NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 3

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
             *Na*
*Jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*

*3*
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A makaranta ma dai ban wani mayar da hankali nayi karatu ba saboda yawan tunane-tunanen da na riƙa yi har malam sai da ya fuskanci ina cikin damuwa. Tare da Rukayya muka dawo muna tafe muna hirar mu irin ta kawaye, gidanmu tace zata je saboda kawai tana so ta ɗebe min kewa na manta da dukkan damuwa ta, sannan kuma ummansu bata nan ko ta koma gidan babu abinda zata yi sai zaman kaɗaici.

Sallama muka ji a bayanmu gaba ɗaya muka waiwaya ba tare da mun amsa sallamar ba, wani kyakkyawan saurayi ne mai cikakkiyar kamala sanye yake da shadda fara ƙall wacce aka yiwa aiki da brown din zare, takalminsa ma brown ne, kansa babu hula wanda Hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawan kwantaccen gashin sa, bai gajiya ba wajen sake yi mana sallama wucewa muka yi muka kyale shi ba tare da mun amsa masa ba, biyo bayan mu yayi. “Haba bayin Allah bai kamata ku ƙi amsa min sallama ba, ga alamu sun nuna min ku malamai ne baxa ku wulakanta ni ba  wannan dalilin ne ma ya ja ni har nayi kwadayin yi muku sallama nasan baxan samu matsala ba ya kamata ku amsa min kada ku watsa min ƙasa a ido” kanmu a ƙasa muka amsa masa da “wa alaikumussalam” muna gama amsawa muka juya don cigaba da tafiya, saboda idan da abinda na tsana na tsaya ina magana a hanya ko da yar uwata mace ne ban so ballantana kuma da namiji.
 Ganin yadda muka wuce muka kyale shi bai sa yayi zuciya ba sake bin bayanmu yayi, ku yi hakuri na tsayar da ku a hanya ko, na san kuma hakan ba dai-dai bane amma na kasa hakuri ne sbd daya daga cikin ku ce tayi min sata”

Gaba daya muka juya muna yi masa kallon mamaki Rukayya ce tayi ƙarfin halin yin magana sbd ta fi ni baki, gaba ɗaya na kasa cewa komai sbd mamakin jin fitowar kalmar sata daga bakinsa “sata  fa kace bawan Allah?? Sake wani zancen dai ba wannan ba, mu bama sata kuma bamu taɓa satarwa wani dan adam komai ba, muna bakin kokari wajen dogaro da abinda Allah ya wadata mu da shi”

Murmushi yayi wanda sai da fararen hakoransa suka bayyana sannan ya dan sha kunu “ba ke nace kin min sata ba kawarki ce, amma ita ma bata san ta min satar ba” A razane na dube shi kirjina na dukan uku-uku sbd bana so na sake dakkowa innah abinda xai xame mana abin gori da bak’ar Magana, cikin rawar murya na fara magana “ban taɓa yiwa wani sata ba tunda nake malam watakila mai kama da ni ka gani” ban jira amsar da zai bani ba na ja hannun Rukayya muka cigaba da tafiya.
Sake shiga gabanmu yayi “ku tsaya mu warware matsalar mana ko su ku ke yi sai Maganar ta je gaba? Idan haka ku ka zaba shikenan, amma ni shi ne abinda bana so. Tsayawa muka yi cak muna sauraron shi, gyara tsayuwa yayi tare da tambayata kin san satar da kika yi min. Da sauri na amsa masa da ban sani ba, rausayar da kansa yayi.
“To zuciyata kika sata”
Gabana ne ya fadi mamaki ya mamaye ni wai yau ni wani da namiji yake cewa na sace masa zuciya abinda ban taɓa ji ba kenan, sbd tunda nake babu wanda ya taɓa tunkarata da sunan na burge shi ballantana har ya furta yana sona.

Ganin dogon tunanin da na tafi ya sanya shi yi min magana “lafiya naji kin yi shiru ko ba gaskiya bane abinda na fada?” Ban bashi amsa ba na juya na tafi tare da Rukayya na bar shi suna Magana ban san me take fada masa ba. 

Sai da na shiga gida da kusan minti biyar sannan na ganta, sallama tayi na amsa mata duk jikina yayi sanyi.

