NOVELSUncategorized

DIYAM 66

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Sixty Six: The Unbreakable Love 2

Naga adduoin ku, nagode sosai.

For two seconds ya zauna yana kallonta da tsantsar mamaki a fuskarsa sai kuma yayi sauri ya mike tsaye ya kamo hannayenta duk biyun ya mikar da ita tsaye yana kallonta tana murmushin ganin duk yadda
yabi ya rude sai yace cikin saurin murya “No! No”.

Ta bude ido da mamaki tace “no?” Sai ya saki hannunta da sauri ya dafe kansa yace “ba wannan no din ba, I mean no karki durkusa please, karki bata kayanki” ya fada yana ciwo hanky da sauri ya kama goge mata hijab dinta, sai daya dago sannan ta daga gira tace “so? Yes ne ko No?” Maimakon ya bata amsa sai ya dora goshinsa a kafadarta, tana jin yadda ya sauke wata nannauyar ajjiyar zuciya wadda tasa hawaye ya gangaro daga idon Diyam sannan yace can kasan makoshinsa “Yes Diyam. Of cause I will marry you. You have no idea how much I want to marry you” 

Murjanatu ta bude kofa ta shigo, sai kuma ta tsaya tana kallon su sannan tace “wrong room. Ba nan zan shigo ba” sai ta kalli kofa tace “Na’am!” Ta juyo tace “they are calling me so I gotta go” sai ta juya da sauri ta fita. Diyam tayi dariya tana share kwallar idonta tace “she is funny. Babu wanda yake kiranta” ya danyi dariyar da Diyam taji vibration dinta a kirjinta yace “kika sani ko aljanun gidan ne suke kiranta?” 

Ta dan matsa baya forcing him to raise his head from her shoulder. Sai ya kalle ta da idon da suka fara chanja color yace “yaushe kika chanja shawara kuma? What about Saghir? Kin fasa fitar dashi din?” Ta zauna a kujera tayi dagumi but fuskarta da murmushi tace “you won the bet, I can’t continue to deny myself freedom. Nayi kokari ai ko?” Ta fada da sanyin murya. Ya zauna opposite dinta yace “Subay’a fa?” Tace “in muka yi aure Subay’a ta zama yarka. And I trust you will do everything in your power to make your daughter happy” ya gyada kai yace “you bet. She is going to be the happiest girl ever”.

Matar dazu ce ta shigo ta fara gyaran dining table sannan ta zo gurin su tana tambayar Sadauki in akwai abinda yake bukata in babu tana son tafiya. Ya sallameta ta tafi ya juyo yana kallon Diyam da take bin bayan matar da harara yayi murmushi yace “what?” Tace “fire her. Ita da wannan secretary din taka ta Kano” ya bude ido da mamaki yace “why?” Ta turo baki “ni bana son su” yayi dariya yana shafa kansa yace “and you accuse me of being heartless” ta bude hannu tace “sai ka basu wani aikin ai. Kai kuma ka samu maza suke yi maka irin wadannan aiyukan” yayi tagumi da hannu daya yana kallonta yace “yarinyar nan anya kuwa Baffa bada A’isha yayi miki huduba ba? Kishinki yayi yawa. Yanzu suna min aiki kince ba kya so, so tell me idan kuma kika gan mu tare muna cin abinci a cafeteria mai zaki yi? Hmm?” Ta gane inda ya dosa sai tayi saurin cewa “kayi hakuri, an gama ba za’a kuma sakewa ba” bai ce komai ba sai kallonta da yake tayi fuskarsa da murmushi. Ta jawo fuskar hijab dinta ta rufe fuskarta tace “ni kunya kake saka ni in kana kallona” sai ya koma ya jingina a jikin kujerar yace “kinsan tunanin me nake yi?” Ta bude fuskar ta tace “no” yace “tunani nake yi in koma airport a yau in koma Nigeria, gobe inga Kawu Isa jibi a daura mana aure in dawo gurin amaryata a jibin” tayi saurin mayar da fuskarta ta rufe tace “kai dan Allah. Ka dai bani lokaci in shirya dai ko?” Yace “wacce shiryawa kuma? Nasan a gida zasu ce zasu shirya wani abu amma koma menene sai dai su jira sai bayan na tare da amarya ta” sai ta mike da sauri tayi hanyar waje tana hada hanya tace “sai dai ka tare kai kadai” ya biyo bayanta yana cewa “dama ai ni kadai nake tarewa ta kullum on my empty cold bed, it is about time I get some warmth” ta karasa kofar da sauri tana hoping ba irin ta office dinsa bace ba. Tana murdawa taji ta bude ta fita tana raba idon inda zata hango Murjanatu, sai gashi nan ya fito shima ya rufe kofar ya jingina da jikin kofar ya harde hannayensa da kafafuwansa yace “run run little girl. Duk inda zaki je you will come back here” ya fada yana nuna kirjinsa yace “cos that’s where you belong. A heart belongs to the chest”.

