DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ciki sanyi da tausayawa hajiya tace” toh maganar aure da ke kanta fa, tun da ba miji kusa, Kuma ba’asan asalishi ba, balle a Nemo shi”

Daddy yace” Kar kudamu zamu tambeyi malamai akai”

Baya Kwana biyu, an sallamorta daga asibiti, dun ta da warware, Essha duk ta chanza, Bata da wani aikiyi sai kuka, gaba daya ta chanza, gashi yanzu daddy ta ko na da can ya Hana ta fita, ya chanza mata layi wayata cewa yanzu ita matar aure ce, abun na bala’in Kona mata Rai , mummy ne kullum Mai lallashi..Sam yanzu Bata da wuya kuka, mummy mamaki take a kullum , Essha ce ta dawo haka, yariya da batasan Mai ye damuwa ba, ko yaushe murmushi shi ne shimfide akan fuskar ta, yanzu Sam Bata da wuya kuka.

Yau ma zaune take a parlor, ita da siblings na ta suna kallo , mufeedat ne a cinyata, ta zuba uban tagumi tayi zurfi a tunani. Sumaiya(bestie) ta shigo da sallama ta, su amir suka amsa, ta nemi guri a gefe Essha ta zauna, ta kalleta shiru, Essha ba ta masa ta shigo ba sbd tayi nisa, Bestie ta Mike ta zungure ta a kai, a zabure ta juyo tana kallo bestie idon ta har ya fara Tara ruwa, ta marairace fuska kamar zatayi kuka, zatayi magana bestie ta rufe mata baki tace” zo muje” ta sauke mufeedat, sukayi hanya daki Essha , suna karasowa..

Bestie ta kalleta tace” Wai Essha what’s wrong with you? Ki canza gabadaya, tun Ranar da daddy na yagayamin kina asibiti na shiga tashi hankali na tambeyeshi ko accident kukayi bai bani amsaba, Kuma ya Hana ni fita, Kuma Ina trying number ki a kashe”

Essha ta share hawaye da ya zuba mata ta zauna a baki gado , Tana share hawaye wani na sake zubowa, tanason tayi magana ama kuka yaci karfita da Kuma yada kirji kemata yasa baza tai iya ba, kawai ta rugume bestie ta fashe da kuka.. Mai tsuma Rai.

“Subhanallahi, Essha Wai maike damuki ne” bestie ta fada Tana share mata hawaye,

” Bestie ki fada min mana daga wuri Khalid fa nake Yana ciki tashi hankali, Yana Kira ki, number ki a kashe, Kuma yace min first day da ku ka dawo ya Kira ba ki dauka ba maiyasa?

Essha ta kalleta shiru tana hawaye, itama bestie kuka takeyi.

Tace” please bestie kimin magana ko zaji sanyi, Khalid na Bliss park Yana jiramu , na mishi alkawari zan mu zo tare, tashi muje kibar kuka na, nasan bai wuce menstrual pain, shi ne yake bata min bestie, don’t worry zai wuce tashi muje, Kar kice a’a please, khalid na ciki tashi hankali”

Essha zuciya ta zafi yake mata, na ji hali da masoyita ke ciki, gashi ba hali zuwa gareshi ta rike bestie murya kuka tace” bestie kiyi hakuri, ki je kawai, ki bashi hakuri, ki ce mishi ya cire ni a zuciyarsa, ya yafe min in da rabon zamu sake haduwa……

“What!! Kisa Mai kike fada kuwa, Anya ma kina ciki hayaciki, Khalid ne fa ” bestie ta katse ta fada a fusace… Ta sausauta murya tace” wlh bazai iya wa ba, Essha ki tausaya minshi, yace fa bazai taba iya wata ya mace ba , Im bakeba, Kar kimishi haka bestie, ki tausaya ma rayuwa bawa Allah na, Wai Maiyasa ma ki ka canza haka? Wani abun ne ya hadaku? Tunda ki ka dawo ki ka canza why?

Essha bataiya Bata amsa ba ta girgiza Kai Tana kuka sosai..
Bestie tace” toh gayamin reason dayasa bake dauka kirashi, har kina cewa ya cireki a zuciya sa ki gayamin” tasa kuka

Essha tasa hannu a baki ta na girgiza Kai, haweye ne kawai ke ambaliya a fuskata, sumaiya ma kuka take.. dai lokaci waya bestie ya Soma Kara, kira ne , ta duba taga Khalid ne da sauri ta pick ta sa a loudspeaker tace” Essha fa Wai bazata zo ba” ta fada har muryata na rawa….

