NOVELSUncategorized

KWARATA RETURN 1

            *KWARATA RETURN…*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
            *JAMILA MUSA…*


       *SAI NA AURI D ‘ K*???? —— 1


      Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai….      Dakel aka fiddoshi daga wurin , dan bashi da hankali akan ɓarar da kuɗi. Idan zai kwana a haka baya gajiya kuma ba zai daina ba , zaiyi ta zubawa ne baya gajiyawa , haka kuma idan zai bayar yake kyauta maisa ɗimuwa.


      Wace ce ita……………???


      Wata irin dariya yakeyi bayan an fito dashi yana tsaye gaban Momy data bishi da kallon takaici , hahahaha yaci gaba da dariya yana kallonta , nima binshi nayi da kallo ina murmushi saboda ba ƙaramin kyau yakeyi ba idan yana dariya….

       Momy tace idan ka gama haukar ka ɗauki matarka ku tafi gida , daina dariyar yayi tare da taɓe fuska , a yatsine yace ai ba tare nazo da ita ba. Murmushi mai cin rai nayi , ba tare dana sake kallon inda yake ba. Kafin inyi magana akaja Momy wai anayin faɗa , binta Rabiya tayi da sauri ni kuma na kalli Dikko ƙasa da sama a yatsine nima nace , tir tittir nabi tsoho ya ɓatamin wanka , nine tsohon ? Ya tambayeni yana nuna kanshi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
       Yadda ya ɓata ranshi yasa nayi shiru ina kallon ƙasa , jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai sannan yace Allah ya maida mu gida lafiya , banyi magana ba kuma banyi gigin sake ɗagowa na kalleshi ba , nine dai tsoho ko ? Ya sake tambayata da yanayin ranshi ya mishi babu daɗi , hmmm tsoho , ƙara jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai , mtswww , ya wuce daga wurin yana magana ƙasa².

       Da sauri na ɗago ina kallonshi dan harya tafi ya sake dawowa , nine dai tsoho ko ? Dan ina tausayinki kenan yasa kika raina ni ? Har nine zaki kalli tsabar idona kicemin tsoho tsabar kin ɗaukeni sallau , duk shekarar nan ni banma samu wanda ya ɗaukeni sakarai ba kamar ki , ajiye kai yayi da ɓacin rai , zaki ci gidanku Allah ya maida mu gidan lafiya zaki faɗamin nine tsohon idan na riƙeki , yana faɗin haka ya wuce , a firgice na juya bayana da sauri , Rabiya ce ta dafoni ta baya , nayi tunanin shine ya sake² dawowa.

     Ana fita da Dikko itama ta sulale ta fice daga cikin holl in da farin cikinta , ta wani ɓace abunta ba tare da anga fitarta ba , jikin motar ta , ta tsaya ta saka hijabi da niƙaf , bayan ta gama ta wani shige tayi layar ɓata abunta , wannan shine ɗabi’arta , hijabi da niƙaf , bata rabuwa dashi ita musulma , idan kuma zata tafi bariki bata fita da motarta dan gyaran tako…..

       Wai ke me zakiyi mata ne kike neman ta ? Barni na ganta sai in ɗauki mataki a gabanku , tou wai yaushe suka saba haka har ya saki jiki yana mata ɓarin kuɗi a gaban bainan nasi….? Waye ma zai iya sani ? Tsoki ƙawarta tayi cewa wai kema Jiddah bazaki bar wannan banzan Dikkon ba ? Sai kace Dikkon diamond ? Murmushi Jiddah tayi tare da kallon Mardiyya cewa faɗa mata waye Yaya D ‘ K.

Cike da tsantsar soyayyar Dikko Mardiyya ta fara rattafo mata , hmmm ai ya wuce duk inda hankali baya tunani , saima kin ganshi , gashi mai kyau , ɗan gayun bala’e uwa uba ga kuɗi ga mulki , idan yana magana sai ya baki sha’awa , gashi sakatacce wani irin kallo yakeyi mai burgewa , Dikko matashi ne mai wayewar kai , buɗewar ido da gogewar rayuwa amma bashi da mutunci ko kaɗan , damen ɗan iska ne , kuma shiɗin ƙyalƙyal na lariya ne , tantirin kwallon ɗan iska ne yanzu mutum anjima bai sanki ba , yana da baƙon hali , haƙurin zama dashi sai ɗiyar ɗan caca , dan itama “yar tasha ce. Kinsan auren tasha baya ƙarewa saida aci uban juna yanzu , anjima kuma a zama masoya , duk da biyu Mardiyya tayi wannan maganar , sanin manufarta na faɗar haka sai ita da kanta.

       Ƙawar Jiddah tace tou ni me yasa baku kirani na ganshi ba lokacin daya shigo ? Murmushi Jiddah ta sakeyi tare da cewa har hanzu baki makara ba , Mardiyya bata hotonshi ta gani , a duniyance Mardiyya tace waye yaba Mardiyya hatimin nasara ita ba jikar matsafi ba , ai hoton Dikko sai wurin matarshi , gaba ɗaya suka ɗingumo suka yo wurina !

      Sultana Momy tace muje in ajiyeki gida , tou na faɗa tare da kallon agogon wayata 11:22am gaba nayi ba tare dana sake magana ba , ta baya Jiddah ta riƙomin riga , da sauri na juyo dukana dan ganin waye ya rainamin wayau haka ? Cikina ta kalla sannan kuma ta kalleni amma yanayin fuskarta ya nuna taji babu daɗi , amma dake “yar duniya ce , saita wayance da murmushi cewa ina ta magana shiru nace ai nasan bakiji ba , banyi mata magana ba na tsareta da ido , dafe kafaɗa ta tayi kamar ƙawarta tana cewa Aunty Rabiya ai muma a gidan Yayan zamu kwana.

