NOVELSUncategorized

DIYAM

DIYAM Chapter 7
Finale

Sai da Diyam ta gama da Sadauki sannan ta zauna ta kira
Inna ta gaya mata labarin zancen fitowar Saghir. Inna tayi
murna sosai tace “Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah yasa
karshen wahalar sa kenan shi kuma Sadauki Allah ya saka
masa da alkhairi” Diyam tace “ameen Inna” tace “bari in
kira gidan Alhaji Babba inyi masu albishir”. A ranar zance

ya zagaya family, zuwa washegari yab uwa suka fara kiran
Diyam suna confirming “da gaske Saghir zai fito?”.
Ranar da aka kama Kabir kuwa Hajiya Babba har gidan
Diyam ta zo tayi mata godiya ita da sister dinta, hawaye
fal idonta, tana ta bata hakuri dan gane da rashin
kyautawar da suka yi mata a baya. Diyam ta cika su da
abin arziki kuma ta nuna musu babu komai ai yiwa kai ne.
Sun so ganin Sadauki suyi masa godiya amma yaki fitowa
yace ace musu babu komai.
Ranar da Saghir zai fito, Friday kenan, a ranar Sadauki
yace da Diyam ta shirya tare zasu je. Daga gidan su gidan
Inna suka fara zuwa suka dauki Subay’a sannan sannan
suka tafi prison din. Suka yi packing a tsallake, Sadauki
yace musu su zauna a mota ya shiga shi kadai. Bayan ya
tafi Subay’a tace “Mommy nan prison ce ai” Diyam tace
“eh” “inda Daddy na yake” “eh” “to Mommy mu shiga
mana muhe mu ganshi” “a’a ba shiga zamuyi ba Subay’a”
“to Mommy mai uncle ya shiga zaiyi a ciki?” Sai kuma ta
bude ido ta ja numfashi tace “zuwa yayi ya fito dashi,
dama ya gaya min zai fito dashi, Mommy ki bude min
kofa inje gurin su” Diyam ta rike hannunta, sai kuma tayi
murmushi tace “Subay’a uncle zuwa yayi ya fito da Daddy,
amma kiyi zamanki a mota tunda uncle bai ce ki fito ba,
yanzu zaki gansu sun fito tare”. Subay’a ta hakura bata fita
daga mota ba amma kuma bata zauna ba, in ta leka ta
waccan window din sai ta dawo ta leka ta wannan, in
kuma taga motsi a bakin kofar gurin sai ta fara tsalle sai
taga basu bane ba. Daga baya data gaji sai ta kwanta a
backseat tana kuka wai sunki fitowa.
At last sai gasu sun fito. Sadauki ne fara fitowa tare da
wadansu mutum biyu wadanda Diyam ta gane a matsayin
lawyers dinsa. Sai kuma Saghir ya fito tare da wani wanda
ya tsaya yana ta yi masa bayanai har su Sadauki suka
karaso mota. Mutanen suka yi masa sallama suka tafi
sannan wancan ma yayi wa Saghir sallama ya tafi.
Diyam ta zauna tana kallon shi ta cikin motar. Yayi baki
sosai, ya kuma rame sosai, amma wannan kyawun yana
nan sai dai babu gayun, kuma shekaru sun fito sosai a
fuskarsa harda strings of furfura a gashin sa. Ta gane
kayan jikinsa, sune kayan da yake sanye dasu ranar da
aka kamashi a airport, she can remember yadda ya fito
daga arrivals cikin yana taku dai dai yana jin duniya duk a
tafin kafarsa ga kyakykyawar Fauziyya a gefensa but yanzu
da ta kalle shi bata ga komai daga cikin characters din
wancan Saghir din ba. He looked calm and very different.
