NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 29

???? *WA ZAI FURTA?*????
              2⃣9⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

????????????????????  *RUKAYYA  BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*????????????.

    ******************
*ABUJA NIGERIA* 
    Suna Isa daddy ya ce maza Anwar yazo Yana son ganin sa…..
Su biyu a falo daddy bisa kujera Shi Yana zaune a kasa, yayi yayi ya hau kujera amma ya ce hakan yayi….. Ba karamin dadi yakeji ba irin Respect da kunyar Anwar din duk rawar kansa idan Yana gaban daddy bai iya ko kwakkwaran motsi.. 
… Abinda yasa na kiraka anan Ina son mu tattauna wasu maganganu, na farko akan kayan dakin bilkiyne, Anwar bisa ga Al’ada irin tamu ta hausawa kasan cewa duk diya da Kuma iyayenta suna son suga abinda suka saka ma yarta a gidan auren ta Amma Kai kace sammm baka da bukata, shine muka yi shawara zamu tura maka kudi a madadin kayan…
Na biyu, ta fada mun ka ce lefenta sai taje gidan ka, wannan tsari ya Mana dadi matuka….
Na karshe kuwa da zance shine, programs din da zakuyi tayi yawa ka mayar dashi party daya kwal! Kuyi Shi a jibi don in shaa Allah Ranar juma’a Zan dauketa da kaina in kaita daki bana son duk wadannan bidi’o’in…. Ya dago Kai da sauri ya kalli dadyn suna hada ido ya sunkuyar da sauri…. Yayi Yar dariya Kano zaka ajiyeta ko nan sannan ka hadani da mutum daya Wanda zai mun jagora don juma’ar bacin Kai da na fadawa mahaifiyar ta kadai tasan wannan tsarin nawa.
Ya Kara kasa da Kai yace toh…. A Kano zamu Fara Zama in shaa Allah.
…….madallah. Ina ga shikenan kana iya tafiya.
Ya Dan sosai keya Yana son magana Yana Jin nauyi…… Yaya akwai wata magana ne Anwar?
Ya danyi murmushi…. Ranar juma’a din da karfe nawa?……. Ka turon Wanda zai mun jagora gobe don in shaa Allah anan zanyi sallar juma’a bayan na dawo kaita……. Ya dankara kasa da Kai tare da zaro ido..
 Ya rusuna Allah ya Kara girma mun gode….ya Mike.

Ya kalleshi account number zaka bayar kenan?
Ya danyi murmushi ya koma ya zukunna, ayi mun aikin gafara daddy bazan karbi kudi ba, amma idan ko hankali bazai Sami natsuwa Kan hakan ba, to a turawa Bilkisu tunda daman ko kayan akayi mallakin ta ne fatana a Sanya Mana albarka a ciki addu’ar kadai ce zata fi duk wani kayan masarufi ko kudin quality…… Daddy ya kura mishi ido Yana jinjina tunani da hankali irin na Anwar.
  Yana tafiya suka Fara shirye shiryen hada party don cewar Anwar sai fa anyi.
  Abokan sa na kasashen waje duk sun iso masu kudin Nigeria kuwa abokan huldar sa wurin kasuwa kawai ake jonewa Amma duk wani sha’ani na yarinta da ‘ya’yan su Anwar keyi sune abokan…..Amma wannan bikin sun Alkawarin halartar partyn da za ayi a national conference Hall dake presidency a cikin Villa.
  An kayata wurin mawaka duk sun hallara hada yaron nan matashi Dan katsina Mai tashe Yanzu watau *Aliyu nata ( Aure martaba )*
    Iyaye da abokan arziki sun hallara wurin, dangi da duk wani Mai alaka da bikin kowa ya kure adaka…..
   An tsantsara ma Amarya kwalliya suna saman bene za a shirya ta aka shigo da wata matsiyacitar *Gown* maroon color *Innalillahi* bana iya describing rigar saboda rigace akalla idan zuwa zakayi shago ka siyo zata haura millions, duwatsun jikin rigar kansu diamond ne, musamman aka mishi ita special da wasu laces da materials Wanda ya ware don party kawai Amma Yanzu daya zata saka…..
