NOVELSUncategorized

DIYAM 76 & 77

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Seventy Six and seven : Karma

Food for thought: Mun tuna da hadisin da Annabi (SAW) yake mana bayani akan healing power da take cikin
habbatus sauda? Sannan da hadisin da yake gaya mana cewa nemon tsami yana maganin cututtukan annoba? Zam zam fa? Mun tuna cewa yana maganin duk wata cuta da aka sha shi da niyyar neman waraka daga gareta? Add that to bin ka’idodin kare ka kai daga wannan cutar, kar ki/ka fita daga gida indai bada wani kwakwkwaran dalili ba, in za’a fita din kuma a saka face mask da hand gloves. A guji taba mutane, doorknobs, railers etc a lokacin da ake waje, kar kuma aci ko a sha wani abu, a kuma guji taba fuska, in an dawo gida kuma a cire kayan da aka fita dasu a shanya su a rana sannan ayi wanka kafin a taba komai na gidan. 

Don’t forget your morning and afternoon azkar. Insha Allah we will get through this together.
#Don’t panic
#Stay safe
#Stay at home

A ranar da yamma su Diyam suka dawo Kano. Tun a jirgi Diyam take ramuwar baccin ta, sai Sadauki ya daga armrest din tsakanin kujerun su ta kwanta ta dora kanta a cinyarsa shi gyara mata hijab dinta ya rufe mata har kafafunta. Sai da zasu sauka sannan ya tashe ta, suna fitowa already daya daga cikin office drivers dinsa yana jiransu ya dauke su ya kaisu gida. A gidan ma Diyam baccin ta ta cigaba, dan sai yau take huce gajiyar biki, Sadauki bai dame ta ba ya batta tayi baccin ta shi kuma yayi musu order ta abinci aka kawo musu har gida saboda ya tabbatar wa kansa cewa bai iya girki ba. 

Sati daya bayan tariyar Diyam Asma’u tazo ita da Subay’a, ranar Subay’a kamar zata zuba ruwa a kasa ta sha dan dadi musamman saboda ganin dakin da aka ware a gidan saboda ita. Diyam kuma sai ta dauko gift din data samu a Maiduguri ta ware wadanda take so sannan sauran ta hada da wasu daga cikin kayan lefen ta ta bawa Asma’u tace ta kaiwa Inna a raba wa yan’uwa, cousins dinta duk kowa sai daya samu wani abu. Asma’u kam sai data debi rabonta dama tun kafin a fara tabon. A lokacin ne Diyam ta fahimci cewa Asma’u suna waya da Bassam, she did not comment, idan hakan suke so to ita kam sai dai ta taya su da fatan alkhairi.

Sati biyu bayan bikinsu hutun su Diyam ya kare, ta dauka zasu yi drama da Sadauki akan komawarta amma sai taga shine ma mai taya ta lissafi. Da lokaci ya matso sai taga ya fara hada nasa kayan shima. Tace “aikin fa? In ka bini wa zai kular maka da companyn ka?” Yace “my dear Halima. Kin manta I managed my company for the five years din da nake karatu? Ko kin dauka zan barki tafi ki barni ne?” Tayi dariyar yadda ya fadi maganar kamar wani yaro. Amma kuma tana jin dadi a ranta dan ba karamin faduwar gaba take yi ba a duk lokacin da ta tuna cewa zata koma England school ta bar Sadauki a Nigeria. 

