NOVELSUncategorized

RUWAN JAKARA 5

*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*                  
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_) 


                *RUWAN JAKARA*………….    
    { _idan baa sha abirni ba asha akauye_)} 
                *~LITTAFIN~*???????? 

*MARYAM HAMISU YUSUF (maman boy*) 

~TRUE LIFE STORY~“`page“` *5*Saida wutar anwar ta dauke na wani lokaci.. Baitaba tunanin haka hannun zarah yake da laushi ba… Ga wani irin dumin hannunta da yakeji….skin dinta so mmoisture,  Wata irin gigitacciyar ajiyar zuciya Anwar  ya sauke yana murza farar tsintsiyar hannuntna.. Still yaki sakin hannuna … 
Wani irin takaici ya cikamin  zuciya tamkar in Fashe da kuka nakeji.. Dan irin tantirancin da Anwar yazo dashi,  Kakaniyar fizge hannuna nakeyi Amma nakasa…raina yayi masifar baci. Tuni idanuna suka soma ciko da kwallah   Lokaci na farko da wani mahaluki Wanda ba muharramina ba ya taba taba  jikina…  “Kacikamin hannuna mana.. Kasan kuwa haramcin hakan.. Allah yayimin tsaridakai…”. 
Na idar da maganar ina kuma kokarin kwatar kaina.. Wasu irin kwallah suka cikamin idanu masu zafi…. Lokaci guda naji masifar tsanar ya anwar musamman yadda ya zubamin idanunsa yana kallon face dina yana jifata da murmishi … 
Sassauta rikon da yayimin yayi yana murmishi. Wanda yakuma konamin zuciya.. Basar dani yayi tare da sakin hannuna  bakidaya “me yasa kike tsoron mutane  ko ni abun tsoro ne da idan  kin ganni sai Ki dinga guduwa.. Ina fatan kinsan alakar yan uwantakar dake tsakaninmu you all know bazan cutar dakeba okey? “… 
Yadda nakejin zuciyata tamkar ta fashe na Gaza furta komai… Hakan yasa ya cigaba da cewa… “Meyasa kika tafo ba tare da kinyi sallama dakowaba?  “. 


Sai a lokacin na watsomasa idanuna da suka soma sauya Kala… “Ina da wurin zuwa a lokacin “.. 
Na basa amsa  atakaice. . 
Kafa ma lips dina idanu yayi yadda nake sarrafasu yayin furta kalamai bakaramin kara rikitasa yayi ba… Har ya fara hango tsotsar lollipop din dazai musu duk randa suka hadu… 
Lumshe idanunsa yayi tamkar maijin bacci.. Ya na kuma kara kokarin basar dani.. Daga kafadunsa yayi kafin yace “nazone na gaida umma ne nima  thats’ all”…. 
Ya fada tare da kokarin kutsa kansa agidanmu… 
Wata sabuwa tunda na taso bantaba ganin ya anwar yazo inda muke ba sai ayau….banma yi tunanin yasan inda muke ba sai yau…  
Da sauri nasha gabansa…. Hakan yasakashi kara tsayawa… Ya Kafawa fuskata idanunsa saurin dauke idanuna nay na saukesu gefe i ina fadan”da ka  kabari nayi  maka iso… Bai kamata ka fada gidan mutaneba batare da izninsuba.    “

Biting lips dinsa yayi duk da yadanji zafin hakan… Karewa gwamutsattsen gidannamu kallo yayi aransa yana fadan “ko ina gidan yake da zaa wani tsaya taking excuse…Baya tunanin ko Karen gidansa zai iya rayuwa a wannan muhallin,  Idan banda tsautsayi da tsantsar nacin sa mai zaiyi awannan kutsatttsen lungun… 
Ja dabaya yadanyi tare da harde hannayensa a faffadan kirjinsa.. yadan saki murmishi… “To ina jira jeki sanar musu da zuwana”


