NOVELSUncategorized

DIYAM 75

DIYAM Chapter 75

Diyam bata samu shiryawa ba har sai data ji horn din
mota a waje, sannan ta ruga daki da gudu tayi refreshing.
Tana cikin saka kaya Murjanatu ta shigo dakin tana kallon

ta tace “wai sai yanzu kike shiryawa?” Diyam tace “da
wannan complain din da kike yi dama jakar da zan tafi da
ita kika dauko min a closet. Na riga na hada kayan da
zanyi amfani dasu tun a gida” Murjanatu ta shiga ta fito
da karamar jaka a hannun ta, lokacin Diyam har ya dauko
hijab dinta tana checking contents din handbag dinta
sannan ta kara abinda zata kara tayi zipping dinta ta
rataya. Suna saukowa Murjanatu tace “baku da abinci a
gidan nan? Ki zubo min dan Allah ko a mota ne sai inci
yunwa nake ji” Diyam tace “nima yunwar nake ji, in kin
samu nima ina so”.
A waje Sadauki ne a tsaye tare da Al-mustapha wanda
yake cousin din su Sadauki kuma daya daga cikin
maneman Murjanatu suna magana, ya dora jallabiya akan
shorts din dake jikinsa. Su Diyam suna fitowa Al-mustapha
yazo ya karbi jakar hannun Murjanatu ya je ya saka a
mota, Murjanatu tana kallon Sadauki tayi wa Diyam rada
tace “baiwar Allah me kika yiwa yaya na? Na ga ya zama
fari cikin dare daya. Ko dai man bleaching kika shafa
masa?” Diyam tana dariya tace “kakan bleaching ba
bleaching ba” amma ita ma sai ta lura fatar Sadaukin tayi
haske sosai, wani annuri a kwance a fuskarsa and he
seems kamar ya kasa daina murmushi.
Al-mustapha ya dawo suka gaisa da Diyam yana kallon
Sadauki, Sadauki ya lura tsokanar sa yake son yi sai yace
“to ya isa haka, shiga mota” ya nuna Murjanatu yace
“kema shiga, ko a gaban ku zanyi sallama da mata ta?”
Almustapha yace “kaji masu mata, muma dai mun kusa
zuwa gurin” Sadauki yace “kun kusa, amma baku zo ba.
Ka bari sai kazo gurin sannan sai kazo mu jera, amma
yanzu kana baya na” duk suka yi dariya, sannan su biyun
suka shiga mota.
Ya karaso gaban Diyam yana kallon ta, kanta a kasa tana
wasa da fingers dinta, sai ya mika hannu ya kama nata,
tace “zamu tafi” yace “Allah ya kiyaye hanya. I will be on
the next flight insha Allah. Take care of yourself for me
kinji? Sai nazo anjima” tayi murmushi tana gyada kai, sai
kuma tayi ɗage on her toes tayi kissing beard dinsa. Ya
bude mata kofa, ta shiga sannan ya gyara mata hijab
dinta ya manna mata kiss a palm dinta sannan ya rufe
mata kofa.
Suna jan mota Murjanatu tace “I will pretend kamar banga
komai ba” Diyam ta harare ta tace “to ai dama babu
abinda kika gani yarinya. Ni yunwa nake ji wallahi”. Suna
zuwa airport suka wuce VIP lounge. A can suka tarar dasu
Mama already har sun isa, sai a nan Diyam ta samu tayi
breakfast kafin su tafi. A lokacin ne kuma ta yi studying
maman su Murjanatu sosai, sai ta ga cewa akwai tsantsar
ilimi da wayewa a tare da ita wanda Diyam ta fahimci
cewa shine dalilin da yasa bata daukan Sadauki a
matsayin abin ki sai dai abin so, dan jahilci da rashin aikin
yi suna playing role sosai akan wadannan abubuwa.
Kafin 11 na safe sun sauka a Maiduguri. Tun daga yadda
akayi musu a airport, tun daga motocin da Diyam taga
sun zo daukan su harda motar security, Diyam ta kara
tabbatar wa lallai ɗan Umar Mustapha Abatcha ta aura.
