NOVELSUncategorized

DIYAM 64

A Little Advise

Na dan tsaya ina kallonsa ina assessing maganarsa, yana
kallona with a broad smile a fuskarsa, na dauke kai ina
lissafi, yes it will make everything easy amma anya zan

iya kuwa? Not talking to him for months bayan a yanzu
bana iya kwana daya ba tare dana yi magana dashi ba?
But the result is really worth it, amma kuma in na fadi fa?
In na kira shi fa?.
Na sake kallonsa naga har yanzu ni yake kallo yana
murmushi with an unreadable expression a fuskarsa. Na
girgiza kaina, it is too risky gaskiya. Sai ya langwabe kai
gefe kamar abin tausayi, yana robbing palm dinsa a nawa
yace “Please Diyam, shekara biyar tayi yawa. Ba kya
tausayina wai ke?” Nayi saurin zare hannuna daga nasa
ina yarfarwa kamar wadda wuta ta kona saboda wani
blood rush da naji ya taso daga hannun nawa cikin
seconds ya zagaye duk jikina. Cikin sarkewar murya nace
“okay, okay. Na yarda. It is a deal” ya lumshe idonsa ya
bude yana kallon yadda nake yarfe hannuna sai ya miko
min nasa hannun yace “let’s shake on that” na boye nawa
hannun a cikin hijab dina nace “nace na yarda ai, no need
to shake kuma” ya daga gira yace “tsoro kike ji?” Sai na
dauki handbag dina nace masa “goodbye Aliyu” yayi
murmushi yace “till we meet again Halima”.
Na fita da sauri daga motar ina harhada hanya, but I felt
as if gangar jikina ce ta fito ta bar zuciyata a cikin motar.
Nayi kokarin calming down kafin in karasa inda Asma’u
take jirana rike da sobbing Subay’a. Na durkusa na
rungume ta ina jin tafiyar duk ta fita daga zuciyata,
tausayinta naje ji sosai zata zauna without uwa da uba
kuma bayan duk suna raye. Sai da muka je bakin
departure hall sannan na juya na kalli inda motar Sadauki
take, har yanzu yana nan a zaune, bana iya hangoshi
amma ina hango duhunsa. A smiled at him, waved my
hand sannan na shige.
Murjanatu ce ta tare ni a airport a Oxford. Muka tafi gida
tare da ita, sannan washegari ita ta fara kaini school duk
da dai itama bakuwar ce amma kasancewar ta fini
wayewa da sanin kan al’amurra sai ya kasance ita tayi
guiding dina har na kammala duk abinda ake bukata cikin
nasara. I tot about Sadauki alot, tun a jirgi nake nadamar
taking wannan bet din nasa but what is done has already
been done, sai kuma naja damarar ganin cewa nayi
winning dan mu samu nutsuwa gabaki daya ni dashi.
Nasan shima burinsa shine yaci, kuma yana ganin kamar
zaici din saboda yana ganin rauni na, and I decided to
show him am strong. At first abin da wahala, musamman
in naga kiransa ya shigo sai inji kamar in dauka amma
nasan halinsa in na dauka zai iya cewa duk is part of the
deal dan haka kiran nasa ma bana dauka. And it really
hurts. Kullum babu fashi zai kira ni first thing in the
morning, sannan ina dawowa daga school zai sake kira
sai dai in naki dauka ya kira Murjanatu ya tambaye ta
lafiyar mu ko kuma in muna bukatar wani abu. Kudi kuwa
kamar ruwa haka ya sakar mana su, ina so in masa
complain ince kudin sunyi yawa amma ina tsoron kar yace
yayi winning.
