NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 3

A soro na biyu ya salim yayi mana shimfida, zaune na tarar da shi ya tankwashe ƙafarsa, kansa a sama kamar mai tunani har na iso gare shi bai san naxo ba sallamar da nayi masa ne ya dawo da shi hankalinsa, da fara’a  ya amsa min tare da gyara xaman sa.

A ladabce na gaishe shi tare da yi masa barka da zuwa, gefen tabarmar na samu na zauna, sai na samu kaina a jin kunya na kasa haɗa ido da shi tunda wannan shi ne karo na farko da na taɓa fitowa zance da saurayi.

Gyara zama yayi yana kallona, wato Malama Sa’adatu sai an ja min rai za a fito ko, ko da yake ban ga laifinki ba ke din mai tsada ce don kin ja aji ba komai girmanki ne ranki ya dade.

Murmushi akwai nayi ba tare da na bashi amsar maganar sa ba.
Gabatar min da kansa ya shiga yi ” nasan dai baki yi mamakin ganina ba,  tunda kin san da xuwana kuma kawarki ta fada miki komai game da ni” girgiza kai nayi alamar bata fada min ba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Murmushi yayi tare da gyara zama “tunda bata wakilce ni ta fada miki ba to ni bari na fada miki da kaina don waka a bakin mai ita tafi dadi. Sunana Izuddeen Muhammad iyayena mu maxauna wannan unguwar ne gidan malam Muhammad mai yan makaranta , na san baxa ki kasa sanin gidanmu ba, sai a lokacin da yayi min wannan bayanin na gane a gidan da yake (mahaifinsa babban malamin addini ne, yana da rufin asiri sosai, sannan mafi yawan ya’yan gidan manyan ma’aikata ne) nayi karatuna a jami’ar Ahmadu Bello da ke zaria na karanci bangaren engineering, Amma ban samu aiki ba sai dai ina ragewa a wani Company kafin babban aiki ya samu. A gaskiya nayi matuƙar farin ciki da Allah ya bani damar yi miki magana, domin na dade ina sonki amma na kasa fitowa na furta miki, kullum sai na tsaya jiranki a hanyar zuwanki makaranta da dawowarki ko xan samu damar  fada miki abinda ke raina sai yau Allah ya bani wannan dama kuma nayi farin ciki da yadda kika karɓe ni, Allah yasa na xama silar farin cikinki na har abada, ki miƙa min godiyar ki wajen kawarki domin da taimakonta na samu wannan damar mai tsada”

Har yanzu kaina na ƙasa na kasa cewa komai “baki ce min komai ba Sa’adatu, ko dai ban yi miki bane?”

A hankali na dago kaina “Na gode da kulawarka gare ni” ita ce kawai kalmar da na iya furtawa.

Bamu fi minti sha biyar muna tattaunawa ba ya mike tsaye ya fara nade tabarmar da na shimfida masa.

Da sauri nace “ka bari na nade da kaina”
A’a ki bari ai baxan so na fara sa ki aiki ba.
“to ni zan tafi Sa’adatu sai yaushe kenan?”

Murmushi na dan yi “sai bayan sati daya”
Da sauri ya dube ni “sai bayan sati daya fa kika ce, kema kin san baxan iya ba, ki bani dama gobe na dawo”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
“Gobe ina da unguwa ka bari ka dawo jibi” amsa min yayi da Allah ya kaimu.

Sallama muka yi ya juya ya tafi, sai a lokacin na tsaya na  kalle shi sosai, kyakkyawa ne mai matsakaicin tsawo baxa ka kira shi dogo ba haka kuma baxa ka kira shi gajere ba, wankan tarwada ne idanunansu masu kyawun gani Musamman idan ya daga ido xai yi kallo xamu iya kiransu da sexy eyes, bakinsa ma madai-daici ne  ga kuma kyakkyawan saje da ya xayyana fuskarsa.

Har ga Allah ban yi tsammanin wannan kyakkyawan saurayin zai furta yana sona ba, kasancewar ba wani kyau ne da ni ba, haka nake ba yabo ba fallasa.

A tsoro na biyu na ci karo da A’isha da innah salamatu da da dukkan yan matan gidanmu, Maryam saliha da bilkisu sun kasa kunne suna sauraren tattaunawar da muka yi da Izuddeen abinda ya bani mamaki ganina bai sa sun ji kunya sun matsa ba, sai ma magana da naji suna yi “lallai abu ya ci-gaba ɗan iska har cikin soro Allah ya kawo Baba yau za a yita ta ƙare”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ji nayi kafafuna sun yi sanyi addu’a na fara yi Allah yasa kada su hada min tuggu a wajen Baba, don yanzu baya jin maganar kowa sai tasu, daki na wuce na bar su har yanzu dai innah bacci take bata farka ba don haka ban tashe ta ba na kyaleta.

Maganar su na rika ji “Ai wlh baxa mu bari yarinyar nan tayi aure ba sai mun hada mata makircin da sai an koreta daga gidan nan sai yayanmu sun yi aure tsaf sannan xata yi, haka kawai ku fi ta komai sannan Izuddeen yaro nutsatstse yace yana sonta yaron da kowa ya san yayi fice a ilimin boko da dana addini, da ku ya dace ba ita don haka kamar mun sa an kore shi ne”


08094136204

A taimaka a rika comment kuma a rika sharing


*Jeeddahtulkhair ce????*

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button