NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 16

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
             *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*



              *16*

Tun safiyar ranar da zamu koma gida Baba yake ta aike mu taho ya aiko yara sun kai biyar, don mu bamu yi niyyar dawowa a kan lokaci ba, sai mun ƙara hutawa sosai takurar da yayi mana ne yasa ko karyawa bamu yi ba muka tafi, a kofar gida kan benci muka same shi sallama muka yi masa tare da gaishe shi a sanyaye ya amsa babu wani walwala ko farin cikin ganinmu a fuskar sa. Cikin gida muka shiga ya bi bayanmu, kamar jama’ar gidan sun san da zuwanmu duk suna tsakar gida sun jere suna kallon kofar da zamu shigo, da sallama muka shiga cikin gidan abinda ya bani mamaki yau sun ɗan canja kaɗan da fara’a suka tarbe mu, abinda na kasa ganewa shi ne anya ba wani tuggun ake shirin haɗa mana ba kuwa ni da innah. Don na lura da su suna cikin farin ciki sosai har wata yar dariya naga innah salamatu na yi min.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Mukullin dakinmu muka karba a hannun Baba, ni na ajiye kayan da ke hannuna na shiga buɗe kofar, abin mamaki muna shiga muka tarar da komai namu na dakin an kwashe mana, sai yar katifar da muke kwana kawai aka bari hatta kayanmu na sawa da yan kwanukan da muke amfani da su duk babu.
Kallon juna muka yi ni da innah, zan yi Magana kenan naga ta sa yatsanta a bakinta alamun nayi shiru. rausayar da kaina nayi xuciyata cike da damuwa kallonta na sake yi tare da son ta bani damar yin magana amma ta nuna kin amincewar hakan, wajen xama muka samu muka zauna, baka jin motsin komai a cikin gidan duk an yi shiru ana sauraren jin abinda xamu ce.

Mu ma shirun muka yi kasancewar dukkanmu muna cikin damuwa, gaba ɗayan mu duniyar tunani muka tafi, sallamar Baba ce ta dawo da mu daga dogon tunanin da muka tafi.

Gefen katifa ya samu ya zauna tare da yin gyaran murya “Abinda nake so da ku shi ne ku kasance masu bin doka da odar da na saka muku, sbd hakan ne kaɗai xai baku damar cigaba da xama a wannan gida da rayuwa a cikinsa kamar kowa” nuna innah yayi “ke kece sarkin bawa Sa’adatu goyon bayan yin duk wata lalatar da take yi a gidan nan, to ki shiga hanlinki ki, ki nisanci dukkan abinda xai kawo mana sabani saboda ke ba wajibi ne na cigaba da zama da ke ba, amma ita Sa’adatu dolena ce, don haka ki kula da kyau kuma na hana Sa’adatu fita daga rana irin ta yau, ta zauna ta jira ni har zuwa lokacin da zan yanke mata hukunci”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});  Mayar da kallonsa gare ni yayi “kema ki gyara halinki ki zauna da yan uwanki lafiya duk abinda salamatu ta umarceki, kiyi kokari ki rika cikawa idan aka kawo min ƙararki kin yi wani abu da ya saɓa ka’ida ranki ne zai ɓaci sannan na hana ki fita, makarantar ma na soke ki bari kya ƙarasa a dakinki tunda dama gidan ilimi na kai ki, sannan kada na sake jin kin yi zancen saurayinki na raba ki da shi har abada saboda baxan bari ya gurɓata miki rayuwa ba”
Juyawa yayi zai fita “Au na manta ban fada muku ba, kada ku ga babu kayanku na kwashe ne na siyar na siyawa Sa’adatu kayan aure, don yanzu haka ma an jera wasu daga ciki lokaci kawai muke jira”.

Shiru muka yi gaba ɗaya mun rasa bakin magana sai bin sa da ido kawai  muke yi, nice nayi karfin halin yin magana “Yanzu innah haka xamu zuba ido ana yi mana cin kashi a gidan nan baxa mu yi magana ba, haka zamu rika rayuwar rashin yanci kamar wasu bayi?” Mayar da numfashi tayi “uhmm me kike so nace Sa’adatu so kike nayi magana mu riƙa tashin hankali ana jin kanmu da shi, duk abinda yake min da Allah na bar shi, sakayyar aure tun kafin a mutu Allah yake nuna ishara, to ni baxan daka ta tasa mu lalace ba” jin ana motsi a kofar dakinmu ne yasa muka yi shiru.

