DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL
Mami ta nufi haydar da kanshi a kasa ta tasa hannu ta daga shi Yana kallota murya kuka tace” haydar ina yake ? Ina boy Dina ? Tana magana tana jijigashi
Yace” Mami hakuri zakiyi inshallah za’agashi ya fada murya na rawa”
” Haydar boy ya fita gidana tun 8:00am gashi ganshi uku tayi har da minti na,ba’asan inda yashigaba iyye Wai Wana wani iri duniya ne muke ciki”ta durkusa a kasa tana kuka…
Ammi ta dagata da sauri tace” ki daina kuka za’a ganshi inshallah, kuzo mu shiga ciki”
Mami ta juya ga chief security tace” ku bance min dagani baga amfani ku ba” …
Da sauri suka bar gun don Suma sunfisu ciga tashi hankali
Suhaima ne zaune da hajiya binta, sanye take da wani half gown a jiki, wata maid nata na kasa tana gyara mata kumba kafa, a hankali ta dubi hajiya binta ta shagwabe fuska… Hajiya binta tace” yadai Baby na?
” Mummy tun jiya nake trying number Hubby yana shiga ama bai dauka, yau Kuma switch off ne gabadaya, kila ma da gangan ya kashe waya “ta fada murya a shagwabe
Hajiya binta tace” yo Baby na Mai kike ci na baka na zuba, nasha fada Miki cewa Kar kisami damuwa, shi Aliyu guda nawa yake, kawai ki Kira Daddyshi ki gaya Mai”
“A’a Mummy wallahi tsoro Daddy shi nakeyi, Allah Mummy shakkashi nakeji bazan iya ba” ta girgiza Kai
Hajiya binta ta tafa hannu tace” iyye baby duk fadi duniya na Ashe akawai Wanda kike shakka da tsoro , haba dai*2 Kar ki badani mana , kamar ba baki Kisha ba , ta nuna kirjita.. kwantar da hankali ki ai na Gama da uba , yaro muke jira yanzo hannu,kisan nawa na kashe da wuya danasha kafi tycoon ya Amince da aure, Dan kutumar burar uba danya Kai ne dasu, sai ayi dagaske, kawai ki kirashi ki gayamai”
Suhaima ta daka tsale tace” hoho sai mummy na” ta tura Mai gyaramata kumba tace” ke banza tashi ki bar na, kice ma lami akwai pant da brazier na Dana cire tasa yanda zatayi dasu Kuma ta gyarami daki”…
Da sauri jiki na Bari Yar
aiki ta Mike tace” toh hajiya ” ta fice. Suhaima ta binta da kallo tana yamutsa fuska..
Tace”Mmmy nakirashi yanzu ba matsala?”
.
” Ai baby na ki kwatar da hankali ki kamar kiyi filo da gawa, kirashi kawai ai mugama dashi”
Suhaima har da gyara murya za’ayi waya da siriki, ta dauki wayata ta dialing hot line din Tycoon da bakowa ke dashi ba sai family nashi..
CAPETOWN, SOUTH AFRICA..
Tycoon ne zaune a baki beach na babba birni Capetown na kasa south Africa, gaba da bayashi duk bodyguards ne, zaune yake aka kujera beach , da Dan karami table agabashi, samashi kuwa umbrella ne babba Mai fadi Yana Kare minshi rana, sai danne danne kawai yakeyi a laptop dake gabanshi Yana sipping Liptop…
Bodyguards dake rike da wayoyyisa ya karaso da sauri yace” Sir ur phone is ringing Kuma hot line ne” ya fada cike da girmamawa..
Fuskashi na kan laptop din yace” okay answer it, kila Aliyu be, basa matsala shi ba tun jiya bai kiraniba “
” A’a Sir bashi bane ” bodyguard din ya fada Yana Mika mishi waya..
Ya karba yasa a kunne, suhaima ko sallama tace” hi Dad”
Tycoon yayi murmushi yace” ohh siyama Daddy yakike?
Suhaima ta Bata fuska tace” Suhaima ne sir”
Yace” ohh Suhaima yakike?
Ko amsawa batayiba murya tsoro tace” uhm uhm da..da ma..dama ….
Yayi murmushi yace” saki jiki kiyi magana kinji suhaima am ur dad”
” Uhm Aliyu ne, tun jiya Ina Kira shi bai daukaba, yau Kuma a kashe, shine na Kira naji ko lafiya ” ta fada murya a shagwabe….
Dam yaji gabashi ta fadi yace” shi Aliyu ne number shi a kashe?