Ya fada yana daga min gira…. 
Faire fuskata tayi ban kuma kallon inda yakeba , Shiga nayi gidan na sanarwa umma zuwan ya anwar… Ai Baki daya ta rikice.. Tsabar Murna da al ajabin ganinsa …. Jikinta har rawa yakeyi ta sabi gyalenta ta fice da kanta tayiwa anwar iso har dakinta.. Ta shimfida masa tabarma… Ruwan randar mu masu sanyi ta debo masa a kofi ta ajiye sai sannu takeyimasa… 
Nikam bankara bii takansaba na wuce makaranta… 
Dakyar ya iya shan ruwan da ummah ta debo masa dan kyankyamin kofin yakeyi.. Duk da tsantsar tsabtar da ummah take dashi…. 
Amma fa fafur yakicin abincin data ajiyemasa…. Idanu kawai yake rabawa.. Burinsa ya ganni agidan koda babu hijab ne dan yasan duk ustazancina dole na cire abaya agida… 
Saidai ko tafiyata bn yarda ya ganiba na ficewa ta zuwa islamiyya…
 Bayan sun gama gaisawane… Ummah tasoma baiwa ya anwar hakuri akan abinda na fadamata “kayi hkr anwar.. Wlh nikaina bansan meke damun zarah ba… Ina laifin wanda ya kulaka… Kayi hakuri dakaina zan taso keyarta saita  baka hakuri… Wannan ai rashin wayo ne irinnata”… 
Ta idar da maganar taNata Mita… 
Wani irin dadi ya anwar yaji na abinda umma ta fada.. Yaji dadi da ummah ta kassnce a haka Tabbas zata zamo masa tsani anan gaba… 
Murmishi yayi kafin yace “bakomai yarinta ce ai kuma zata daina “…. 
Fira suka dan taba still umma bata daina basa hakuri ba.. 
Dazai tafi dubu hamsin ya dire mata cas… 
Anan fa umma ta gigice ganin kudin da ya ajiye mata..baki Yaki rufuwa abun nema ya samu . Hatta gwaggo kwazo saida ya yagamata nata kasonta… Har bakin mota ummah ta rakasa sai godiya take zuba masa kamar wata marokiya…. 
Cike da nishadi ya anwar yabar unguwar mu….

Ina shigowa makarantar na tsinci kaina da wucewa office din malam kamal… Jinayi kirjina na tsananta bugawa… Cikin karfin hali nayi sallama na shiga… 
Zaune  Yake akan kujera yana dubawa wasu dalibai yan mata wani littafi da suka kawo masa domin. Karin haske akai… 
Tun kafin na yaye nikab dina ya jefomin wani irin narkakken murmishi tare da amsa sallama ta ya bani izinin karasowa… 
Hakan ya tabbatar min da ya shaidani…. 

Cikin girmamawa daliban suka gaidani… Wadanda zasu kai sa’annina koma su. Girmeni..  Nan da nan ya sallamesu ya bani izinin zama akujerar dake fuskantarsa… 
Zama nayi tare da yaye nikab dina… Sai naji wata irin kunyarsa ta rufeni tamkar a lokacin nakejin umma take masa wulakanci… 
“Malamata sai yau zan ganki… Na lura guduna kikeyi.. Fatima na fara takuuramiki ko? “
Yadda yakemin maganar tare da tsareni da idanu..ya sani saurin dago da kaina idanuna suka gauraya da nasa nayi saurin ssukar da kaina kasa.. Nan da nan idanuna suka kawo kwallah… Muryata na rawa nake masa magana cikin harshen larabci…. “Ba haka bane ya mu allim daman .. Daman…. “
Daman me? “
Ya jefomin tambayar shima cikin harshen larabci…. 
Na cigaba da cewa “daman nazone na baka hakuri akan abinda ummah tayimaka… Kayi hkr.. Bazaka ta6a fahimtar ummah na ba “… 
Na. Idar da maganar ina hawaye… 
Wani irin tausayina ne ya rufesa… Mikomin hankacif yayi, ba musu na karba ina share hawayen. . 
Furzar da ajiyar zuciya yayi kafin ya dubeni “wlh Fatima banji komai ba… abinda nasani shine munason junanmu… Ki manta da abinda umma tamin.. Domin ni anan na barsa.. Kidaina kukannan… Idan Allah ya ruvbuta abu… Wlh saiya tabbata… Babu mahalukin da zai Hana… Idan Allah ya kaddara kedin mata tace… Allah ya Riga tya rubuta kuma saikiga ya tabbata… Andauuke alkalluma.. Takardu kuma sun bushe babu mai canja kaddarar Allah …. 

