NOVELSUncategorized

SOORAJ 20

????????????????????????????????????????

             *SOORAJ !!!*

  *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna

#romance

           *Chapter 20*

Numfashinta ne yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, saboda tsabar tsananin tsoron da ta samu kanta aciki, ƙasa tayi da idanunta, tana me kallon hanun da aka rufe mata bakinta dashi, hanun namiji ta gani, wanda ke ɗauke da kwantattun gargasa da sukayi luf akan farar fatarsa,  jikinta ne ya ɗauki tsuma, wani irin tsoro mai ƙarfi ya ziyarceta,   wani ɗan corridor dake cikin kitchine ɗin ya shiga da ita,  ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi, ba tare da ya sake mata bakinta ba, ya juyo da ita suka zama suna fuskantar juna,   idanunta ta zaro waje tana me sake kallonsa.  Sake mata bakinta yayi, tare da ɗaura hanunsa akan laɓɓansa cikin ƙasa ƙasa da murya yace.
“Shiii!! kada kimin ihu, ina da baƙi a falo ki zauna anan kada ki fito”  yana gama faɗan haka ya saketa,  tare da juyawa ya nufi hanyar fita daga cikin kitchine ɗin,  bakinta a wangale haka ta bisa da kallo har ya fice, wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da jingina bayanta da jikin bango, har acikin zuciyarta tayi bala’in tsorata, duk atunaninta wanine daban yazo saceta,  hanunta ta ɗaura adaidai kan chest ɗinta dake ta bugawa da ƙarfi, aƙalla takusan mintuna 9 ahaka, kafun tasamu ta iya daidaita nutsuwarta, kan wani plastic chair dake cikin kitchine ɗin ta zauna,  tare da kifa kanta akan cinyoyinta.  

Shikuwa Sooraj yana barin kitchine ɗin, komawa cikin falo yayi, wajen  abokan business ɗinsa, da suka kawo masa Ziyara, yana zaunene amma gaba ɗaya hankalinsa naga ƙofar kitchine, sam  bayaso tayi gangancin fitowa,  ba tsoronsa ganinta da zasuyiba, tsoronsa shine wani irin bahagon kallo za suyi masa?  tabbas ba lallai suyi mishi kyakkyawan zato ba, shikuwa ko kaɗan bayason ayi masa irin wannan kallon.  Sunjima suna tattaunawa akan business ɗinsu, kafun daga bisani sukayi masa sallama, har bakin motarsu ya rakasu, shima daga rakiyarsu bai dawo cikin gidanba, motarsa ya shiga ya fice daga gidan gaba ɗaya.

Jin anata ƙiraye ƙirayen sallan ne yasata takowa saɗaf saɗaf taɗan leƙa cikin falon,  ganin ba kowa acikin falon yasa ta sauƙe ajiyar zuciya. Fitowa daga cikin kitchine ɗin tayi ta wuce ɗakinta.  

*MONDAY*

Yau yakasance ranar da zasu fara exam, 8:00 am daidai zasu shiga exam ɗin inda zasu fara da Biology.   Zaune suke akan wani bench su dukansu ukun,   kallon Shukra da Nasmah Ziyada tayi murya asanyaye tace.
 “Tun safe ƙirjina yaketa bugawa, wani irin tsoro nakeji, anya zan iya zana exam ɗinnan kuwa?” 