Sadauki ne yayi knocking a tagar da Subay’a take, ta dago
tana kallonsa sai yace “Subis ga Daddy nan” ta mike da
sauri ta kalli kofar prison din, tana hangoshi sai ta kama
kokawa da handle din motar sai Diyam ta bude mata
central lock tana dariya. Ai kuwa nan take ta bude ta fice
daga motar a guje, Diyam ma ta bude ta fito tana cewa
“careful Subay’a akwai titi fa”. Daga tsallake Saghir ya
hango fitowar ta, ya kuma lura da yadda tayo kan titi da
gudu dan haka sai shima ya taho da sauri gurin ta
zuciyarsa tana bugawa. A tsakiyar titi suka hadu, ya daga
ta sama amma sai ya kasa juyi da ita ya sauke ta yana
haki yace “kinyi girma Subay’a, Daddy kuma bashi da
karfi” sai ta rungume ƙafafuwan sa tana murmushi.
Ya kamo hannunta suka karasa tsallako titin zuwa inda su
Diyam suke a tsaye. Unintentionally hannun Diyam ya
sauka akan cikinta tana kallon Saghir, sai taga ya kalli
cikin sai kuma tayi sauri ta dauke hannun tana sunkuyar
da kanta. Yayi murmushin takaici Yace “amarya” sai ta
gaishe shi ya amsa yace “a sake min godiya gurin Mr
Abatcha. Na goge sosai Allah ya bar zumunci” ta gyada
kai a hankali tace ameen tana kallon Sadauki wanda yake
ta danne danne a waya kamar baya jin me suke cewa. Sai
ta kalli Saghir tace “congratulations. Allah ya kiyaye gaba”
daga haka ta bude mota ta koma ciki. Sadauki ya dago
kansa yana kallon Saghir ya nuna masa mota yace
“Bismillah, sai mu ajiye ka a gida ko?” Sai Saghir ya kalli
Diyam, ya hadiye wani daci a ransa ya girgiza kai yace “no,
thank you. Kar in takura muku maybe akwai inda zaku je.
Bara in hau napep kawai” Sadauki ya daga kafada kawai,
sai ya tare masa napep din ya kuma biya kudi sannan ya yi
wa mai adaidaitan kwatancen sabon gidan Alhaji Babba,
tunda Saghir din bai sani ba.
Saghir yace da Subay’a “zaki bini gidan Alhaji?” Ga
mamakin su sai ta kalli su Diyam ta kuma kallonsa sannan
ta girgiza kai tace “no, Aunty Asma’u tace yau Uncle
Bassam zai zo, kuma na bashi sakon abubuwan da zai
taho min dasu in zai zo, ka ga kar yazo bai same ni ba”
Sadauki ya bude ido yace “Subis akwai zarar magana sai
kace wata babba” Saghir yayi murmushi yana kallon inda
Diyam take yace “gado tayi ai”. Har adaidaitan zai ja sai
Subay’a tace “Daddy zan kawo maka ziyara gidan ka”.
In silence suka bar gurin kowa yana lissafe lissafe a
zuciyarsa. Sai can sannan Sadauki yace “ba zan bashi aiki
ba kamar yadda kika bukata. Bana son drama, nafi sonsa
a nesa damu” bata ce komai ba, ya cigaba “amma zanyi
masa komari ya samu kudin sa na gurin Kabir” Diyam tayi
sauri ta kalle shi tace “kudin ka dai, ai kudinka ne” ya
girgiza kai yace “nayi signing takarda cewa na bar masa
kudina daya dauka, so legally yanzu kudin sa ne ba nawa
ba. I have already talk to my lawyers, za’a siyar da
kadarorin Kabir maybe za’a samu part of kudin amma
nasan ba za’a samu gaba daya ba” Diyam taji dadi sosai a
ranta tana yabawa kyawun zuciyar Sadauki, kamar yadda
ya taba fada mata shi fire ne da ice, duk da wadda kazo
dashi za’a tarye ka.
Tayi masa godiya sosai sannan yace “kin san wani abu? Ni
da Saghir are alot alike” ta bude ido dan ita bata ga hadin
su ba bayan kasancewar su musulmai kuma half fulani
tace “ta yaya?” Yace “kinga ni da shi duk only sons ne a
gurin iyayen mu. Kuma iyayen mu suna son mu sosai
sannan sun nuna mana soyayya in their own different
ways. Duk kanin mu iyayen mu sun bamu kudi, the only
difference is yadda muka yi da kudin da suka bamu.