Ta amsa da eh Daddy”
Yace” hold on, kashe bara nakirashi”
Comment & share????????❤️????
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
DOCTOR ESSHA
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
_WRITING BY_
_J Hajara_
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION????????
Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣
Nan take ya dialing number Aliyu, number akashe, yanaa trying ba adadi, yace bara na mishi video call” ..ya jayo laptop nashi, daya Dana number Aliyu ko ringing baiyi sai yanuna disconnect, inyakara trying abun daya yake nunanawa.. .. ” bara nakira ammishi dai naji ko lafiya” yakirasu duka bawanda ya dauki waya..lokaci kam su Ammi sufita dukasu suduba ko aganshi ,Basu fita da wayaba… Ranshi ya Soma baci kawai yace bara yamusu video call direct da number gida yaga ko lafiya…layi ya Soma ringing ba’a dauka har Kira ya dauke, yasake dialing …
Rahma da shigowanta falon kenan taga Kira Daddysu, wana abun dai kamar tv ya bayana sai surutu yake Yana cewa” alert alert Daddy is calling” da gudu tafita sukaci karo dasu Ammi a hanya..
Jiki a sanyaye tace” Ammi daddy ne ke Kira Kuma video call ne”
” Inalilahi waina ilaihi raju’un” shine abunda Ammi ke ta nanatawa. ..
“Ammi kawai muje mu amsa Kar anunamishi komai nafaruwa” Suleiman ya fada…
Siyama tace” eh haka za’ayi Ammi “
Suna shiga wani Kira nasake shigowa, duk suka zauna suka natsu kamar ba komai..Haydar ya picking kira… Tycoon ne ya bayana a screen, dun dole duka suka sa murmushi dole,ya bin ya parlor da kallon daya baya daya, suka gaisheshi ciki girmamawa, ya amsa..
Ya Kai dubanshi ga Haydar ya jefa minshi tambaya” Haydar ina takwaraka?”..
Haydar yaji tambaya a bazata ya kasa motsi in ya kalli Ammi sai ya kalli mami… Ammi ta mishi Alama yayi shiru…
” Haydar nace Ina abokika? Yasake tambaya
Haydar ya tsure ya rasa wani amsa zai bashi …
Sofia ta amsa charaf idota da haweye ta Soma magana tace” Mami , Ammi kuyi hakuri, ta juya ta kalli tycoon tace” Daddy Yaya tun safe yatafi kaduna, kuma Ummi ta Kira tace baizoba, ba Ina ba’a duba ba’a ganshi ba” ta fashe da kuka …
Isa yasa hannu akai yace ” shikena yau munshiga uku”
A fusace Tycoon ya Mike cike da kidima da razana har jikishi na Bari yace” Aliyu nawa ne ba’agani ba tun safe” kit ya kashe Kira….
Mami da Siyama suka fashe da sabon kuka… Ammi tayi lalashi har ta gaji ita kanta daurewa takeyi.. su Fawaz ba motsi sanda aka Kira sallah la’asar tukun suka Mike zuwa masalaci …
Tycoon na katse Kira jikishi sai rawa yakeyi, yakasa natsuwa … Yace” ismail maza maza kiramin pilot ” ba da jimawa sai ga pilot ya karaso…
Yace” muje ku Nigeria zamu koma yanzu na” Yana jikishi na bari…
Ko yajira a bude minshi motar dankashi ya bude yashiga, aka tada motoci sai airport, private jet dayazo dashi ya wuce direct ya shiga , da sauri guards suka bi bayashi suna shiga jirgi na tashi.. bada jimawa su ka sauka Nigeria, kaduna airport , da sauri guards suka sauke motoci dake ciki jirgi.. saboda emergency iri haka suke ajewa..
A ciki motar kuwa sai ma driver matsifa yake Wai bai sauri, gudu kawai suke akan hanya kamar zasu tashi a sama , har suka karaso anguwar su Ummi , sai horn kawai suke zubawa , da sauri gate man ya bude gate din suka shigo…
Ummi dake sama balcony tana sauraro redio taga shigowar motoci tace” wato shakiyi yarona sai yanzu ya karaso, zanyi maganika ka ai” ta dauki walking stick nata ta fara saukowa tana zuba matsifa… Tana sauka taga Tycoon ne.
” Wato ma Kai ka rakoshi kenan ? Ummi ta fada cike da matsifa tana ta leleka ko zantaganshi..
Tycoon ya nufo Ummi yace” Ummi ba’aganshi ba, Wai yazo na kaduna ” ya fada jikishi na Bari”…