Uncategorized

TAKUN SAKA 30

 *_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

_________________________

*_Chapter Thirty_*

………..Saurin kallon hannun tayi, ƙamshin mayen turarensa dake daɗewa jikinsa yana rige-rigen shigaa hancinta, hannunta tai ƙoƙarin fisgewa ya ƙara damkewa. Zafin daya ratsata saboda yanda ya matse tafin hannunta da spoon ɗin ne ya tilastata ɗago idanunta dole ta dubesa fuska a kumbure. Kallon ido cikin ido sukaima juna. Tai azamar janye nata dan harga ALLAH ƙwayar idanunsa mai kama data gawurtaccen bajimin zaki tsoto take bata. Ɗan luuu yay da idanun tare da dafa makarin kujerar da take zaune ya ranƙwafo kanta har yanzu hannunsa na riƙe da nata.

       Gaba ɗaya ta dabirce, ta matse jikinta tana sake ƙoƙarin fisge hannunta amma ta kasa. 

       “Bayan satan waya ashe har na abinci kin iya kandala?”. 

       Ya faɗa a saitin kunneta cikin wani irin slow voice daya saka Hibba ɗan zabura ta matsar da kanta saboda wani irin harbawa da zuciyarta tayi, yayinda gaba ɗaya tsigar jikinta ya miƙe. “Ni wlhy bana sata, kuma ba sunana kandala ba”. Tai maganar da saurin yunƙurawa zata tashi ya sake tsare ko ina har tana jin fita da saukar numfashinsa.

        Wani ɗan lalataccen Murmushin gefen baki ya saki tare da ɗago hannun nata ya kai spoon ɗin bakinsa batare da ya saki hannunba ya sake faɗin, “Tunda na sameki akan abincin da ba naki ba ai sata ne. Sai shegen handama kin cinye naki zaki haɗa da nawa. Da kin sake ko spoon ɗaya ya shiga wannan bakin mai kama dana akku sai kinyi amansa”. Yay maganar yana sake ranƙwafota da ƙyau cikin alamar tabbatar da zancensa. Sai kuma ya saki hannun nata. 

        Da sauri ta yarfar da cokalin tamkar wadda ta riƙe maciji. Shima ɗagawa yay da ga ranƙwafawar da yay kanta ya miƙe tsaye sosai akan kafafunsa. Kujerar kusa da ita yaja ya zauna duk da bai ra’ayin cin abincin ba da farko. Plate ɗin data zubama abincin yaja gabansa, tare da sake ɗaukar wani cokalin ya fara ɗiba ya kai bakinsa. Miƙewa tai cikin fushi ta ture kujerar baya tabar gurin hawaye na sakko mata.

         Yi yay kamar baisan da tashin nata ba. Sai da ta kai ƙofar ɗakinta ya ɗan ɗaga ido ya kalleta yana sakin murmushi da kai abincin bakinsa. (Burum!!!) ta rufo ƙofar ɗakin da ƙarfi. Ƙasaitaccen Murmushin ya sake saki yana miƙewa. Ya ja tissue ya goge bakinsa sannan ya janye idonsa daga ƙofar ɗakin nata. Ɗakinsa ya nufa dan babu abinda yake bukata sama da son jin ruwan ɗumi a jikinsa. Tun kafin ya shige ya zame facemask ɗin fuskarsa ya bayyana a Isma’il ɗinsa. 

     Hibba na shiga ta faɗa saman gado ta riƙe ciki, dan da gaske yunwar takeji sosai. Babu yanda Baba saude batai da ita ba taci abinci bayan fitarsa gidan amma taƙi. Har tea tace ta haɗo mata tace ta ƙoshi. Hawayen da suka ciko mata ido ta share tana matuƙar jin kewar Umminta da su yaya Muhammad. Ga kayan jikinta sun isheta matuƙar har ƙyanƙyaminsu takeji. Miƙewa tai da tunanin bara ta ɗanyi wanka ko zata rage halin da take ciki ma ta samu damar yin tunanin mafita akan azzalumin nan ɗan homo.

      Kusan mintuna sha biyar sai gata ta fito ɗaure da ɗankwalin kayan nata da dudu iyakarsa cinyarta, cinyar ma ko rabi bai rufeba. Da ace zata duka babu abinda zai hana a ga jikinta. Bakin ɗan kwalin ta ɗan sa tana goge gefen kunnenta zuwa goshinta da ƙananun gashi suka kwanta sosai. Dan masha ALLAH hibbah nada gashi yalwatacce. Ga cika ga tsaho gwargwado. 