Sannan kuma duk muna sonki” ya fada yana kallon ta, tayi
saurin girgiza kanta tace “he doesn’t” yace “he does. I saw
it in his eyes yanzu da yana kallon ki”
Tayi saurin kawar da maganar ta hanyar cewa “kuma duk
ku biyun kuna da kanwa mai suna Murja” yayi dariya yace
“ni kanwa ta Murjanatu sunan ta ba Murja ba, kuma ni nafi
shi son kanwa ta” tace “ita kuma duk duniya gani take yi
kafi kowa kinta” and they laughed together.
*************************
Saghir ya juyo yana kallon Subay’a, yana kallo Sadauki ya
kama hannunta ya bude mata kofa ta shiga mota sannan
shi kuma ya zagaya ya zauna kusa da pregnant Diyam.
Yayi sauri ya rintse idonsa tare da dafe kansa yana jin
hawaye yana zuwa idonsa. Bai dauka har yanzu Diyam
tana da gurbi a zuciyarsa irin haka ba, ya dauka ba zaiji
komai ba inya ganta musamman saboda kokarin da mr
Abatcha yayi masa, amma ita zuciya bata da linzami dole
ya ja baya dasu ya daina ganinsu, ko kuma abinda yaji din
yana da alaka da yadda Diyam din ta zama? Irin kyawu da
cikar halittar da tayi? Wai hakan na nufin da ace ya kula
da ita tsahon shekarun da suka yi a tare da irin haka zata
zama kuma maybe da zata so shi? Lallai gaskiyar
hausawa da suka ce tun ranar gini tun ranar zane, shi
kuwa nasan ginin ya bushe dole sai dai ya hakura da
zanen ko kuma ta sake sabon gini, sabon ginin wata
rayuwar.
But with who? Wannan wata tambaya ce for another time.
Maganar da Subay’a ta fada ta dawo masa zuciyarsa “zan
kawo maka ziyara gidan ka” wanne gidan? Shi fa yanzu ko
gidan kansa ba shi da shi, wayake ma maganar gida, shi
ko kwandala bashi da ita. Bashi da komai sai freedom
dinsa, kuma ya dauki freedom din nasa ya zama another
chance at life. Chance din kuma da insha Allah zai yi
amfani dashi sosai yadda har sai mutane sunyi
mamakinsa. Yadda har sai iyayensa sunyi alfahari da shi.
Iyayen da a wancan lokacin ya wofantar ya wulakanta,
abinda yake tunanin shine dalilin zuwansa inda yaje ba
wai Diyam ba.
Maganar mai napep ce ta dawo dashi hankalinsa, yace
“yallabai munzo” ya leko dakansa yana kallon gurin yace
“nan ne?” Mai napep yace “nan dai yayi min kwatance,
yace jaen layin shago tara, gashi nan kuma har mun kusa
fita daga layin tunda mun fara hango diga. Sai dai ka
sauka ka tambaya” Saghir ya sauka yana kallon gurin, not
that bad. Mai adaidaitan ya miko masa dari biyar yace
“dubu biyu ya bani, ga dari biyar ka sha ruwa kai ma”
Saghir ya karba harda yi masa godiya sannan ya tafi gurin
wasu mutane su uku da ya hango a kasan bishiya ya
gaishe su yace “dan Allah tambaya nake yi, gidan Alhaji
Babba, bai dade da dawowa unguwar nan ba” duk suka ce
basu sani ba, yayi gaba ya cigaba da tambaya amma babu
wanda ya sani sai ya juyo ya fara retracing ta inda suka
shigo yana yi yana tambaya, ga rana gashi dama jikin sa
duk babu karfi.
Da kyar ya samu wanda yace “inda akayi biki watannin
baya?” Da sauri Saghir yace “eh” sai aka hada shi da yaro
suka koma can inda ya baro, suka je har gaban wani gida
sannan yaron ya nuna masa ya juya. Ya tsaya yana kallon
gidan, a tsahon rayuwarsa bai taba tsammanin duniya
zata yi juyawar da har nan gidan zai koma shine gidan
baban shi ba, gidan ma kuma gidan haya, gidan hayar ma
kuma Diyam ce ta ke biya masa.