Kallonta Shukra tayi tare da ɗanyin murmushi.
“Zaki iya mana, ki daure ki ƙarawa kanki confidence, amma ai babu wani wahala”   Shukra tace haka cikin son ƙarawa Ziyada ƙarfin guiwa, shiru sukayi daganan basu sake cewa komai ba.   Takwas na cika dai dai suka shiga jarabawa, 1 hour suka ɗauka suna rubuta exam ɗin, cike da jin daɗi  Ziyada ta miƙa booklet ɗinta,  sannan tafito daga cikin exams hall ɗin, tsayawa tayi ajikin wata bishiya tare da lumshe kyawawan idanunta, wani nishaɗi takeji acikin ranta saboda tana da yaƙinin cewa zata ci duka tambayoyin da ta amsa.  Su Nasmah ne suka fito nan suka haɗe suka ci gada da hiransu,   kasancewar yau paper biu zasuyi  ƙarfe 10 daidai suka sake shiga wata jarabawan na Islamic.  Suna kammala jarabawan  kowa ya fara haramar komawa gida, tsayawa tayi tare da dafe goshinta,  gaba ɗaya ta manta batace da Kamalu driver yazo ɗaukarta da wuri ba,  gashi yanzu sun gama exam kowa na ƙoƙarin ko mawa gida.   Kai tsaye ta nufi babban ƙofar gate ɗin makarantar.   Tana fita daga cikin gate ɗin ta soma kalle kalle, batasan ya zatayi ba don bata da wata mafita, gashi su Shukra sun tafi.  Wata baƙar motace tazo ta tsaya agabanta, hakan yasa ta ɗan ja baya.   Ahankali ya sauƙe glass ɗin windo’wn motar,  kyakkyawar fuskarsa ta bayyana wacce ke ɗauke da murmushi.

Kallonshi tayi tare da sauƙe idanunta ƙasa, tabbas bazata manta shiba shine wanda ta buge kwanaki.  

Murmushi yakumayi tare da buɗe murfin motar ya fito, takowa yayi har zuwa inda take, murmushine akan fuskarsa wanda suka bayyana dimples ɗinsa.  “Tsayuwa acikin rana bai kamaceki bafa ƴan mata” yafaɗi haka yana me ɗan ɗaga kansa ya kalli sararin samaniya.
Ɗago manya manyan eyes ɗinta tayi, tare da sauƙesu akan fuskarsa.  Idanunsu ne suka sarƙe acikin na juna, murmushi yaƙara yi mata tare da cewa.
 “Mai kikeyi anan? ba’azo ɗaukarki bane?” 

Samun kanta tayi ta kaɗa masa kai alamar “Eh”   

“Okay muje na sauƙeƙi agida” yafaɗi haka yana me ƙoƙarin buɗe mata murfin motar, ɓangaren mai zaman banza.

Saurin kallonsa tayi tare da ɗan matsawa can gefe, sam batajin zata iya shiga motar, ita da batasan kowa ba banda MR. HANDSOME (Sooraj)  yaza ayi ta yarda ta shiga motar wani, kalan ma yaje ya sayar da ita. Abunda tafaɗa acikin ranta kenan.

Ganin alaman cewa bata yarda dashi bane yasanyashi sake ɗanyin murmushi cike da son ya gamsar da ita yace.  “Calm down dear, i will not hurt you, trust me!”  

Yanzu kam salon kallon da tayi masa, yana ɗauke ne da ma’anoni masu yawa. Horn ɗin motar da taji abayanta ne yasata waigawa, ai kuwa Kamalu driver ta hango acikin mota, da sauri ta juya ta nufeshi, buɗe murfin motar tayi ta shiga,  ƙarasowa yayi har jikin motar,  sannan yayi knocking glass ɗin window, Kamalu driver ne yayi ƙasa da glass ɗin tare da ɗan dubansa,  shikuwa idanunsa akan kyakkyawar fuskarta yake, cikin ƙasa da murya yace. “Yace kin ƙi yarda dani ko? ba damuwa ki kulamin da kanki!” yana gama faɗan haka ya juya ya nufi wajen motarsa.  

Tafiya suke amma gaba ɗaya tunaninta yana ga maganan da ya gaya mata “Kikulamin da kanki!” mai hakan yake nufi kenan? tambayar da take ta yiwa kanta kenan gaba ɗaya kanta ya kulle, ahaka har suka isa gida. 

