani amma tawa zuciyar tafi bakanta a kan taka” yace “nima na bata miki ai. I shouldn’t have said what I said about Saghir. Matsalata ina kishinki da yawa Diyam” nace “Amma ka yarda cewa bana sonsa kai nake so?” Yayi dariya yace “kara fada min inji?” 

Mun jima muna hira har credit din yawa ta ya kare. Sai ya kira muka cigaba. Yana ta bani labarin rayuwar sa a Canada da University din da yayi. Sanyin da naji gari yayi yasa na fahimci dare ya ja sosai. Da kyar nayi masa sallama. “Zaka je office fa gobe” sannan dai yayi min sallama ya kashe. Ina yin addu’a ko minti daya ban kara ba nayi bacci.

Da safe Murjanatu ta tashi tana ta jera hamma. “An hana ni bacci jiya da I love You I Love You” na jefa mata pillow nace “zaki koma kwana a palo” tayi dariya tace “wai su yaya Aliyu an iya soyayya. Lallai in na koma gida akwai labari” sai na tambayeta in tana ganin Papa zai amince, ta bata rai tace “why not?” Nace “ni na taba aure. Aliyu kuma bai taba yi ba” tace “and so what?” Bazan iya miki describing Papa ba, but duk randa kuka hadu you will feel ashamed in kika tuna cewa kinyi min wannan tambayar”.

Ranar ma inna ta sake fita unguwa. And I stated to suspect something. Har yamma bata dawo ba, a lokacin ne kuma Sadauki yazo. Na bude masa palon da yake a matsayin na baki muka zauna a ciki. Sai a lokacin na samu courage din yi masa tambayar da take raina nace “Sadauki baka gaya min labarin yaya ladi ba” yayi murmushi yace “sai yanzu kika tuna da ita? Na gaya mata ai nace kin manta da ita gashi kuma kin kwace mata miji” na zaro ido nace “tana raye? Tana ina? I tot ta rasu ne kuma bana son tuno maka da old painful memory, you are already bitter ba sai na kara maa wani ciwon ba” yace “tana nan. Tana damagun gurin wata cousin dinta. Bayan na tafi Canada ta tafi can ita kuma, kuma tunda na dawo taki dawowa gurina tana can sai dai inje in ganta, one day zamu je tare as a couple” na ture maganar gefe nace “baka kuma fada min ba, tuwo na na ranar nan, ka ci? Na jima ina son inji ko kaci ko baka ci ba” sai naga ya bata rai kamar ba zaiyi magana ba sannan yace “naci, sai da safe amma. I drove throughout the night” 

Muna cikin hira aka kira shi da kamar ba zai dauka ba kuma sai ya dauka yana cewa “Inna ce” naji sun gaisa sai yace “ina gidan ma. Okay bara in fito sai inzo” na yi masa alamar tambaya da hannuna sai yace “Inna ce tace inje in same ta a gidan Kawu Isa” ina jin haka nasan magana tace, amma ya inna zata yi min haka bayan mun gama magana da ita na roke ta kar ta shiga maganar? 

Sai dare inna ta dawo. Bata ce min komai ba sai ta shiga harkokin ta nima kuma ban tambaye ta ba amma sai na kira Sadauki na tambayeshi. Ya kukayi a gidan Kawu Isan?” Yace “babu komai. In tayi tsami zakiji ne ai” amma ni kuma ai bana son tayi tsamin. Nafi so in samu maganar a fresh dinta yadda zan iya tackling dinta. Amma Sadauki yaki gaya min. 

Da weekend Murjanatu ta koma gida. Sai naji duk babu dadi saboda na saba da ita a kwanakin da tayi a tare damu. Bayan tafiyar Murjanatu kamar yadda nayi wa Subay’a alkawari na shirya ta muka tafi central prison gurin Saghir. Amma sai da muka samu ganin sa sannan nayi nadamar zuwa gurin cos it really broke my heart to see him a wannan condition din. Ya rame sosai fatarsa tayi baki ta lalace. Yayi datti. Uniform dinsa na prisoners wandon ya yage daga gwuiwa. Sai na tuno wancan Saghir din dan gayu mai iya daukar wanka da kwalliya yana kyalli kamar tarwada. 