     Rabiya bata kalleta ba tace ai kina da numbershi ki kirashi ki faɗa mishi , ai basai na kirashi ba kuje gidan muma muna zuwa (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); bayanku , Rabiya bata sake magana ba ta wuce , sauke hannun Jiddah nayi daga jikina nima na wuce muka tafi , har muka zo gida Rabiya batayi magana ba nima banyi ba , a waje ta ajiyeni ta wuce. Ni bansan abinda ya haɗasu ita da ɗan uwanta ba , ni na shiga da kaina ciki raina a jagule , a get na biyu na haɗu da Ashiru , yana gani na ya tsaya yana cewa ranki ya daɗe mai gida yace naje na taho dake , ko inda yake ban kalla ba kuma banyi masa magana ba na wuce , shi kuma ɗayan marar kunyar a get na ukku na haɗu dashi shima fita zaiyi , wato bai gaji da iskancin ba zai sake komawa , kenan dawowa yayi gida ya sake sabon wanka , yanzu garin nashi ya waye , ko wane bawan Allah idan dare yayi yana gidanshi yana bacci , koba a gida ba duk inda kake idan dare yayi zaka samu natsuwa , idan bakayi bacci ba , tou kana kusa da ubangiji kana bauta masa a dai² irin wannan lokacin , amma banda Dikko daya maida dare lokacin huɗɗoɗinshi.

      Shima magana yayi min wai daga ina nake ? Kuji fa ? Wai ma daga ina nake ? Kamar ma baisan ina ya baroni ba , shima ko inda yake ban kalla ba na wuce , An mata bakyaji ina miki magana ne ? Ban dawo ba kuma ban tsaya ba na wuce , da ribos ya biyoni saida yazo inda nake yace ke Yarinya bakiji ina magana ne ? Canja hanya nayi naci gaba da tafiya , An mata dake nake fa ? Ganin Sultana tabi hanyar da zata shigar da ita ciki batayi mishi magana ba , yasa yayi parking ya fice da sauri yabi bayanta.

      A palo na zauna ina cire takalmi na , idona cike da hawaye , ai dama Inna ta faɗamin Dikko ƙyalƙyal na lariya ne , bana iyawa da duniyancin shi , tace Dikko ba mijin aure bane ba , amma na kafe kai nace ni ina sansa a haka , yau naga kaɗan daga iskancin shi. Goge hawayen da suka gangaromin a fuska nayi tare dayin shashshekar kuka , shine saida aka tara taron dubu da dubu ya fito yana ma wata liƙi dan ya nuna ma duniya ni ban kai mace ba , ni ban kai sahun irin matan da yake aura ba , ya nuna ma duniya ni ba’a bakin komai nake ba a wurinshi , Momy tace masa ya taho dani gida yace shi bashi ne yazo dani ba , ashe kuma gidan zai taho dan ya sake nunamin ban kai macen dashi zai saka a gaban mota ba ko wayewa yasa ya taho ya baroni , hakan bai mishi ba zai tura Ashiru ya ɗaukoni dan ita budurwar tashi taga shi bashi ne ya taho dani ba , ta gani saida shi ya koma gida sannan ya turo driver ya ɗaukoni , dole Ashiru ya ɗaukoni mana tunda dare yayi yanzu ne yasan amfani na , maganar Inna ta sake duwomin da tace , haka zaiyi ta ɗura miki ciki kina haifar mishi “ya “ya nan ne kaɗai matsayinki.

       Da sallama ya shigo palon , takalmana na ɗauka nayi gaba , ban ansa sallamar ba haka kuma ban kalleshi ba , An mata baki lafiya ne ? Yayi maganar yana biyo bayana , ban mishi magana ba har ɗakina , ina shiga na fara tattara kayana , miye haka kikeyi ne ? Haba An mata wai duk miye na fushi ? Kiyi haƙuri akan abinda ya faru dan Allah , goge hawaye na sakeyi naci gaba da tattara komai nawa , kusa dani ya matso yace An mata Dikko zaki ma yaji ? Haba jarumar mata ban sanki da irin wannan halin ba , kiyi haƙuri ya ƙarasa maganar yana riƙeni jikinshi , kalleni , saida na sake goge hawaye na kalli Dikko , nine ? Yayi maganar kamar zaiyi kuka , banyi magana ba ina kallonshi shima ni yake kallo , a kasalance yace kinyi haƙuri ko ? Ya ƙarasa maganar yana warware fuskarshi da yanayin burgewa , har yayi surutunshi ya gama bance masa kaci kanka ba , saida ya gama rattofo yaudararrin kalamanshi yai tafiyarshi ya barni.

     Tun daga ranar Dikko ya sake ɗaukewa , ma’ana ban sake ganinshi ba , nima ban sake komawa gidansu ba , Jiddah kuma a ranar waje ya ganta masu gadi sun hanata shiga , saida yayi mata rashin mutunci mara ɗaura zani ya ƙara da cewa dama yana cike da ita akan abinda tayi ma Papi , akwai lokacin daya iba mata zai sameta har gaban uwarta anan zai nuna mata tsabar rashin mutuncin shi , duk su basu san halinshi ba labarin iskancin shi sukeji. Tou zaizo har Kadunar , shiru yayi yana kallon wayarshi , bayan wani lokaci yaci gaba da cewa tou a ranar zataji shi yadda yake , kuma idan take sake shiga sabgar iyalinshi kota kuskura ya sake ganinta a goruba koba gidanshi tazo ba , ya jinjina kanshi tare da cin taya ya barɓaɗeta da ƙura , ta gane abinda yake nufi , kawai zaibi ta kanta ne kamar yadda yaci ƙasa ya wuce abunshi….

