NOVELSUncategorized

DIYAM 65

7❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Sixty Five: The Unbreakable Love

Ta tsaya tana kallon sa for some seconds. Sai kuma tayi murmushi very brightly sannan tayi dariya, shima dariyar yayi and they laughed together sannan tace “thank you Bassam.
Nagode sosai” yace “no, thank you. Nine da godiya” wayarsa tayi kara ya dauko ta yana duba prayer alarm dinsa, lokacin magrib yayi. Suka mike a tare sannan suka jera suna tafiya suka bar garden din, taking their steps together kamar yadda suka shigo but unlike yadda suka shigo kowa rai a bace yanzu da zasu fita kowa a cikinsu murmushi yake yi. A bakin kofa ya tsaya yace “wait a minute, naji kince Umar Mustapha Abatcha, Umar Abatchan dana sani kike nufi ko kuma wani daban?” Tayi murmushi tace “shi din dai da ka sani, do you know him personally?” Ya girgiza kai yace “sunanshi dai na sani. But the son, ya taba zuwa gidan mu ones. Last year lokacin auren Ya Ameen Daddyn mu ya gayyaci father din sai bai samu damar zuwa ba but he sent the son to represent him. Ko gaisawa ba muyi ba amma zanso mu gaisa wata rana” Diyam tace “am sure shima zai so haduwa da kai” sai kuma tayi murmushi ta kara da “idan ya huce”.

Yayi murmushi yana kallonta yace “goodbye Halima” tayi murmushi tace “see you soon Sadiq”. Sai ta juya ta tafi shi kuma ya tsaya yana kallon bayanta, sai kuma yayi murmushi yana girgiza kansa yana tunanin irony din rayuwa. 


Duk wanda ya shigo rayuwarka da akwai dalilin shigowarsa, some enter your life to teach you a lesson, some to take lessons from you, some enter to help you and some to accept a help from you. Duk wanda ka hadu dashi to ya shigo rayuwar ka ne for a reason. Da akwai point din da zaka hadu da mutum akwai kuma point din da zaka rabu dashi bawai lallai dan bakwason juna ba sai dan role dinku to each other ya kare. The only person that will stay from start to finish in your life is YOU and YOU are the only person responsible for your happiness.

People are not perfect, nobody is, so if you truly love a person you just have to accept him/her the way s/he is, accept both the good and the bad sides of them and together you can bring out the best in each other.

Ya juya da sauri ya koma cikin hotel din sannan ya hau zuwa dakinsa. Yana zuwa ya fara gabatar da sallah sannan ya jawo jakarsa ya fara zuba kayansa a ciki. It is time for a change a rayuwarsa, Nigeria zai tafi ya gyara rayuwarsa but before that he have to pay a visit to his Aunt first, yasan haduwarsu ba zatayi masa dadi ba but dole yayi clearing mess din da yayi creating da kansa.

Diyam tana zuwa gida itama sallar ta gabatar sannan ta tsaya a gaban mudubi tana practicing yadda zata fuskanci Sadauki gobe. Tasan akwai battle a tsakanin su dan ta tabbatar da daurarriyar fuska zai sauko daga jirgi. Sai ta fara making faces a mudubi tana zabar wacce zata fi melting frozen heart dinsa. Ta gwada fuskar tausayi, ta gwada fuskar shagwaba ta kuma gwada serious face amma duk sai taga basu yi mata ba. Ta binciko kaya tana zaben wadanda zata saka saka suma kuma taga duk basu yi mata ba, ta tuna ranar nan a Kano da Murjanatu tayi mata kwalliya ya yaba sosai dan haka gobe ma zata saka ta tayi mata. And she is going to wear dogon hijab kamar yadda yake so. 

Ta ajiye kayan ta fita da sauri zuwa dakin Murjanatu, ta tarar da ita tana waya sai ta tsaya har ta gama sannan tace “Murjanatu Please zo ki taya ni zaben kayan da zan zaka” Murjanatu ta ajiye wayar tana kallonta, sai kuma tayi murmushi tace “kayan da zaki saka yaushe? Biki zaki je?” Diyam ta harare ta tace “kakan biki ba biki ba. Malama ni fa yayarki ce kuma am ordering you to do something for me” Murjanatu ta hade hannayenta tace “to babbar yaya tuba nake yi, tunda yaya na za’ayi wa kwalliya dole in tashi”. 