Ta zo ta zauna akan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta ta saka fuskarta a wuyansa tana dan bubbaga bayansa tace “kar kayi kuka, bazan tafi in barka ba kaji habibi” ya shafa mararta yace “habibi yana cikin nan gurin a kwance” ta zaro ido tace “ba wani nan” yace “to ni dai banga kinyi period ba” tace “sati biyu ne fa kadai” yace “koma kwana biyu ne, ni ai nasan irin shukar da nayi kuma nake yi so nake inga na fara girbi” ta boye fuskarta a wuyansa tace “kai dan Allah, sai kace wata gona? Ni bani da komai Allah. Kuma ma ai kaga karatu nake yi yanzu ko? Ko so kake in ke faduwa exams dina?” ya dago fuskarta yace “tare zamuyi karatun ai, muna yi kuma muna cigaba da planting seeds din mu, kafin mu gama in Allah ya taimake mu sai mu girbi ko da biyar ne” ta zaro ido “biyar fa kace? Sai kace kaza?” Sukayi dariya tare. Yace “biyar din ma rage miki nayi ai dan kar ki sha wahala da yawa, in za’a bani zabi twins nake so duk shekara. In akayi twin boys sai ayi girls, sai a sake boys a sake girls, kinga a shekara hudu anyi takwas kenan” ta mike da sauri tana cewa “in yaso a shekara ta biyar sai inga an shigo min da amarya ko” ya jawo ta ta fado jikinsa, ya gyara mata zama tana facing dinsa yana tracing jawline dinta da finger dinsa yace “kina so ta mutu ne amaryar saboda bakin ciki? Ko kuma kina so ranar lahira in tashi da shanyayyen barin jiki saboda na kasa adalci? Kina ganin zan iya jera wata dake a zuciyata Halima?” Ta turo baki tace “daɗin baki” yace “au baki na yana da dadi dama? Ai ban sani ba nasan dai naki yana da mugun dadi. Let’s taste and find out na waye yafi dadi”.

Tafiyar su tazo dai dai da hutun su Subay’a. Dan haka Sadauki yace zasu tafi da ita da Asma’u suyi musu hutu a can kuma su taimaka musu gurin settling a sabon gidan su. Murna gurin Asma’u kamar zata tashi sama dan dadi, Diyam tana kallonta tace “kina murnar zaki je England ne ko kuma kina murnar zaki je gurinsa?” Asma’u tayi saurin yi mata signing akan tayi shiru kar Sadauki yaji. Diyam ta daga murya tace “eh, Bassam da kuke waya dashi Asma’u nace kinga kuwa a can yake karatu, nasan zaku ke haduwa in kinje” Sadauki yayi saurin juyowa daga kallon news yana kallon su yace “Bassam, menene hadin Yar asama da Bassam?” Diyam ta nuna ta tace “gata nan, tayi maka bayani”. Asma’u ta fara kame kame tana rarraba ido, ya kalle ta strictly yace “bana son shashanci, idan yana sonki da gaske yazo ya same ni first kafin ya cigaba da neman ki. I know his family, amma shi din zan saka a bincika min halayensa in kuma basu yi min ba kin gama ganin sa kenan. Kinji abinda nace?” da sauri Asma’u ta gyada kai.

Ranar dasu Diyam suka sauka a ranar ne suma su Murjanatu suka zo. Sun taho gabaki dayansu tare da sisters dinta dan su taya su Diyam tarewa a sabon gidan su. Gidan da Diyam taga kamar yayi musu girma dan haka ta saka aka rufe part din matar gida suka zuba kayansu a part din maigida ita da Sadauki. Sai bangaren yara kuma anan Murjanatu zata zauna tare da Judith din da Diyam ta kuma gayyatowa. Daga nan kuma sai gurin ma’aikatan gidan wadanda dama suna nan already, masu kula da tsaftar gidan, masu abinci da masu gadi. A cikin kwana biyu aka gama settling komai, a ranar suna zaune gabaki dayansu matan a palo suna hira sai Sa’adatu take basu labarin abinda Papa ya gaya musu kafin su taho daga Canada, cikin kwaikwayon muryarsa tace “ke Sa’adatu dake Falmata, ku fito da miji ayi muku aure hakanan, tunda naga karatun nan naku ba karewa zaiyi ba” duk suka kwashe da dariyar yadda tayi maganar, Diyam ta harare ta tace “yanzu haka baban nawa yake magana?” Falmata ta bude hannu tace “yanzu fi sabilillahi ni ina naga mijin da zan fitar? Ni ina naga saurayin ma? Samari fa basa kula yayan masu kudi” Murjanatu ta gyara zama tace “basa kula ku dai, ku da kuke musu girman kai, ki zo in koya miki yadda ake jawo hankalin maza” anan Sadauki ya bude kofar bedroom ya fito ya tsaya yana kallon su, duk sunyi tsuru tsuru saboda basu san yana cikin daki ba sai Diyam ce kawai ta sani. Bai ce musu komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing sannan yace “hello Papa” ya gaishe shi yace “maganar nan da ka yiwa su Sa’adatu, ina ganin a hada harda fanna saboda duk tafi su samari. Okay. Insha Allah. Thank you Papa. Love you too” ya juyo yana kallon fanna yace “ke ma ki fito da naki. Gaba daya guri na zasu fara zuwa First, sai nayi approving sannan zasu je gida” bai sake cewa komai ba ya saka hannayensa a aljihu yayi tafiyar sa.