Innah salamatu ce ta tsaya a bakin kofar tare da kirana naxo na karbar mana abin karyawa, cikin nutsuwa na karasa wajenta, murmushi take min mai cike da ayoyin tambaya tare da cewa 
“Sannu Amaryar malam har naga kin fara kyallin amarci, amarya kenan bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida” 
kallon mamaki nake mata don ban fahimci abinda take nufi ba, ban amsa mata ba na karbi kwanon na koma wajen innah a gabanta na ajiye ina fuskantar ta 
“innah kin ji zaton da nake yi yana son zama gaskiya ko, dama nace miki ba a banxa suke wannan fara’ar ba, tabbas akwai abinda ake shirin kulla mana a gidan nan, tunda ga abinda innah salamatu ta faɗa shi ma kuma Baba ya bamu satar amsa, shi yasa nace miki kada mu dawo takurar da ake mana dai ita za a cigaba da yi, baxa su taɓa sonmu ba kuma baxa su daina musguna mana ba tunda dama ba burinsu mu yi farin ciki ba, sun fi son kullum mu dawwama a bakin ciki”
 murmushin takaici innah tayi “Har yanzu bakya fahimtar rayuwa Sa’adatu wani abin ko kana da ikon ramawa dole kayi hakuri saboda magabatanka sun shiga maganar, banda su gwaggo sun sa baki babu abinda xai dawo da ni, wallahi na fiki takaicin dawowata gidan nan, amma maslahar rayuwarki na duba, idan bana nan zaki shiga cikin matsala ne, wata rana ma zasu iya cewa baxa ki kwana a gidansu ba ko kuma duk wanda suka ga dama su aura miki duk munin halinsa, tun a gabana ana wulakanta ki ina kuma ga bana nan, duk abinda xan fuskanta nafi son mu yi rayuwa tare da ke, saboda na baki kariya irinta uwa”

Har Cikin ƙwaƙwalwata nake jin kalaman innah tausayinta ne ya kama ni, gaskiya soyayyar uwa ta musamman ce ga ƴaƴanta babu wanda zaka samu a duniya yayi maka irin son da mahaifiyarka take maka, ta zaɓi mu sha wahala tare a kan ta tafi ta bar ni, Allah sarki innata, Allah ya bani abinda zan saka mata da shi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Da yamma nayi wanka na nemi iznin innah ina son zuwa wajen Rukayya saboda ina cike da kewarta, amma ta hanani saboda ta faɗa min hakan zai iya janyo mana wata matsalar, wannan dalilin yasa na hakura na zauna a cikin damuwa.

Bayan sallar isha har mun yi shirin kwanciya bacci Baba ya shigo da kansa ya kira ni, a ladabce na tsugunna tare da cewa “gani Baba” fuskarsa a daure ya dube ni 
“Yi maza ki canja zani mijinki ya zo zaku yi magana ta fahimta da shi, idan naji kin faɗa masa wani abu wanda ya bata masa rai ni da ke ne”
Zan bude baki na tambaye shi wanene mijina ya dakatar da ni
 “kada ki min wata tambaya ina da halin zaba miki duk mijin da naga dama saboda ni ne mahaifinki ina da ikon yi miki duk abinda naga dama matuƙar bai saɓa ka’idar Shari’a ba”

Idanuna ne suka cika da hawaye “Baba wannan kayan ne kaɗai suka suka rage min ba ni da wasu” shiru yayi na wani ɗan lokaci “to naji kije a haka idan kika ci Sa’a ma kafin auren naku zai iya yi miki dinki, ni da nace na yafe masa saboda sadaka na bada ke”
 A sanye na dube shi 
“sadaka fa kace Baba” Idanunsa a zare yace “kwarai kuwa sadaka na bayar da ke ko ban isa bane?” Ban iya bashi amsa ba sai kuka da nake yi kawai, nuna min hanyar soro yayi alamar na fita.