Gidan da suka je kuwa ba gida bane ba, Diyam ta fahimci
kamar wani estate ne amma family estate mai dauke da
gidajen kakanni, iyaye da ya’ya. Gidan baban Sadauki a
ciki yake, uncles uncles dinsa duk suna ciki, da kuma
cousins dinsa da sukayi aure. Ko wanne gida ka gani a
cikin estate din abin kallo ne, amma babban abin kallon
shine gidan Umar Abatcha, tsarin gidan, motocin da suke
gidan, kayan alatun da aka kawata gidan dasu, su suka
saka Diyam ta fahimci dalilin da yasa Sadauki baya jin fitar
kudi daga aljihunsa dan akwai su din.
Yadda ake tayi mata ya saka take ta jin kunya, abincin da
aka sauke su dashi ma takasa ci sai da Murjanatu ta ja ta
suka tafi part dinsu su yammatan gidan wanda shi a kansa
ma gida guda ne. Murjanatu tana ta tsokanar ta “wallahi in
kika ce kunya zaki ringa ji ko? To wallahi a gidan nan sai
an kusa mayar dake tababbiya” Diyam tayi murmushi,
amma ita tasan ba zata iya cire kunya daga ranta ba
kamar yadda ba zata iya cire jini daga jijiyoyin ta ba.
Anan ta samu taci abinci sosai tare da sauran yammatan,
sai kuma duk suka yi wanka har ita suka fara shiryawa, ta
jawo jakar kayanta zata saka sai Sa’adatu tace “Mama fa
ta bayar anyi miki dinkin da zaki saka yau, sai dai ki gwada
abinda baiyi ba aje yanzu ayi miki adjusting” Diyam tayi
godiya, amma kuma ta so saka nata kayan data tanada
musamman saboda yau din sai dai kuma hausawa sunce
yaba kyauta tukuici, in bata saka kayan ba Mama ba zata
ji dadi ba. Dan haka sai ta yanke shawarar zata saka yanzu
in yaso in an jima sai ta saka nata. Aka kawo mata kayan
ta saka, komai yayi mata sai hips ne da za’a dan buda
mata. Nan take Sa’adatu tayi waya aka zo aka karba
kuma suna cikin yin kwalliya sai gashi an dawo dashi.
Farar shadda ce da akayi mata wani irin stone work da
golden brown stones a gaban rigar da kuma hannayenta,
in ka gani zaka dauka aikin sirfani ne amma stones ne
kawai aka jera su, Falmata tayi mata dauri mai kyau da
dankwalin shaddar sannan ta saka bungles na danyen
gold wanda ta dauko daga kayan lefenta, ta saka takalmi
ta rike clutch golden brown nan take ta fito a matsayin
Mrs Aliyu Abatcha. Bayan suma su Murjanatu sun gama
shiryawa sai suka fita babban palon gidan, aka zaunar da
Diyam a kan kujera kusa da Mama wadda Diyam tana
zama ta rike hannunta tana yaba kyawun da Diyam din
tayi.
Already mutane sun fara zuwa gidan, yanuwan Sadauki,
kannen babansa mata da matan kawun nan sa, matan
abokan babansa, abokan arziki da sauran matan manyan
gari. Duk wadda tazo zata zo su gaisa da Mama sannan
Diyam ta gaishe ta, Mama kuma tayi introducing dinsu,
kuma duk sai sun yaba kyawun Diyam sannan suyi mata
wasa saboda kasancewar su barebari ita kuma sai dai tayi
murmushi kawai dan ba zata iya mayarwa ba.
Wasa wasa gida ya fara cika, duk girman palon sai Diyam
taga mutane suna neman cika shi. Kowa kuma tazo zata
kawo mata gift ta karba tayi godiya sannan sai Mama ta
saka a shiga dashi ciki. Sai a lokacin ta fahimci ma ashe
ba wai anan ne za’ayi taron ba, akwai hall da suke dashi a
gidan wanda suke amfani dashi dan gudanar da tarurruka
ko kuma family meetings. Sai da akayi la’asar sannan aka
fara kai mutane can gurin taron, Diyam kuma ta koma daki
dan shiryawa. Tana shiga sallah ta fara yi sannan ta dauko
kayan da ta taho dasu ta ajiye akan gado a lokacin da
Sa’adatu ta shigo dakin tana kallon kayan tace “wow”
Diyam tayi murmushi. Kayan Fulani ne na saki complete
set din da abin wuya da hannu da kafa da komai. A
gaggauce tayi wanka, sannan ta danci abinci kadan kafin
ta shirya tsaf ta fito a cikakkiyar bafulatanar ta. Nan take
ta dauki kanta a hoto ta turawa Sadauki wanda tun dazu
da suka tare da su Mama yake ta kiranta a waya amma ta
kasa daukan wayarsa a gabansu. Yana gani yayo reply
“Diyam, na taba gaya miki kuwa cewa ke din kyakykyawa
ce?”