Murjanatu ta zamo daga kan kujera ta fado kasa tana birgima dramatically, tace “wallahi yau na kuma tabbatar wa yaya Aliyu baya so na” su kuma duk suna tayi mata dariya. Diyam tace “alhamdulillah. Zuciyata fess yau. Karyar tara samari ta kare. 

Satin su Sa’adatu daya suka koma. Su kuma su Asma’u sai da sukayi wata daya sai da hutun su ya kare sannan suka koma gida. Washegarin da suka tafi ne da assuba Diyam tana karatun Alkur’ani akan sallaya sai ga Sadauki ya dawo daga masjid. Ya zauna akan gado yana kallonta har ta idar sannan ta mike ta hawo kan gadon ta kwanta tana lulluba yace “ni fa har yanzu banga tazo ba” bata kalle shi ba tace “wacece zata zo? Bakuwa zaka yi?” Ya yaye rufar yace “yau ba zaki yi baccin nan ba sai kin gaya min akwai ko babu” ta fara yi masa shagwaba “ni me zan gaya maka. Ni babu abinda zan gaya maka” ya cire rigar da yaje masjid da ita yayi astriding dinta yace “ko ki gaya min ta lallami da lumana ko kuma ki gaya min in kinji wuya” ta fara dariya, ya sakar mata nauyinsa shima yana dariya, tayi kokarin ture shi ta kasa sai ya rike hannayenta duk biyun da hannunsa daya, yace “akwai ko babu?” Tace “to ni yanzu me kake so ince maka” yace “cewa zaki yi ‘sadauki kayi min ciki” ta kwace hannunta da sauri ta rufe fuskarta tace “la ila, wai kai baka jin kunya ne?” Yana dariya yace “ina ji mana, ina jin kunyar mutane amma bana jin kunyar matata” tace “ni dai bazan iya fada ba” yace “to kinga, in akwai ki gyada kanki, in babu ki girgiza kanki” tayi shiru, yace “akwai ko babu?” Ta bude ido tana kwallon sa ta miko masa hannu tace “kawo tukuici” yace “say it, duk abinda kike so, anything” ta rufe hannun tace “in ka kawo tukuici sai kazo a gaya maka” yace “a bani bashi zan biya” ta turo baki “har yau fa baka biya ni bashin kaza ta ba kuma kake neman a kara maka wani bashin?” Ya dafe kai “wannan kaza, wannan kaza. Yanzu duk kajin gidan nan amma ban biya ba?” Tace “waccan special ce” ya mike yana saka rigarsa. “Zan siyo miki kaza yanzu, zan kuma kawo miki tukuicin ki”.

Sai daya loda rigunan sanyi a jikinsa saboda sanyin da ake yi a waje, gashi kuma gari bai ko gama wayewa ba amma haka ya fita, da kyar ya samu kazar saboda duk eateries din kusa dasu basu fito ba sai da ya shiga cikin gari sosai sannan ya samu, ya siyo mata chocolates duk wadanda yasan tana so leda guda sannan ya dawo gida. 

A gado ya same ta har lokacin ta lulluba tana baccinta. Ya zauna a gaban gadon ya bude ledar gasassun kajin ya yanko cinya daya ya bude fuskarta ya kai naman kusada fuskata, ta motsa idonta sannan ta bude idon cikin nauyin bacci tana kallon naman sai kuma ta kai hannu da sauri zata karba sai ya janye yace “kwadayayyiya. In kina so sai kin fada min abinda nake son ji, akwai ko babu?” Ta tashi zaune ta leko tana kallon naman kajin daya bude ya cika dakin da kamshi ga kuma chocolates din daya zube a kasa suma. Sai ta kalleshi ta gyada kai da sauri ta koma ta kwanta ta rufe fuskarta.