Haka sukayi spending the night preparing. Har takalmi da sarka sai da aka ware. Sannan suka yi plan din abincin da zasu dafa masa. Tuwo dai yafi so miyar yauki amma basu san inda zasu samo ingredients din ba dan haka Diyam ta yanke shawarar dafa masa farin couscous garnished with vegetables sannan kuma suyi masa farfesun kifi sai kuma suyi pepper meat. Drink tasan yana son kunun aya amma bata da aya dan haka zata yi masa banana smoothie.


Ta kira shi da niyyar tambayarsa sanda jirgin su zai sauka amma kamar yadda tayi tunani sai yaki picking, tayi masa text babu reply. Ta saka Murjanatu ta kira shi itama yaki dagawa duk sai taji babu dadi, shi wannan zuciyar tasa ce problem dinsa, yana da saurin hawa amma kuma yana da saurin saukowa dan haka ta shirya sauko dashi goben in yazo. 

Ta lura Murjanatu duk ta daga hankalinta sai ta zaunar da ita tace “kar ki wani damu kanki da fushinsa, zai sauko na gaya miki ki barni da shi kawai” Murjanatu tace “baki san halinsa ba, zai iya raba ni da makarantar nan fa wallahi. Akwai abinda ya taba yi min a gida Canada akan wani saurayi na an gaya masa bad abubuwa akan sa sai yace min kar in kara kula shi ni kuma na cigaba da kulashin. Ashe yasa a saka masa ido a kaina sai gashi an tura masa da videon mu tare a gurin cin abinci. Ba wani abin muke ba kawai muna hirar mu muna dariya. Akan haka ya karbe wayata kuma yayi grounding dina a gida for three months ko kofar gida bana fita. Papa da Mama kuma suka biye masa yanzu ma kuma nasan duk abinda yace biye masa zasuyi” Diyam tace “ba zai ce komai ba, ki barni dashi”.

Suka duba suka tabbatar suna da abubuwan da suke bukata, abinda basu da shi kuma sai sukayi order online da niyyar a kawo musu da sassafe. Sai kuma suka shiga website din airport suka duba flights schedules na gobe, anan suka ga time din da jirgi zai sauka from Nigeria. Sai yamma. Wannan yasa suka yi baccinsu sosai sannan suka tashi a tsakane suka yi komai tare har da Judith itama ta taya su, suka ci abincin su sannan suka yi wanka aka zauna kuma yin kwalliya a shafa wancan a goga wannan a ja wancan suna ta rigima har aka gama sannan aka yi dressing aka kuma bi da turare. Murjanatu ce ta dauko hijab da kanta ta bawa Diyam tace “gwara ki saka tun kafin yayi ball damu tun daga airport har gida”.

Tare suka tafi airport din a mota, suka bar Judith a gida tana gyara musu gidan. A hanya duk sukayi shiru kowa tana lissafe lissafen ta sannan Diyam tace “Murjanatu a tunanin ki ta yaya Aliyu yasan ina kula Bassam?” Murjanatu ta daga kafada tace “yaya Aliyu ne fa, ya iya bincike ta karkashin kasa I guess wani ya saka ya saka masa ido akan mu. The guy might have saw you two together and reported to him” Diyam tayi shiru tana tunani, she will have to talk to him about that, hakan kamar rashin yarda ne. Murjanatu ta katse mata tunanin ta ta hanyar cewa “there is nothing between the two of you, is there?” Diyam ta harare ta tace “in kina son shi just say so, sai in hada ku” Murjanatu ta tabe baki tace “bai yi min ba, he is definitely not my type. Daga ganin sa nasan lady’s man ne, Allah kadai yasan yawan yammatan sa” Diyam tayi dariya tace “wai dama kura tana iya cewa da kare maye? Ke ma Allah ne kadai yasan yawan samarinki” Murjanatu ta yi murmushi ta fara bata labarin new catch din da tayi a school last week.

Suna tsaye suna jira jirgin ya iso, Diyam tana ta jujjuya hannun ta feeling nervous dan bata san da wacce zai zo ba sannan kuma ga zuciyarta da take neman betraying dinta saboda dokan tuwa da tayi gurin son ganinsa after almost three months of not seeing him. And then suddenly sai idonta ya sauka a kansa, yayi kyau sosai fuskarsa tayi fes gashinsa na fulani da sajensa sun kwanta lufluf suna daukan ido. The freshness of his dark skin alone zai tabbatar maka da cewa he is taking good care of his body, yanayin takunsa kuma da posture dinsa sun nuna yawan ziyarar da yake kaiwa gym. Their eyes locked, and everything in her stopped except bugun zuciyarta da yayi doubling. He walk straight to gabanta ya tsaya one hand inside pocket, his expression unreadable yace “hello Madam”.