Ya dauki Subay’a ya daga ta sama ya rungume a jikinsa irin yadda yakeyi mata a gida. Sai ta kankame shi tana cewa “Daddy ka dawo gida gurin mu dan Allah” ya sauke ta yana lakuce mata hanci yace “Daddy zai dawo gida kinji princess, ki ringa yiwa Daddy addu’a kullum in kika yi sallah” sai ya juyo yana kallona yace “look at you. Kinyi wata kiba kamar wata Hajiya. Me Inna take baki kike ci ne?” 

Sun jima suna hira shida yarsa, tana bashi labarin sabuwar makarantar ta da sababbin kawayenta. Sai da zamu taho yace “Diyam ya labarin alkawarin mu? Wannan alkawarin da kika yi min shi kadai ne yake keeping dina going a gurin nan. The hope that one day zan fita shi yasa har yanzu banyi loosing sanity dina ba”.

Na dauka Subay’a zatayi kuka amma sai naga bata yi ba. Muna zuwa gida tace min “Daddy yace zaki saka uncle Sadauki ya fito dashi ko?” Nace “mommy da uncle Sadauki zasuyi iyakacin kokarin su, amma sai kinyi min alkawarin kin daina maganar, ba zaki kara yiwa kowa maganar ba kuma ba zaki kara yin kuka ba”.

Da yammacin ranar nayi baki. Kawu Isa aunty Fatima da Mama. Ina ganinsu naji hankalina ya tashi dan nayi guessing maganar data kawo su. Basu jima da zama ba sai ga Sadauki shima yazo, naji haushinsa for not telling me abinda ake shiryawa. A gaishe su, shima ya gaishe su sannan sai na gaishe shi sama sama. 

Kawu Isa ya fara magana. “Diyam innarki ta same ni da maganar ki da yaron nan. Tace yazo yana neman aurenki amma ke kin dauko wasu sharadai marasa tushe kin gindaya masa. Menene dalilinki nayin hakan?” Na dago kai ina son hada ido da Sadauki amma ya sunkuyar da kansa. Na fahimci lallai ni ake jira inyi magana amma kuma ban fahimci me ake so ince din ba. Shin wai su basa ganin abinda nake gani? Sai dai na fahimci akwai banbanci a tsakani na dasu, su basu san gadar zaren da Sadauki ya saka wa Saghir ba, su basu san maganar siyan gida da motar Saghir da Sadauki yayi dan ya taimaka wa Kabir wajen guduwa da kudin da Saghir ya sata ba. Nace “ni ba cewa nayi bazan aure shi ba Kawu. Ni cewa nayi ya yafewa Saghir kuma ya taimaka masa yayi clearing case din drugs dinsa” Mama ta kara da cewa “Sannan kuma ya bashi aiki ko?” Sadauki yayi sauri ya dago kai ya kalle ni, shi baisan da wannan part din ba ma. Nayi niyya ne sai Saghir ya fito sannan zan gabatar masa da wannan kudirin. Na dauke kaina daga kallonsa yayinda Kawu Isa ya rufe ni da fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Ni mamaki yake bani sosai musamman saboda nasan ba wai dan zumunci yake yin wannan abin ba, yana yi ne dan ya batawa Alhaji Babba rai kuma dan ya tabbatar da zaman Saghir a prison saboda abinda yayi wa suwaiba. Sai na tambayi kaina “anya kuwa akwai family din daya kai namu lalacewa?”

Sai daya gama yi min fadan sannan yace “kuma yaron nan yana iyakacin kokarin sa gurin ganin an fito da Saghir, jiya ma sai da muka je tare dashi har ofishin commissioner of police, kuma sun gaya mana suna iyakacin kokarin su akan maganar amma akwai rudani a cikin maganar sosai. Sunce zai fito amma sai ya dauki lokaci” Ya juya yana kallon Sadauki yace “shekara nawa ma suka ce mana?” Sadauki yayi gyaran murya yace “drug case is complicated. Kamar five years haka zuwa sama. Amma zai fito”. 

