NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 6

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
          *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


*Wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gareka kanina sarkin fitina Buhari y ophicial (It’z B Y ebrerheem) Allah ya bar zumunci ina godiya da yadda kake taya ni sharing littafina*

              *6*

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Hawaye na gani ya cika idonta da sauri na fara tambayarta “menene ya sa ki kuka Rukayya? Kiyi hakuri insha Allah alkhairi ne xai same ni, ki daina damuwa da halin da na shiga a yanzu wata rana sai labari” ƙarfin halin mikewa tayi tare da riƙe hannuna “tashi mu je wajen innah hankalina baxai kwantar ba har sai mun samu amsar abinda malam ya fada miki, to ni me ma yake nufi da Maganar nan ni fa na fara tsoron al’amarin sa,, saboda tunda yake tare da mu bai taɓa kiranki ya faɗa miki wani abu makamancin wannan ba, gaskiya idan wani abu ya faru Baba ya cuce mu” tashi nayi ba tare da nayi mata gardama muka riƙe hannun juna muka tafi gida.
Izuddeen muka hanga tun daga nesa yake mana murmushi babu wacce ta iya mayar masa da martanin murmushin da yake mana saboda dukkanmu muna cikin damuwa, ya lura da yanayin da muke ciki, sauri ya riƙa yi har yana tuntube don yazo ya tarar da mu.
Sallama yayi mana gaba daya muka amsa Rukayya ce tayi ƙarfin halin yi masa magana “Izuddeen ya kake ya gida” amsa mata yayi da “lafiya” mayar da kallonsa yayi gare ni “nasan rashin ganina ne yasa kike fushi da ni to kiyi hakuri ba ni da lafiya ne shi yasa ban zo ba, sai yau na samu kaina” 
Kawar da damuwar da ke xuciyata nayi “Ai dole naji haushi kwana ɗai-ɗai har uku ban ganka ba kaima kasan dole na damu, kuma a ce kayi rashin lafiya baka faɗa min ba ai da naxo na duba ka, ko ban zo ba nasan Rukayya xata wakilce ni gaskiya kayi babban laifi kuma baxan hakura ba”

Tsugunnawa yayi”ranki dade na san nayi laifi a yi hakuri kada a hukunta ni” murmushi nayi wanda bai kai zuci ba “baxan hakura ba har sai kayi min tsallen kwado” dariya muka saka gaba daya Rukayya ce tace “baza a yi haka ba tunda ya fadi uzurinsa shikenan” mun ɗan yi barkwanci sosai da shi kasancewar sa mutum mai saukin kai, kuma yana da nishadi da sakin fuska. Ya jiki muka yi masa, sannan na faɗa masa yadda nayi kewarsa amsa min yayi da “Na warware, nima nayi kewarki sosai ba don uzurin rashin lafiya ba da kullum sau biyu xaki ganni.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Murmushi nayi “kada kasa a ce ka xama tun yanzu ka xama tace” rausayar da kansa yayi “Ai dama na xama ni kan kice ne ma ba tace ba, indai a wajen kyautata miki ne na yarda a kirani da kowane suna, idan kina da lokaci yau zan shigo”

Gabana ne ya fadi saboda bana so yaxo Baba ya yanke mana hukunci karshe ya raba ni da shi ya janyo min asara, shirun da yaji nayi ne ya sanya jikinsa sanyi, cikin Siriya muryarsa yake min magana “ko dai bakya so naxo ne Sa’adatu, idan akwai wata matsalar ki fada min, don na san yadda zan yi na shawo kanta”

Gargixa masa kai nayi alamar babu komai, sauke ajiyar xuciya yayi tare da furzar da numfashi mai zafi “shikenan Allah yasa abinda kika fada min haka ne” eh nace ai kasan baxan faɗa maka abinda yake ba dai-dai ba
 sallama muka yi da shi sai da ya rako mu daf da layinmu sannan ya juya.
Ko da muka koma gida innah bata dawo ba, rashin dawowar innah ba ƙaramin damuwa ya jefa ni ba, muna cikin wannan halin naji maganar Baba sai a lokacin na san yana gidan, cike da fargaba da rashin sanin yadda xan tunkare shi da abinda malam Jibo ya fada min na tashi jikina babu ƙarfi, tunda na fito naga su A’isha da zaliha suna ta tuntsura dariya, wacce ni kaina na kasa gane fassararta wucewa nayi na kyale su suna ta haukansu.
A dakinsa na tarar da shi yana cin abinci, da sallama na shiga ina ganin haka na juya saboda na san indai yana cin abinci baya saurarar duk wanda yazo wajensa.

Juyawar da nayi ne yasa shi kwala min kira, jikina na rawa na koma “gani Baba” cikin ɓaci rai ya fara min magana
“Lafiya naga kin zo kuma kin juya wane munafuncin ne kuma ya kawo ki da har yasa kika juya?”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kaina a ƙasa na fara magana “Dama malam Jibo ne ya kira ni daxu da naje makaranta yace idan naxo gida na tambaye ka maganar da ku ka yi”
Ajiyar zuciya yayi “ina da dama da ikon da zan yi duk abinda naga dama a kanki, bana buƙatar shawara da ke ko wani abu da yayi kama da haka, kije idan da rai da lafiya zaki ga amsar tambayar ki a aikace”

Ji nayi kafafuna sun kasa ɗaukana jiri na shirin dibana ya fadar da ni a kasa, don haka na nemi guri na tsaya. Tsawar da ya daka min ce ta dawo min da ni hankalina jikina “fice min daga daki munafukar banxa munafukar wofi kin tsaya kina sand’a kamar mutuniyar kirki”

Da sauri na fita na bar masa dakin, abinda na kasa ganewa shi ne mai baba yake nufi da xan ga abinda yake nufi da idona idan muna da rai da lafiya??????


*Yau ba comment da yawa, idan ana comment pages uku xan dinga yi kullum matuƙar aka daina comment ni kuma xan daina typing gaba daya*


Kada a manta a taya Ni sharing

*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button