Tsaye yake agaban drawer, dagashi sai dogon wando fari dake sanye ajikinsa, yayinda murɗaɗɗiyar surar jikinsa ta bayyana, gaba ɗaya shape ɗin bayansa abun burgewa ne.  Kayansa yake cirowa daga cikin drawer’n yana shiryawa acikin trolly bag ɗin dake aje kan gadonsa. yana gama shirya kayannasa ya ɗauki wata rubber t-shirt yasanya ajikinsa.   Wata jaka ya ɗauko irin wacce ake goyawa a baya, buɗe jakan yayi ya zuba wasu takardu aciki,  saida ya tabbatar daya haɗa komai nasa wanda yasan zai buƙata, sannan ya ɗauki wayarsa ya sanya acikin aljihunsa, direct falo ya nufa.  Direct dinning area ya nufa,  haɗa tea ɗinsa yayi, tare da dawowa cikin falon ya zauna.   Sipping tea ɗin yake ahankali, yayinda lokuta zuwa lokuta ya ke kai dubansa  ga agogon bangon dake cikin falon. 6 pm daidai jirginsu zai tashi.  5:40 ya kammala gaba ɗaya abubuwan da zaiyi,  ɗaukan troly ɗinsa yayi tare da rataya jakarsa akafaɗansa,   yana fitowa daga cikin ɗaki, dai dai lokacin ita kuma tana fitowa daga kitchine, sanye take da riga da wando na pakistan sai kuma hijab dake jikinta.   Idanunsu ne ya sarƙe acikin na juna.  Da sauri ya ɗauke kansa, ya nufi hanyar fita daga cikin  falon, bin bayansa tayi da kallo harya fice daga cikin falon. Samun kanta tayi da kasa ɗauke idanunta daga bakin ƙofar fita daga falon,  komai nasa abun burgewane,   wasu irin hawayene suka cika idanunta, sannan suka samu daman fitowa alokaci guda.  Jingina bayanta tayi da jikin bango, tare da ɗan cije laɓɓanta, akullum rayuwarta ta baya, ta zame mata abun tunawa, tunanin babanta ne akullum yake damun zuciyarta,  tayi rayuwa cike da rashin gata da kuma ƴanci, ta taso cikin maraici, sam bata wani san menene daɗin mahaifiya ba, tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu,  har i’yanzu tana buƙatar sanin wacece ita, gaba ɗaya rayuwar da tayi abaya cike take da duhu,  Maraici, Kaɗaici, da kuma Ƙunci su suka cika rayuwarta ta baya, babu wani wanda ya damu da ita, itake shanye damuwarta komai girmansa, ɗan zamewa tayi ta zauna daɓas akan tiles ɗin dake malale a wajen,  lumshe kyawawan idanunta tayi, tare da soma murza ƴan yatsun hanunta.  Ƙamshin turarensa da taji yana shiga hancinta ne, yasanya ta buɗe idanunta da suke cike tab da ƙwalla, ganinshi tayi tsaye akanta ya zuba mata idanunsa masu matuƙar rikitata.   

Saurin ɗauke idanunsa yayi daga kanta, domin bazai taɓa iya juran kallon yanda ƙwayan idanunta ke cike da ƙwalla ba,  envelop ɗin dake hanunsa ya miƙo mata, hanunta na rawa haka ta amshi envelop ɗin, shikuma ya juya ya fita,  samun kanta tayi da kasa buɗe envelop ɗin jiki asanyaye ta koma ɗaki.

6:00 pm daidai jirginsu ya ɗaga zuwa sararin samaniya.  Jingina bayanshi yayi da jikin kujeran da yake zaune,  tare da lumshe idanunsa,   wani tunani da yazo ranshi ne yasanyashi sakin murmushi, lokaci guda kuma ya haɗe fuskarsa tare da buɗe idanunsa da sukayi jajur dasu. 

*** *** 

Wasa wasa har sunyi sati ɗaya da  fara exam, a ɓangaren Ziyada kuwa sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa tana amsa tambayoyin jarabawan da iyakayi mata, da duka iya ƙoƙarinta. 

Zaune take a inda aka tanadar musu don cin abinci, kasancewar yau ta riga su Nasmah fitowa daga ɗakin jarabawan, yasa take zaune ita kaɗai,  kanta ta kifa akan ɗan madaidaicin table ɗin dake gabanta wanda yake zagaye da kujeru. 

Wani irin ƙamshin turarene yashiga kawowa hancinta Ziyara,    lumshe idanunta tayi tana mai shaƙan ƙamshin turaren batare da ta ɗago kannata ba. 