More comment, more typing ❤️❤️❤️❤️❤️

????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️
DOCTOR ESSHA
????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️

WRITING BY
J Hajara

???? MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ???? ????️

Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.????????
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa


4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣

Khalid yace” love mainamiki? Wani laifi na aikata Miki da kikeso ki hukutani haka? Baby love please talk to me, please forgive me Ina azabtuwa”

Essha naji muryashi ta rutse Idon ta na fitar da hawaye masu zafi, ita kadai tasan yadn takeji a zuciya ta, ta kalli bestie murya a hankali tace” ki ce mishi ya manta dani
Bestie ni……. Ta kasa karasawa kamar an rufe mata baki ta fashe da kuka tace” kawai ki ce mishi ya fita daga rayuwa na, ya daina sona”

Khalid daji haka ya sarke da wani mugu tari, Basu Kara ji komai ba, sai hayaniya mutani, duk hankali su ya tashi, bestie na kuka tace” ki gani ko, kigani Zaki kashe yaro mutani a banza, ki manta alkawari daku ka ma juna ne, Essha Bata ba zato zakiyi haka na, ni zanje na sameshi” ta fice rai a bace.

Essha ta kife a gado tana kuka, bestie na fita mummy ta shigo, duk ta ji hirasu, ta dagata ta rugume Tana lalashita, sanda taga ta bar kuka tace” Essha ki cika Yar halak, ki na bi duk sharadi da daddy ki ya daura Miki, baki bi so zuciya ba,am proud of you, a kullum ki kasace Mai tawakali, in khalid mijiki ne, in Allah yaso Zaki aureshi, komai mai wucewa ne, watarana sai lbr, nasiha sosai ta mata Wanda ya rasata, yasa ta Kara saduda ta mayar ma Allah lamarita..

Bestie lkc dai Mai napep ya sauke ta a Bliss park, tun zurutu mutani tagani su taru a gefe daya, sai baza Ido take ko zata ga Khalid, banshi, wayashi take ta trying ama bai dauka ba, kawai ta yake taje inda aka taru ko Allah yasa tagashi, tana zuwa ta samu ta kusa ciki, Tana shiga khalid tagani kwance numfashi sama sama yake fita, tana ganishi tasa ihu tana a taimaka mata,ba Wanda ya kulata karashe ma watsewa akariga yi daya baya daya, tana kuka ta rasa yanda zatayi , ta fara neman wayashi, ama ba waya, batasaniba, tun lkc da suke waya ya sarke da tari, waya ya fadi,daga ciki masu zuwa kallo ne, wani ya dauke waya.

Khalid numfashi Dakar ya ke fita ga tari ga amai jini, da sauri ta dauki wayata ta Kira Bashir, ta gayamishi hali da Khalid ke ciki, da address din guri, bada jimawa ba sai gasu su karaso, suka Parker motar a gabasu, su uku suka zo, da Bashir sai wani saurayi Mai Kama da Khalid din, ama Khalid ya fishi girma, sai mahaifi Khalid.cike da matsifa baba Khalid ya fito Yana babbali matsifa ya nufo khalid yace” wlh ko zaka mutu, bara ka auri yariya na ba, yariya da aka gayamin tagama talla kanta a titi, shine kake neman kashe kashe ka ka akanta, toh wlh ba ka isaba, Kai ko Mai halaka da yariya bara na bar wani nawa ya aura ba, labari tas yazo kunne na, har hanata fita akayi, sbd abun kunya da ta aikata( ohh ni ya su???? mutani mutani, hmmm)..

Toh bakai bar Yar iska yariya na har abada nagayama kenan”

Bestie dake zungune ta kasa gasgata abunda kunnuwata suka jiyo mata, bestie ta ne ake mata Wana shairi , Wana abun da mamaki yake, abun daurai Kai ma Bashir(saurayita) tunda yazo guri yashareta Yana wani kauda fuska kamar bashi ba, bai ko kulataba, tun shekarajiya ta lura da chanzawashi, ga Kuma abunda baba khalid ke fada ya matukar girgiza ta, ta Soma tambaya kanta maiyasa yake aibanta bestie na haka? Yana kirata da Yar iska baya ba halita bane, toh maiyasa ma bestie ta canza? Tsikaro murya baba Khalid tayi Yana cewa” sa shi a motar , Kai Kuma Bashir na ji ance kana nema kawata ko? Toh ku rabu tun da wuri,kafi su shafa ma Kashi kaza”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button