Ya shiga soro yayi sallama, Hajiya ya hango ta fito daga
wani guri daya ga kamar kitchen tana amsa sallamar
hannunta rike da wuka tana goye da wani yaron da bai
sani ba a bayanta. Ta yarda wukar tana kiran sunan Alhaji,
Alhaji ya fito, Hajiya yalwati ta fito, sai ga yaran gidan
suma sun fito daga wani daki duk suna binsa da ido. Shi
ya karasa shigowa, ya tafi gaban mahaifinsa ya durkusa
amma sai ya kasa gaishe shi sai kuka ya kwace masa.
Alhaji ya sunkuya gabansa ya jawo shi jikinsa ya rungume
shi shima yana hawayen yace “bansan yau zasu fito da kai
ba Saghir, da ko ba zan iya zuwa da kaina ba da sai in
gaya wa mahaifiyarka ta je ko ta tura aje a taho da kai”
Saghir ya goge hawayen sa yace “Mr Abatcha ne yaje ai,
dashi da Diyam da Subay’a” ya fada yana jin dacin zuciyar
dazu yana dawo masa. Alhaji yace “madallah dasu. Allah
yayi musu albarka ya jikan Usman”.
Nan fa gida ya rude da murnar dawowar Saghir, dan ma
yanzu duk yaran babu saura kadan. Hajiya Babba ce ta
kama shi ta kaishi daki, Hajiya yalwati kuma ta dora masa
ruwan wanka, alhaji kuma ya aika a siyo masa nama da
lemo kafin a gama abinci. Babu laifi suna cikin rufin asirin
su duk da cewa alhaji har yau bai kuma gwada kasuwanci
ba amma matansa suna yan sana’o’in su sannan yayansa
mata da suke aikin gwamnati suna kokari gurin taimaka
musu sosai, haka ma surukan gidan lokaci zuwa lokaci
suna aiko musu da kayan abinci ko kuma suttura.
A dakin Hajiya ya huta, naman da Alhaji ya siyo masa
sannan yayi wanka ya chanja kaya zuwa wanda Hajiya ta
ajiye masa akan gado. Sai ta kunto yaron bayanta ta mika
masa. Kallo daya yayi masa yasan waye, sai kawai ya
ajiye shi a gabansa ya sunkuyar da kai, tace “sunan
babanku ne dashi, Jawad ake ce masa” yaron ya rarrafa
da sauri yabi bayan Hajiya yana kuka alamar bai san shi
ba.
Dakin da yake soro, wanda kuma yake da kofa a waje shi
dama Alh yasa aka gyara tun sanda yaji labarin dawowar
Saghir gida. Aka shimfida carpet aka saka katifa,
wardrobe, da kuma standing pan. Nan ne ya koma dakin
Saghir.
Kwanan Saghir biyar ya warware, duk da dai babu inda
yake fita sai yan’uwa da suke ta zuwa yi masa murna. Inna
ma tazo ita da Asma’u da Subay’a, suka kuma bar Subay’a
anan tayi weekend tare da mahaifinta da kakannin ta. A
ranar ne Alhaji ya kira shi dakinsa. Suka zauna sai ya
dauko wata leda ya miko masa, Saghir ya karba ya bude
sai yaga kudi a ciki, ya zaro ido “Alhaji kudi ai, kudin
menene wannan?” Alhaji yace “kudi na ne, sauran kudin
gida na ne da kuma abinda na samu daga gadon Usman,
su nake ta ajjiye dasu da niyyar duk ranar da ubangiji ya
sake baka dama a rayuwa ya saka ka fito daga prison
nima zan sake baka dama in baka su kayi jari” Saghir yayi
saurin girgiza kansa hawaye yana bin idonsa yace “Alhaji
kar kayi haka, ka bani kudi sau ba adadi ina salwantar wa,
kai ma kana bukatar kudin nan alhaji, kana da iyali kaima.
Ka rike kudinka alhaji ka kula da kanka da matanka da
kanne na” Alhaji yace “da wanne karfin Saghir? Ni ai tawa
ta kare, karfi na ya kare, dan haka kai na dora wa wannan
nauyin ka juya wannan kudin ka kula da kanka sannan ka
kula dani da iyayenka da kannenka, kuma ka cigaba da
kula dasu ko bayan rai na ne”.
