Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
DOCTOR HEESHAM HAUSA NOVEL

DOCTOR HEESHAM HAUSA NOVEL

Ad

_____

Dasauri Heesham yasaukuya ƙasa yace,” A’a Daddy wllh banason shiga tsakanin ka da ɗan’uwanka kawai dai nakasa haƙura da ita wllh Daddy inasonta sonda nikaina bansan Adadinsaba wllh innarasata mutuwa zanyi dan Allah Daddy kataimaki Rayuwata,” hawaye yafara zubarwa.

Kamal da shigowarsa gidan kenan dan yataso daga Aiki Heesham yamasa text Akan Akwai matsala shine yazo yaji, ganin ɗan’uwan nasa nazubda hawaye yasa da sauri yariƙesa yana tanbayar lafiya.

Gaya masa komai Heesham yayi, Shima fara roƙon Daddy yayi dafaɗamusu kyawawan halin yarinyar,

Da ƙyar Akasamu Daddy ya Amince suka ɗau hanyar Hotals ɗinda Abba yasauka.,
Text Heesham yaturama deeyana kamar haka <~<

•°°••°°•••°°• KISANAR WA DASU BABA GAMUNAN ZUWA GURIN NEMAN AUREN KAMILALLIYAR ƳARSU ƳANZU •°°••°°•

Yana gama tura mata text ɗin yakashe wayar ,,
Kamal dake lura dashi murmushi kawai yake,..

Basu ɓata wani lokaci ba suka isa hotals ɗin, Heesham yasan ɗakin dan haka direct ɗakin yanufa ,

A zaune suka same mesa yana waya, Da sallama suka shiga sukajira sada yaƙare sannan su Heesham suka gaidashi,

Ansawa yayi yatanbaye kamal iyalansa kamar baisan da zaman Daddy gurin ba yanuna yace,” Kutashi muje ko dagacan nawuce dan banason narasa jirgina yau zankoma,”

Daddy yace,” yace,” Au wai dagaske Heesham yashiga tsakaninmu irin wanan fushi haka kanada ni amma harda zama hotals? haba ɗan ƙanena kamanta Mama dama baba sunce kada musake murabu Ko Aji kanmu? Shinkamanta sunmaka wasiya taƙarshe Akan kada kayi musu dahi kayi mun biyayya kamanta ne kodan kaga basa raye yasa kayi fatali da maganarsu,”?

Yatsareshi da idanuwa,

Dik jikin Abba yayi sanyi yace,” yi haƙuri yaya Amma kaima kasan kana Aikata Abunda baidace ba,”

"Hakane to najanye nazo muje neman Auren yanzu Amma wanan karon badan Heesham nayi ba saboda kai nayi,"

Murmushi dikansu sukayi, daga nan suka ɗau Hanya..

Deeyana dawowar ta daga islamiyya kenan tana shigowa Mama tace,” kinbar wayar taki yau A kunne gatacan sai ruri take,”

Heesham yafaɗo matsa Arai dantasan shine ma kawai zaikira irin wanan lokacin,
Dasauri tashige ciki taɗauko wayar taduba da messeger ɗinsa tafara cin karo tabuɗa takaranta ganin meyace harda tsallen murna tayi takirashi Amma wayar kashe,

Dasauri tafito waje tasame Mama tagaya mata, Mama tace,” kai masha Allah Abu yay kyau Amma dikanku keda shi kunmuna bazata gashi bamu shirya musu komai ba kawai jeki kan wanan tasar Akwai ƴan ƙuɗinda na Aje saboda wanan ranar saikije kisiyo musu lemuka, nikuma bara ingayawa Mahaifinki daga nan yanemi Alhaii marsoor mahaifin Zeenarh,”

Cikin zumuɗi da murna Deena yataɗauko ƙuɗin tafice ko uniform ɗin bata cireba,

Murmushi mama tayi Aranta tace,” Yaran zamani badama kunason junan ku keda wanan yaron sosai kai Allah yasadai Shiɗin Mijinki ne,”

Baba dake shigowa da kekensa yace,” wai meke faruwa ne nahange Mamana Saifaman Murna take tanata zabga sauri da murna itaƙaɗai wai meke faruwa ne,”?

