Uncategorized

WAYAFI SONTA 10


 p10

 

…..Da sauri hjy ta janye hannun kasay kunnun yazube…tanata faman yimasa sannu had’e da cewa kada yawanke hannun…ta Masa tofi….faruq kuwa da mamakin ganin  yadda yyi wannan abin dabako Dan uwanka na jini zaka iyamawaba! Meyasa yyi wannan taimakon?”kallonsa yyi yaga Yana niyar tafiya yatashi Yana cewa sannu Yaya! Muga Gurin , yafad’a Yana duba lallausan tafin hannun haidar  Mai cike da gargasan gashi… zainab kuwa mutuwar zaune tayi,Bata tab’a zaton hakan zai faruba ,sbd ita ta alak’antashi da Mai girman Kai,Kuma besan aikinsa ba!marar tausayi gashi yabata mamaki…

haidar yazare hannunsa dg na Umar yadubi hjy dake cewa ka kyauta dakayi taimako da yanzun zainab ta k’one cinyoyi wlh”””yace bbu komai hjy kinsan hakan nacikin aikinah! K’warai da gaske ALLAH ya k’ara baka saa aduk inda kashiga yatsaremunku…. murmushin gefen Baki yyi ya amsa akan labb’ansa” zainab tayi wa hjy nuni datayiwa haidar godiya…hjy tace zainab namaka sannu da Kuma godiya… girgiza Kai yyi ya wuce kawai…faruq bbu kunya ya matsa gab da zainab yace zeetah ni baza’a mun godiyarba?”juyowa zainab tayi cike da faduwar gaba jin yakirata da sunan da yah Umar kekiranta!Koda taga hjy bata nan ,saita gallawa faruq harara…ta tashi…yyi saurin Shan gabanta had’e da cewa Wai meyasa kkmun hakane?”inazakije?” Sotake yagyara ta wuce yaki yagyaran”mitsss taji anyi tsaki ta d’ago da sauri ta ga haidarne zaifita har yazanxa Kaya…inkagama sakarcin kazo zanyi mgn dakai, yafad’a cikin dakakkiyar muryarsa….uhum uhmm….to…to Yaya gani nan zuwa.faruq yafad’a Yana shafa Kai! Yakalli zainab yad’age gira Yana cewa zamu hadu anjima kinji baby! Kallonsa tayi ta Masa gwalo ta wuce….yyitsaye yanata kallonta cike da buegewa harta wuce….kafin yawuce waye…Zainab ce zaune itada anty mariya a parlourn gdn anty mariyar” kunnenta kange da waya tana murmushi” anty mariya tace to autar baba nidai kada kicinyemun credit” inkungama bani! Zainab nadariya ta mik’a Mata wayar byn ta kashe…

Elham ta dubi zainab tace anti muje driver najiranmu…tashi zainab tayi had’e da yin rolling d’in kanta! tabi bayan elham tanawa anty mariya sallama! anty mariya tamusu fatan dawowa lfy!

     Suna fitowa compound din gdn”elham ta nunawa zainab had’ad’diyar motar faruq tace anty mushiga awannan za’a kaimu…da mamaki zainab takalle ta,saikuma ta bud’e gdn baya tasaka elham, sbd ganin driver din yabude gdn gaba!

Na niyar shiga taci muryar faruq “nacewa driver d’in yafito”yadubi zainab dake Masa kallon mamaki”yad’age gira had’e da cewa yayadai madam?”fasa shiga tayi….da sauri faruq yace zainab kishiga motar nan ,kokuma da kaina nasakaki wlh! Kinji na rantse zankuma iya hakan!

yafad’a in a serious tone…turo baki tayi zata shiga…yyi saurin cewa afront sit Zaki zauna!

Batare data kallesaba ta bud’e tashige…yashiga shima,Yana dubarta ,murya can qasa qasa yace kokefa! kinfison kitamun gaddamako?” rufe Ido zainab tayi sbd jin wata kasala…yaja motar had’e da bata wuta suka fice dg gdn had’e da hawa titi… zainab tayi ajiyar zuciya tana kalle kalle sbd tun zuwanta Abuja inbacin islamiya da hospital bbu gundatake zuwa gashi watanta 5 yanxun a abuja sai yau dasuka fito take ganin gari…inafatan garin yyimiki dad’i ko?” Sannan pls intambayeki Mana?”girgiza Kai tayi alamar ah ah! Yadubeta ya langab’e Kai yace pls Mana zeetah! Dole kima amsamin tambayata” waye yaron danaganku tare last 2 weeks ?” Murmushi tayi had’e da Masa nunin d’an uwantane! Ok bbu wata alak’a atsakaninku?” Kallonsa tayi…da sauri ta d’auke kanta….ta girgiza Kai alamar batada wata alak’a dashi…parking yyi yafito”had’e da budewa zainab ta fito itama”kafin ya bude yafito da elham dake bacci agdn baya..