Saghir ya karbi kudin ya rike yana jin nauyi a zuciyarsa
“anya kuwa akwai soyayya sama data iyaye?”
Alhaji yace “akwai kuma wata magana da nake so muyi.
Ina so ka kawo karshen rashin jituwar da take tsakani na
da danuwana, ina son ka auri Suwaiba” ya dago kai yana
kallonsa, Alhaji ya gyada kai yace “ta inda ake hawa tanan
ake sauka. Tunda kuka bata dan haka ku zaku gyara”. Sai
Saghir yaji Fauziyya ta fado masa a ransa. Bayan ya bata
takardarta sun rabu, daga baya sai ta koma tana gaya
masa cewa tana da cikinsa, ta kuma ce zata haifi cikin za
kuma ta jira shi as long as bata samu miji ba har ya fito
sannan kuma yana da sha’awar mayar da ita. Bayan ta
haihu kuma ta kai masa babyn ya gani. And after seeing
Subay’a rike da hannun Sadauki, baya jin zai kuma barin
wata yar tasa a wani gidan. Dan haka indai Fauziyya bata
yi aure ba to sai dai ya hada su ita da Suwaiba.
Wata daya bayan nan Diyam tazo yi musu sallama zata
koma Oxford, England. Washegarin zuwanta kuma alert ya
shigo masa. Ya bude ido yana kallon kudin cike da
mamaki ya tafi da sauri ya nunawa Alhaji. Alhaji yayi
murmushi yace “Diyam ta gaya min jiya, kudin da Kabir ya
gudu dasu ne aka dawo maka dasu. Zabi kuma ya rage
naka kasan me zaka yi dasu”.
Abinda Saghir ya fara yi shine ya dauki kudin da Alhaji ya
bashi ya sayi gida madaidaici amma me kyau. Ba shine ya
tare a gidan ba, Alhaji Babba da iyalin sa ne suka tare. Sai
kuma ya sayi karamin fili a kusa da gidan a matsayin nasa
“sai in zauna a kusa daku yadda zanfi jin dadin kulawa
daku” next sai yaje har gidan Kawu Isa ya durkusa ya
bashi hakuri sannan ya nemi ya bashi auren Suwaiba. Sai
kuma ya tafi gidan su Fauziyya itama ya nemi auren ta.
Amma duk kan su yace sai shekara mai zuwa idan ya
samu nutsuwa sosai.
Daga nan sai ya tafi kantin kwari, tsofaffin shagunan Alhaji
wadanda wuta ta cinye babu komai sai ginin, shima ginin
duk ya mutu an sace kwanukan. Cikin kwanaki kadan ya
tayar da ginin su, yayi komai ya saro kayan duk da yasan
Alhaji yana siyarwa ada da kuma kayan da yasan zamani
ya zo dasu ya zuba a ciki. Sannan ya nemo tsofaffin yaran
Alhaji wadanda suke kular masa da shagunan a da ya
dawo dasu dan su suka san kan kasuwa, shi kuma ya
zauna cikinsu dan shima ya fahimci harkar.
Watanni kadan abubuwa suka warware wa Saghir, ya hada
kudin neman aure ya kai gida biyu aka saka masa rana
watanni takwas masu zuwa za’ayi duk a tare, sannan
kuma ya fara ginin gidan sa a hankali. Gidan da yake da
yakinin zai zamanto tushen sabuwar rayuwa a gurin sa.
****************************
A lissafin Sadauki so yayi in sun bar Nigeria su fara tafiya
Canada suyi kwana biyu tukunna, amma Diyam ta tubure
masa ita bata son zuwa, ya gane abinda yasa bata so, ita
kunya take ji ake ganin ta da ciki. Yayi dariya “to wai ke
banda abinki, ni fa banga abin kunya anan ba, kowa ma fa
yana yi” ta juya masa baya tana kallon Subay’a a cikin
swimming pool tace “kuma kawai sai in je gidan inyi ta
yawo da ciki suna kallona?” yace “baiwar Allah, idan baki
je da ciki ba in kika haihu dai ai dole zasu ganki da dan
ko? Ko shima cewa zaki yi ba ke kika haifa ba?” Tace “ai
kuwa in naje gidan da baby to har in bar garin ba zan
dauke shi ba” ya rike baki “to waye zaiyi feeding dinsa?”
