NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 9&10

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH**SPECIAL GIFT TO…*
*MMN MUHAMMAD*9⃣&1⃣0⃣Tinda Malam ya fita be qara yiwa yakumbo maganar auren nijlah ba,gashi Yau Har anyi wata guda, Dan haka yakumbo ta garzaya zuwa gidan jummai dillaliya Akan tanaso Akai nijlah birni itama tayi aikatau kosa Samu su rage zafi.

Dakyar jummai ta yadda Dan acewarta nijlah ‘yar shagwabace su Kuma alhazan birni Basu San shagwababbun yara indai ba nasu bane,,Seda yakumbo ta Hada da ban hakuri tare da cewa zata jama nijlah kunne..

Nijlah Najin batin aiki tayi murna tare da cewa bazata yimusu rigima ba,,nan yakumbo ta Maida hankali gurin tafiyan nijlah birni aikatau..

Yau nijlah da farin ciki ta Tashi sabida ana bikin yayar kawarta,tinda safe ta tafi Suna party, yayinda Ake al’adu irin Na Fulani.

Ke kikace kinaso amarya,,da bakyaso da ba’a Baki shiba,,haka ‘yammata suka riqa wucewa suna rera waqa,,gefe guda manyan matane dauke da wata yarinya ‘yar qarama bisa doki,,kawunan kowacce su dauke da kwalla da fanteka sai ‘yan komatsan Kaya!!!
 Ta ko ina suke shigewa,, wasu gada cikinsu suna rangada guda …


Tsaki mashkur yaja Yana kallan abokan nasa da sukabi tawagar Yan Kai amarya da kallo,,, washe Baki Bello yayi Yana cewa kagani fa,, aure ya tabbata,, Allah yasanya alkairi,,duka sauran Suka amsa,da ameen  Banda mashkur Daya hade giran Sama data qasa…

Kai dallah Malam ware,idan zaka zabo yarinya a karkaran nan ka zaba,bamusan wannan miskilancin naka,, daba kaiwa zuci yayi ba..

Allah ya sawaqe,,ni duk garin nan babu yarinya data isa aura agurina,,Dan wallahi Basu Kai Mata ba,,Zan so kuje birni Kuga inda Mata suke,, hhhhh Bello ya fada Yana kallan mashkur..

Kai kujimin Dan rainin hankalin nan to idan ba Mata bane suwaye””‘ yauwa tambaya mana Shi cewan Nasir dake zuwa gurin…

Kwailayene,, ko nayi karya,, gaba daya suka amsa da cewa kwarai ma kuwa..


Tabe Baki mashkur yayi Yana cewa,,Ku duba yarinyar nan indo, dududu shekaranta nawa Amma har Malam ya’u ya auran da ita?

eh mana kuma Ka zuba ido nan da wata Tara zata iya haihuwa,, ai mu matanmu na karkara da iya zaman aure suke ba irin naku na birni ba..


Dariya mashkur yayi Yana Sosa Dan yafisu Sanin abinda yake Gaya,,sedai su bazasu gane hakan ba,,sabida nasu al’adan suka sani…

Shirune ya ratsa gurin kafin Nasir yace,, to wai Kai mashkur dama ba soyayya kake da nizlah bah” qayataccen murmushi mashkur yayi Yana Sosa Kai yace,,

Ai nizlah kanwace agareni,,ina kuma yimata so Wanda bansan irinsaba,, dan da ace ta isa aure nizan aureta na kaita can birni itama ta waye,,


Dariya suka sa suna kallan mashkur Wanda tinda aka ambaci sunan nizlah bakinsa yaqi rufuwa,,,

Koma dai menene munsan kana San nizlah,, Dan shaguwarku da ita abin dubawa ne, Nasir ya fada Yana kallan Bello..

Dariya Bello yayi shiko mashkur ya zuba musu Ido Yana kallansu,, be iya magana ba sabida Jin Kiran sallah da yayi..

Ni kunga tafiyana,, kafin kumin wani fassara na daban,, atare suka tashi suna qara jandada masa abinda ke zuciyarsa…

Sedai Shi Babu wannan a ransa soyayyar Yasmeen kawai yakeji,sedai Yana yiwa nijlah so irin Na tausayawa Amma Bada aure ba.

        *******************

Uhmn uhmn,, Allah ni saikin Bani biyar naje dandali,, yaushe raban daki Bani biyar dinki,, kodan kinga Dan birni Yana Bani,,kayya nijlah,, Nima Bani dashine,da inadashi Babu abinda Ze Hana ni baki..

Turo baki nijlah tayi tana kuka tare da birgima a qasa,, kayya mezan gani haka sukaji Malam ya fada,,yakumbo kodai Wani Abu kikayiwa yarinyar nan..


Kai madai Malam Sai kace bakasan halin nijlah ba,, wannan kukan daka ga tanayi Bana komai bane illah Na naira biyar,, ita adole Saina Bata biyar ta kashe,Nace Bani dashi ta kwanta tana birgima,,kaga Idan kayan jikinta yayi datti Sai Muga inda Zan samu kudin sabulun wanki..

