NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 11

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

   

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


             *11*
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Magana ta ji ana yi ƙasa-ƙasa har bata iya jin abinda suke fada saboda ta fuskanci kamar tattaunawar sirri suke yi shi yasa basa so wani ya fahimci abinda suke cewa, ƙara bada hankalinta gare su tayi don a yadda taji salon zancen kamar maganar Sa’adatu ake yi, don ta ji kusan duk kalmar da xa a fada sai an ambaci sunan Sa’adatu, kuma dama tunda ta ga wannan tarin jama’ar ta san an taru ne saboda ita.
Ji tayi an kwalawa Sa’adatun kira, cikin mintunan da basu wuce biyu ba ta gabata a gaban taron jama’ar da suka haɗu sbd ita.

A ladabce ta gaishe su, amma ga mamakin Rukayya bata ji sun amsa ba, wani dattijo taji ya fara magana “yanzu dan Allah wannan hanyar da kika dakko mai bullewa ce kuwa, kina ganin hanya ce da zata sadaki da tafarkin tsira, kina yarinya yar asali mutuniyar kirki yar mutanen kirki xaki bata rawarki da tsalle, xaki daka ta yaro ɗan masu kuɗi ki lalace iskancin naki har ya kai ki fara kawo shi gida yana abin kunya da ke, naga alama so kike kiyi cikin shege ko? to mu hakan baxai faru da zuri’ar mu ba, yanxu xamu yi maganin abin, amma kai kayi ganganci tun farko malam yarinya kamar wannan shekara sha tara baka aurar da ita ba ai dole haka ta afku, idan ma miji ta rasa me xai hana mu baxa kayi mana magana mu kawo mata ba, sai ka kyale yan iska su lalata maka ita”

Neman yawu nayi na rasa a bakina kululin baƙin ciki ya toshe min makoshina, duk da cewa ana dan sanyi amma haka naji xufa na yanko min, yanzu a ce duk jama’ar nan saboda ni suka taru? Kannen kakana ne da suke xaune a wani kauye da ake kira Bankaura, ina kyautata zaton jiya Baba ya je ya sanar da su Wannan sharrin da ake kulla min, shi ne yau suka zo ku san su goma duk a kan maganata

 Ita ma Rukayya da ke soro irin halin da ta tsinci kanta kenan, jiri ta ji na shirin dibanta don haka ta nemi waje ta tsugunna.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Wajen ne yayi shiru kowa na sauraren bayanin Baba musa, sai da ya gama magana tsaf Baba ya karbe shi.

“Ni fa dama Baba na dade ina xargin Sa’adatu da wannan aikin saboda a lokuta da dama ina ganinta da abubuwan da ba ni na siya mata ba, kuma mahaifiyarta ma ba tada kudin siya mata, amma ko menene ita uwar ke bata goyon baya salamatu na iya kokari wajen kula da tarbiyyar ta sai take ganin kamar takura mata take yi, ina rokonku dan Allah ku tafi da ita Bankauran ta xauna a can ko zata ƙara hankali, sannan kafin nan da sati biyu xan turo mijin da na bayar da ita sadaka a daura musu aure kowa ya huta”

Hawaye masu xafi suka riƙa sauka a kan kuncina, wace irin rayuwa ake so nayi a kauye? Tunda nake ban taɓa sati guda a can ba sannan yanxu dare daya a ce can xan koma da rayuwa, wane hali innah xata shiga idan na tafi na barta, kawai niyyar kashe ni ake yi da raina.

Da farin ciki ɗaya kanin kakan nawa ya amsa “kwarai kuwa kayi tunani malam Salisu can din ne gatanta kuma shi ne ya fi dacewa da ita, dama an ce duk wanda ya bar gida gida ya barshi, taje can ta shiga cikin yan uwanta tayi aiki, a haka ma xata koyi wasu sana’o’in tunda duk yan uwanta noma suke yi ita ma ya kamata ta shiga ciki tayi tarayya da su”

Gaba daya suka amince da komawata Bankaura, cikin fushi Baba yace na tashi na hado kayana, da gudu na shiga daki ina kuka, tambayata innah take yi dalilin kukana amma na kasa bata amsa saboda takaicin shekara da shekaru da ya cika xuciyata, ita ma ganin halin da nake ciki ne ya sanya ta kuka, innah salamatu ce ta dage mana labule tare da cewa “tafiya dole a yi ta, baxa mu xauna da yar iska a cikin gidan mu ba”
Sai a lokacin innah ta gano dalilin kukana tambayata ta shiga yi
 “Sa’adatu kokar ki malam yayi daga gidan nan ko kuma me”???

Hawayen da ya cika idona na share “cewa yayi sai na bi su Baba musa Bankaura wai baxan xauna masa a gida na lalace ba”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Kwalla ce ta cika idon innah
 “Allah sarki rayuwa Allah kaine Allah, ka saka mana wannan cutar da ake mana” kafin innah ta rufe baki har Baba ya shigo dakin cike da fushi yake mata magana.

“Munafuka wato kin sakata a gaba kina kitsa mata sharri ko, na lura da ke duk dokar da xan yi a cikin gidan nan sai kin rusata, ke dama kike goya mata baya har ta lalacewa, idan har kika bari ta dakko min abin kunya wlh kin gama xaman gidan nan, kuma xuwan Sa’adatu Bankaura ya xama dole saboda ‘yata ce ba ‘yarki ba ina da iko da ita, ki taka a hankali kafin na ci miki xarafi”

Mayar da kallonsa yayi gare ni “ke tashi ki dakko kayanki kafin nayi ƙasa-kasa da ke” A sanyaye na tashi na nufi inda jakar kayana take, a hankali nake xakulo su kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.

Sake daka min tsawa yayi “za kiyi aiki da jikinki ko sai naxo nan” kayana kala uku na dauka na xuba a leda, tankada ni waje yayi tare da cewa “shege mu je ja’ira” har na bar daki innah na sunkuye tana kuka, nima kukan nake har na fita ina waiwayenta.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A soro na biyu na tarar da su sun yi cirko-cirko suna jirana, idona a rufe na fita xuwa soron farko ji nayi an riko hannuna a hankali na bude idona, Rukayya na gani ta sha kuka har ta gaji, cikin kukan take min magana “wlh kada ki bi su Sa’adatu ki gudu, babu alheri a ransu neman ruguza miki rayuwa suke yi” 

Daga soron Baba ya jiyota, ita ma cin mutunci yayi mata ba shiri ta tafi gida tana ta rusa uban kuka.

A dai-daita sahu aka kawo mana don xuwa tasha, ni na fara hawa sannan sauran kakannin nawa suka bi bayana, babu wanda ya rarrashe ni ballantana na sa ran za a bani hakuri ko za a ji tausayina zuwa gaba.

Har muka isa tasha abinda nake yi kenan, sauke kayana nayi na samu gefe na tsaya, su kuwa sun kafa min ido kamar masu gadina, fakar idonsu nayi na ajiye kayan a kan wata mota, ina lura da basa kallona na gudu na bar musu kayan a wajen, gudu nake cin karfina ban san ina na nufa ba ni kaina.


A yi hakuri da kadan ba ni da lafiya ina bukatar adduarku
.kada a manta da comment da share

*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button