Ta bude baki zatayi magana amma sai taji duk rehearsal din da tayi na abinda zata ce masa ya gudu ya barta. Yayi mata kwarjini da yawa, and the fact that he called her madam have added to that. Sai ya dauke idonsa daga kanta ya mayar da dubansa kan Murjanatu da take kusa da ita tana mishi murmushin dole, suna hada ido tace “sannu da zuwa yaya, ya flight din?” “Fine” yace mata in short sannan ya zagaye su yayi hanyar fita, Murjanatu taja hannun Diyam da sauri suka bishi a baya. Suna fita suka ga cab tayi packing a gabansa Murjanatu tayi saurin cewa “ga mota munzo da ita fa” ya juyo yana kallon Diyam yace “thank you” sai ya shige suka ja suka barsu a wajen.

Murjanatu ta juyo tana kallon Diyam tace “you kept quiet, me yasa zaki yi shiru?” Diyam tace “he called me Madam. Kin san kuwa yadda nake jin haushi in yace min Madam?” Murjanatu tayi dariya tace “to menene na jin haushi? In yace miki Madam sai kice masa Sir, ba shi kenan ba? Now we have to follow him kuma” suka shiga mota suka bi bayan cab din data dauke shi but sai suka ga sunyi wata hanyar daban ba hanyar gidan su ba, Diyam zata yi magana Murjanatu tace “gidan Papa zashi. Inda muke sauka in munzo gari” sai Diyam ta juya kan motar suka yi hanyar gidansu. Murjanatu tace “ba binsa zamuyi ba?” Diyam tace “we cooked for him, dole kuma yaci abincin da muka dafa”.

Suna zuwa gidan Murjanatu ta shiga ta hado kan girkin da suka yi masa ta jera a babban basket sannan ta dawo motar suka kama hanyar wajen gari inda anan ne gidan yake. Suna packing Diyam ta tsaya tana kallon gidan a ranta tace “wow, da gaske dai Umar Mustapha Abatcha ne ya haifi Sadauki” ba mutane a gidan sai security daya bude musu gate suka shigo, amma komai na gidan tsaf yake daga alama ana zuwa aba gyaran gidan akan kari. Kofar da suka hango a bude suka dosa, suka shiga wani palo madaidaici Diyam tana iyakacin kokarinta na ganin bata yi kauyanci ba. A kan dining suka hango shi yana zaune yana kallon kofar da suka shigo. He kept his eyes on them har suka karaso Murjanatu ta ajiye basket din hannunta ta gaishe shi ya amsa tare da tambayarta karatu, sai kuma tace da Diyam bara taje ta dubo wani abu a cikin gidan. 

Sai data fita sannan Diyam ta dauke idonta daga kansa ta sauke kan wata baturiya sanye da apron da hular cooks tana ta jera abinci akan dining table din gabansa. Diyam ta tako ta karaso gurin tana kallon baturiyar tace “thank you, I will take it from here” sai matar ta juya tana kallon Sadauki shi kuma ya yi mata alamar ta tafi da hannunsa sai ta juya ta bar gurin. Diyam tabi bayanta da kallo tana jin haushinta ba tare da matar tayi mata komai ba. Sai kuma ta fara tattare abincin kan table din tana ajiyewa gefe sannan ta dauko basket din da suka shigo dashi ta dora akan table din ta fito da abincin ciki ta jejjera sannan ta jawo kujera kusa dashi ta zauna. Tunda ta fara yayi folding hannayensa yake kallonta har ta gama ta zauna sannan ta jawo plate gabanta tace “banyi maka tuwon da kake so ba saboda bani da kayan hadi. Amma nayi maka something da nake tunanin zaka so” still idonsa akanta yace “how is he” ta gane maganar da yake amma sai ta cigaba da hada abincin ta, carelessly tace “how is who?” Sai ta debo abincin a spoon ta kawo bakinsa tace “ha” and she saw his lips curved in a smile amma sai ya juya fuskarsa gefe kar ta gani sai ta sake bin bakinsa da spoon din tace “ha muga ni” sai ya langwabar da kai sannan a hankali ya bude mata bakin ta saka masa abincin a ciki sai ta zauna tana kallon sa with wide opened eyes shi kuma yana taunawa a hankali sannan tace “please tell me yayi dadi. I spent hours ina shirya maka abincin nan kamar yadda nayi spending hour ina yi maka kwalliya amma gashi nan ko yaba wa ba kayi ba” ta karashe maganar kamar zata yi kuka. 