      Ko a makaranta , haka nake kasancewa suku². Banayin wata walwalla , ina ɗauke da damuwar da tafi ƙarfin shekaru na , cikin kwanakin da basu wuce biyu zuwa ukku ba nayi duhu na rame , kuma ba rashin ci ba nasha , babu abinda na nema na rasa , ina tunanin Dikko ne kawai dakemin wahalar gani , dan yanzu ankai gafen dako text na tura mishi baida lokacin bani ansa , idan na dameshi sai yacemin wai bansan yadda abubuwa suka sha mishi kai ba , saiya rufeni da faɗa ta waya , idan kuma nace na taga barinshi Inna bama zata anshe ni ba , haka nan kawai na fashe da kuka a class , kuma gaba ɗaya ajin yayi shiru saboda malamin dake ciki , duk wanda ke cikin kilas in maza da mata kowa ya juyo yana kallona , miƙewa nayi na fara tafiya ina ƙara yawan kuka na , har nayi nisa. Na dawo na ɗauki sch bg ina da makullin mota naci gaba da kuka ina fita daga cikin ajin ko malamin baimin magana ba.

      Daga makaranta kai tsaye gida na nufa har naje kuka nakeyi , dakel nayi parking na fita ko gabana bana gani na shiga ciki , a palo na sameshi zaune , hankalinshi kwance yana cin abinci baida wata damuwa , kenan idan ina makaranta yake dawowa gidan yayi duk abinda zaiyi ya tafi kafin in dawo tunda yasan lokacin dawowana , sannu da zuwa ya faɗa tare da bina da kallo , cike da ɓacin rai na nufi kicin na ɗauko wuƙa ina cewa saina kashe ka , da sauri ya tashi yana innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , An mata kinyi hauka ne ? Yake tambayata yana nuna saman ƙoƙon kanshi , ey hauka nakeyi , na faɗa ina matsawa kusa dashi , da sauri ya koma can saman inda ake jingina na kujera idan an zauna ya zauna ƙafafuwanshi a saman wurin zaman , yace waye yace miki ana wasa da wuƙa ? Ba wasa nake ba kashe ka zanyi kowa ya huta na gaji da baƙin halinka ko kuma ka sakeni in kama gabana , ta baya ya sauka yana dariya. Lallai An mata amma ban taɓa sanin mahaukaciya bace ke sai yau. Ai dole zakacemin mahaukaciya tunda ka samu mai hankali , riƙe wuƙar nayi dai² yadda zatamin sauƙi wurin burma mishi nace ka sakeni kafin in tuno maka asiri , dafa kujera yayi yana kallona ,

    Zagayawa nayi inda yake har yanzu ban daina kuka ba , dariya yakeyi sosai , cikin dariya yake cewa ni idan wasa kikeyi nawa na gaske ne , ina nan yadda kika sanni ban canja ba. Dan kinga kwana biyu na ƙyaleki kike duk iskancin da kikaga dama , cike da tsantsar ɓacin rai yazo kusa dani yace cakamin wuƙar , cikin hayaniya yace caka׳ , shiru nayi nasa wuƙar ta kalli ƙasa , ƙaryar rashin kunya dakin sake nunamin ita dasai na burma miki ita kin mutu kuma na kashe banza , bari jin Mama tace ke taurin kai gareki , ke kuma kina iƙirari idan kika sa kanki abu babu wanda ya isa yasa ki bari ni nafiki taurin kai da rashin kunya , zanje in zauna ko motsi mai ƙarfi kika sakemin sai kinga yadda zanyi dake , yayi maganar yana komawa inda yake yaci gaba da cin abincinshi.

Kuma koba yau ba saina kashe ka , ke idan wasa kike ni zan kasheki da gaske ne , a tsorace na wuce ban sake magana ba , shi kuma yace zoki ki zauna muyi magana , ƙara fashewa nayi da kuka nace bazan zo ban , ki daina ganin ina lallashin ki , duk ranar da kika cika ni idan kika bari na riƙeki jikinki zai baki labari yayi maganar yana nunamin belt in dake ɗaure ƙugunshi , a wurin da nake wucewa na yadar da wuƙar na wuce ciki ina gunguni , kuma saina ɗauki number duk wata mace a wayarshi , anan zan gano wace ce zai aura saina cicci ubanta…..

     Satina ɗaya rabona da zuwa makaranta , kuma Nabeela da kanta ta tabbatar min cewa Yaya zaiyi aure , zai auri ɗiyar ƙanwar Dady da suke Baba ɗaya , { idan baku manta ba shi Dady a ɗakinsu shi ɗaya ya rage , “yan uwanshi kaf sun rasu sakamakon gobara data cinyesu , su kuma sauran matan bayan an basu kuɗi ko wace ta kama gabanta ita da “ya “yanta , dalilin auren ne yasa yake aikin gidanshi na G R A , kuma itace yarinyar da yayi ma liƙi , Dady ne yakejin farin ciki Dikko zai auri ɗiyar “yar uwarshi kuma shine yayi mishi tayin auren dan ƙara ƙarfafa zumincinsu a matsayin shi na babba , wanda shima Dadyn Mamar yarinyar ce ta nuna masa alfanun hakan , tunda tayi tayin Dady ya karɓa dan cika farin cikin mahaifinsu da yace yasan ko baya raye Umar zai zama jigo ga “yan uwanshi , wanda shima Dadyn yake fatan Dikko a zama bango ga “yan uwanshi mata idan baya nan , shi yasa ya miƙe tsaye saida ya tabbatar Dikko ya daskaru hankalinshi ya kwanta tare da binshi da addu’a , Momy ce bata san auren dan ta raina ahalin Dady yadda mai tunani baya zato , wannan dalilin ne yasa duk suke fushi da Dikko , da Momy ta fara wani tirje² Dady yace ta bari kar rabo ya kashe ta , ai itama an auri nata “yan uwan amma ba’a dace ba , dan haka a bari a taga gaba ko a dace dan auren zuminci abu ne mai kyau , wannan kenan. }

