DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummi tace” iyye ku shagwaba Wana Kato da yawa, kamar shi haka ace ana wani lalashi shi, irishi a kauye su aje hudu biyar, ku gashi ku sagarta dashi, sai abunda yafada, irishi tsumagiya (bulala ???? )za ku neman ku chala mishi, ama ku……..

Mami ta katse ta Tace” yihakuri ummi, yaro ne, Yana bukata lalashi”

Ummi tace” iyye Wana kato ne, yaro, Mai aure wata gobe”

Aliyu ya hada fuska tam jiyake kamar ya wulata a waje.

Ammi ta zauna daf dashi ta rike mishi haiba tayi maganar kasa kasa Wanda daga ita sai shi sukeji tace” haba mana dan lalle Mami da daddyshi, yihakuri kaci wani abun ko, ummi kishi take shiyasa, inshallah zakaga ta, ama fa sai kaci abinci” yayi murmushi Wanda har dimples nashi suka lotse gabadaya.. Tycoon ya zuba musu Ido Yana kallo su gwani sha’awa uwa da Dan kenan, rabuwashi dagani murmushi Aliyu tun shekara jiya ama gashi Ammishi, ko minti bai bugaba, tasashi murmushi..

Aliyu yace”Allah Ammi” ta gyada mishi Kai… Ai da sauri ya dauki coffee, ya shanye tas ya aje cup, tayi dashi yaci abinci, yakici ta hakura ta bashi magani, sanan aka fara ruqiya, bin malamai yake da kallo, suna qira’a ya na ratsashi, yanaji wani sanyi aranshi,( Aya Allah rahma), tun Yana bin har bacci ya bige dashi agun.

Ummi tasa kabara tace” ai sutafi shikena sauki yazo.. Tycoon dakashi ya daukeshi ya haura dashi dakishi har ka gado, ya gyara Mai kwanciya, Yana fata Allah yasa komai yazo karshe.


Suhaima tuki take Rai a bace, speed tasa ma motar tana gudu Kamar zata tashi a sama, sai dai a kauce mata a hanya badai ita ta masa ba, har ta karasa gida, wani mahaukaci horn take dannawa kamar zata ballashi, Kara ya cika ko’ina . Baba maigadi har yafara bacci, Yana ji Kara horn a firgice ya farka, ya fara Bari dun yasa Mai horn din dako Alhaji ma baya haka, da sauri ya Mike don yaje ya bude mata gate, suka ci karo a hanya har ta shigo, tabar motar a waje, suhaima ta dauki hannu ta zuba ma tsoho na lafiyayu Marika har biyu, ta hankadashi da kafa, Allah sarki tsoho na zaiyi jika da ita.tana ya mutsa fuska tace” Kai tsoho na koreka a aiki”

Ya durkusa Yana kuka yace” da Allah hajiya ki tausayamin, wanane kadai hanya samu ci na da iyalaina, ki taimakeni” Yan aiki gida duk suka zuba musu idon tsoho yabasu tausayi, suhaima takama hanya. Baba maigadi yabin ta Yana kuka yace” hajiya inshallah bara na Kara kuskureba, ki ceci rayuwa na” ya tsuguna a kasa Yana rokota.

Ta juya ta dakamishi tsawa Rai a bace tace” Kai talaka banza, talaka wofi, bakasan aiki ka ba, sbd haka ka bacemin dagani , Kar na huce fushi na akanka, na koreka na koreka” ta Kara hankadashi da kafa, ta wurga ma wani Ma’akaci car key nata da sauri ya cafke ta wuce ciki. Baba maigadi durkushe yake Yana ta rusa kuka, ya Mike yashiga daki tatara kayashi yabar gida ya na kuka.

Suhaima na shiga ciki Rai a bace, feenat zaune Tana latsa waya, taji shigowarta ta Mike da fara’a tace” ke Wai Ina kika shigane, ki dawo Rai a bace, to nvm, tun dama accessories Dana muna order ne a Jumia nazo na nunamiki , koyayi” ta Mika mata waya , suhaima na amsa ta buga waya a bango, ya bada Kara Tass, ta daka tsawa dayasa feenat ta firgita tace” banza inanana Ina fama da zuciya ta, Ina fama da Aliyu ya Soni, ama ke ta accessories kike, Yana na can wata yake Kira bani ba, wata yakeson daban, baimasan Dani a lissafishi ba” ta dauki glass cup dake gaban feenat ta hadashi da center table dake tsakiyar parlour, ta fisge dogo home theater, takama duka babba plasma da aka kawatar da parlour dashi. Feenat zata riketa ta daga mata hannu tace” hey u stupid don’t touch me, soyayar Aliyu zai kasheni” ta cigaba da rutsa Kaya Mai amfani dake parlour, yan aiki da feenat Dan suyi yukiri riketa sai tamusu rauni, duk taji musu Rauni a jiki, Bata sadudaba sanda ta ta tabbatar ta runguza komai Mai amfani dake parlour, ta durkusa a kasa ta fashe da kuka , duk ta hargizai, ta dago Kai ta nuna kata tace” ni Aliyu zai cimi mutuci yace bai sona wata yakeson, ni ” ta Kara fashe da kuka,