Most of the times in suna waya da Murjanatu sai in yi ta
straining kunnena wai dan in jiyo muryarsa, wani lokacin
kuma shi da kansa zai ce ta saka a handsfree yayi ta yi
min magana amma sai in ki yin maganar duk a tsoron kar
yace yayi winning “please Diyam, please, please kiyi min
magana” amma na daure na cije na cigaba da ignoring
dinsa hoping wannan ta zama karshen wahala ta. Gani
nake yi taimaka wa Saghir da nake so yayi shine zai gyara
image dinsa a gurin family dina, kuma ina hopping hakan
ya zamanto sanadiyyar daidaituwar al’amura a cikin family
din. And Subay’a. Ina so in aure na ya kasance Sadauki
Subay’a ta rike shi a matsayin uba ba wai matsayin enemy
ba, wannan shine zai tabbatar da zaman lafiya a tsakani
na da shi. Sannan taimaka Saghir zaiyi softening heart
dinsa ya zamanto mai yafiya ga wanda ya munana masa
sannan mai tausayi ga na kasa dashi, wannan kuma zai
kara kusantashi da mahaliccin mu. Dan haka ni a ganina
duk abinda nake yi ina yinsa ne domin Sadauki.
And then he tricked me into calling him and also found
out about Bassam. And now he is angry. Nasan kishi
yakeyi dan nasan yana da kishi sosai, ni kuma har cikin
zuciyata ba wai ina kula Bassam bane saboda wata alaka
ta soyayya, na fara kula shi saboda in goge haushina da
yake ji, and we became friends, sai kuma na lura cewa shi
Bassam din ya fara developing feelings for me wannan shi
yasa nayi deciding in yanke alakar mu tun kafin abin yayi
nisa but the decision was made late, dan already Sadauki
yasan maganar Bassam ba kuma na son yazo yayi wani
abinda ba dai dai ba. Ban kashe wata wutar ba bana son a
kunno min wata.
Wannan ne yasa na yanke shawarar bawa Bassam labari
ne dan ya fahimci dalilin yanke alaka ta dashi, dan yasan
waye Sadauki da kuma alaka ta dashi, sannan kuma ina
hoping labari na zai taimaka masa wajen solving family
issue dinsa kuma maybe zai iya bani shawarar yadda zan
bullowa crises din Sadauki da Saghir.
(Now, some people need to re-read episodes 1-10. Diyam
is in love with wanda yake kiranta. Kuma ba labari take
bawa Bassam ba, she is going over the story a kanta
kafin ta bashi. Lol)
Bassam yace “ina jinki. Ina so inji labarin naki” ta dauke
idonta daga kallon ruwan da yake tsiri a fountain, sai ta
samu kanta da yin murmushi ganin yadda ya nutsu yana
kallonta, tace “ba labari ne mai dadi sosai ba, and get
your hanky ready cos you might cry at some point” yayi
murmushi amma baice komai ba sai ta bashi labarin ta in
summary, asalinta, soyayyar su da Sadauki, mutuwar su
Baffa, aurenta da Saghir da yadda sukayi rayuwar auren
tsahon shekaru, dawowar Sadauki cikin rayuwarta da
kuma mutuwar aurenta ta farko data biyu. Ta bashi labarin
a takaice but without missing all the main points da zasu
saka ya gane manufarta sosai. Sai kuma ta gaya masa
winning din da Sadauki yayi da kuma text din da yayi mata
dazu akan Bassam din. Tana bashi labarin yana yi mata
tambayoyi a gurin
Baiyi kukan ba kamar yadda ta tsokane shi da, amma
idonsa yayi ja fuskarsa ta nuna bacin ransa akan abinda
ya faru da ita, abinda bai taba tsammanin yana faruwa a
kasar sa har a yanzu ba. Ya kuma jinjinawa jarumtarta dan
he can’t even imagine a girl of 14 years going through
what she went through.
But his heart breaks daya fahimci karfin soyayyar da take
tsakanin ta da Sadauki. Yes, da gaske ya fara jinta a
zuciyarsa har yana hoping alakarsu will lead to something
da zai fitar da khausar daga zuciyarsa. But daga labarin ta
ya fahimci cewa cigaba da rike soyayyar ta a ransa will be
a wrong move. She is already in love, deeply in love with
someone else, just like Khausar.