Murmusawa Mama tayi sa’annan tahau bashi labari dik Abinda yake faruwa,

  Shiɗinma Murmusawa yayi yace," wato nafahimta tana tsananin son wanan yaron nima naƙagu naganshi wllh  dahar yayi farat ɗaya da ƴata haka," 

.

Mama tace,” Ai ko yau zaka ganshi dan haka jeka kagayawa Alhaji mansoor kafin kadawo nashare wancan zauren,”

  Baba yace," To Angama kuwa,"

Miƙewa yayi yatafi yaga yawa Alhaji mansoor tare suka dawo koda sukazo Mama da Deeyana sungyara palourn Baba tsaf sai kamshi yake dik da ɗakin bawani babba bane Amma bayada kayan Hauka ƴan ƙanan kujeri ne guda 3 cikin ɗakin sai ɗan ƙaramin capert da ke tsakar ɗaki..

 Ba'a jima saigasu sunso motoci 3 Sukazo dasu, 

Izini Baba yamusu sukashigo ɗakin

Da Alhaji mansoor suke ɗan taɓa fira

Deeyana tashigo ɗakin da sallama kanta A ƙasa take gaidasu sanan ta’aje tiren da takawo mai ɗauke da kayan drinks da snacks ,
Murmushi kawai Heesham keyi yana neman suhaɗa ido Amma taƙi,

Abba yace,” wanan itace ƴartamu ko,”?

Kamal ya’ansa da eh

Da sallama Baba yashigo kan Heesham ƙasa yake sam baiga Baba ba Amma dajin muryarsa saida gabansa yabuga daƙarfi, Agefen kamal ma baƙaramin tsorata yayi ba daganin baba fata yake Allah yasa bashi ne Baban Deeyana ɗin ba,

Baba yace,” To waima waye Surukin Aciki,”?

Nunashi Abba yayi yace,” Wannan ne Sunanshi Heesham kuma shine Mamal lakin DOCTOR HEESHAM LUXURY HOSBITAL wadda itace take Aiki Harsuka haɗu Anan munzo ne dan nema masa Auren ƴarta ku wato MARYAM DEEYANA, Saikuma wannan Alhaji Ibraheem mainera shine yayana kuma shine Ubansa,”

Baba yace,” masha Allah ai namasan dika bayanin wanann Agun Alhaji mansoor, “

Abba yace,” kaɗago mana Heesham kawani sunkuyar da kai haka kagaidashi mana,”

Ɗagowar da Heesham zaiyi wazai gani???

Hakashima baba wazai gani???

Miƙewa tsaye baba yayi cikin rawar murya yake nuna Heesham yace,” badai wannan mara tarbiyan yaron zanbawa ƴata ba! wllh koda ƴata zata dawma ba Aure bazata taɓa Auren wanan iskan mara kunyan yaronba!, kutashi kufitarmun gida kubarmin gidana!,” yaƙarshe maganar cikin tsawa.

Kasa koda motsi Heesham yayi Atake dik Abubuwanda suka faru A shekara 5 Abaya suka dawo masa sababi ful tabbas wannan shi Ake kira Anyaka kuma ta tashi zufa ce ketsarto masa kota ina jinsa yaɗan tsaya na wucen gadi..

Dik kansu Aɗan razane suka miƙe tsaye suma suna tanbayar lafiya 

Amma sai Baba yace,” gashi nan kutanbayeshi dalilina kuma bazan taɓa bawa wannan sagartaccen ɗan nawa ƴata ba,”

Kuka deeyana tafara da tindazu take zubda hawaye sai yanzu kukan yafito mai ƙarfi cikin kuka tace," Haba Baba meke faruwa kagayamuna dan Allah wllh inason Heesham fiye da tinaninka dan Allah Akan wane dalili zaka haramta masa ni bayan kaida kanka kace suzo kuma kace zakaban wanda nakeso meyasa zaka canza baba why,"?