Masifa ta fara yi min “ke shikenan daga fara magana sai ki wani tafi ki kyale mutane sai ni nayi masa bayani, na fada masa sunanki da kwatancen gidan nan dan haka ki shirya yau kina da babban bako”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Fito da ido nayi “Haba ya xaki min haka ban so kika bashi kwatancena ba” hararata tayi “ok so kike ki xauna a cigaba da miki gori ba mai tayawa ko, ai ko ba aurenki xai yi ba yana da kyau kema a ga kina xance kin huta gori” dakatar da ita nayi “Kinga ni duk wannan bai dame ni ba sama da yadda idan nayi aure xan tafi na bar innah a wannan gidan shi ne abinda ya fi tayar min da hankali”

“Wannan duk na Allah ne Sa’adatu baki san alkhairin da ke tattare da wannan bawan Allahn ba, watakila ya zama silar farin cikinki ke da innah” a takaice na bata amsa da haka ne yar uwata.

Aiki ta taya ni muka gyara ko ina sannan muka yi wanke-wanke muna aikin, mutanen gidanmu na hararmu duk wanda  Rukayya ta gaisar babu wanda ya amsa mata, ita ma baƙin jinina ya shafeta.

Har yamma muna tare da ita sai da aka kusa sallar magariba sannan na rakata hanya ta tafi gida. Ina dawowa bayan nayi sallah ban dade ba na dan ji hayaniya a tsakar gida, ban mayar da hankalin sauraren abinda ake yi ba sbd nasan alkhairi bai fiye fitowa daga bakinsu ba, muryar yan matan gidan mu naji suna cewa ” sam baxai yiwu a ce da Sa’adatu ake sallama ba sbd tunda take ba a taba xuwa ana sallama da ita ba, me xa a yi da mummunar yarinyar nan ga baƙi ga baƙin hali ai farare irinmu ake yayi, kai koma ka sake tambayarsa ya faɗa maka wa ake nema”

Ajiye littafin da nake karantawa nayi nasan mutumin da muka gamu da shi daxu ne yaxo, sallamar yaron ce ta katse min tunanina.

 “yace Sa’adatu yake nema wacce suka haɗu tare a hanyar makaranta”

Jikinsu ne yayi sanyi saboda sun san duk cikin ya’yan gidanmu ni kadai nake xuwa makaranta ragowar basu san komai ba sai yawon gidajen makota. Umma ce tace da yaron “je ka fada masa bamu san da zaman wata Sa’adatu a gidan nan ba”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Hawaye naji na ƙoƙarin fito min yanzu a ce na samu mai son nawa ma sai an yi min bakin ciki, ban samu ba kuma ana min gori. ni kuma baxan iya fita na fada musu Ni ake nema ba ballantana na cewa yaron ya faɗa wa mai nemana ina zuwa ba, saboda na san duk rintsi duk wuya rabona baxai taba wuce ni ba, mayar da idona nayi kan innah tana ta sharar bacci abinta, da nayi ƙoƙarin tashinta na fada mata sai kuma na fasa kasancewar yau bata jin daɗin jikinta.

Ina cikin wannan halin naji sallamar ya salim ta window ya leko da kanshi “Sa’adatu kina ina, yi sauri ki leko xan yi magana da ke”

Sauri nayi na janyo hijabi na saka, nima lekawa nayi ta window nayi masa magana sbd bana so Mahaifiyarsa ta san ina kula mata danta.
“Ya salim gani” nace masa. Karasowa yayi wajena
 “Ba kece kika yi baƙo ba Sa’adatu kin barshi tsaye yana jiranki tun daxu, ga sanyi ana yi, baki kyauta ba wlh, abinda muke nema Allah ya kawo mana xaki mana asara”

Ban fada masa abinda ya faru ba illa kawai murmushi da nayi “na zaci wajen su A’isha yaxo shi yasa ban fita ba”

Hararata ya dan yi “menene alaƙa tsakanin sunan A’isha da Sa’adatu ke dai kawai kice kina jin kunya, tashi ki shirya yana can yana jiranki” 
Har ya juya ya tafi ya dawo “Au na manta ba ni tabarma na je na shimfida masa”

Ɗan bata rai nayi “Haba ya salim daga xuwa sai a fara ba shi tabarma ka bari mu tsaya a tsaye, ni baxan dade ba minti biyu na dawo” 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Riƙe baki yayi yana kallona lallai Sa’adatu har yanzu ba ki san rayuwa ba, wanda yaxo wajenka abin girmamawa ne  ya cancanci kayi masa dukkan abinda xai sa yayi farin ciki. Saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da kansa ya fada mana cewa wanda ya bada gaskiya da Allah da ranar lahira ya girmama bakonsa, ke malama ce amma kuma kina mantawa, maza miko min na tafi”

Ban tanka Masa ba na miƙa masa tabarmar, hijabin da naje makaranta da shi na sake sakawa na fita.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button