Kallon shagon dasuka nufa zainab tayi taga gun saloon ne! Kallon tambaya tamasa duk batasan yawan kallonsa ko su had’a ido da shi” ahankali yace gun saloon ne kuje keda y’arki agyaramuku Kai ko?”kimun kwalliya anjima pls bantab’a ganinki da make up kullum fuskarki fiyau….yallab’ai sannuko! Wata hamshak’iyar buduwa tafad’a tana dubar faruq tana murmushi! Had’e Rai yyi had’e da cewa lfy daiko?” Wlh ni masoyiyar kace! Ina karanta jaridunku dakuma saurarar shirinka na gdn redio na matasa….meye dalilinki na tsayar Dani?” Inaso zamuyi pics ne pls! Zainab datun zuwan yarinyar gabanta yafad’i kirjinta yamata nauyi Amma Bata nunaba,saima ta mik’a Masa hannu alamar yabata elham!dake hannunsa tana bacci! Kallon yarinyar faruq yyi fuska atamke yace malama Zaki iya tafiya ,kin ganni tareda family na,hakan baihana ki k’in tsaidaniba ko?” Sbd bakida tarbiyya da kamun Kai…amma ai y’all…shout up!inkuma kinfison my wife d’ina ta Miki hukunci…fine… zainab ta karb’i elham had’e da kallon shida yarinyar sama da k’asa ta wuce ciki… yarinyar ta tab’e Baki sbd ganin faruq yabisu…wacce ke bayanta tace maganinki kenan tun sadda kki gansu nace karkije gashi kinje ya yarfaki,dama ance bashida mutunci wlh…

Dg waje faruq yatsaya sukayi mgn damai saloon d’in…yabiya tukum yafito yabarsu ciki…Sai bayan awa guda kafin yadawo,yatarda angama musu! Jere suke suka nufo motar… yyinda wasu tsirakun jama’a ke kallonsu, kasancewar faruq sanannen d’an jarida! Daddy kaga gashin anty zainab! cewar elham tana rik’e hab’a” faruq yyi murmushi yace Dan ALLAH! elham tace eh wlh andaure matashi…kallon zainab yyi dazata shiga mota yace to nima sai abudemun nagani ko?”

Bayan yatada motar suka nufi wani had’ad’d’en pack! Sosai fuskar zainab ta nuna walwala,alamar taji dad’in zuwa Gurin!Gurin wasanni suka nufa,sai murmushi Zainab da elham keyi suna kan dokin roba,faruq yyi musu k’uri da Ido Yana kallo” shidai kawai yatsintsi kansa dajin soyayyar zainab,dayakejin yanamata Sona aure ,uwa uba yadda ta damu da tilon y’arsa da kula da ita! Fatansa kawai ALLAH yasa zainab ta karbesa’lalurarta ta bebantaka insha ALLAH zaiyi wani Abu akai ko wajene afitar da ita,Koda tace bazata soshiga to bazai fasa ba,insha ALLAH sai zainab tayi mgn da bakinta”yasan ba kyau ko wani Abu yaja shi dajin son zainab ba,ah ah halayenta kawai ,dakuma shak’uwarsu da y’arsa…wayarsa yafito da ita, yyita musu pics Basu saniba! Can zainab ta d’ago Kai taga abinda yakeyi…saita hararesa,shikuma yyi murmushi had’e da nufosu” gab dasu yatsaya….gaba d’aya k’amshin turaren sa yacikamata hanci! Takauda Kai! Ahankali yace zeetah!lah daddy kacanxawa anty zainab suna?” Kallon elham yyi yace kitambayeta kiji” amma wuce ki koma gun shillo kiyi gamunan zuwa… zainab kuwa tayi mamakin wayon elham….pls ki kalleni manah,Kinga elham ta Fara gane bakisan kula daddynta ko?” amma king…shiru yyi ya had’e girar sama da k’asa” kafin yakama hannun zainab yace muje ko!sakamakon anin wasu Yan Mata sunnufosu…