      A makaranta kuwa an kira Dikko cewa na daina zuwa makaranta , su kuma ƙawayena har gida suka zo , suka tambayeni abinda yasa nayi kuka a waccan rana , da abinda yasa na daina zuwa makaranta , na faɗa musu mijina ne zaiyi aure , kuma auren ma na zuminci dan dai kawai su haɗemin kai da “yar uwarshi ni a juyamin baya , na kuma basu labarin liƙin da yayi mata , wanda ni bansan dalilin da yasa yayi shi ba , juyamin baya da rashin san kasancewa dani a inuwa ɗaya , rashin dawowa gida da wuri sai nayi bacci , fita tun safe kafin in tashi , da dai wasu halayya dani bansan yana dasu ba sai yanzu da zai ƙara aure , shine Farisa tacemin ai mazan yanzu idan ana raga musu iskanci suke na wuce (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); shari’a , kar in wani damu kuma na daina ajiye damuwa idan ba haka ba hawan jini zai kamani na mutu a banza in bar yarana , shi kuma zaiyi jimamin rashina na kwana 3 daga nan yayi aurenshi ya buɗe sabuwar rayuwa ya manta da labarina , “ya “yana kuma ayi ta gana musu azaba , su tashi babu wani galihu ko “yanci kamar almajirai , itace ta bani shawara ƙauracewa ɗakin miji , daina bashi abinci , rashin kunya kuma saina cire shakkun Dikko dan matsoraci baya zama gwani ko waye , ta ƙara da cewa na fita sabgar kaf ahalin miji dan dasu ake haɗa duk munafurcin , wannan duk ɗabi’ar mahaifiyarta ne , idan suka samu matsala da Dadynsu bata zuwa ɗakinshi kuma batayin yaji saida tanayin gayu mai ɗaga hankalin namiji , tace idan anyi yaji babu ta inda za’aga miji bare a samu damar gasa masa aya a hannu , a gida za’ayi duk masifar ayi a gama , tou kundai ji matan aure , shine fa tun daga wannan rana na birkice na zama fitsararriya , abun bai tsaya a iya Dikko ba ya shafi kowa da kowa.

     Wani irin gigitaccen mari na yankawa Papi tare da ce masa dan ubanka waye yace ka zubarmin lemu a kafet……? Tashi Papi yayi ya tafi wurin Dikko…….! Da fatan mai karatu ya gane………..???

     Ci gaba nayi da cewa ni banajin tsoron wani zare²n idon banzar mutum , idan taƙamar mutum yace zai dakeni saina bari ya kwanta bacci in mishi wanka da ruwan zafi ko in dafa mai in toye mishi fuska , ko inda nake Dikko bai kalla ba yaci gaba da rirriga Papi da yaƙi ya daina kuka , ni har an nunamin iya zare ido ? Ko rashin kunyar kafi ni iyawa ne ? Nima nan na iya ai shiru² ba tsoro bane ba , kace tuf ka gani , saboda nasan nayi masa nisa , dan tunda na mari Papi na koma matakal bene na zauna daga wurin nake yanko magana , { idan kun tuna benen g r a ya sauke lokacin dana faɗo , na goruba kuma na hau nace zan faɗo ? Yace shine zai jefani na faɗa na mutu , wanda bayan na gudu da yake bani labari yace shi ya ɗaure kanshi da wayar wuta ya faɗo daga sama , wanda ya tafi doguwar jinya…. } fita yayi yaje ya bada Papi ya dawo , har lokacin ban daina zage² ba , shine yajani yakaini ɗakinshi ya rufe bakin rashin kunya.

    An mata wai meke damunki ne ? Gaba ɗaya kin zama mahaukaciya , cike da ɓacin rai nace kaine mahaukaci…….. , duk girman kwanakin da kake saukewa ai ba’a kaina kakeyi ba , wannan matsalarki ce , tunani da neman mafita ya rage naki ƙaramar yarinya……! Riƙe yatsana yayi a bakinshi……. ` saida ya gama duk abinda zaiyi ya shirya ya fice abunshi…..

    Wasu irin zafafan mata ne zagaye dashi ,,,,,,,,,,,,, duk girman daren nan batajin shi bata kuma ganin shi.““, tsaye take a jikin madubi , fitowarta daga wanka kenan , da wayarta ta saita kanta bayan ta danna video , cire towel in dake jikinta tayi taci gaba da ɗaukar kanta tana iskanci ………. Madaidaicin gida ne a cikin anguwar kwaɗo duk yara²n mata ne suke ta gulmar mazajensu , wayarta ta kanga a jikin ƙugunta tayi wasa da jigidar dake ɗaure a ƙugunta , Jiddah bata da burin daya wuce Yazeed yayi auren kishin wuta da ita ,  *KWARATA RETURN…* fatan mai karatu ya fahimta ko….?
     
      Ƙwas׳ ƙarar takalmin ta kakeji a saman tayils , duk lokacin data motsa dan takawa sai jigidar dake ɗaure jikin ƙugunta ta wani ce cas׳ , idan tayi girgiza kuma sai ta wani ce kacau׳ , gyara zaman ɗaurin kallabinta tayi tana ci gaba da tafiya , harta bayyana a cikin palon , sai yanzu ta samu damar fesa turare bayan ta tsaya a gaban wani mutum wanda shekarunshi zasu kai kimanin 50 , Alaji barka da safiya , ta faɗa a shagwaɓe tana kwarkwasa , ɗagowa yayi da niyar ansa gaisuwar , ita kuma ta ɓalle botiran gabar rigarta dake sanye a jikinta , after dress ce a jikinta. Tana buɗewa ƙanan kayan data saka daga ciki suka samu damar bayyana , a aljihun wando ta tura kwalbar turaren data gama shafawa dakel tare da gyara kitson atach ta watsoshi ta gaba da bayanta , miƙa tayi sosai tana cewa yi haƙuri Alaji na rashin fitowa ta da wuri take maganar tana wani mimmiƙewa kamar macijiyar data samu wurin sanyi a lokacin zafi , cikin ɓacin rai mutumin yace ke me yasa baki da ɗa’a ne ? Kuma ni bake nake nema ba mijinki nake kira , 