A hankali yace “waye yace miki ban yaba ba?” Ta turo baki tace “you called me Madam, kuma kaki shiga mota ta” ya danyi murmushin daya tsaya a iyakacin idonsa yace “to ba Madam din bace ba ke?” Tace “I am not Madam, in ka kara gaya min kuma nima Sir zan ke ce maka” and his smile widen to his lips. Ta sake dauko wata lomar ta kuma cewa “ha” ya bude ta saka masa yana ci ya kuma cewa “how is he?” Ta gyara fuskarta zuwa serious one tace “kana magana akan Bassam ko?” Ya daga kafada yace “bansan sunansa ba and I don’t want to know” tace “he was fine as of yesterday, bansan ya yake yau ba. Kamar yadda bansan me yasa kake wani tunani akan sa ba. He is just my friend, department din mu daya muna lectures tare and he is a Nigerian” ya bata fuska yace “shi yasa kuke cin abinci tare?” 


Ta saka masa wata lomar a baki sannan tace “and how do you know that? Wani ka saka yake spying on me? Baka yarda dani ba?” Yace “babu wanda na saka yayi spying on you. Akwai mutumin da muka yi harkar admission da registration dinku tare. He saw your pictures then. A lokacin kuma na gaya masa ke matata ce then he saw you with that boy and thought ya kamata in sani. I told him bake bace ba cos I thought you would never do it sai ya tura min da picture of you two together” ta ajiye spoon din hannunta tana kallon yadda fuskarsa take nuna bacin rai, yace “do you like him?” Ta dafe kanta tace “I just told you, Bassam is my friend. Na bashi labarin ka ma na gaya masa zaka zo yau kuma har cewa yayi zai so ku hadu. There is nothing there. Please stop looking for something that isn’t there” she saw him relax a little yana kallonta yace “he is handsome” tace “really? Ni ban gani ba. He may be one of the thousands of stars in the sky amma ni duk bana ganinsu, only one star shines brightly a ido na, you. Kai kadai nake gani a matsayin mai kyau sauran duk dusudusu nake ganin su. You are the only star in my sky”. 

And he smiled. This time genuine smile yayi mata ya lumshe idonsa ya bude yace “I always remember that night duk sanda naga starry sky” ta sunkuyar da kanta kasa tace “me too”.

Sai ya saka dogayen fingers dinsa guda biyu ya dago fuskarta yana kallon cikin idonta yace “feed me” ta hadiye wani abu a makogwaron ta amma taji yaki tafiya, sai ta yi sauri ta dauke idonta daga cikin nasa ta dauki spoon with shaking hand ta cigaba da bashi abinci. Bai kuma magana ba sai ido daya tsare ta dasu har sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta bashi drink ya sha sai kuma yace “thank you, this is the best food I have tasted for a while. Ko kuma yadda aka bani abincin ne ya saka naji yafi kowanne dadi?” 

Sai kuma ta danji kunya ta rufe fuskarta da bakin hijab dinta, suddenly sai taji babu abinda take so irin ta kuma jin wannan kalmar daga bakinsa but as her husband yadda zata ji dadi fiye da na yanzu kuma ta samu lada mai yawa. 


Sai ta zame daga kujerar da take zaune ta durkusa a gabansa tana kallon yadda yake kallonta da mamaki tace “Aliyu Umar Abatcha. Will you do me the honor of marrying me?” 

Please, duk wanda Allah ya bawa ikon karanta wannan page din ina barar a karanta min surorin Falaq da Nas. Da niyyar Allah ya gina mana katangar tsari tsakanin mu da duk wanda yake neman mu da sharri, Allah kuma ya tabbatar mana da alkhairi tsakanin mu da duk mai neman mu da alkhairi. Allah yayi mana jagora kar ya barmu da iyawar mu dan mu ba zamu iya ba. Allah ya tabbatar mana da alkhairi a kasar mu baki daya.

Nagode

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button