Idanuna a rufe na lalubi takalmi na saka sai da naje soron farko na ɗan goge hawayen da ke idona sai a lokacin na lura da takalmin da ke kafata wari da wari ne.

Tarar wa nayi har an yi masa shimfida a xuciyata nace da alama an shirya cutata don naga wannan baƙo ne mai matukar muhimmanci ga Baba sallama nayi don ina son naji muryar bakon kafin na karasa inda yake, don nasan ko wanene kasancewar soron da ɗan duhu kuma babu hasken fitila.
Bai amsa min ba sai da na matso daf da tabarmar da aka shimfida masa sannan ya zaro touch light ya kunna, haske soron da tayi ne yasa naga ashe malam Jibo ne ya sha uban rawani.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Jajayen hakoransa wanda suka sha goro ya shiga buɗe min a yatsine na dube shi “lafiya malam na ganka a wannan lokacin, dama kaine kake kirana”?
Murmushi yayi “nine Sa’adatu samu guri ki zauna xamu yi magana ne ta fahimtar juna ni da ke” ban yi masa musu ba na samu kan wani ɗan dutse na zauna 
“ina jinka kayi sauri ka faɗa min don bacci nake aka taso ni”
Wani kallo yake bi na da shi kamar xai cinye ni
 “Ba ki da labarin xuwan bikinmu ne naga kamar baki san komai dangane da hakan ba”
A firgice na dube shi  “Bikinku da wa?? kai zan aura malam ni bana sonka kuma baxan aureka ba, domin a matsayin ubana kuma malamina na ɗauke ka baxan iya zaman aure da kai ba, kuma ni gaskiya bana sonka kayi min girma ina da wanda nake so kuma har an gama magana da shi”

Murmushi yayi “Haba Sa’adatu kenan idan an gama magana da shi me yasa mahaifinki yaxo ya same ni yace ya bani ke, ki daina rudar rayuwarki da wannan shashan saurayinki naki mayaudari wanda ya lalata miki rayuwa, da kike ganin na tsufa, tsufan iya fuska ne kawai, amma duk namiji namiji ne babu yaro babu tsoho, abinda nake so ki gane yanxu shi ne, ki kwantar da hankalinki mu yi magana ta fahimta don wannan auren wallahi babu fashi sai an yi shi matuƙar muna numfashi ni da ke, idan kinga an fasa sai dai idan na mutu ko kin mutu, don haka ki bawa xuciyarki hakuri ki tsaya mu tsara bakinmu da yadda zai kasance. Kece baki san abinda ke faruwa ba har kike wannan maganar ba don tsutsayi ya gifta ba da tuni an daura auren nan, yanxu haka ma kina gidana, kuma ko jiya mun tattauna da mahaifinki a kan a sake daurawa nace a bari mu dai-daita junanmu, sbd bana son takura miki, amma naga har kina taurin kai kina wata fiffi’ka ko? To mahaifinki ma yaso bani ke, sbd ya faɗa min cewa ke bazawara ce a rigar yan mata tsohon saurayinki ya gama da ke, sbd na rufa miki asiri yasa xan miki lefe ko kala biyun ne saboda kada mutane su gane halin da ake ciki, amma tunda haka kika zaba bari na tashi na tafi, aure za a kaura ko ta halin kaka kuma gidana ya zama dole kixo”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Yana gama magana ya miƙe ya tafi a fusace, dama malam Jibo mutum ne mai fushi da zuciya, a tsugunne ya barni ina kuka.
Ni Sa’adatu naga ta kaina dama Baba yawo yake da ni yana kwance min zani, yanxu mutane duk kallon lalatacciya suke min, wayyo Allah ina xan sa rayuwata, yanxu ko Malam Jibon da nake rainawa na aura wane irin kallo zai rika min, a yanzu dai na zaɓi na mutu a kan na cigaba da wannan muguwar rayuwar da nake yi, baxan iya auren malam jibo ba wlh sosai nake faɗa.
Kwanciyar nayi ina kuka mai cike da ban tausayi.


Kwana biyu ban yi typing ba bana jin dadi a yi min uxuri

Kada a manta da comment da share


*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button