Tace “sai ya sha madara” ya kwanta akan camp bed din
da yake zaune akai ya rufe ido yace “you are impossible
Diyam, ke fulatancin kamar a kanki ya kare” ya sake cewa
“kiyi addu’a to, kar a saka bikin su fanna kafin ki haihu, sai
muga yadda zakiyi da cikin a gurin biki” tayi saurin cewa
“Allah ya kiyaye, insha Allah sai na haihu”. Sai ta jawo
kujerar da take kai kusa dashi tayi tagumi tana kallon sa,
ya bude ido yana kallon ta yace “what?” A hankali tace “I
want to kiss you, kuma Subay’a tana kallon mu” yace
“ohh, a wannan bangaren kam kin ajiye fulatancin ko?”
Sai kuma ta rufe ido tana dariya.
Addu’ar Diyam dai bata karbu ba, dan suna komawa
makaranta aka saka ranar bikin su Sa’adatu kuma wata
biyu kadai aka saka, meaning cikin Diyam yana da wata
takwas kenan za’ayi bikin. A dole Diyam ta taho Maiduguri
lokacin bikin da katoton cikinta, Sadauki yana ta yi mata
dariya amma sai ta maze da shiga harkokin bikinta sosai
ta rike role dinta na matsayin babbar yaya. Da ita akayi
shawarar komai, da ita aka sayi komai, wani abun ma in
ana nema sai Mama tace azo wajen Diyam.
Su Inna da Mama da Asma’u ma duk sunzo gurin bikin
sun kuma Kawo wa amaren gift sosai har sai da Maman
su Murjanatu tace “kayan nan anya basu yi yawa ba
Amina?”
Aka daura aure aka kai amare gidajen su. Sa’adatu ta auri
Aminu an kaita Abuja. Falmata kuma Saifullahi mutumin
Kano amma mazaunin Canada dan haka can zasu koma,
Fanna kuma ta auri cousin dinta Al-mustapha zasu zauna
anan Maiduguri amma zata zauna a gurin su Diyam ta
karasa karatun ta.
Bayan su Diyam sun koma England sai hankalinsu kuma
ya koma kan haihuwa, Sadauki yana ta rawar kai, duk
zuwa asibiti tare suke yi idan kuwa yaga namiji ne zai
duba ta sai ya ja abarsa su bar asibitin. Twins ne kamar
yadda Sadauki yake ta addu’a. Diyam tayi tunani sai taga
cewa ba zata iya tuno yadda haihuwa take ba tunda bata
yi labor a haihuwar Subay’a ba, haihuwar twins kuwa ba
zata iya tuna yadda abin ya kasance ba dan haka sai ta
shiga maternity classes, anan ta fahimci komai ta kuma yi
browsing wasu abubuwan ta sake fahimta.
Abinda take tsoro guda daya shine shigar Sadauki gurinta
in tana labor, tasan kuma za’a bashi option din shiga
kuma tasan zai shiga din. Sannan tasan in dai ya shiga sai
ya hargitsa daga ita har me karbar haihuwar kuma in yaga
wahalar da ake sha a gurin haihuwa sai sunyi rigima kafin
ya barta ta samu wani cikin. Ta kuma san yadda yake son
yaya, dan haka ta yanke shawarar yi masa dabara yadda
ba zata haihu a gabansa ba saboda ta haifa masa yaya as
many as yadda Allah ya basu.
Ranar data fara jin alamar labor da daddare sai taki
nunawa Sadauki, da safe kuma sai tayi pretending as if
bacci take yi har ya gama shiryawa a hankali dan kar ya
tashe ta, ya zo yayi mata kiss ya fita. Sai bayan fitarsa
sannan ta tashi ta dauko jakar tafiya asibitin ta wadda
already ta riga ta shirya ta ta kuma yi driving kanta zuwa
asibitin. Sai da taje suka aunata suka kuma tabbatar mata
da cewa haihuwa zata yi sannan suka bata daki suka
kuma nemi su kira mijinta amma ta hana su tace sai ta
haihu tukuna.