Kilibabbu magulmata wadanda ba a rasa irin su a kowane dangi Baki yayi gummm, saboda suna ta korafin duk kudin Bushara bikin sa ba lefe…… sunfi awa shida wasu abokansa a waje cikin motoci suna jiran fitowar Amarya bayan shiga da rigar saboda ganin rigar yasa dole aka canza pattern na kwalliyar.
   Tunda ta Fara saukowa ake daukarta  hoto, gidan ya rikice,Yan sanda da sojoji gewaye da ita sunki yarda ma a rabeta…… Su mommy da kawayenta na babban falo ana fama da ita Kan zuwa wannan party Amma tace sammm baza ta je ba.
    Suna hango fitowar su ya fito mota dasauri…… Ya Sha farar shadda ta karshen karshe Yana isa duk aka dare kawai ya rungume ta…..wuri ya dauki ihu kanka yane cikin gyale sai da suka shiga mota ya daga Shi ya leka……. Ya tallabo fuskar…… tsarki ya tabbata ga mahaliccin Bilkisu….. Ya Kai bakin sa ga nata tayi saurin fadawa jikin sa ta na murmushi….. Ya danyi dariya…. Ke wallahi dadi na dake Yar garin mu ce, ya dagota ba da yawa zanyi ba please……ta Kara komawa jikinsa….. Ya kyalkyace da dariya kaiii  Ni Kuma tawa ta sameni daga ni kada ki batan Kaya da Jan Baki toh, nasan karamin aikin ki ne…… Yayi juyin duniya taki yarda ta dago don tasan halin sa tunda yace zaiyi kissing dinta sai fa yayi…..
  Ya Kama dariya ya rungume a sosai, ga son jiki ga Kuma tsoro sai a daga ni tunda ba’a son tukuici.
Yana shafa bayanta Yana magana a hankali wallahi nasan rigarnan dole ta Miki kyau. Tunda wasu suka ji labarinta an Fara damuna….. Ya dago ta da karfi Kuma sarkar nan ta hau kayan ko?
  Sosai, ta fada tana murmushi…. Wuf!  Yakai bakin sa ga nata sai kawai ta tafi jikin sit luuuuu tayi baya…….
   Tsayuwar motar yasa Shi sakinta a hankali, tayi kasa da Kai ya danyi dariya na shanye Jan baki ya kura Mata ido ta sunne Kai kawai……. Ya shafi gefen fuskar ta Yana murmushi *shy girl*
  Wuri ya dauku, Shi kansa bai taba tunanin ganin wasu mutanen ba Amma sun mishi surprise.
    Rike yake da hannunta suna tafiya a hankali Kota Ina Yan daukar hoto ne, abokan su na bakin kofa suna jiran isowar su.
 Kawayen Bilkisu sun Sha Anko na light pink lace da blue head sun hadu sun Gama haduwa abinda ga fresh and young graduates.
    Daga ciki wani sound na kidi ya Fara tashi kawai Anwar yaga Yan matan nan sun Fara rawa iri daya Nan da Nan wuri ya dauki ihu da sowa…… Rawa sukeyi ta birgewa Anwar nata dariya ya tallabo kugun Bilkisu ya Dan duka ya Mata rada hada chorography kuka hada haka?
Tayi murmushi kawai. Rawar sukeyi sosai har suka raka su mazauni Anwar na Zama ya janyo Bilkisu ta fada bisa cinyarsa lokacin da take kokarin Zama wurin ya Kara rikicewa……
   Yan matan suka ja layi tare da canza salon rawa hall din yayi tsit kidan kawai ke tashi an masu kuri da ido ba Wanda ke son ko kiftawa yayi kada ayi wani step din ba gani ba…….
