BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________
® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com
★★★★★★★★★
Page…1⃣
★★★★
بسم الله الرحمن الرحيم
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikkai, tsira da aminci su tabbata bisa ga shugabanmu annabi muhammad(s.a.w).
Kamar yadda kuka sani cewa, ina Rubuta cikar muradin zuciyata kuma ban k’arasa ba, tabbas! Hakan ya faru ne, saboda wani k’wak’k’waran dalili da ya hanani k’arasa shi. Ina mai baku hak’uri masoya cikar muradin zuciyata da ku bi littafin Baki Biyu domin shima da nashi sak’o mai k’arfi, tare da Nishad’antarwa, da kuma fad’akarwa, had’i da soyayya mai zafi irin ta wannan zamani. Kuyi hak’uri ku biyoni, domin ganin yadda al-amarin yake.????????
*
“I love you Anwarah! Ke ce mace ta farko da na fara so a rayuwata ta duniya, wallahi bana jin akwai macen da zan iya so bayan ke, ke ce komai nawa, zuciyata da rayuwata duka na baki, don Allah kema ki mallaka mini taki rayuwar baki d’aya.”
Wani sanyi ya ratsa zuciyar Anwarah, wani shauk’in soyayya ya kwasheta, sanyi A.c dake d’akin na shiga duk wata kusurwa dake jikinta, sai taji a duniya babu wani yanayi mai dad’i kamar wannan. Hakan yasa ta jawo filon da ke bayanta ta gyarashi, da d’aura kanta a filon, yatsun hannunta ta saka a tsakiyar gashin kanta da ya bazu a fuskarta, tana dinga shafar gashin kan nata.
Lumshe idonta tayi, sannan ta bud’e su, tare da jujjuya kyawawan idanunta, sannan ta saki murmushi mai sauti, wanda zai iya jiyar da na kusa da ita, da kuma wanda take wayar dashi.
Jin murmushin da tayi, ya saka Faisal gane cewa, kalamanshi sun ratsa zuciyar Anwarah, don haka sai ya k’ara k’arfi gurin ganin ya narkar da zuciyarta da kalamai masu dad’i. Cikin hanzari ya ci gaba da cewa,
“Hmmm…! Ya sanyi idaniyata, kina jina kika barni inata zuba, ke kuma sauraro na kawai ki ke yi, ko ‘yar amsar nan ba zaki bani ba naji sanyi, bayan kin fini sanin kalamanki sun fi mini komai dad’in sauraro a kunnena, please my Anwarah! Ki ce wani abun mana.”
Murmushi shine abinda yafi k’arfi a zuciyar Anwarah, domin banda juyi a makeken gadonta, babu abinda take iyawa, domin Faisal ya gama kamata baki d’aya. Hakan yasa ta daure ta fara magana a kasalance,
“To ni me zan ce ne……bayan ko kalamanka suna rud’ani? My honey kaima kasan cewa, ina sonka so na gaskiya, a halin yanzu na kai stage d’in da kalaman kowa basa burgeni sai naka, Ina yi maka so wanda ni kaina a halin yanzu bansan ko wane iri bane, abu d’aya na sani, sonka da kuma k’aunar ka.”
“Da gaske my Anwarah?”
"Sosai Habibi nah."
"Me kike so nayi miki a matsayin gift d'in wannan kyakkyawan albishir da kika bani, wanda na dad'e ina dakon zuwanshi, sai yau na samu a gareki?"
“Hmmm….! ” Anwarah ta yi ajiyar zuciya, sannan ta saki murmushin da sai da Faisal ya ji a kunnenshi, sannan ta fara magana a hankali, ta sigar jan zuciyar wanda zaiji maganar,
“Gift d’in da zaka bani ai na rigada na samu, domin A halin yanzu nasan cewa, Anwarah ce kawai a zuciyar Faisal, don haka kula dani kamar yadda ka saba, yafi mini dukkan wata kyauta daga gareka, gift d’ina shine zuciyar my Faisal, idan na samu hakan komai yayi mini dad’i.”
“My Anwarah…!” Faisal ya ambaci sunanta da wata murya mai razana zuciyar Anwarah, sai dai ya kira sunan sau biyu, sannan Anwarah ta amsa sau d’aya, saboda tsananin rud’ata da kalaman sunan nata sukayi, bayan ta amsa ne, ya ci gaba da cewa,
“Idan dai zuciyar Faisal Tahir ne, Anwarah ta samu, kuma ki saka a ranki cewa, zuciyar nan taki ce ke kad’ai dear tah.”
“Nima ka sani, Idan dai zuciyar Anwarah Muktar Ahmad ce, to babu kowa ciki sai Faisal d’ina.”