      Cire after dress in tayi ta wurgar a ƙasa ta ƙara matsawa sosai kusa da Alhaji tana cewa taya zanyi ɗa’a , mai siyar da kayan ƙara kuzarin maza me ya haɗata da ɗa’a tarbiyya ko kunya ? Kaje anguwarmu kayi binciken Sa’adatu mai gilashi kaji me zasu ce maka ? A wannan duniyar idan akwai wani sirri daya kamata al’umma ta sani akan mu’amalar aure tou bai wuce na mata da miji ba , dalili kuwa shine sirrin da ba’a koyar dashi a makarantu ko a gidaje , shi kaɗai ne sirrin da sai wani da wani ke saninsa , to amma kasancewar hanyoyin isar da saƙon sun yawaita nake ganin ta wannan hanyar ya kamata kasan wani daga cikin irin nawa sirrin , matar malam bahaushe ce kan gaba wajen shiga (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); matsalolin aure , kamar yanda zakaji matan na faɗa babu soyayya tsakanina da mijina , shi yasa nake fuskantar matsaloli a gidan aure na , ni gaba ɗaya wannan matsalar duk na tattarata na jibgata akan mata , ɗan yatsina fuska tayi tare da ci gaba da cewa nima dai hakan take daga gareni tunda banyi auren soyayya ba , tsoki tayi sannan taci gaba da cewa , kawai ƙusani akayi wanda ni ba haka naso ba , wannan auren baya hanani neman mazan waje kamar dai yadda nake nemanka. Ci gaban da aka samu na sanin sirrin rayuwar da nayi maka magana shine , hanyar kula da mazaje ta yawaita , wayewar kai da buɗewar ido , zamani ya kawosu sun kuma yawaita ta haryar gidajen karuwa da kuma ganin wannan sirrin ta kafofin yaɗa labarai a nahiyar yana giza gizo a maimakon da can zamanin iyaye da kakanni da wannan sirrin yake ɓoye , an samu ci gaba sosai wanda har takai yanzu idan za’ayi ma yarinya aure basai an faɗa mata cewa idan mijinki yazo yaja zariyar wando karki gudu , ko kuma idan yayi haka , ta zage zif in wandonta , cikin yanayin jin kunya Alhaji ya kauda kanshi gefe guda , wata “yar munafikar dariya tayi tare dayin wasa da yatsun hannunta taci gaba da cewa , suma ƙawaye dake zuwa gidajen ƙawayensu idan sunyi aure danjin labarin sirrin auratayyar yadda yake sun daina zuwa saboda zamani ya kawo manashi sauƙaƙe , ni da kuma kai kowa yasan abinda yake faruwa tsakanin namiji da mace idan suka keɓance , amma ci gaban zamani yasa yanzu su kansu iyaye sun daina wannan huɗubar wa “ya “yansu saida kaji ana cewa yi nayi bari na bari , me zakiyin me kuma zaki barin ne……?

       Murmushi Alhaji yayi tare da kallon Sa’adatu , ɗan girgiza ƙirjinta tayi cewa tou ya kaga nan , da kuma nan tayi maganar tana nuna gabanta da kuma bayanta , bayan ta tabbatar ya kalla ta fara bada step tana tafiya cikin salon mai ɗaukar hankali , saida ta ɗanyi tafiya kaɗan ta juyo tare da ɗan zira yatsunta a aljihun wandonta , gaɓar hannunta riƙe da ƙugunta taci gaba da karkaɗo ƙugunta tana tahowa wa da girgiza , girjinta yaci gaba motsawa , dariya tayi a dai² lokacin data dawo gaban Alhaji ta riƙo kanshi ta ɗora fuskarshi a saman ƙirjinta cewa ya kagani ne ? Shiru Alhaji yayi , ita kuma tace karka damu ina da sirri , sakin kanshi tayi tare da ɗaukar rigarta bayan ta ajiye mishi number wayarta a rubuce jikin takarda tace idan kana da buƙata ka kirani , tana faɗin haka ta rataya rigarta a ƙafaɗar ta fice ba tare data maida rigar ba……. Kamar wani gelele haka yabi bayan Sa’adatu da kallo. ????????

    Cikakken sunan nata shine Sa’adatu Ibrahim , iyayenta talakawa ne na bada misali , babu arabi ba boko haka ta taso a sake kamar ɓatattar dabba , bata nan bata can , bata da aiki sai tallace² , cikin tasha kasuwa da sauran madakatar “yan iska , idan kuma dare yayi sai a kasa mata tallar kayan mata take bin gidajen karuwai , a gidan karuwai ta fara sha’awar shiga sabgar karuwanci dan tana ganin yadda karuwai keyin sabgoginsu , da kuma yadda suke wasa magungunanta da faɗar irin matsayinsu da aikinsu idan sunyi amfani dasu , ita abinda yafi bata mamaki shine , yadda karuwa ke cika ƙatuwar roba irin ta wankan jego da ruwa , mintuna kaɗan namiji yana jiga ɗaki zai fito ya bada maƙudan kuɗaɗe , idan namiji ya fita sai ita karuwar ta shiga cikin robar ta wanke ƙasanta da wannan ruwan , ashe lemun tsami ne ake matsawa a ciki shine ke hana namiji daɗewa idan ya kwanta da mace , yana zuwa akan mace batsal² zai sauka ba tare da ya biya (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); buƙatarshi ba yadda yaso ,