Wannan ciki na Diyam ya sha gata, gayu da soyayya a gurin sabon shiga Sadauki. Rigimar da tayi tunanin zasu yi akan komawarta school basu yi ba sai yanzu akan zuwa school da ciki. “Idan kuma kika fara rashin lafiya a can fa? Ko kuma in kina son ki kwanta ki huta babu gurin kwanciya? In zaki yi amai fa? Ko kuma kina sauri kin makara ki gurde ki fadi” tana dariya tace “baban baby kenan” yace “babies, kar ki rage min daraja mana” tace “okay Baban babies. Wannan cikin fa ba me laulayi bane ba, dame laulayi ne da ni da kaina zan nemi hutu. Ka barni in cigaba da zuwa please kaga yafi inyi ta zama a gida ko?” Amma fir Sadauki yaki, sai yayi enrolling dinta a online classes yadda zata zauna a gida tayi connecting da class dinsu online, duk abinda suke yi ko suke cewa tana ji kuma tana gani a screen din computer dinta, za kuma ta iya yin question a amsa mata, in bata kusa kuma zata iya saving lecture din sanda take free ta bude ta gani. Sai Murjanatu ta koma ita kadai take tafiya school sai Judith, dan ma dai ta samu at last ta koyi driving an kuma bata mota tana zuwa da ita.

Diyam babu abinda take yi sai dai taci ta sha ta kwanta tayi bacci sannan ta kula da mijinta, wanda sun rasa gane a cikinsu waye yafi kula da danuwansa. Kullum tamkar kara wa musu kaunar junansu ake yi. A lokacin ne kuma ya bayyana mata abinda yake shiryawa. “Branch nake so in bude na Abatcha Motors anan kasar, kinga sai inke siyan motocin daga nan ina aikawa dasu Nigeria kuwa zanke siyarwa anan din ma. Tunda muka zo nake processing abin amma saboda kasancewar ni ba dan kasa bane ba sai na kasa samun permit na bude Company, but alhamdulillah yanzu na samu” ya dauko takardar ya nuna mata, ta karba tana karantawa yace “har na sayi fili ma, yanzu zan fara gina gurin tukunna sai in dauki ma’aikata insha Allah” ta rungume shi cikin jin dadi tace “congratulations darling. Allah ya cigaba dayi maka jagora mijina” ya zagayo da ita gabansa yace “ameen. Yanzu problem din shine, bana son harkar bude wannan branch din ta saka ni in kasa saka ido akan wancan, though lafiya lau komai yake tafiya a can din but I need an assistant, someone that I can trust” tayi shiru tana tunani sai tace “Alhaji Bukar bashi da ya’ya? Kayi masa magana mana ya hada ka da mafi aminci a cikin yayansa kaga shima zaiji dadin ka karrama shi” yayi murmushi mai kyau sannan yayi kissing forehead dinta yace “that is one of the reasons I love you, saboda kina da tunani mai kyau. You know what? Kema na baki aiki” ta bata rai tace “wanne aiki kuma bayan wanda already nake dashi?, na matarka?” Yace “you are now my special advisor” tace “duk ka dai part of my job ne as your wife”.

Koda yaushe Diyam tana lissafin Saghir a ranta, amma bata taba yiwa Sadauki maganar ba saboda bata son taba masa zuciya, duk kuma sanda suka yi waya da Subay’a sai tayi mata maganar sa, duk da cewa Inna tana yawan kaita ta ganshi. Shima Sadauki bai taba yiwa Diyam maganar Saghir din ba amma shima Subay’a bata barshi gurin tambaya ba. 

A lokacin dasu Diyam suka kammala second semester dinsu a lokacin cikinta yana da watanni biyar, a lokacin kuma Sadauki har ya kammala ginin sabon branch din Abatcha Motors. Cikin Diyam ya dan fito kadan amma baiyi girma sosai ba, abinda ya fito sosai shine kyawunta, dan sanda suka fito daga jirgi a malam Aminu Kano international airport ita da Sadauki hannayensu rike dana juna, duk wanda ya kalle su sai ya sake kalla. Gidan Inna suka fara zuwa, a can suka ci abinci suka huta Diyam tana ta jin kunyar cikin jikinta, anan Sadauki ya barta sai dare yazo ya dauke ta duk da tayi ta rokonsa ya barta ta kwana biyu a nan. Yace “ina garin zaki kwana gida? Ki bari in nayi tafiya sai kiyi zauna ko kwana nawa ne kiyi musu”.