Murmushi suka saki tare, wanda sai da suka shayar da kansu k’auna a waya a wannan daren, inda Faisal ya nemi yardar Anwarah da tayi mishi izinin ganinta a gobe, domin ba zai jure rashin ganinta ba.
Babu musu kamar yadda ta saba, domin Anwarah tana dad’ewa kafin ta yarda da mutun, ko da kuwa k’awace a makaranta, amma kasancewar Faisal k’wararre a fagen soyayya, duk iya turjewar Anwarah, sai da ta kamu da sonshi cikin wata guda, wanda take jin, ba zata iya rayuwaba, a halin yanzu sai sa Faisal.
Da kyakkyawar soyayya sukayi sallama, wanda hakan shine karo na farko, da wani ya samu damar yin waya da Anwarah har ya turo mata sautin kiss a waya bata ji ta tsaneshi ba, yin kiss d’in harda su replay na cewa,
“Na gode dear na.” Su kayi sallama da junansu, Anwarah ta jefar da wayarta gefen filon da kanta ke sama, sannan ta saka hannunta ta gyara gashin kanta da ya baje mata a fuska, ta turo d’an k’aramin bakinta alamar kiss d’in Faisal a bakin bata, sannan ta saki sautin k’arar kiss d’in da k’arfi, ta saki dariya da jawo bargon da ke gefen gadon ta rufe rabin jikinta tana dariya, sannan kuma cikin k’an-k’anen lokaci ta tsayar da dariyar da yin addu’a ta kwanta.
Faisal tunda suka k’arasa waya yake dariya, sai da ya d’auki lokaci mai d’an tsawo yana wani tunani a zuciyarshi, sannan ya sauka a doguwar kujerar da yake kwance, ya saka charging d’in wayarshi, ya fad’a toilet d’in d’akinshi yana dariya.
ku bini a hankali, a wannan karon, insha’Allah babu tsayawa, sai mun kai k’arshe, da yardar Allah. Akwai darasi da soyayya mai Amfani da marar amfani ciki, kuma ko wace abar d’auka ce, ku dai ku biyoni da Addu’ar nasara aciki.
Taku har kullum…..
Bee²Ta masoya♥
[10/20, 6:15 AM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????
___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________
® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com
★★★★★★★★★
Page…2⃣
★★★★
“Alhmdulillahil-lazi ahayana,ba’ada ma amatana, wa’ilaihin-nishur. Astagfirullah!.”
Addu’ar Anwarah kenan da take yi duk lokacin da ta tashi barci, sannan tayi mik’a da hamma.
Duba wayarta tayi, inda idonta ya kai akan agogon wayar ta-ta, da ya nuna mata 8:30am.
“Subhanallah! Kai! Amma gaskiya barcin nan ya yi mini dad’i, na gode Allah da period nike yi, da na lokacin sallah ya wuce ni sosai, amma me yasa yau momy bata tashe ni ba…. Ko tasan cewa banayin sallah ne?”
Da wannan zancen da tambayar kanta, Anwarah ta sauka a saman gadon tare da jawo towel a k’ofar toilet d’inta, cire rigar baccin jikinta tayi, sannan ta d’aura towel d’in da yin murmushin da ita kanta, ta dai ji ya zo a bakinta.
Nad’e gashin kanta tayi, sannan ta lunke rigar barcin nata a zuwa drawer d’in sleeping dress d’in nata ta ajiye, sannan ta fara gyara gadon da ta tashi, da jera komai ta yadda ya kamata a wurin zamanshi, sannan ta nufi dressing mirror domin d’auko air freshener ta feshe d’akin da shi.
Wannan na d’aya daga cikin halayyar Anwarah, wanda kowa ke farin ciki da murnar ya kasance tare da ita, domin tsaftar ta.
Bayan ta tabbatar da komai ya yi normal, sannan ta mik’i hanyar shiga toilet domin yin wanka. Tura k’ofar da za ta yi ne, taji ringing d’in wayarta na tashi. Hakan ya sakata juyowa domin amsa kiran wayar ta-ta, domin ta san ba zaya wuce momy bace.
Cikin hanzari Anwarah ta d'auko wayar tare da dubawa, wani murmushi ta saki, wanda sai da gefen kumatunta d'aya ya lotsa(dimple), sannan ta d'aga tare da zaunawa a gefen gadon nata da aza wayar a kunnenta tace,
“Barka da tashi aminin zuciyata.”
"Barka dai farin cikina, fatar ki tashi lafiya?"
“K’lau na tashi sahibi na.”
"Hmmm! Ni kuma wallahi ba k'lau na tashi ba."
“Innalillahi…..!.” Anwara ta fad’a da k’arfi, tare da dafa k’irjinta ta zaro manyan idanunta a waje, jin murmushin da Faisal ya saki ne, ya saka Anwarah natsuwa ta saki baki tana sauraronshi.