Tasake fashewa da kuka,

Cikin muryar fusata baba yace”, Koda sonai zaizama Ajalinki to saidai kimutu Maryam dan bazaki Aure wanan sangartaccen yaron ba,”

Abba yace,” wai dika saboda kaketa Aibata muna ɗa gabanmu kakira muna dan kaci mutuncin mu,”

Baba yace,” bako ɗaya Amma bazan bawa ƴata ɗankuba saboda …. ………. tsaf yabasu labarin dik Abinda yafaru tindaga farko,”

Miƙewa Heesham yayi yamaso kusada baba yana mai sunkuyawa ƙasa yana kama ƙafarsa cikin kuka yake magana “wllh na canza baba yanzu bahaka nakeba dan Allah kayafemun wllh innarasata mutuwa zanyi,” turesa gefe baba yayi “kabar nan nace!!,

Miƙewa tsayi yayi yana zubda hawaye yatinkari inda Deeyana take,

Ja baya tafara cikin tsoro da raunin murya tace,” Baba kana nufin wannan shine wanda yajimaka ciwo wancan lokacin harya mareka,”?

Baba yace,” ƙwarai kuwa mamana shine dan haka bazan bari ki Aureshi ba idan kinmanta Alƙawarin da kika ɗauka lokacin ni ban mantaba inko kinjanye Alƙawarin saboda soyayya to ni bazan taɓa lamunta ba,”

Jikake tass tass tass Deeeya tawanke Heesham da kyawawan maruka har 4 A kowanne kumatunsa tace,” wanan shine cikar Alƙawarina gareka Baba kaikuwa kasani natsaneka! natsaneka!! natsaneka DOCTOR HEESHAM!!! Kasani bazan taɓa Auren kaba wllh kuma kabar nan domin gidan Mahaifinane!,”

Kalamanta baƙaramin ruguza tinani brain ɗinsa sukayi ba Atake yaji jinsa ganinsa yaɗauke kawai gani mukayi DOCTOR HEESHAM Yafaɗi fako numfashi………………….. ..

_HMMMMMMMM RIGIJI GABJI TABBASA WATA MIYAR SAI A MAƘOTA KOYA ZATA KAYA??🤔🤔🤔🤔
1-SHIN DOCTOR HEESHAM YAMUTU NE? 2-SHIN AURENSU ZAIYU? 3- SHIN BABA MLM SANUSI ZAI AMINCE DA AUREN? 4-SHIN DAGASKE DOCTOR HEESHAM YATUBA KUWA? 5-SHIN DAGASKE MARYAM-DEEYANA TATSANE HEESHAM? 6-SHIN DADDY DA ABBA WANE MATAKI ZASU ƊAUKA? 7-WAIMA DOCTOR HEESHAM ƊIN YAMUTU NE KO YANA RAYE??????🤔🤔🤔🤔

 _DOMUN SAMUN DIKA WAƊANNAN ANSOSHIN MUTARU A NEXT PAGE ZAIFARA AGOBE FEBUARY FORT 1 INSHA ALLAH AMMA GA WAƊANDA SUKA BIYA ƘUƊIN AMMA DOMIN PAID BOOK NE 200 KAWAI ZAKA ZAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT-  

( 0086780772 Sterling Bank. UBAIDAT ALIYU )

IDAN KINTURA ZAKI IYA ƊAUKAR SCREEN-SHOURT KITUROMUN TA WANNAN WHATSAPP NUMBER 07064904617 KO KUMA NUMBER KIRANA 07031012948•• SAINAJIKU KADA KISAKE KADA KASAKE ABAKA ABAKI LABARIIII💃💃💃💃 MAZA ANTAYO DA ƘUƊINKA DAN SAMUN NAKA RABON WANNAN ƘASAITACCEN LITTAFI WATO DOCTOR HEESHAM 2022 TAKU ƊINCE DAI 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖MALAM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN°°° GULBI MAGANIN RAFI°°°

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsApp number 07064904617 OR CALL NUMBER 07031012948

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button