Ta katse masa tunanin sa ta hanyar cewa “ina fatan ka
fahimci duk abinda nake so ka fahimta” ya gyada kai yace
“na gane, sosai. Kuma bana jin da akwai wata kalma da
zan iya furta miki wadda zata nuna how sorry I am akan
abinda kika yi passing through a rayuwarki. It was
unfortunate. Kuma bazan iya misalta miki how happy and
how important I feel right now da har kika zaunar dani
kika bani wannan labarin. Naji dadi sosai, na karu sosai,
nayi wa rayuwa kallon da ada ban taba yi mata irinsa ba”
tace “thank you, thank you for understanding Bassam” ya
sake murmushi yace “nine da godiya, you have no idea
how this is going to change my life. My family, I have
been taking them for granted duk da irin kauna da kulawar
da suka yi kokarin gina min rayuwata a kai, a lokacin dani
nayi watsi da supportive family dina nayi kokarin rusa
zumuncin dake tsakanin mu saboda budurwar da bama ta
sona a lokacin ke kuma kike against mutumin da ya ke
miki soyayya ta gaskiya irin aliyu saboda family din da
suka yi everything possible dan ganin sun rusa rayuwar ki.
You truly are an angel. I now understand the real value of
my family, kuma zanyi iyakacin kokari na inga na gyara
kuskure na. And like you said, story dinki ya kara nuna
min ma’anar true love, it is not feelings like I said. It is
much more than that, true love means sacrifice. Kayi
sacrificing happiness dinka dan wanda kake so yaji dadi,
ka sa farin cikin wanda kake so a sama da naka. Na koyi
wannan daga Aliyun ki kuma nima zanyi applying dinsa a
case dina da khausar, ina sonta dan haka zan dora
happiness dinta a saman nawa, happiness dinta kuma
shine kasancewa tare da wanda take so. Am going to let
them be, and hope to find my one true love nima
watarana”.
Tayi murmushi tana jin tausayinsa a ranta, tasan so tasan
zafinsa dan haka tasan decision din nasa is not an easy
one. But it is for the best.
Tayi ajjiyar zuciya tare da gyara zamanta tace “to saura ni.
Ina so inji menene view dinka a game da sharadin dana
kafawa Sadauki” ya girgiza kai yace “ni a fahimta ta, daga
ke har Aliyu kuna kan gaskiyar kune, dan haka sharadin da
kika kafa masa from your point of view dai dai ne. But
where you are wrong is on the approach, hanyar da kike bi
wajen ganin yayi abinda kike so ne ba tayi dai dai ba. Mu
maza a yadda Allah ya halicce mu shine bama son ake
directing din mu, do this, do that. Wannan hikima ce ta
ubangiji sai ya saka mu as heads of the family mata kuma
yace kuyi submitting to us. Amma inda hikimar take shine
indai mace tabi namiji sau da kafa yi nayi bari na bari to
zata juya shi ba tare da shi yasan tana juya shi din ba.
Musamman ace idan yana sonta. Duk mijin da zaki ji ance
mijin tace to shi bai san ma yana yin abinda mutane suke
tsegumin ba. Irin son da Aliyu yake miki if you submit to
him ba fito da Saghir kadai ba, in yana da dama zai iya
fito da duk mutanen prison for you”.
Ta jinjina maganar sa, Mama ta taba fada mata something
similar to this, tace in ta nuna wa Sadauki soyayya zaiyi
duk abinda tace but ita a ganinta ai tayi ta fada masa
tana maimaita masa cewa tana sonsa kuma gashi nan
har yanzu baiyi abinda take so din ba. Sai tace “yanzu me
kake ganin ya kamata inyi?” Ya daga kafada yace “Marry
him. Aurensa kawai zakiyi to make him feel loved,
pamper him, take good care of him, ki tabbatar masa da
cewa you are his and his alone kuma ki daina o da
mentioning sunan Saghir then shi da kansa zai dubi
yarinyar da take tsakani ya sake shi ba tare da kin furta
hakan ba”.
Ayi hakuri da wannan. A kuma yi hakuri da jina shiru
kwana biyu, abubuwa ne suka cushe min but insha Allah
in komai ya warware za’a cigaba da jina akan kari.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button