  Wani juyi da sukayi kawai sai ga maza sun shigo cikin rawar , sadeeq, Suleiman, Anas, mustapha da su Joseph…… Wayyo Allah wuri ya Kara rikicewa da ihu ganin mazan sun dauki sabuwar tsarin rawar da Yan matan keyi suna juyi iri daya……ai sai turawan nan da sauran abokai da mutanen arziki suka Mike ana barin dollars.
 Anwar ya Kara kyalkyacewa da dariya ya Mata rada a kunne keda wa kuka tsara haka? It’s seems like you people are surprising me …… Ta danyi dariya tun a school suka fara practice…… Ke me yasa bakiyi ba?
Ta Kara dariya Kai ma ai baka rawa.
Inji waye? Yau Zan yi.
Tayi murmushi Nima zanyi anjima zamu sake wata….. Keda wa?
Nida su Helen……. Irin waccen?
Ta danyi dariya waccen tafi wannan kyau saboda mu shida kawai zamuyi ta…. Banda ni ko?
Ta Dan duke tana dariya ai baka yi rehearsal ba……. Ina menu na program din?
Ka fiye sauri gashi can ga Mc sai ma can wajen karshe zamuyi fa…… Can’t wait. Ya fada Yana kallonta yana murmushi……
Amma Suleiman ya birgeni Kuma yaban mamaki duk ustazancin sa yau Yana rawa haka?
  Ta Kara murmusawa ko a school anyi ta mamaki…….
  Ana gama rawar aka Fara gabatarwa, kaiii wurin an tara basawan Nigeria wani ma sunan sa kawai kakeji, su Aisha ne kirjin biki  ko Zama sun kasayi.
    Komai order akayi abinci ma musamman akwai masu bayarwa , basket ake ajiyewa mutum bisa table din sa komai a ciki. Duk abinda kake so akwai a basket din….
   A ka umurci Ango da Amarya su fito fili….. Masu wakokin kowa nayo gaba gaba….. Anwar ya ce a Bata *Aliyu nata* ya rera musu *Aure martaba*…… 
   Ai ana cewa rangwal….. Anwar ya Fara takawa Bilkisu da mutane aka Fara dariya….. Kafin kace kwabo fili ba masaka tsinke ana masu barin nairori …… Ya samu ya gewaya ya kamo hannun Bilkisu ya Mata rada “`Ke maza sunyi yawa muje ki zauna“` sai kawai ta Kama dariya…. Kishin Anwar yayi yawa ranar bikin nasu ma?.
Ya kaita har inda suke zaune sannan ya sauko ya dawo filin…… Nan da nan su sadeeq suka far mishi…… Ya Kama dariya suka Kama rawa…..
 *Nata* har tsalle yakeyi duk ya rikice ganin irin barin dollars din da akeyi.
      Bayan an gama ne aka Fara cin abinci.
  Bilkisu taga ice cream a table din su…. Ta kalleshi yayi dariya kowa abinda yake so ake bashi, Suma can duk basket din da Kika gani ba abinda babu ke kuwa ni nace akawo ice cream don nasan Shi kikafi kauna …… Ta danyi dariya.
Ya dauko katuwar robar ya bude ya Fara Bata a Baki ….. Kai Anwar karshene..
  Bayan an gama ciye ciyen, aka ce Amarya da kawayenta zasuyi rawa…… Anwar ya washe baki yau zanga rawar ki…… Ta kalleshi ta danyi murmushi kawai ta sauka….
  Ya kishingida bisa kujera ya Dora yatsa a Baki ya bita da kallo….
Ita ce gaba, Aisha da Na’ilatu nasir bayanta, sai Helen, maryam da chinyere a karshen layi duk sun canza Kaya sun kaso jeans dark blue da white t-shirt sai farin kambas da dark blue facing cap…….
A hankali kidan ya Fara tashi Bilkisun ta Fara wani moves suna kallonta kafin Suma su dauka ……. Wuri ya dau tafi da ihu ganin yanayin daukar rawar kanta….. Ga Na’ilatu daman da son rawa kawar Bilkisu ce ta cikin unguwa tun suna Yara. Mowa na son takawa amma Aure ya Mata katanga don tabbas da wurin ya Kara bada kala.