     A gidan karuwai ta fara laɓe jikin window idan mace da namiji sun keɓe , nan ta fara sanin muhinmancin kanta da kuma taƙama da ƙatuwar ƙaddarar da gareta , jin manyan maganganun da suka girmi tunaninta yasa itama ta farajin shauƙin buƙatuwa da abun , wannan dalili yasa ta fara kokowa da maza a tasha , da namiji yayi mata abu saita kamashi da kokowa , shine ta samu wani damen ɗan iska ya fara ɗora mata hannu akan alƙalaminshi , daga nan abun ya zame mata abun tunani da san ganin alƙalamin rubutun maza yadda yake a bayyane , tun daga wannan ranar taci gaba da binshi da kokowa , shi kuma duk lokacin data kamashi saiya ɗora mata hannunta , a hankali ta fara warwarewa ta kwace gaba ɗaya , ta daina bari saiya taɓa mata , daya zo sai kawai ta cafko wurin , shi kuma idan ta taɓo sai yake ƙara gudun numfashin alƙalamin , a hankali dai ya samu ya maida ita “yar hannu ,

     Itama lokaci guda ta faso ta zama riƙaƙƙar “yar iska , tafi ƙarfin iyaye ta daina ɗaukar talla , kafin wani lokaci ta zama Sa’adatu mai gilashi , bayan wani lokaci kuma ta koma mai gilashi kawai , ganin tana ta ansar wuta a harkar bariki yasa iyayenta suka kwantar da ita da aure , tsaye take har yanzu , tunda akayi aurenta taga ita bata dace da zaman BQ ba , Alhajin ne ya kamata ya aureta ko kuma kawai taci gaba da saƙashi a ɗaki tana ci mishi uwa a gado , tunda tazo gidan ta fuskanci yadda Alhaji ke zama da iyalinshi shi yasa take ta mishi tayin kanta , amma ya cika kafiya har yanzu bai amshi tayi ba , ita kuma ta duƙufa akan saita farautoshi ya zama nata ita ɗaya , ta bashi yaƙi ansa , shine wata rana taje ta bashi number wayarta , yadda ya fara kiranta har aka ƙulle duk zamuji….

      Riƙe take , ta wanku iya wankuwa , tana sanye cikin wasu irin sheɗanun kaya masu nuna shatin bireziya da fant , a haka ta tunkari Dikko tana tafiya irin ta riƙaƙƙin “yan bariki , ƙafa ɗaya ake fara shigar da ita ta gaba sai wata ta biyo bayan waccan ta fita , ba bazar² ake tafiyar ba a nutse akeyin tafiyar kuma takon bada tazara ake miƙashi ba , sai tafiyar taɗan riƙayi kamar mutum yana harɗewa kai baƙon abun sai kaga kamar mutum zai faɗi , ba kuma kamar yayi tuntuɓe ba , sudai “yan duniyar sune suka san dalilin yasa sukeyin irin tafiyar a gaban maza , ita kuma tafiyar idan anyita zata ba jiki damar motsawa , kafin ta ida isowa ya gama kalleta tsaf daga ciki , tunda munafikin gilashi ne motarshi , wato na ciki ke ganin na waje , shi kuma na wajen baya iya ganin ka dan duhun gilashin motar , ɗan taɓe baki yayi tare da ɗage girarenshi ya gyara gemunshi sannan ya saka cingom a bakinshi. Saida tazo jikin motar ta kama da niyar buɗewa taji ta a rufe ,

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
     Ɗan fara kwanƙwasawa tayi , bata san ya ganta ba kuma yaga zuwanta iskanci ne kawai yasa ya basar da ita saiya gama kallonta zai fito , idan ya fito kenan bazai kalleta ba bare ta gane tayi ko batayi ba , har ta gaji da tsayuwa taɗan fara canja wuri Dikko bai fito ba kuma bai buɗe ba haka kuma bai daina kallonta ba , Sultana ya kawo ya jera kusa da Yusra , girgiza kanshi yayi tare da cewa kai An mata fa ƙarshe ce , murmushi yayi tare da kallon hotonta a waya yace rashin kunya kenan , Dikko ׳ suna na kenan a bakinki ƙaramar yarinya , dariya yayi tare da ƙara zuƙo hoton yace wai nine zaki dafa mai ki ƙonamin fuska ke mahaukaciya , in Allah ya yadda saina samu lokaci na zaneki An mata dan naga iskancin naki kullum gaba yakeyi , ya ƙarasa maganar yana sumbatar hoton yace ina sanki ƙawar faɗa ta. Ƙara kallo Yusra yayi sannan ya sake kallon hoton Sultana , yace An mata babu inda Allah ya rage ki amma da wannan yajuju wa majujun aka tsere miki , me na rage miki ne ? Fita goma idan zanyi saina shigo miki da duk abinda nasan zaki ƙara sama dashi a zuciyata so goma , ragamata gaba ɗaya na miƙa miki amma kin kasa riƙewa , babu abinda kika aje sai rawar kai kafiya da rashin kunya nan kaɗai kikafi auki.