“Really? Ba zan iya tunawa ba. Maybe ka taba fada but
not directly”
“To yanzu zan fada directly din. You are very beautiful
Halima. Kina da beauty na fuska, na jiki dana zuciya. Ki
godewa Allah Diyam dan yayi miki komai”
“Anya kuwa na kaika kyau Aliyu? Ni in ina kallonka har
mamakin kyawunka nake yi. Komai naka tamkar kai ka
zabar wa kanka. Komai ya dace da komai a fuskarka
wadda ita kuma ta dace da jikin ka. Jikinka kuma ya dace
da sunanka, Aliyu Sadauki. Strong in the heart and the
body.
Imojin heart mai beating
“I love you so much my husband”
“I love you more, my wife”.
Dakin taron ya cika sosai da manyan mata, ga makada
nan suna ta aikin su mata ana ta cashewa ana barin kudi.
Diyam tana zuwa aka saka ta a tsakiyar fage aka fara yi
mata ruwan kudin da har sai da ta fara tunanin anya
wannan ba almubazzaranci bane ba? Ba’a tashi daga
event din ba sai daaka fara kiran magrib.
Karshen gajiya Diyam ta gaji, jikinta gabaki daya ciwo
yake yi mata dan haka akan sallayar da tayi magrib anan
ta zame ta kwanta sai bacci. Cikin baccin aka zo aka
tasheta wai taje su gaisa da matar governor wadda bata
samu zuwa dazu ba sai yanzu. Can palon Mama aka kaita
ta tarar dasu suna ta hirar su suna dariya, ta gaishe su
suka amsa mata da fara’a suka yi ta tsokanar ta tana rufe
fuska sannan matar ta dauko wani set din scent burner
mai kyau ta bata a matsayin gift sannan tayi musu
sallama Mama ta tafi ta raka ta. Bayan Mama ta dawo ne
sai kuma ta zauna tana ta yiwa Diyam nasiha da kuma
dabaru irin na zaman aure, wadansu maganar sai Diyam
taji sunyi mata nauyi da yawa amma kuma duk tana
ganewa kuma tana dauka. In dai Sadauki ne, she can and
will do anything for him.
Suna tare su Murjanatu suka shigo, sannan aka gabatar
musu da abinci suka hadu a dining din Mama suka ci tare
sannan suka dawo palo suka cigaba da hira, Diyam tana ta
mamakin yadda Mama take yi da yayanta kamar
kawayenta. Suna nan tare Sadauki ya shigo, Diyam ta
kalleshi sau daya suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya
je ya gaida Mama sannan ya samu guri ya zauna yana
amsa gaisuwar kannensa, Diyam ma ta gaishe shi ya
amsa yana danna phone dinsa, Murjanatu tayi dariya
Diyam ta harare ta.
Mama tace “kaje gurin babanka kuwa?” Yace “eh, muna
tare dashi ai tunda nazo, sai daya shiga ciki sannan na
shigo”. Ya turo wa Diyam text “ki taso mu tafi” ta karanta
sai ta dago kai ta harare shi. Ya hade hannunsa alamar
roko sai ta gyara zamanta yadda bama zata ke kallon sa
ba. Sai kawai suka cigaba da hirar su shida Mama, tana
bashi labarin taron da irin matan da suka zo da kuma gifts
din da Diyam ta samu. Sai yayi mata godiya sosai sannan
ya mike tsaye yana cewa “Fanna kawo min abinci daki na
Please” Mama tayi sauri tace “wacce Fanna kuma? Mu ai
mun yaye ka yanzu. Halima tashi maza ki hada abinci ki
bishi ki kai masa” bai ce komai ba yayi hanyar waje
sannan ya juyo a wayence yana kallon Diyam, yayi mata
gwalo.
Ta tashi ta hada masa duk abinda tasan zai so ta zuba a
basket sannan tace da Murjanatu “tashi ki rakani”
Murjanatu ta harare ta “kinga in kika fita daga gidan nan ki
kalli gabas, gini na farko da kika gani a gurin shine part
dinsa” Adama tayi dariya tace ” me dakin gabas kenan, shi
yasa mu a gidan nan bamu fiye kallon gabas ba sai in
zamuyi sallah” Falmata tace “to ai dan kar mu kalla ace
harara mukayi” Mama ta jefi Fanna da remote tayi mata
magana da barbarci sai ta mike suka fita tare da Diyam.