  Unex kuwa ai ita akwai kamewa tana can da kawayenta suna kallon kowa dai dai.
Alawiyya kuwa bayan kujeru ta tsaya tana murza kattan duwawukanta ana Mata nata barin dalolin daga gefe.
   Dariya kawai Anwar keyi , turawan nan kuwa duk sun rikice an Gama kashesu da salo.
   Wani juyi da sukayi cikin wata rawa ta duke Anwar bai San ya sauko ba ya balle rafar kudi. …. Wuri ya dauki ihu…gani Bilkisun ta canza salon rawa sun mayar dashi tsakiya suna wani takun….. So sai mutane suka karasa gigicewa kawai ya canyota da karfi ya rungume aka dauki ihu aka taso ana barin kudi……..
    Biki yayi biki…. Partyn ya bada kala…….live aka ringa nuna program din a tashoshin television na gida da waje…..
Sai Sha biyun dare aka gama….. Sai da suka tabbatar kowa ya tafi sannan suka shiga mota .
Ya janyo ta jikinsa, waye ya koya Miki rawa haka?
Ta danyi dariya….. Bude Baki kiyi mun magana ko Kuma na yakai hannun bayanta zai zuge Mata zip din Riga…… Ya hakuri jira inyi magana… Ya kyalkyace da dariya kaiii kin fiye tsoro.
   Daddy jiya ya aika da motoci na abinci na ce kada ya siyi komai Amma yaki yarda, Ni Ina da kamfanin shinkafa meye za a kai mun?
 Ni ke shigowa da Mai Ina da kamfunan man gyada Amma….. Duk da Haka ai al’ada ce….. Al’ada addini ce?
Ni yaban ke tsingirin gatarin ki na tafi abina….. Ta danyi dariya.
  Ya Kara matsawa kusa da ita ….. Ina son salo irin na daddy Bilkisu a gaskiya ya iya dattako da daukar ma Kai mutunci…. Ta ce hmmm kawai tare da Dan muskutawa don taja baya…. Ya Kara matsawa ya janyo ta ya Fara lalube…… Ta ce innalillahi na shiga….. Ke! Kin shiga ukun ko?
Ke Wai kin San shiga uku kuwa?
Ta soke kai… Ya Kai Baki wurin kunnen ta ya ce “`please in zuge zip?“`…. Ta ja baya da sauri….. Kayi meye?
Nidai don Allah ka rufan asiri. Ta fada kamar zata mishi kuka .
Ta Riga ta Kai karshe bakin kofa ….ya Kara matsowa Yana Yar dariya to Wai ke gobe ya zamuyi anya bazaki bani wahala ba?……. Ta kudundune Kai ta ce *Na bani* ya kyalkyace da dariya yace ikon Allah…. Motar ta tsaya. Ta say hannu zata bude ya kamota jira Mana saurin me kikeyi?
Anwar nidai Zan tafi gida Dan Allah….. Na Fara Baki tsoron ko?
Tayi shiru. Yayi dariya….. Ya tallabo fuskarta ke ko Yar karar Nan ki kawon gudummuwar tsumi Nasha ko?….. Ta zaro ido.
Ya kyalkyace da dariya, amma dai kin San nasan su waye sokotawa ko?….. Kai Ni ban Sha komai ba….. Ya Kai hannu zai kamota ta makale jikin kofa….. Karya kikeyi kinsha Mana Dan Allah an dafa Miki kaza?…… Na shiga uku ni Bilkisu…. Ya kyalkyace da dariya… Nidai Dan Allah ki dauri kici Kisha kinji ko?……. Naji sai da safe…. Ya janyo ta da karfi ta fada jikinsa yace …. Yawwa kin yarda kenan nasan Kuna ci.
Ohh yau ni tawa ta sameni ni Bilkisu…. Ya kyalkyace da dariya kina birgeni wallahi.