      Mafiya yawan maza da irin wancan ƙarshen duniya mata ke fizgar imaninsu su cusasu harkar bariki ko basu shirya shiga ba, wasu kuma mazajen laifinsu ne , misali , banbancin matar aure da karuwa , rashin adalci da wasu mazajen sukeyi shine , su kansu kaɗai suka sani kuma rayuwarsu kawai suke ginawa ta hanyar ba kansu cima mai gina jiki da kuma sutura mai martabasu , ka auri matarka ka kawota gida ka jibge , sabulun wanka da turare man wanke baki da kuɗin kitso da ƙunshi ka gagara tsare mata su , amma kai duk sabon yadi ko shadda takalmi da agogo sabuwar fitowa ko wata hula ka siya kai kanka kawai matarka kuma ko oho , kamar Babansu Sultana kenan , ka gagara ciyar da iyalinka da abinci mai kyau ka haɗata da ƙanzo ko garin kwaki , kwaɗon tuwo taliya da manja , kai ko kullum kana can biye da santa lungu da saƙo kana gano sabbin gidajen dahuwar abinci da aka buɗe , kabar matarka da koko kai kuma kaje ka raya kanka da lafiyayen shayi da biredi saboda rashin adalci , abin nufi anan shine ita matar aure ga Allah ta dogara gareka ta dogara , kaine duniyarta kuma kaine take jira ka bata komai na rayuwa , tou bakayi mata ba kuma baka bata ba , ba tada wata wadata ga kuma rashin kwanciyar hankali lokaci guda saita buge gaba ɗaya ta tashi aiki , ga masifar ka na yawan buƙatuwarta gareka , bata da wani ishashen ƙoshi bare ta samu ƙarfi da kuzarin anshe jarabarka kafin a ankara mace ta tashi aiki.

       Shikenan kai kuma ka gama da ita , baka da aiki sai zaginta idan ka zauna majalisa , matarka ƙazamiya ce , bata kitso ba wanka ba ƙunshi gaba ɗaya ta tsofe , tare mukayi aure da wane ko wane ya rigani aure amma har yanzun matarshi kamar yanzu ya (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); aurota , bata tsufa kullum “yar yarinya take komawa kaza׳ bayan kaine mugun , kuma kaine ka tsofar da ita , ka kuma ƙazantar da ita ta hanyar rashin bata duk irin kular daya kamata , shi kuma wanen da kake magana yana kula da matar tashi , yana tsaye akanta wurin ganin ya ciyar da ita ta yadda ya kamata , duk sabuwar atamfar data fito ko wani less janbaki sabon yayi saiya siyo ya kawoma matarshi , sai kuma akaci sa’a mai gayun ce da ansar wanka ba dole zata zama yarinyar ba ? 

    Ana haka sai kaga wata “yar budurwar tana wucewa da ƙyallinta , iyayenta suna tsaye kanta suna ta siyen fauda jagira da sutura basa gajiyawa , data wuce ku majalisa saita bar muku ƙamshinta , daga nan sai kace saika aurota , kaje kayita ɓarin kuɗi ka samota dakel itama ka kawota gidanka , kamar ta farkon itama haka zata bige saboda rashin kula kafin ka ankara ka tara mata kuma duk ka kasa riƙesu , babu sauran wurin dan haka saika fara harin na waje. Tunda su sun iya shafa fouda,

Bayan duk “yan shafe²n da sukeyi da ƙwalisar suna ɗaukar ido duk a aljihunanku suke tatsar kuɗaɗen , baka raya gida ba amma ka raya waje , baka siyawa matanka kayan shafa da sutura ba ka siyawa matan bariki wanda bakai kaɗai ne kake morarta ba , wasu kuma matan laifin nasu ne , a siyo a kawo musu amma basa dai gyarawar , matsalolin dai daban² ne , wasu rashin kula da mazajen nasu ta hanyar gagara fita haƙƙinsu da kuma rashin iya kula dasu a makwancin , ɓangaren sabta rashin iya kalami mai laushi da kuma rashin girmama miji kesa suna fita daga zukatan mazajensu , mtswww nima dai gani nan…. Fita dai haƙƙin iyali kawai shine mafita.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
      Ɗaure fuska yayi ya fito da fuskar rashin mutunci , baima Yusura magana ba ya wuce tabi bayanshi tana mishi sannu da zuwa , bai tsaya ba bai kuma ansa ba itama bata daina binshi ba , motarta ta koma ta ɗauko wayarta da wata “yar ƙaramar food flarks wai tayo mishi danbun nama….

        Da Abbakar suka gaisa shima ba magana sukayi ba hannu sukayi kawai ya wuce , Abbakar shima bayanshi yabi kamar dai yadda Yusra kebin bayan shi , haka yaita gaisawa da mutane sune rufa mishi baya , duk taron mazan nan Yusra ce kaɗai mace da shiga irinta kafirawan da basa zuwa coci , har wurin da Dikko yake zama , daga nan yace kowa yaje kenan zai gana da Yusra , bayan sun fita ne ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa ya gda ? Lafiya qalau ranka ya daɗe ta faɗa tana miƙa mishi kular data zubo mishi danbun , ansa yayi a mutunce tare da kallonta kamar na minti ɗaya , sauke kanta tayi ƙasa tanajin kunyarshi , ɗan tauna cingom yayi sannan yace zauna yayi maganar yana harɗe ƙafa ɗaya saman ɗaya.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
      Bata zauna saman kujera ba ta zauna ƙasa dan bashi girma , ta fahimci shi mutum ne mai san a girmamashi , su masu kuɗi duk ƙanƙantarsu suna so a basu girma na musamman saboda kuɗi , kuɗin ne kesa musu girman kai , izzar kuɗi kesa suke ganinsu su wasu manyan shegu ne na daban , tou bare Dikko daya raina mutane , gashi da rainin hankali dan idan ya raina maka ƙura babu daɗi , bare su dama Mom insu bata nuna musu sanin darajar mutane ba wanda yin haka ba kyau ba , kawai dai iskanci da rashin kunya a cikin jininsu take.