Ta juya suka hada ido, feeling like yau ta fara ganin sa. She couldn’t help but look at chest din daya nuna, very broad and very strong, sai taji babu abinda take so irin ta jita a gurin feeling the warmth and the strength that she so much miss. Ta hadiye wani abu tare da saurin girgiza kanta a kokarin ta na goge image din daga kanta tace masa “uhmmm. Lokacin Sallah. Murjanatu” yayi mata murmushin gefen baki sai ya nuna mata wata kofa da hannu” ta juya da sauri ta tafi can. Sai data bude kofar ta shiga sannan ta rufo kofar ta jingina da jikinta ta yi ajjiyar zuciya. Sai kuma tayi murmushi tana girgiza kanta. 

Daga gefenta taji ance “hmmm. Wato da can anaso ana kaiwa kasuwa akeyi ko?” Ta juyo ta harari Murjanatu tace “ke nifa yayarki ce, bana son rashin kunya”. Anan tare sukayi sallah tare sannan suka fita Murjanatu tana zagayawa da ita gidan Diyam tana ta kashe kwarkwatar idonta. Komai na gidan abin kallo ne, exact lissafin da Diyam take yi na abinda ake cewa aljannar duniya. Suna cikin zagayen suka hadu dashi, yace da Murjanatu “thank you Fanna, zaki iya komawa daki” ta turo baki tana buga kafa amma yana yi mata wani kallo ta juya ta koma. Diyam tace “kai kuwa ka barta mana mu karasa” yace “a gabanta zanyi hira dake? Kina sone ma ta raina ni kenan” suka jera suka cigaba da tafiya tare, but ba kallon gida sukeyi ba hirar su kawai suke yi suna jin dadin iskar da take kadasu. 

Ta rungume hannunta tana jin sanyi amma bata son nunawa dan tana jin dadin hirar da yake yi mata, sai ya cire top dinsa ya saka mata, ya cigaba da bata labarin irin yadda ya yi ta kokarin ganin ta kira shi dan yayi wining amma taki. Yace “har halucination fa nake yi. In wani ya kira ni sai inga kamar ke. It was hectic. I almost lost it” tayi murmushi tace “kasan me? Wani lokacin sawa nake Murjanatu ta saka min kai a handsfree” ta fada tana rufe fuskarta, yace “laaa ila, that was cheating” ta bude fuskarta tana hararar sa tace “har zaka yi maganar cheating?” Yayi dariya yace “bature yace ‘nothing is fair in love and war”.

A lokacin suka kai karshen gidan sai suka juyo suna retracing steps dinsu sai yace “sanda zaku taho Papa cewa yayi ku zauna a nan gidan, but sai na nuna masa cewa yayi nisa zaku ke shan wahalar transportation. But ni personally ba wai dan haka na samo muku wancan gidan ba, ni a ganina you are my responsibility kuma nan ba gida na bane ba bana son matar gidan ko sauran siblings dina suzo gidan suyi miki wani kallo, gwara can nawa ne babu mai daga miki kai” tayi murmushi tace “bansan sauran ba amma Murjanatu tana da kirki sosai” ya gyada kai yace “tana da kirki, suma duk basu da problem amma hausawa sunce maganin kar ayi kar a fara”.

Sai da sukayi sallar isha sannan suka bar gidan. Zuciyoyin su tas kamar takarda. Suna zuwa gida sukayi wanka suka yi shirin kwanciya saboda duk sun gaji. Diyam ta kwanta tana bitar maganganun su da Sadauki. Yes, ta karbi shawarar Bassam, Sadauki baya son tana maganar Saghir dan haka ta daina amma bawai ta bar maganar bane ba, zata jira taga if he will come around and do the right thing da kansa.