Girgiza kai malam yayi Bayan yagama Jin bayanin yakumbo,,nijlah Ko Bata daina birgima ba Dan Har tirken dabobi ta kai tanayi…


Ahankali Malam ya taka ya isa Har inda take ya kamo hannunta”ba musu ta tashi tana turo baki,,kiyi hakuri kinji nijlah ta,,gobe Idan Allah ya kaimu naira Goma Zan baki kije dandali kisai Duk abinda kikeso..

Kawu dagaske kake,,nijlah ta fada tana kallan bakinshi,, kai nijlah meyasa wayenki yayi yawa,,kin tabaji Malam yayi Karya??sukaji yakumbo na tambaya..


Shiru nizlah tayi tana girgiza kai,,Sai kuma tace,,Naga yataba cewa Nima za’a kaini birni nayi aiki irin na jummai,Amma haryanzu be kaini ba,,Kuma Naga hajiyar tana zuwa…

Bata rai Malam yayi yace,kinga nijlah banasan shirme,,kima ajiye wannan maganar Babu ita,,haba Malam ya zakayi haka,,zuwa aikin nizlah shine cigabanmu,,kana Dai kallo abinda zamu kai bakinmu,,wahala yake mana..

Yakumbo,,Malam ya Kira sunanata Har sau uku,,amsawa tayi tana kallansa,,kisani Daga Yau nafasa kai nijlah aiki,,auran da ita zanyi..

Zaro Ido yakumbo tayi tana kallan nijlah,da tinda aka Kira aure tafara rawa tana juyi,,bakin yakumbo na rawa tace Malam aure fa kace,nawa shekarun nijlah,,yake,saifa gambon wata take shekara Goma..


Ni wallahi nayi tinanin ka janye wannan maganar danaji kwana biyu Baka qara yiba.


Eh, nasani,Naga Dai ba haramun bane,,damu zauna da ita,cikin wahala Ai gwara taje can gidan mijinta Kota samu ladan aure,, wannan wanne irin ladane,,nijlah fa Ko wanke wanke Bata Iya sosaiba,,balle azo maganan gyaran gida,,nidai kayi hakuri a kaita gidan aiki hakan zefimin kwanciyarsa hankali…

Hmm Ni kinga tafiyana,, Naji an tada Sallah,,fita Malam yayi yabar nijlah Na rawa tana cewa yakumbo Nima Zaki saimin wannan abun da Ake dafa tuwo..


Ke dallah rufemin baki,ki Kuma Dena wannan rawan kan,,Ko an gayamiki auren Cin tuwo ne,, fari nijlah tayima yakumbo tana cewa,,eh mana nidai gwara akaini gidana,,nasan Ko Goma Zan riqa samu Ina zuwa dandali,,


Acan masallaci Bayan an idar da Sallah Malam ya matsa kusa da Liman ya gayamasa Magana a hankali,, murmushi Liman yayi Yana cewa,,kayi daidai Malam hukuncin daka yanke yayimin Dadi..

Har mutane sun fara bita akace su dawo za’ayi wata Magana,, lah mashkur zo muje naga mutane na koma cikin masallaci,, jeka kawai nizan jiraka ana,,sabida sanin hali yasa Nasir da Bello suka barshi anan su suka dawo cikin masallacin..

Liman ne yafara magana,,to jama’a Allah ya kashe Yaba Wani,,game dukiyar aure Kuma yake sha’awar qarawa mace yazo gata,, Ko saurayin daya shirya,, charaf,,Wani tsoho yayi saurin Daga hannu..

Malam ne ya katse Liman ta hanyar cewa,, *’YAR SADAKA CE* to kunji abinda Malam yace,,yarinya sadaka ce..


Yauwa ga Wani Chan ansamu Liman ya fada Yana nuna tsohon mutumin dake rankwafe Yana murmushi,,yauwa Ala gafatta Malam matso kusa Liman yace da wannan tsoho,,matsowa tsoho yayi kafin Liman ya tambayeshi.

Menene sunanka,,sunana laman ya’u,,to Malam ya’u,,ita wannan yarinya da kace kanaso sunanta nizlah..

Nijlah,, Nasir ya maimaita Sunan tare da fita aguje Yana Kiran mashkur,,

Mashkur mashkur,Dan Allah mashkur kazo ka cece yarinyarnan indai soyayya na gaskiya kake yimata,,kai lafiya wacce yarinya kake Magana,,bakin Nasir Na rawa yace nijlah ce,,gata can za’a Bada sadakanta..

What kana nufin aurenta za’a Bada,,eh wallahi kayi sauri muje Kar a daura auren,,da gudu suka nufi masallacin mashkur Na tinani a cikin zuciyarsa…


Yanzu Idan na Karbi auren nijlah ya zanyi da Mummy,,Waze yadda temakonta,nayi,tayaya Zan fahimtar da iyayena,, Daga zuwa bautar qasa na biqe da aure,,auren ma Na qaramar yarinya Wanda Bata wuci shekara Goma ba!!!