Wayyo ALLAH wani electric shock zainab taji tundaga k’afarta har kanta,jikinta yadauki rawa,jin tattausan hannunsa me d’imi kan hannunta…dakewa tayi had’e da son k’wacewa! Ahankali yace zeetah kidena manah! Gabadaya Yan matan sai kallonsu suke harsuka nufi Gurin elham kafin yacika Mata hannu! Saidai yaga bacin Rai sosai afuskarta!I’m really very sorry zeetah nayi hakan sbd y’an matancan,ko a office haka suke damun mutane,ko waya shiyasa bani d’aga bak’uwar number! Zainab batad’ago kaiba,har cikin zuciyar ta ,bataso yatab’a Mata hannuba…In aka cire yah Umar bbu nmjin daya tab’a taba Mata hannu sai faruq….har sukaje wani mall ,yamusu shopping zainab ta ki sakin fuska ,yyi mgn da rarrashin har yarabu da ita,Yana zaton ko k’ila batasonsa,saidai dama yasan bakowane mutum kake  burgewa ba,Mata da yawa sun kawo Masa kansu akan yasosu amma yak’i! Yanzun zainab tamasa ,Kuma Bata mgn ,ahaka yake sonta amma ta nuna batasonsa…

     Parking yyi da sauri sbd anfara Kiran magrib,yabude back sit yafito musu da ledoji ,kafin yajuyo har zainab tabar Gurin…Kama hannun elham yyi suka wuce ciki” har d’akin su yarakata da ledojin yace ta awa antinta,kafin yafito..

Awaiting parlour yasami hjy najera abinci kan dining table…ta dubesa tace kundawone?” Eh hjy amma zainab  naga bata ciki ,intashigo kinsata ta karb’i kayan shopping d’in… murmushi hjy tayi tace to shikenan ai haka take dabawa abin duniya baya..

 

   ************

Yau kimanin kwana 2 kenan zainab Bata sakewa faruq fuska ,inhar Yana guri bata fitowa,in ya aika akirata bata zuwa inya shigo d’akinsu saita shige toilet!sbd Sosai zuciya ta kemata wasi wasi akan faruq ,ai har yanzun bece zahiri yana son taba ! To inma sonta yake da aure ko kuwa?” Bacin yasan ita kurma ce,ita azatonta faruq ba ajinta bane,ba sa’an aurenta bane ko soyayya dashi….mutum D’an gayu kyakykyawa ,yace zai tsaya gurinta,ita  y’ar talakawa ,Kuma kurma da sake! k’ila badan ALLAH yake sontaba ,tasan bbu macen dazata k’isa sbd ita shaidace agabanta mata kesan yakulasu….amma ita batason huddarsu kada takamu da sonsa ya yaudareta….shikuwa faruq  Sosai abin yabasa mamaki ganin kwata kwata zainab batason kulasa…

 

Tafiya takeyi kanta d’uk’e…da kayan islamiyarta ajikinta ,antaso zata shiga gd… assalamu alaikum! Bewar ALLAH inbabu damuwa inason mgn dake! Cak zainab ta tsaya tafasa tura k’ofar get din….ta juyo taga wani saurayi,Wanda talura tana yawan ganinsa awurin islamiyarsu…nuni da hannu tamasa akan bata mgn yatafi Dan ALLAH….. Kafin saurayin yyi mgn   anbud’e k’ofar get din….hancin motar faruq yafito…hakan yasa jin gabanta yafad’i! Ta matsa baya,faruq daya hangota ya juyo yaga itada wanine! Cike da fushi da b’acin Rai da kishi ne duk yahaddasa Masa….afili yace wato nita d’auka Wawa ko?”

Afusace yafito yadubeta” fuska adaure  yace ke shiga ciki”da sauri ta zuwe ciki….kafin yadubi yaron yace kada nakoma ganinka anan?Ko meyasa?bansaniba,zaka tafi kosai nasaka jami’an tsaro sunkama mun Kai….mittss yaja tsaki…da sauri saurayin ya ware…shikuma yashige motar yabar Gurin….saidai yasha alwashin dole yatambayi zainab inbata sonsa yahak’ura kawai…

 

   ********

Tsatstsaye suke  a compound d’in gdn,haidar da faruq sun saka suits…da trolley ahanunsu zaa saka musu a boot” hjy ta dubesu tace gsky baniso ace bbu kowa acikinku agdn nan ga Alh baya gari saimu kwana mukadai….ai akwai masu gadi hjy karki damu nasaka security….binciken nan dole sainaje da faruq amatsayinsa na d’an jarida ,Kinga mutanen nan glna gunmu ,munkamasu ,Nanda kwana4 zamushiga kotu,dole zamuje bincike sbd samun hujjah hjy ,adduarki muke buk’ata”cewar haidar cike da k’arawa hjy k’warin gwiwa… addua ta musu,suka shiga mota,faruq daya Gama yiwa elham rad’a akunne..akan taje gurin zainab tabata sakonsa…..Yana d’agawa elham mota har suka fice…

 

 

Da dare Gurin k’arfe 2 darabi….baba Mai gadi ya ji Harbin bindiga har2 da sauri yajawo d’amararsa yad’aura ak’ugu(maganin tsarice inya d’aurata mutum mugu baya ganinsa )