Watarta tayi kara ta dauka tana murmushi. Bai gaji da hirar ba kenan. Ta dauka da sallama yace “so nake in taho nan kin yarda?” Tace “nan kuma? Me zaka yi anan din?” Yace “hira zan yi miki kadai” tace “to kayi min a wayar mana, ai ina jinka a haka” yace “nafi son inke ganin ki as ina miki maganar. Nafi son in yi miki joke kiyi min murmushi in gani. Nafi son in tsokane ki ki harare ni in gani. Nafi son in fada miki sweet sweet words inga kin rufe fuskarki kina jin kunyata” sai taja abin rufa ta rufe fuskarta. Tace “ni dai kar kazo zuwa zakayi kayi ta sakani jin kunya” sai kuma tace “amma bada gaske kake ba zancen daurin aure jibi ba ko?” Yace “in da zan samu yadda nake so da ko gobe nema ina so. But nasan ba zan samu ba, Papa zai ce abokansa da sauran mutanen sa, Mama zata ce zasuyi biki, and you, I want you to have all the wedding things da baki samu ba ada. So, I will wait. Kinsan ni am a patient bird. Yanzu ki gaya min duk abubuwan da kike so for the wedding” ta lumshe ido tana tunanin childhood dreams dinta, but those are only dreams kuma yanzu sun zama past, dan haka tace “ni bana son komai fa. Sai dai ko in kai kana son wani abu” yace “ni ke nake so. I want only you, and that’s the only thing that matters” taji ta tamkar tana narkewa tana shigewa cikin katifar da take kwance. Is it possible to love someone this much? 

Suka cigaba da hirarsu mai ratsa zuciya, tana bashi labarin makaranta da yadda tayi adapting, shima yana bata labarin lokacin da yake tasa makarantar. She told him about Bassam abinda ya hada su da yadda rayuwar su ta kasance tare but sai taki gaya masa cewa Bassam ya fara sonta. She told him yace ya taba ganinsa yaje daurin auren brother dinsa. Sai a lokacin yace “Abuja? Last year you said?” Tace “eh” ya danyi tunani yace “naje daurin auren gidan sarki. Maybe can yake”. Sai da yaji alamar ta fara jin bacci sannan yace “kiyi addu’a ki rufe idonki. I will talk to you sai kinyi bacci saboda ina son kiyi mafarki na” 

Took my hand, Touched my heart, Held me close. You were always there, By my side. Night and day, Through it all. Baby, come what may.
Swept away on a wave of emotion, Oh, we’re caught in the eye of the storm. And whenever you smile, I can hardly believe that you’re mine, Believe that you’re mine.
This love is unbreakable. It’s unmistakable. And each time I look in your eyes, I know why.This love is untouchable. A feeling my heart just can’t deny. Each time I look in your eyes, Oh, baby, I know why This love is unbreakable.
Shared the laughter, Shared the tears. We both know We’ll go on from here. ‘Cause together we are strong. In my arms: That’s where you belong.
I’ve been touched by the hands of an angel. I’ve been blessed by the power of love. And whenever you smile, I can hardly believe that you’re mine.
This love is unbreakable. Through fire and flame. When all this is over, Our love still remains.
This love is unbreakable. (Lyrics by Westlife)
Washegari Sunday, Diyam tayi baccin safenta sosai sannan ta tashi. Tana mikewa ta jawo wayarta ta tura masa message cewa tana gayyatarsa breakfast. Ta fita ta tarar duk su Murjanatu suma babu wanda ya tashi dan haka ta zarce kitchen ta fara shirya abinci. Tana cikin aikin Judith ta shigo suka cigaba tare har suka kammala sannan ta tafi ta tashi Murjanatu ita kuma ta shiga tayi wanka ta shirya sannan suka fito kusan a tare da Murjanatu. A palo suka hadu suka baje kayan breakfast suna yi sai gashi ya shigo. Suka gaishe shi gaba-daya ya amsa da sakakkiyar fuska tana bude warmers din gurin. “Me aka shirya mana ne?” Murjanatu ta tashi tana serving dinsa yayinda Judith tayi musu sallama ta fita. Ya jingina da kujera yana shan tea yana kallon Diyam yace “kin yi kyau sosai” ta sunkuyar da kanta tace “thank you”.

Ranar wuni sukayi tare, ya dauke su a motar Diyam suka fita yawon zaga gari. Sai dare suka gama suka dawo gida ya ajiye su shi kuma ya tafi da motar. A daren Diyam ta kira Inna dan rabon da suyi waya tun sanda ta kira ta suna tare da Bassam. Inna ta dauka suka gaisa suka kuma gaisa da Asma’u da Subay’a. Sannan Inna ta karba tace mata “ya bakon naku?” Diyam tace “lafiya lau Inna” Inna tace “ya gaya miki abinda yayi? Naji bakiyi mana magana ba” Diyam taji gabanta ya fadi, me kuma yayi? Sai ta dake tace “me yayi kuma Inna? Ni bai gaya min komai ba” Inna tace “nasan dama bai gaya miki ba, na dauka zai gaya miki yanzu da yazo. Ya kwashe dabbobin nan daga gidan Alhaji Babba ya mayar dasu bayan gari tun kusan sati biyu da suka wuce. An buge katangar tsakiyar gidan Alhaji yace ya bar masa gurin kyauta”.

Ga breakfast, ayi enjoying tare da oga.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button