      Buɗe kular yayi tare da cewa ya akayi ne ? Ya maida ya rufe , ba komai ranka ya daɗe kawai dai naji anyi maganar dambun nama ne shekaran jiya da kuna fira sai nace bara inzo maka dashi , ba tare daya sake kallonta ba yace da kyau , bayan wani lokaci yaci gaba da cewa zaki iya tafiya , ba haka taso ba , dole ta tashi ganin shima ya miƙe ya fice , kallon kular tayi sannan tabi bayanshi da kallo tuni ya fice , a waje ta sameshi yana magana da mutane , saida safe tayi musu ta wuce , su Abbakar suka cinye dambun nama , shi kuma mota ya koma yana tunanin girman rashin kunya da raini irin wanda Sultana tayi mishi har 12 tayi , lokacin nayi ya buɗe wayarshi ya fara ansa kira daga mutane daban² , waya biyu kawai ya ansa duk da tarin yawan kiraye²n dake shigowa ya leƙa yanar gizo , a whatsapp saƙo biyu kawai yayi reply , ɗaya na ɗiyar ƙanwar Dady , data turo mishi fatan alkairi da addu’ar samu nasara a rayuwarshi , ya tura mata ngode. Saina wani  abokinshi daya ya samu ƙaruwa , yace Allah ya raya , saƙon Yusra kuwa kasa kalla yayi , yana ƙorarin gogewa text in Sultana ya shigo a ɗayar wayarshi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
       Dubawa yayi , bayan ya gama karantawa ya kirata , An mata ki kiyayi ɓacin raina tara ki nakeyi karki bari in riƙeki , magana tayi cikin kuka , yanzu me zan miki ne ? Magana ta sakeyi , to wai me zan miki a gidan ne ? Bayan tayi magana , yace da Allah bazan dawo ba , wallahi bazan zo ba karki ɗaukeni ƙaramin yaro mana , ba yanzu kika gama zagina ba ? Ey bazan dawon ba sai 3 na dare , yana faɗin haka ya ajiye waya.

    Yauma bai dawo gida ba sai 3 na dare , kuma idona biyu , inajin lokacin daya shigo ya kwantar da Papi ya kashe fitila ya fita , yana fita na kunna hasken , saida na tabbatar ya isa ya shiga wanka na nufi ɗakinshi , wayarshi na ɗauka nabi jerin kira babu kiran mace ko ɗaya kuma shima bai kira ba , danshi dama ba ma’aboci waya bane ba , inbox na koma ban samu ba dan haka na tafi whatsapp na fara dubawa , har cht in da bai buɗe ba saida na buɗe , 

    Wayata na ciro daga jikina na fara ibar numbobi , bayan na gama naci gaba bin cht ina dubawa , wata irin zufa ta ketomin ganin hoton mace tsirara aihuwar uwarta a wayar Dikko , kyarma jikina ya fara , da sauri na fara ƙoƙarin turawa a wayata , jikina yana kyarma , bansan lokacin daya fito ba kuma har yanzu jikina bai daina kyarma ba , saida na gama na ajiye wayar , zan fita na ganshi jikin ƙofa tsaye ya rumgume hannayeshi yana kallona.

      Baimin magana ba ya taro hannunshi in bashi wayata , ba gardama na miƙa mishi , goge videon yayi ya maidomin wayar tare da bani hanya ya nunamin da hannunshi in fice , ƙin fita nayi ina kallonshi , ya akayi ne ? Ya tambaye ni , cikin kuka nace kadai ji kunya , da yanayin ko a jikinshi yace you sai me ? Ni banji kunya ba kece dai kikaji kunya da kika kasa ɗaukemin idona akan su , yayi maganar yana nunani da ɗan yatsa , to kinga ke kin ɓoye naki , ga na wata nan a wayata , kyauta ta bani ko sisi ban biya ba duk saboda inyi farin ciki , kuma banyi “yar murya ba cewa a taimaka min na gani , bina takeyi na taimaketa na bata abinda ke nake haɗaki da Allah in baki bakya so , to ita ni take haɗawa da Allah in bata ya ƙarasa maganar yana riƙe ƙugunshi yana ci gaba da cewa shin na bata ne ko kuwa kina so ? Tirrrr na faɗa tare da fashewa da kuka , hanya ya sake bani a karo na biyu yana nunamin da hannunshi cewa ai baki fara kuka ba sai amarya tazo tunda ke daƙiƙiya ce , zoki fitar min daga ɗaki.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
     Fita nayi ban mishi magana ba na nufi ɗakina ina kuka , ɗan gajeren tsoki yayi bayan fitar Sultana sannan yace kyaji dashi , kashe haske yayi yai kwanciyarshi , tunda ya kwanta zuciyarshi ke cewa ya kira Sultana kartaje taita kuka , gyara kwanciyarshi yayi a bayyane yace da Allah ƙyaleta tunda bata da wayau.


      Bayan sati 2.

       Har yanzu banje makaranta ba , Dikko yayi faɗa harya gaji ya ƙyaleni , dan yanzu ko zai kasheni bana magana , bana tura mishi saƙo , idan dai yacemin inyi mishi kaza , zanje inyi ne , amma bana masa magana kuma bana masa dariya , idan ina palo ya shigo kawai zan tashi ne , ko ina naje idan ya biyoni zan bar mishi wurin idan yayi magana ba amsa saidai in aikata kawai a aikace. Na zamar mishi kurma a magana.

      Ita kuma Inna naje wurinta kuma na faɗa mata Dikko zai ƙara aure , tace ni na (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); jiyo kuma damuwar nice wannan bai shafeta ba , a ranar gidan na yini dani da Papi sai 9:37pm na koma gida , yace ina wuta ya sakani ina naje nayi wannan zaman ? Yafa gaji da iskanci na in ajiye mishi ɗanshi in koma daga inda na fito , keda ke gidanki idan kinji shi tou naji abinda yace , cike da masifa yazo gabana ya ɗallarmin bakina da yatsunshi , da sauri na zabura tare da rufe idona saboda azabar ɗallin da naji a bakina, bakyaji ina miki magana ne ? Ban kalleshi ba kuma banyi magana ba , shigowar Papi ɗakin ne yasashi fita yana magana ƙasa² wai zai dawo dana rainashi yanamin magana nake mishi shiru.

    Har safe bai dawo ɗakina ba , ni kuma yau na shirya dan zuwa makaranta……..
*JAMILA MUSA…*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button