Mama tace “to alhamdulillah. Wanda ake tunanin ya tafi kenan kuma aka zo aka samu sassaucin da har za’a saka ran fitowarsa? Ai babu abinda zamuyi sai godiya ga Allah. Kai kuma Sadauki Allah ya biya ka” suka ce ameen. Aunty Fatima tace “ai wannan commissioner Ahmad Muhammad yana kokari sosai” suka ci-gaba da hirarrakin su yayinda ni kuma hankali na ya tafi wani gurin daban. 

“Ahmad Muhammad” a ina nasan wannan sunan? Na dago kai muka hada ido da Sadauki sai na tuno inda nasan sunan and everything become clear to me. Ahmad Muhammad shine babban abokin Sadauki wanda suka taba zuwa min visiting makaranta tare, Ahmad Muhammad da yace bashi da buri irin yaga ya zama commissioner of police dan ya kama yan iskan gari ya rufe su a cell. That Ahmad Muhammad. Sai na tuno da kamun Saghir na farko, lokacin da aka je bail dinsa akace wai commissioner yace kar a bada bail dinsa. Sai nayi realising cewa Sadauki yana playing Kawu Isa ne, wato ya dauke shi ya kaishi office din abokin sa sun hadu sun ninke shi a bai bai da maganar cewa suna iyakacin kokarin su bayan kuma babu wani kokarin da suke yi. And I realized with a sinking feeling that Sadauki bashi da niyyar fito da Saghir.

“Ahmad Muhammad” na maimaita a fili. Duk suka juyo suna kallona sai muka hada ido da Sadauki a take kuma na fahimci cewa ya gane cewa na gane abokin sa ne. Nace “shekara biyar ko? Allah ya nuna mana shekara biyar din. Kawu kuyi hakuri kuyi min afuwa ku barni in tafi karatu, kafin shekara biyar din na dawo insha Allah. A lokacin in Saghir din ya fito sai ayi maganar auren”.

Gaba-daya suka yo kaina da fada, har bama na jin abinda suke cewa ni kuwa na sunkuyar da kaina. Su basu san cewa decision din yafi yi min zafi a kansu ba amma dole ce ra saka ni. Sadauki bashi da niyyar fito Saghir bana jin kyma zai fito dashi ko da kuwa bayan na aure shi dinne. Option dina daya a lokacin shine inyi relying da son da yake min in hana shi cikar burinsa na aure na har sai ya warware daurin dayi da hannunsa.

Fada suke tayi min har saida Sadauki ya koma basu hakuri, inna kamar zata dake ni tana cewa “ya fasa auren naki to, aurensa zaiyi ya rabu dake. Yarinya sai shegen taurin kai” Aunty Fatima tace “ikon Allah, wai kamar ba Diyam din da take ta kuka an raba ta da Sadauki ba ce ba, yanzu kuma ita ake cewa ta auri Sadauki tana ki”

Ni kuma bana son in bayyana musu gaskiyar laifuffukan Sadauki saboda bana son in bata shi a wajensu. Gwara ni in dauki laifin shi kuma ya zauna fes.