Ya Kai Baki a kuncinta Bari ko nan na Dan sumbata…… Ta runtse ido, ya Dan Kara tattabata yana fadin, ai nayi namijin kokari Bilkisu na ba da mamaki shekara daya ban komai ba …..Hana ai wallahi ko ban nema ba ya kamata gobe ki nemeni da kanki ko?  ya saketa…. Da sauri tabar motar yabita da dariya…..
  Gabanta sai faduwa yakeyi ita kawai tasan ta Gama mutuwa taje gidan sa. 
 Washe gari ko ita bata San inda zasuje da daddy ba don baya son fada Mata kada ta Tara mishi jama’a da kuka.
A airport ta kura mishi ido Amma yasha mur babu fuskar tambaya.
Koda ta shiga jirgi ta fahimci abinda ke Shirin faruwa sai kawai ta Fara kuka….. Ashe tun kwana biyu da suka wuce an kai duk Wanda zaiga gidanta ya gano.
  Tsinken ragin ta ya Kai daki……. Gidan ba kowa sai Mai gadi kadai, Shi kansa Anwar din bai sanar da kowa ba .
  Kuka take wiwi….gidan Yana daddy tsoro ya firgita ainun yasan waye Anwar Amma zahiri gidan ya tayar mishi da hankali Shi kansa ya tabbatar diyarsa ta Gama Dace duniya.
Ya Mata nasihohi masu shiga jiki ya janyo Mata ayoyi da hadisai, kannen ta duka biyun suna gefe suna Yan kwalla Yanzu gida ya koma sai su daddy kadai saboda su Daman London suke karatu basa Zama Nigeria sosai.
   Da zasu tafi ta rike su, ta na wani irin kuka.
Haka suka lallabata suka barta kwance bisa gado ji takeyi kamar zata mutu.
Anwar kuwa karfe Sha biyu ya Gama sallamar duk wasu Baki. Banda Aisha da Maryam saboda su daga Kano zai Sanya akai su gida.
Ana saukowa masallaci suka wuce Kano din .
   Gidan su makil da jama’a ana wani sabon bidirin.
  Kano ta Kai ta kawo unguwar ta cika makil……. Isowarshi yasa garin da unguwar Kara rikicewa….. Yayi ma Aunty Salma waya da Hajiya rukayya Bako da su zo su dauki Amarya a tafi da ita can cikin dangi…..
   Har lokacin Bata daina kuka ba, bayan ta shirya sun fito kawai ta hango su Aisha Nan ne zuciyar ta, ta Dan saki.
 Bai yarda ko da wasa ta ganshi ba…. Acan aka kaita inda Hajiya… Nan fa ta ringa ganin gata da tarairaya……karfe hudu su Aisha suka tafi ba tare da ta sani ba, ya masu Sha Tara ta arziki Maryam duk ta gigice hada kukanta.
Karfe takwas aka shirya wata kwarya kwaryan dinner wacce har taso tafi ta Abuja danginsa sun yi namijin kokari.
  Sai basarwa yakeyi, ita abun ma sai ya ringa Bata mamaki ganin bai waccen zakewar ko me yasa yake ma Yan Kano Isa da takama?.
Sha daya nayi yace a tashi haka dare yayi.
Suna fitowa ya shige mota da Amarya sukayi gida kawai……
   Hannunsa da nashi rike maimakon taga sunyi bangarenta Wanda aka kaita dazun sai taga yayi nashi da ita.
 Gabanta ya bada ras!
Suna shiga falon farko ya saki hannunta ya garkame kofa ya zare key ya kalleta muje sama ko?…………✍???????? 

Ayi hakuri da kadan jiya biki nayi na babban Abokina, aminina Kuma kanina sannan dan’uwana. Ayi masu fatan Alkhairi please.
*ibrahim and naja’atu*

*Zainab wowo ce kawar rukayya Bako danbatta ( Allah ya raya Miki sauda da Salma ya Sanya masu albarka amin*????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button