Feenat a tsorace tazo gefeta, tana dar dar, tana tsoro Kar tasake hi mata wani Rauni ta dafata tace” haba mana nawa, maiyesan kike haka, Aliyu fa naki ne ke kadai, ba wata sai ke, ki daina fada kalma baya sonki bai…. Bata barta ta karasa ta dago da idanuta da suka rine ta katse ta dacewa”wlh, wlh talahi , sai na sa Aliyu ya Soni, Dan doleshi, ko da kuwa duniya zata tsaneni sai nasa yasoni , ko ta hali ka’ka, Kuma na ratse da Allah zan iya kisa akan Aliyu ” tayi murmushi muguta tacigaba” wlh feenat koda kuwa kece, zan kasheki, har lahira , duk Wanda na kashe na kashe banza”

Feenat ta tsorata da kalamanta tayi murmushi kamar ansa ta dole tace” haba nawa, Mai zai kaini, ai Aliyu naki ne, ke kadai , ki kwantar da hankali” Tana rufe baki hajiya binta ta shigo, wata Mai aikisu na janye mata da trolley, ta tsaya kallo yanda parlour ya hargizai, duk anfasa komai , takai dubata ga su suhaima dake zaune ciki fasasu glass, ga ya aiki su yi cirko cirko, suna jira hukuci su San dole abunda zai biyo baya kenan.

Hajiya binta ta wangale baki tace” what babyna Mai zagani haka? Waya Bata Miki Rai? Ta nufota zata tabata,

suhaima ta Mike ta buga mata tsawa tace” Kar kitabani , baki Sona “

Hajiya binta tace” haba babyna, Mai nayi Kuma? Yihakuri zoki gayamin maiyasa maiki? Kodai kina fushi akan nayi tafiya basanar Miki ba?

Tace” Ina ruwana da tafiyaki” cike da matsifa tace” mummy sau nawa Kisha gayamin na kwantar da hankali na,Aliyu zai Soni, maganar ki duk yatafi a iska, bai Sona ko kada, wata mayake Kira daban a matsayi matashi, Kuma wlh mummy ko waye sai na rabashi da ita, sai nasa ta daina numfashi a doro kasa, dun su Raina mi hankali , Wai ita ba mutum bace”

Hajiya binta tasa wani uban shewa tace” dat is my baby, zo ki ji, maganar da na Miki akan Aliyu bai tafi a iska ba, dun ya kusa tabata, Aliyu sai dai yaji Mai sunashi na zance soyaya da wata ama badai Shiba, har abada abada kuwa” ta kada Ido iri na goggu mata tacigaba” baby na ,yanzu daga nijer nake, kuma sbd ke naje, naje guri babba malami, sunashi malami kan dutse ama afi sani shi da Aiki da cikawa. Baby na bukatiki sukusa cika, taja a jiki tace”zo muje daki, ba yarda da waena masu Ido kamar munzuru ba” ta nuna yan aiki da sauri suka sukarya da Kai kasa tace” ku tabbatar ku gyara parlour na, tsaf darling na zai dawo yau, zan sa akawo sababi Kaya ku jera , waena Basu da amfani Kuma, ta kalli suhaima tace” baby badai ki sake hali naki ba ko?

Ciki da gatse tace” Mai nayi kuma?

Hajiya binta tace” baby na dawo, driver na ta horn babu Wanda yazo ya bude gate, sai jamilu driver yazo ya bude, Mai ki ma baba maigadi?

Tace” mummy na koreshi , Kuma basan kikara cewa komai akai, kawai ni munkarasa ki gayamin abunda yakamata naji” ta fda cike da Rashi kunya…

Hajiya binta ko ya yadamaita tayi murmushi tace” toh baby na, naji Allah ya huce zuciyarki, muje”

Suna isowa dki feenat da suhaima suka zauna a baki gado, hajiya binta ta nufi mirror tasa hannu ta cire sarka gold din dake wuyata.

Suhaima tace” mummy ke fa mukeji ra”

Tace” Kai baby matsala dakai Rashi hakuri” ta dauki baki handbag nata baki ta zazage musu agbsu da wani gora cike yake da madara shanu, suhaima sai bin kaya take da kallo tana yamutsa fuska..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button