Washegari da safe Sadauki ya kira ni a waya. Da kamar ba zan dauka ba kuma sai na dauka dan inji me zai ce min sai yace “Oxford din ce kenan” na danyi tunani. I need a break gaskiya, from Sadauki and from my family. Maybe in nayi nesa da Sadauki zaifi tabbatar wa cewa da gaske nake maybe rashina yayi breaking dinsa. Sadauki loves me, and that love shi nake relying on. Nace “Yes, Oxford din ce” ya danyi shiru sannan yace “na gaya miki tuntuni, I can’t do abinda kike fada. Ki bar maganar Saghir, he deserves halin da yake ciki” nace “deserves? Sadauki Allah ne fa kadai yasan waye yayi deserving kaza wate baiyi ba, Allah ne kadai yake judging mutane akan laifuffukan su ba wai mu bil’adama masu tarin laifuffuka ba, Saghir yayi laifuffuka na sani, Alhaji Babba ma haka, amma Allah shi zaiyi judging dinsu bamu ba. Me yasa ba zamu zamanto masu yafiya ba saboda muma Allah ya yafe mana?” Sai yace “Allah yana judging wadansu ta hanyar wadansu. Wanne department din za’ayi miki applying for?” Nayi shiru. I had been thinking about that for years na kasa tsayar da shawara sai a ranar da Saghir ya bani takarda ta, a ranar da na samu freedom dina, a ranar ne na yanke shawarar abinda zan karanta. Law. 

“Law” na fada masa. Yace “wow. But why law” nace “nayi tunani, kusan duk abinda ya same ni a rayuwa, tun daga auren dolen da akayi min har zamana a gidan sa da rabuwar mu ta farko da karbar Subay’a da yayi da farko. Duk wadannan sun faru ne saboda abu guda daya. Saboda rashin sanin yancin kaina da banyi ba. Alhaji Babba a both musulunci da kuma a dokar kasa bashi da right din yi min auren dole. Ko da mahaifin daya haife ni ne bashi da wannan right din sai dai zan iya yi masa biyayya dan in samu lada amma ina da option din cewa ‘no’. Zaman da nayi a gidan Saghir, wahalhalun da nasha wadanda suka yi kokarin lalata both rayuwata ta duniya da kuma ta lahira duk sun faru ne a saboda bansan yancin kai na ba balle in nemi rabuwa da Saghir, both matsayi na na musulma da kuma matsayina na yar Nigeria sun bani yancin zabin wanda nake so in zauna dashi a matsayin mijina, na tuna rabuwar mu ta farko lokacin da ya dauke Subay’a ya tafi da ita da irin halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashinta, shima wannan duk ya faru ne saboda bansan yancina ba, ba kuma ni da courage din fighting for my right dan shari’a ni ta bawa rikon ƴata, ko da mutuwa nayi rikon Subay’a baya hannun Saghir sai dai a bawa Inna, wannan itace Shari’a ta gaskiya. Amma rashin sanin yancin kai da matan hausawan mu suke fama dashi shi yasa ake tauye musu islamic and constitutional rights dinsu”

“Wannan shi yasa nayi deciding in karanta law, dan in samu damar tsayawa duk wata yarinyar da iyayenta ko marikanta zasu tursasa ta gurin auren wanda bata so, dan in tsayawa duk wata matar auren da take zaune da abusive husband kuma take son rabuwa dashi, dan in tsaya in tabbatar iyaye mata sun samu right dinsu da ubangiji da kansa ya basu na karbar rikon yayayensu a lokacin rabuwar aure ko kuma lokacin mutuwar miji. Wannan shine zai zama role dina a society” 

Yace “Masha Allah. I am very proud of you Diyam. Kuma ki sani ina tare dake tun daga farko har karshe”.

Na fahimci cewa Sadauki shi ko a jikinsa da nayi suspending auren mu nace sai na gama karatu. Shi dai kawai in dai Saghir zai cigaba da zama a prison shikenan. Da nayi kokarin yi masa complain cewa bama so nake tunda bai damu da aurena ko rashin aurena ba sai yace “you have no idea how much I want to marry you. This is just a phase we are going through. Am sure zaki chanja mind dinki along the way, in ma baki chanja ba I will wait har ki gama din ki dawo”. 

Wato ni ina depending on son da yake yi min cewa zai sauko ya chanja shawara ya fito da Saghir saboda muyi aure shi kuma yana depending on son da nakeyi masa yana saka ran zan sauko in bar maganar Saghir muyi aure. Ni dashi aga wanda zai fasa.