Ta sha wahala ba kadan ba, Sadauki ya sha kira kamar
sunan sa zai kare ta kuma yi nadamar kin gaya masa dan
da yana kusa  ko ganin sa in tayi zata ji dadi. A haka har
Allah ya sauke ta lafiya ta haifi namiji first, sai data huta
sannan labor ya sake dawowa ta haifi mace. Ana miko
mata su taga fuskar babansu amma fatarta, sai dai
namijin bai kai macen haske ba.
Sai da aka gama garata aka kuma gyara babies din ta
kuma danyi bacci kadan ta huta sannan tace su kira shi.
30 minutes after kiran nasa sai gashi ya shigo asibitin
hakan yasa Diyam ta tabbatar da cewa yayi breaking every
traffic rule a hanya saboda sanin nisan asibitin daga
office dinsa.
A rikice ya bude kofar dakin da aka nuna masa ya shiga.
A tsaye ya ganta a gaban window ta juya masa baya. T-
shirt dinsa ce a jikinta, wadda ta kawo mata har zuwa
rabin cinyarta, gashin kanta a barbaje wani ya sauka a
bayanta wasu akan kafadun ta wasu kuma sun zubo kan
kirjinta. “Diyam” ya fada cikin sarkewar murya. Ta juyo
tana kallonsa, hannunta rike da jariri tana rocking a
hankali, fuskarta da faffadan murmushi. Ya karaso cikin
sassarfa ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yace “don’t you
ever do that to me again” ta kwantar da kanta akan
kirjinsa tace “am sorry my Lion. Bana son in tayar maka
da hankali ne” yace “kinsan tashin hankali da naji kuwa?
Kinsan da yadda nazo asibitin nan kuwa? I tot karya suke
yi min da suka ce lafiyar ki kalau, I tot ba zaki iya haihuwa
ba tare da ni ba” tace “I missed you sosai, nayi ta kiran
sunanka” ya danyi dariya yana dago fuskarta da hannun sa
daya, taji kunya ta mayar da fuskar kasa.
Ta zaunar dashi akan kujerar da take dakin ta mika masa
babyn hannunta, ya dan leka cikin diaper dinsa fuskarsa
kamar zata yage dan murmushi. Ta dauko dayar da take
bacci a kan gadon su ta mika masa itama. Ya rike su
hannu bibbiyu inya kalli wannan sai ya juya ya kalli wannan
ya kasa tantance wanne yafi kyau a cikin su. Yayi musu
addu’a. Tana tsaye a gabansu tana kallon su sai ta fara
buga kafa cikin shagwaba, ya dago kai yana kallon ta cikin
alamar tambaya sai tace “ni a ina zan zauna, sun tare min
gurin zama na” ya daga babies din da sauri yace “zo ki
zauna akan cinya” ta tafi ta zauna tana karbar daya, ta rike
ta da hannun ta daya dayan hannun kuma ta zagayo
wuyansa dashi. Sun jima a haka suna kallon kyautar da
Allah yayi musu sannan yace “Baffa ne da Ummah. Baki
ga yadda suke ta kokarin rike hannun juna ba?” Diyam tayi
dariya tace “babu ruwana sai na gaya wa Inna” yayi
murmushi yace “so kike ta biyo ni da muciya?” Sukayi
dariya a tare. Sai ta kwantar da kanta a wuyansa shi kuma
yayi kissing forehead dinta tare da sauke ajjiyar zuciya. A
hankali yace
“ALHAMDULILLAH”
Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani ikon kammala
wannan littafi lafiya. Allah ya kara salati ga fiyayyen halitta
(SAW) Allah kuma yasa muna da rabon ganin sa baki
daya.
Godiya ga fans dina wanda na sani da wanda ban sani ba
a duk inda suke, alkhairi ya kai muku har dakunan ku, ina
sonku sosai da sosai, idan babu ku to kuwa tabbas babu
ni.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button