Yafito dg d’akinsa ahankali,hankalinsa atashe…gawar security 3 yagani sai wasu 3 da akeyin musayar wuta dasu….yaduba yaga wasu manyan k’attin samudawane  majiya k’arfi suka shigo gdn ,fuskokinsu arufe da alama harda Mata acikinsu… Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un kawai baba Mai gadi keta nanatawa azuciyarsa!be auneba yaji wata kakkasar murya tace kuk’arasasu komunshiga ciki ,kunsan ogah yasanar Mana mahaifiyar shi kawai zamu dakko ,muyi garkuwa da ita,dole afasa shiga kotu wlh…kokuma mukaita jami’ar mik’akk’u inyaki Dena adawa da oganmu…Ina biliya ya shigar damu ciki…zaro ido baba Mai gadi yyi sbd jin sun anbaci biliya yashigar dasu ciki! Sbd biliya inspector ne,wato amanar DSP ALIYU haidar zaici kenan? Baba Mai gadi yafad’a azuciyarsa…da sauri yazagaya ta baya…yabude window din dayagani abude yadira….cikin sa’a Ashe bed room din zainab da elham ne…atsorace zainab ta kunna fitila sbd tunda taji k’aran bindiga ta farka ,atake taga  baba Mai gadine , ci ke da tsoro take kallonsa gabanta na dukan 100 100 ta zaro Ido cikeda rawar jiki! baba Mai gadi ahankali yace ke ki saurareni dolece tasani dirowa….wasune Yan dabane ko me afahimatata ture akayiwa DSP ALIYU haidar gashi baya gari,Kuma sunzo da niyar suyi garkuwa da hjy kamar yadda naji Dana lab’e , shiyasa na shigo kije kusan yadda zakuyi wlh…. yafad’a had’e da ficewa ta window din…

Tashin hankali baa samasa Rana! Juyawa cikin zainab keyi ,tayi saurin kashe fitilar ta fice dg d’akin gudun kada elham ta tashi…ahankali ta fito tanajin karar Harbin bindiga…..tanufi parlourn hjy ,ta murd’a k’ofar bed room d’in ta shiga ta Sami hjy kwance kan bed tana bacci! Bubbuga pillow din zainab tayi da k’arfi… bayan ta kunna wutar d’akin…jikinta na rawa…hjy atsorace tabude Ido taga zainab….dafe kirji tayi tace lfy zainab? Zainab ta Mata nuni bbu lfy b’arayi sunshigo zasu tafi da ita….tsabar rudewa yasa hjy bata fahimta ba ,tadai gane barayine suka shigo….motsi da sukayi awaiting parlourn gdn yasa zainab saurin murd’a k’ofar toilet tama hjy nuni data shiga! Innashiga kekije Ina zainab?” Girgiza Kai zainab tayi had’e da Jan hannun hajiya ta turata toilet,itakuma tasaka hijab din hjy dake ajiye kan prayer mat…ta kashe wutar d’akin ta kwanta kan bed had’e da rufe fuskarta…hjy dake kallon zainab ta hudar kyaure taga takashe wutar d’akin…..harzata murd’a k’ofar toilet d’in taji anmurd’o kafar shigowa bed room d’in! Hakan yasa ta dakata gabanta na faduwa tanata inna lillahi wa inna ilaihir Raju un! taduk’a Gurin hudar k’ofar bayin sbd hango haske datayi,Ashe torch light ce suka kunna,taji wata murya tace ku watsamata poda….tana ganin sadda aka watsawa zainab powder,wasu Mata biyu suka d’auketa! Wani yace muje da ita dama ance in masu tsaran gdn sun Mana gardama mugama dasu Amma karmutab’a kowa agdn , kawai mutafi da uwarshi ,inyak’i sake oga mugama da ita, sannan sai munkarbi manyaan kud’ad’en sa,tukum,yadda zamu talautashi….iya nan hjy taji taga sunkashe fitilar suka bud’e k’ofa suka fice….???????????????? Wasa farin girki yanxun aka soma….

 

Da yawa fans kunbani mamaki gameda wannan book , akalla na rubuta novels free guda7 Amma Wai wasunku 300 tagagaresu biya ,sun zuba Ido suna jiran na bati…Ina sanar daku da babbar murya duk wacce takaranta mun book Bata biyaba banyafe ba,keda ALLAH! Bazanyiwa kowa ALLAH ya isaba!

Kuna cewa ai duk wacce ta Bari aka ga book nata harvaka karanta itama tanada zunibi…to wannan book ba kirkira bane da gaskene! Inma kinkaranta Baki biyaba dan kanki…keda ALLAH..

 

Wad’an da suka biya harsuka linka mun Ina godiya sosai Allah yak’ara arzik’i…????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button