Ya gama nema mana admission, kuma mun samu successfully. Anan na fahimci cewa su ba yearly suke bada admission ba kamar in batches suke yi kuma mu namu session din zai fara ne January. Daga nan kuma sai ya shirya ya tafi yaje yayi one week a can ya dawo yace “all set, an samo muku apartment a kusa da school din an kuma ajiye muku mota saboda zirga-zirga. Abinda ya rage miki shine koyan driving” shi ya koya min, ya ajiye duk harkokinsa yake zuwa yana dauka na muna fita koyon mota kuma cikin kankanin lokaci na iya sosai. Zamu yi ta hirar mu amma da zarar nayi masa maganar Saghir zai dauke wuta in ba hakuri na bayar da kuma to sai dai mu dawo gida ranar ba za’ayi koyon motar ba. 

Shi yayi min komai na harkar student’s visa, muka je Abuja ni da shi da Asma’u. A embassy na UK na hadu da Judith itama tana neman student’s visa, daga gaisawa naji yarinyar ta kwanta min muka yi ta hira har na fahimci scholarship ta samu daga program na African Initiative for Governance kuma session din karatun mu zai fara tare ne. Sai na roki Sadauki ya karbar mana visar tare da ita sannan kuma nace mata in mun hadu a can tazo mu zauna tare a apartment din mu.

Bayan everything ya zama set kuma sai na ji duk jikina yayi sanyi. Naji bana son rabuwa da gida, da Inna da Subay’a da Asma’u. Bana son rabuwa da Sadauki. Inna nasamu wadda har lokacin bata daina fushi dani ba akan kin auren Sadauki, nayi mata bayanin manufa ta akan hakan, na nuna mata nima bawai hakan naso ba sai dai hakan nake ganin shine dai dai, sai ta dan sauko, ta saka min albarka sannan tayi min nasiha a game da zaman da zanyi a can.

Ranar tafiya Sadauki ne yazo ya dauke ni muka tafi airport, su kuma yan rakiya ta suka biyo mu a mota daban. A hanya babu wanda yayi wa wani magana a cikin mu har muka je muka yi packing sai kuma muka ci gaba da zama a motar. Can ya juyo yana kallona yace “can you promise me something?” Nima ina kallonsa nace “what?” Sai kuma yayi shiru kamar ba zai yi magana ba sannan yace cikin rikakkiyar murya “zaki tafi jami’a, Oxford, akwai mutane da yawa a can, maza, and you are very beautiful am sure some of them will ……. God, bazan ma iya fadar kalmar ba” nayi murmushi nace “soyayya? I won’t. Nayi maka alkawarin Halima ta Aliyu ce. In ba Aliyu ba kuma to babu wani namiji a gaba na” yayi dan murmushi yace “Allah yasa ki rike alkawarin nan. Dan ni yanzu am not sure about you anymore. Tsoro nake ji. Gani nake anya kuwa zan iya wannan zaman jiran kar inje fa zuciyata ta buga” sai nayi dariya nace “tsoro da girmanka” ya juyo and for the first time ya kama hannuna a cikin nasa ya rike yana kallona yace “let’s play a little game da zai making everything easier for everyone. Let’s make a bet” na girgiza kaina nace “ni kasan bana son wadannan games din naka fa” yayi dariya yace “tsoro kike ji? Tsoro kike ji kar kiyi failing?” Nace “kaima kasan ko sanda muke games din bana faduwa” yace “yes, kina winning, saboda ina barin ki kiyi winning dan kar kiyi kuka” sai muka fara musun cewa ba barina yake ba ni nake winning da kaina sai yace 

“let’s do this one mu gani. Yanzu in muka rabu a airport din nan in kika sauka a UK, through out your stay har zuwa sanda zakuyi hutu in dai har kika dauki wayarki kika kirani da kanki then nayi winning and I got to decide whether or not zan saki Saghir. In kuma baki kira ni ba har kukayi hutu kika zo gida then kinyi winning kuma zanyi duk abinda kika ce”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button