Suna fita Diyam tace “kun takurawa bawan Allah nan.
Mutum mai hakuri da kawaici irinsa, mutumin da ko hannu
aka saka masa a baki ba lallai ya ciza ba” Murjanatu tace
“waye hakan? Lallai so hana ganin laifi. To in gaya miki
saboda muguntar sa kwanan baya sai da ya saka ni
Murjanatu na share gidan nan gabaki daya, tun daga
sama har kasa” Diyam tayi dariya tace “daga ji wani
babban laifi kika yi masa, shi bawan Allah ne mai sanyin
zuciya mai kuma hakuri da yafiya idan aka bata masa” a
lokacin suka zo kofar part din Sadauki. Murjanatu ta bude
kofa ta tsaya a gefe tace “wacce take fadar maganar tafi
wacce ake fadawa sanin cewa ba gaskiya take fada ba.
Good night friend” Diyam tayi dariya tace “yanzu zan
dawo ai” Murjanatu tace “we will see about that”.
Ta ajiye abincin a palo tana studying kyawun gurin, sai ta
tafi kofar da jikinta ya bata yana ciki tayi knocking ta tura
kofa, yana kwance a kan gado da yawa a hannunsa, dakin
cike da sanyin ac da kuma kamshin sa, ya ajiye wayar yayi
mata murmushi yana folding hannayensa yace “welcome
wife” tace “ga abincin” ya dan bara rai “waye yace miki
yunwa nake ji? Ni matata nake so” ya karasa maganar
yana langwabe kai, ta fara bubbuga kafa a kasa “ni wallahi
bacci nake ji, ni wallahi na gaji jikina ciwo yake yi min” ya
mike zaune yace “good. Kinga sai inyi miki massage” ya
fada yana tattare hannun rigarsa. Ya nuna gefensa akan
gadon yace “come and lay down here inyi miki tausa. You
will thank me tomorrow”. Ta yi kamar zata yi kuka, ya
miko mata hannunsa yana kara marairaice wa sai kuma
tayi murmushi ta tafi tasa ka nata hannun cikin nasa.
Da safe sai da kowa ya tashi a gidan aka kuma gama
komai har breakfast an gama shiryawa amma babu Diyam
babu Sadauki babu kuma labarin su. Anyi ta kiran
wayoyinsu kuma da suna shiga amma daga baya
switched off. Sai da aka zo yin breakfast sannan Papa
yace aje a kirawo su, yana son suci abinci tare gabaki
dayansu saboda a yau yake son komawa Canada.
Cikin bacci Diyam taji kamar ana knocking kofa, ta bude
ido da kyar saboda nauyin bacci, ta hannun Sadauki daga
jikinta sannan ta juya tana kallon fuskarsa so deep in his
sleep sai kawai ta dulmiya wajen kare masa kallo tana
murmushi. Wani bugun kofar da aka sake yi shi ya dawo
da ita daga duniyar kallon Sadauki. Ta mike tana gyara
kayan jikinta sannan ta dauki hijab dinta ta saka still cikin
baccin ta fita palo ta bude kofa. Murjanatu ta gani a tsaye,
ta harare ta tace “kika ce min ba kwana zaki yi ba” Diyam
tace “wannan ne dalilin da yasa kika dame mu muna
bacci? To bara inje in kira wo shi sai ki maimaita a gaban
sa” ta daga hannu tace “Papa ne yake kira, in kuma inje in
gaya masa kunce kar a dame ku ne to?” Diyam bata ce
komai ba ta koma da sauri ta tashi Sadauki ta gaya masa
sakon kira sannan ta fita da sauri a ranta tana cewa
“wannan wanne irin abin kunya ne nayi ni Halima”.
Da sauri Diyam tayi brush ta wanke fuskarta ta chanza
kaya sannan suka tafi part din Papa inda anan ake neman
nasu. Tana shiga Sadauki shima yana shigowa, fatar
idonsa a dan kumbure alamar bacci bai ishe shi ba. Shi ya
fara zuwa ya durkusa ya gaida mahaifinsa sai bayan da ya
zauna sannan Diyam itama ta karasa for the first time ta
gaishe da surukinta. Ya amsa da madaukakiyar fara’a
“Halima, ance min jira kinyi kyalliya da kayan fulani, ni
kuma sai nace to lallai zamu yi miki zanen barebari dan
mu tabbatar miki kin zama tamu yanzu” duk suka yi dariya
har Diyam data rufe fuskarta da hijab dinta. Sai data zauna
sannan ta samu damar ganin fuskarsa. Sai a lokacin tayi
mamakin yadda akayi duk ganin da take yi masa a hotuna
bata fahimci suna kama sosai da Sadauki ba sai data gan
shi ido da ido tukuna. Bayan shekaru, banbancin fuskarsa
data Sadauki shine hancin Sadauki yafi nasa tsaho sai
kuma sumar Fulani da Sadaukin yake da ita.