Ahankali ya jawo kujeran dake fuskantar nata ya zauna.  Sexy eyes ɗinsa ya zuba wa ƴan yatsunta dake aje kan table ɗin.  Hakanan taji kamar akwai mutum akusa da ita, saboda hakane yasa  ta ɗan ɗago kanta, waro idanunta tayi cike da mamaki, duk da cewa aƴan kwanakinnan yaɗan matsa mata, amma kuma sam bata tsammaci ganinsa a wannan lokacinba.  Murmushi yayi mata tare da ɗage giransa sama.   “Surprise!”  yafaɗa yana me sake ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo.   Kawar da kanta gefe tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. 

“Idan kina cikin yanayi na damuwa kinfi kyau, but even at that, i don’t want to seeing you in this situation, ki ɗan saki fuskarki kinji ƴan mata na!”  Ya faɗi maganar yana mai langwaɓar da kansa gefe tamkar wani ƙaramin yaro.  Yanayin yanda yayi maganar shine abun daya sanya ta ɗan juyo ta kalleshi,  irin kallon daya keyi mata ne ya sanya taji jikinta yayi sanyi.    Yana shirin sake yi mata magana ne wayarsa ta soma ringing alaman shigowan ƙira.  Ɗaga wayan yayi tare da karawa akan kunnensa,  baiwani jima yana wayanba ya kashe, tare da maida wayar cikin aljihunsa.  Miƙewa tsaye yayi, tare da ɗan ranƙwafowa dai dai fuskarta.  in a silent voice yace.  “Kina da kyau sosai, komai naki me kyau ne, zanyi baƙin ciki idan kika kasance saɓanin tunani na!!”  yana gama faɗin haka ya juya ya soma  tafiya, binsa tayi da kallo har ya ɓacewa ganinta. Dai dai lokacin su Nasmah suka ƙaraso.  Shukrah na zama ta kwashe da dariya.  “Har angama shan love ɗin?” Nasmah tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin gumtse dariyarta. 
“Love kuma?” Ziyada ta tambaya.
Dariya Shukrah da Nasmah suka sanya tare da tafawa, ganin haka yasa Ziyada ci gaba da sabgoginta, domin ta sansu abu mai sauƙi ne su fassarata da wata manufar.

*** *** 
LAGOS NIGERIA.

SOORAJ!!!

1:00 am, ƙarfe ɗaya na dare, kwance yake akan makeken gadonsa, wanda yaji zanin gado na alfarma.  Sanye yake da white pencil jeans ajikinsa,  bai sanya riga ba hakan yasa  gaba ɗaya surar jikinsa take abayyane, musamman ma sick packs ɗinsa, wanda suka samu daman kwantawa raɗau akan fatar cikinsa,  sama sama yake jiyo motsin mutane acikin kunnuwansa, ahankali ya buɗe idanunsa,  aikuwa nan ya tabbatar da cewa ba karya kunnuwannasa keyi masa ba, tabbas motsin mutanene acikin gidansa,  saƙƙowa yayi daga kan gadon tare da nufar ƙofan fita daga cikin ɗakin, ahankali ya murza handle ɗin ƙofar ya fita, taku uku kacal yayi ya samu kanshi a babban falon dake gidan,  hanu yasanya akan makunnin ƙwan wutan dake falon ya kunna, kunnawansa yayi daidai da sakar masa bullet  da akayi akan ƙirjinsa, wani ƙara yasanya sakamakon wani irin zafi da raɗaɗi da suka ratsa shi, tun daga ƙasan ƙafarsa harzuwa tsakiyar kansa,  kafun yayi wani yunƙuri ansake sakar masa wani bullet ɗin akan hannunsa, wani irin azabane yaji yana huda jijiyoyin jikinsa, yana ratsawa ta ƙwaƙwalwarsa,  take idanunsa suka soma rufewa,  wani irin abu yaji acikin jikinsa wanda bai taɓa jin irinsa ba, take yafaɗi awajen baya ko motsi. 


*(Kuyi haƙuri saida na gama typing ya goge gaba ɗaya, da ƙyar nasamu nayi wannan, nasan kuna fushi dani amma dan Allah kuyi haƙuri????????????????????????)*     *Vote Me On Wattpad*
         @fatymasardauna

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button