A week after that, ya dawo daga office sai taga mood dinsa ba shi da kyau, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera tare da lunshe idonsa. Ta zauna a hannun kujerar tana shafa fuskarsa tace “wanka ko abinci?” Ya dan bude ido ya kalleta yace “bara in dan huta tukunna” sai ta sauka ta durkusa a gabansa ta cire masa takalmi ta hada da briefcase dinsa ta kai sama ta dawo ta sake zama a gabansa ta cire masa safar kafa ta dora kafafun a kan cinyarta tana mammatsa masa ita, tana jan yatsun kafar. Ya dan janye kafar yana cewa “ke! Chakulkuli fa kike min” ta sake jawo kafar tace “tausa fa nake yi maka, haka ake chakulkulin?” Sai tayi masa chakulkulin gaskiya a tafin kafarsa, Yayi dariya yana tashi zaune sosai ya janye kafarsa, sai ta mike tayi kneel down tana murmushi ta faki idonsa ta saka hannunta cikin rigarsa tayi masa chakulkuli tana cewa “gana gaskiyar nan nayi maka to” ya kama dariya har da zamowa kasa ya jawo ta suka fadi tare, sai shima ya yi mata yana cewa “sai na rama wallahi” ta kama kyalkyata dariya tace “wayyo zan mutu, ka bari wallahi, chakulkuli fa kanin mutuwa ne” ya sake ta ta janye daga jikinsa tana dariya, yace “kinci sa’a bake kadai bace ba” ta murguda masa baki sannan ta dawo kusa da fuskarsa tace “wanne mai tsautsayin ne ya taba min lion dina” ya danyi tsaki yace “mutane, yanayin rayuwa, cin amana. Babu abinda wasu mutanen ba zasuyi saboda kudi ba. Babu wanda ba zasu ci amana ba akan kudi. I don’t know mai mutanen mu suka mayar da kudi, abinda zaka iya samu yau gobe ka rasa, abinda zakayi bayani a lahira dalla dallar yadda akayi ka samu” tace “me ya faru?” Yace “Saghir zai fito next week insha Allah” taji dadi har cikin ranta amma sai ta boye ta danyi murmushi tace “alhamdulillah. An samu Kabir din kenan?”.

Yace “tun kafin ku koma school ake neman Kabir an kasa kama shi, iyayensa sunki bada hadin kai dan haka ba’a san sanda yake shigowa gari ba ballantana sanda yake fita, nayi nayi abu ya gagara, daga baya ma sai na samu labarin wai ya kwashe iyalansa daga kano sun koma kaduna da zama baki daya. I told Ahmad amma sai yace ba zai iya kama shi a kaduna ba saboda kaduna ba a ikonsa take ba, in dai zai kama shi a can sai yana da arrest motive da zai nuna wa commissioner of police na kaduna, kuma a lokacin babu wani motive na kama kabir tunda zargi kawai akeyi babu shaida. Sai nayi tunani a kan wani abu, Nayi tunanin yadda son kudi ya kai Saghir inda yake a yanzu, na kuma tuna yadda son kudi ya saka abokinsa yayi framing dinsa, sai na tuna maganar hausawa da suke cewa sai hali yazo daya ake abota, da kuma maganar bature da yace birds of the same feathers flock together, sai na saka aka bincika min wanene next friend dinsu su biyun, sai aka hada ni da wani Bashir, kin sanshi?” Diyam ta gyada kai, yace “ranar da muka zo gari na kira shi nace ya same ni a office dina, and he came, na gaya masa abinda Kabir yayi wa Saghir ba kuma nemi ya taimaka mana mu kama Kabir din, farko sai yaki, but then as I expected sai ya fara bargaining, ya fadi kudin da yake so in bashi in ina so ya fada mana sanda Kabir zai shigo gari da kuma inda za’a same shi. I told him in yana so in bashi kudi sai dai yayi making Kabir yayi confessing cewa shi yayi framing Saghir and he agreed. I gave him some money. Yau sai gashi ya dawo, can You believe ge got Kabir drunk ya ringa yi masa questions yana amsawa shi kuma yana recording? It hurts me cewa duniya tayi lalacewar da friend zai iya yiwa friend dinsa haka, but considering abinda shima kabir din yayi sai naga yayi deserving shima ayi betraying dinsa”

“Nayi submitting record din to Ahmad, yanzu zasu iya shiga har Kaduna su kama kabir, and Saghir is coming out latest next week”.

Not edited. Ayi hakuri da typos.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button