Da wannan tinani suka Shiga cikin masallaci,sunyi sa’a baa daura auren ba,,sedai ana gab da daura wa,,ku dakata Nasir ya fada Yana nuna mashkur,, wannan shiyafi dacewa da auren nijlah indai sabida Allah za’a Bada sadakanta..

Wannan gaskiya ne, mutane suka amsa Suna goyan Bayan mashkur”” Malam ya’u Najin haka yace Sam be yadda ba..

Akan me nasamu Mata zakumin bakin ciki,, hakuri Liman ya Shiga ba Malam ya’u Amma Duk da haka ya dage Shi saiya auri nijlah..

Nasir ne yace kaga tsoho karka damu,,wannan Ze Baka naira dubu Goma kabar masa ita..

Kai yaro kalla idona Malam ya’u ya fada Yana zaro Ido waje..
Atare Nasir da mashkur suka zuba Alhaji ya’u Ido Suna sauraransa.
Nan alhaji ya’u yacigaba da Magana,,wallahi Ko naira dubu hamsin zaku Bani Bazan hakura da auren nijlah ba,,Har Sai kun auramin budurwa me suffa irin ta nijlah,,

What? What me kace tsoho,,to wallahi Ko ka amsa dubu Goma Ko kayi asara gaba daya,,nan Nasir ya juya inda liman Ke zaune yace..

Liman kaga wannan abokina ne dashi mukeso adaura wannan aure indai Malam ya amince.


To Malam Kaji abinda yaro yace,,Liman yafada Yana Kallan Malam,,

Sassanyan ajiyar zuciya Malam ya safke kafin yace,,Liman Bani da zabi kawai kayi Mata zabin daya dace,,to shikenan Liman ya fada tare da gyaran murya.

A matsayina na limamanin wannan kauye Zan auran auren nijlah da wannan yaro,kai yaro Mene sunanka”” kasa Magana mashkur yayi nasir yayi saurin cewa mashkur Hussain.

To Masha Allah, mashkur ka amince Zaka auri nijlah,, mashkur besan lokacin daya Daga kai alaman eh ba.

Ba’a Wani bata lokaci ba aka daura auren nijlah abbakar tare da zankadeden angonta..

Nan Alhaji ya’u ya riqa zagege zagege Yana cewa an nuna bare yafisu,, ya qara da cewa Allah yasa Dan birni ya siyar da nijlah kowa ya huta,,maganganu marasa kai da gindi ya riqayi Har Saida manyan ‘ya’yansa suka fiddashi a masallacin.

Mashkur Na fito yaji Wani irin tashin hankali ya ziyarci zuciyarshi nan ya barsu Nasir Suna tattaunawa da Malam Dan koya tsaya Baze Iya cewa komai ba sabida tsantsar tashin hankali..

Jiyayi Idan beyi waya da mummy ba Baze samu kwanciyar hankali ba, Dan haka ya nufi inda suke waya,, Da zuwashi ya fara Kiran layin mummy sedai wayar Na Shiga mummy taqi amsawa tana me Jin haushinsa.

Karin ya qara Kira wayar yaya ta shigo,,nan yayi saurin kai hannu ya dauka Yana Kiran hello yayan mashkur,,ba Wani yayan mashkur da Zaka kirani,,kasa mana uwa a tashin hankali sabida bakasan me kake ba Ko mashkur???

Kayi hakuri yaya wallahi ban tafi da fishin mummy ba Har Saida ta amince Na tafi”
Karya kake mutumin banza da wufi,ahaka kakeso karatun yayima albarka?
Kayi hakuri yaya mashkur yafada zuciyansa Na halbawa day sauri da sauri.


Inaso ka Bude kunnanka da kyau ka saurarani” bakin mashkur Na rawa ya amsa da to yaya.

Kaje yanzu ka Hada kayanka ka dawo gida Idan Har bakasan bacin ranmu” Wani irin Abu mashkur yaji ya buqi zuciyarsa Har Sai da ya dafe da hannunsa yace ,yaya Yau fa kace?

Eh Yau Nace Ko bazaka iyaba Ni a gobe Na dawo qasar nazo Har inda kake,,ah ah yaya kayi hakuri Zan dawo yafada yanajin kuka Na zuwa masa,,yadau Fi kyau yaya ya fada Yana katse Kiran.

Hannu mashkur ya Dora akai Yana cewa Na Shiga uku Ni mashkur meya kaini auren nijlah gashi Ina neman sa kaina a 100,yanzu yaya zanyi?

Be Iya samun amsa ba yaji Wani Kiran Na shigowa cikin wayarsa” Yana dubawa Yana aunty ladefa,zaro Ido yayi waje Yana tinanin fadan da aunty ladeefah zata masa,sedai Baze Iya Qin daukaba sabida yasan abinda Ze biyo baya,hannunsa Na rawa ya dauka Yana Kara wayar a kunne aunty ladeefah tafara da……………….

Dan Allah Dan annabi Idan kinsan bazaki Iya comments ba Karki soma karantawa.Comments &share????*Momn sultan takuce*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button