. maganganun malam kamal sunyi matukar sanyaya min zuciya….. Da haka ya dinga rarrashina har saida yasakani yin dariya… 
Shima dariyar yayi yake fadan “wannan shine dalilin da yasa kike boyemin kyakyyawar fuskar nan taki… Shysa kike guduna ko Fatima? “… 
Yadda yakemin maganar da yadda ya kafeni da idanunsa yasa duk nauyinsa da kwarjininsa ya cikamin ido…. Akunyace na tashi nabar office din ina Yar dariya… 
Na daga cikin abinda ke dada sawa malam kamal na nacemin hallitar kunya da Allah yamin… Hakan bakaramin burgesa yakeyiba…. Lallai kunya ado ce Ga ya mace!!! 


Ina shigowa gidan na tarar da umma naTankaden garin masarar tuwon dazata tuka na dare suna fira da gwaggo kwaZo…. 
Hijab dina na cire na ratayata a kyauren dakina na ajiye Jakar makaranta ta… 
Na dawo wajensu umma na karbi tankaden da takeyi inayi…. 

“Ke kuwa batula kun gaisada yayanki anwar… “
Tambayar da umma ta tillomin kenan.. Wanda tayi sanadiyar rage faraar dake fuskana…. 
Kallon umma nayi da take jiran amsata nace “eh mungaisa “
Na bata amsa a atakaice… Da alamu  maganar tawa bata shigetaba… Dan na lura yadda  take ballomin harara… “Gobe in Allah yakaimu Ki shirya kafata kafarki zamuje gidan Alhaji mansoor Ki kara baiwa anwar hakuri., na fadamasa ma zuwannamu”

Ai bansan lokacin da nasaki rariyar dake hannuna ba… “Nashiga uku umma… Ni ba abinda nayimasa meyasa zan basa hakuri… “
Na idar da maganar ina duban ggwaggo kwazo da rinannun idanuna da suka sauya Kala inaso ne tashiga cikin zancen… 
Duka ummah takaimin da bayan hannunta mai shegen zafi.. Saida. Na saki Yar kara… 
Tana huci take maganar “shiyasa nace babu inda kika baro ubanki wurin taurin kai na tsiya… Da kafiya…tsabagen bakincikine kawai irinnaki.. Har gida yaronnan yazo babu KO canji ya ajiyemin dubu hamsin yan dubu dubu   Amma ko gaisuwar arzikibakiyimasaba. To wallahi ko zaki mutu sai munje “. 
Jin yadda take daga murya kuma duk akaina Ga bacin ranta ta silata… Cikin kuka nake magana “ummah dan Allah kiyi hakuri.. Zanje wlh.. Kidaina fadan hakanan dan girman Allah… “
Ai kamar kara tura ta nayi… Takuma hawa sama tana tijara
Saida gwaggo tasa baki sannan tayi shiru… Anan gwaggo ta dinga rarrashina… Nayi shirune kawai.. Domin na samawa umma na natsuwa daga masifar da takeyi… Amma zuciyata tamkar tayi bindiga nakeji……… 

Saidai har lokacin ummah ta dauki zafi sosai…… 
A dakinta na sameta tana shirya kayanta a wardrobe tunda tamin kallo daya ta watsar bata kuma kallo na ba… Hakan yasa na kuma fashewa da kuka dan idan akwai abinda nake
 tsoro bai wuce naga ummah na tana fushi ta sila na ba…. 
Rike kafafunta nayi ina kuka inabata hakuri Amma tayi birus dani… 
Rai bace gwaggo kwazo ta hankado labulen dakin ta dagoni tanayiwa ummah fada “waike wane irin taurin kai ne dake hajara, yarinyar nan ta batamiki kuma tana rokonki ya kamata komai ya wuce… Kinsan wannan zafin zuciyarka dole Ki rage sa “… 
Fada sosai gwaggo ta dinga yiwa ummah harsaida ta fara saukowa sannan gwaggo taja hannuna muka fita tana kuma rarrashina…. Shigowar Anwar arayuwata ya fara zama babban kalubale agareni… Lokaci na farko Dana fara tsanar wani mutum a zuciyata kuma dan uwana……


Maman boy

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button