Suna zama masu aiki suka matso suna tambayar kowa
abinda za’a zuba masa daga cikin menu, kowa ya fada
aka fara saving, Sadauki kuma ya fadi nasa dana Diyam
dan yasan ba zata yi magana a gaban su Papa ba.
Sai da suka gama cin abincin sannan Mama ta sake yiwa
Diyam barka da zuwa family. Papa kuma ya dora da cewa
“ina so Halima ki saka a ranki cewa nan gidan ku ne ba
wai gidan surukan ki ba, ki dauke ni a matsayin baban ki
ba wai baban Aliyu ba. Saboda baffanki, malam Usman
yayi min halaccin da babu wanda ya taba yi min irinsa a
duniya. Ya rike min Aliyu tamkar shi ya haife shi dan haka
nima zan rike ki tamkar ni na haife ki insha Allah. Wannan
shine abinda zanyi in kwatanta abinda Usman yayi min”.
“Nasan Aliyu ya baki labarin dana bashi akan rabuwata da
mahaifiyar sa amma ban gaya masa dalilin da yasa bayan
nayi bincike na gano wanda yake neman halaka su kuma
na dauki mataki akan sa ban koma na dawo dashi gida
gurina ba. Na barshi ya cigaba da zama a hannun Usman
ba tare da yasan nine mahaifinsa ba saboda a lokaci nayi
tunanin hakan shine dai dai a gurinsa, maybe I was
selfish, but I wanted what is best for my son. Ni mutum
ne mai harkoki da yawa wanda ban fiya samun lokacin
kaina ba ballantana na iyali na, tarbiyya, nuna soyayya,
nuna kulawa ga dan karamin yaro bayan kuma bana tare
da mahaifiyar sa ba abu ne da zai samu a gurina ba.
Wannan ne yasa na bar shi a hannun Usman da Zainab.
Na kuma boye kaina daga gare shi ne saboda ina son ya
zama strong, bana son yasan nine mahaifinsa ballantana
ya dora wani abu a ransa ko kuma ya raina marikansa. Sai
na nemi alfarmar Usman nace ya koya masa neman na
kansa tun yana karami. I used to go to the garage duk
sanda na samu dama, I used to watch him work,
drenched in oil and sweet, na kan ce a raina “good, yanzu
zaka san darajar kowacce kwandala da ka samu”. Usman
kuma bai taba neman ko kwandala daga wajena ba
saboda kula da Aliyu, sai lokacin daya kasa samun
admission ne ya nemi in taimaka masa ni kuma nace ya
barshi ya sha wahala ya samu da kansa, har yayi fushi
dani a lokacin yana ganin kamar nayi tsauri da yawa.
Amma yanzu gashi naga result din abinda nayi din, Aliyu
yayi turning into more than yadda na saka rai. Yes, na
bashi kudi nace ya juya, shekaru biyu bayan nan dana
bincika sai naga already yayi doubling kudin da na bashi.
A yanzu haka bansan adadin me yake dashi ba. Allah ne
kadai yasan me ya tsara wa rayuwar sa amma ni ina saka
ran cewa this is just the beginning for him. Allah yayi
muku albarka gabaki dayan ku, Allah kuma ya baku zaman
lafiya da zuriya mai albarka”.
Duk suka amsa da ameen. Diyam ta saci kallon Sadauki
sai taga kansa a kasa amma fuskarsa tana nuna tsantsar
farin ciki. Mama tace “a matsayin wedding gift, Papa and
I decided to give you two, Aliyu da Halima, gidan mu na
Oxford, mun bar muku shi duniya da lahira. Allah ya baku
zaman lafiya” nan take gurin ya kaure da murna, siblings
din Sadauki duk suka taho suka ringume Diyam suna taya
su murna. Ta gefen idonta taga Sadauki ya durkusa gaban
mahaifinsa yana godiya, sai taga ya dago shi ya rungume
shi a jikinsa yana bubbuga bayan sa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button