       A dai-dai lokacin ne kuma Master da har yay shirin barci bayan ya watsa ruwa ya iso bakin ƙofar riƙe da plate daya zuba abincin kaɗan sai tab.. Da kaya kala ɗaya. Hannu ya ɗaura bisa handle ɗin yana sake tsuƙe fuska dan kansa ciwo yake masa matuƙa. A firgice Hibba ta juyo jin an buɗe ƙofar. Ta zazzaro idanunta saboda daburcewa ma ta gagara neman mafita. 

        A kanta ya sauke mayatattun idanunsa da barci da gajiya suka maidasu fici-fici. Janyewa yay cike da basarwa yana cigaba da takowa cikin ɗakin tamkar ma bai fahimci dalilin ruɗewar tata ba. Hibba da ta samu nasarar jan hijjab ta saka ta haɗe fuska sosai tana hararsa. “Shi dai musulinci ya bada dokar yanda ya kamata mutum ya shiga waje ai. Amma ba’a dinga faɗoma mutane kamar wata kirsimeti (Christmas) ba”.

      Banza yay mata kamar bai jita ba. Sai ma ajiye tarkacen hannunsa da yay saman mirror ɗin ɗakin. Batare da ya sake dubanta ba ya fara magana a daƙile. “Kiyi shopping na duk abinda kike buƙata ta online, idan kika cimin data bayan haka kuma….humm”. Ya ƙare maganar yana watsa mata hararar data hanata sake magana.

     Harya fara tafiya tunanin da tayi yanzu-yanzu yasata azamar zabura tai saurin zuwa tasha gabansa. Wani irin shegen kallon da ya saka hantar cikinta kaɗawa yay mata, amma itama da yake gwanace ta taurin kai da kafiya sai tai ƙasa da kai kawai bata miƙe ta bashi hanyar data tare masa ba.

       Sake raɓawa ta gefenta yayi zai wuce tamkarma bai gantaba. Sai dai yanda ta durƙusa a gabansa hawaye na zirara a kan fuskarta ya sakashi satar kallonta ta ƙasan ido yana ɗan takawa ya wuceta, sai da ya kama handle ɗin ƙofar sai kuma ya ɗan rumtse idanunsa yana cijar lip nasa tare da dakatawa.       

     Jin ba’a buɗe ƙofar ba yasa Hibba fahintar bai fita ba, bazai tanka mataba ne ya sata fara magana cikin raunin murya na drama ɗin data shirya masa cikin ƙanƙanin lokaci, dan halin da Ummi zata iya tsintar kanta a ciki kawai take hangowa. “Na roƙeka dan ALLAH ka maidani ga ahalina. Mahaifiyar mu tana da rauni na ciwo da kan tashi a dalilin damuwa. Rashina kuma yana ɗaya daga manyan abinda zai iya tada mata shi. Indai nice na janye alwashina, bana buƙatar wani TAKUN SAƘA da kai. Da ga karshe ina roƙonka dan ALLAH ku barmin ahalina. Ku duba maraicinmu da raunin mahaifiyarmu????????”.

      Ta kare maganar da haɗa hannayenta waje guda alamar roƙo kukan gaskiya na suɓuce mata yanzu kam. Jin bai tanka ba yasa ta ɗago idanunta da hawaye ke cigaba da mata zarya a kumatu ta dubesa. Har yanzu idanunsa a rumtse suke, kuma bai juyoba bai kuma saki ƙofar ba, sai dai sarai yana jinta. Amma tsabar ƙasaita da mulki yamayi tamkar bai san da kasancewarta a wajen ba.

     Wasu irin zafafan hawaye ne suka sake ziraro mata na tsananin tausayin yayunta da begen Ummin ta. Tana buƙatar zuwa garesu kodan ta sanar musu abinda taji ga Abbah, shiyyasa ta ƙudiri ɗaukar duk wani wulaƙancinsa, indai hakan zaisa ta dace da fatanta na komawa gida.

      Tsahon mintuna biyu bai tanka ɗin ba, yana dai sauraren kukanta dake ƙara saka jijiyoyin kansa miƙewa. Ganin haƙanta bai cimma ruwa ba ya sata miƙewa da nufin barin wajen, dan ta gama sallama taurin rai da rashin tausayinsa. Takunta biyu ana uku Ƙasaitacciyar muryarsa ta sakata dakatawa.

        “Ni bana magana biyu”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button