NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 7

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
          *Na*
*Jeeddah Tijjani*
       *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*



*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


*Wannan shafin sadaukarwa ne gareki DALA admin Dala novel Ina godia da gudunmawarki gareni*

               *7*


Da kyar na ja kafa na shiga daki, ina zuwa na zube a ƙasa, mikewa Rukayya tayi tare da tambayata “ya faɗa miki abinda maganar malam ke nufi”? Cike da damuwa na yi mata bayanin yadda muka yi da shi, haɗa kai muka yi muna kuka mai cike da ban tausayi ni ina tausayawa kaina ban san ma’anar abinda Baba yake nufi ba, Rukayya na tausaya min halin da xan tsinci kaina a ciki. Har yamma innah bata dawo ba wannan dalilin ne ya ƙara saka ni a tashin hankali sbd tunda nake da ita ban taɓa ganin taje unguwar ta kai yammaci ba iyakar dadewarta la’asar, hankalina ne ya ƙara tashi ga damuwar Baba ga damuwar tafiyar innah, ga shi babu waya a hannuna ballantana na kira gidan da taje. Mayar da kallona nayi ga Rukayya “Ni fa na fara damuwa dadewar nan ta innah tayi yawa” cike da kulawa take min magana “Nima haka wlh magana ne kawai ban yi ba kada na sake ji miki wani ciwo a xuciyarki, amma tashi mu je gidanmu ki xauna zuwa anjima sai mu dawo mu duba ko ta dawo” tashi nayi na dakko hijabi na saka muka tafi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); A cikin damuwa ummansu ta ganmu tambayar mu halin da muke ciki tayi, ban iya yi mata magana ba saboda na san ina farawa xan iya fashewa da kuka sai Rukayya ce ta faɗa mata abinda ke shirin faruwa da ni. Kwantar min da xuciya tayi da kalamai masu ratsa jiki da sanyaya ruhin ɗan Adam musamman idan yana cikin damuwa, abinci ta xuba mana bai fi cokali uku nayi ba na ajiye saboda damuwa ta cika cikina.
Sai da muka yi sallar magariba sannan muka dawo gida, abin mamaki a kulle na sake ganin dakin innah tashin hankali ne ya bayyana a fuskata sai naji kamar na fashe da kuka amma sai na daure saboda bana so su A’isha su gane halin da nake ciki, jan hannun Rukayya nayi muka koma soro saboda baxan iya jure xama a dakin innah ba, ba tare da tana cikin dakin ba. Zama muka yi shiru babu mai cewa kowa komai sai dai tunani da kukan zuci da nake yi.
Sallamar ya salim ce ta dawo da ni hayyacina, haska mu yayi da wayarsa “Au dama ku ne a zaune ai na zaci aljanu ne” dariya muka saka gaba daya nice nayi ƙarfin halin yin magana “Haba ya Salim aljanu xaka gani a haka” murmushi yayi “Eh mana idan ba aljani ba waye xai xauna a duhu shi kadai” 
“Akwai abinda muke jira shi yasa ka ganmu a nan” kallona yayi yana murmushi “ko dai mutumin ne zai dawo” girgiza kaina nayi “ba shi bane innah nake jira ta tafi unguwa tun safe bata dawo ba” ɗan hararata yayi ” ka ji ta da wani zance wai innah kike jira banda abinki innah xata bata ne, xata dawo duk inda ta tafi bwatakila ma tana kan hanya, ke dai naga yadda xaki yi idan aurenki yaxo lokacin da xaki rabu da innah”
Kwalla naji na ƙoƙarin fito min da sauri na mayar da ita “Ba don aure sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam bane da nace baxan yi ba saboda rabuwa da innah a rayuwata ba ƙaramin tashin hankali bane” ji nayi mahaifiyarsa ta kwala masa kira, bai amsa ba sai da muka gama magana sannan ya amsa mata da yana zuwa.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Duk da cewa muna ɗan nesa da juna amma sai da na jiyo sautin muryarta tana yi masa faɗa “kai wane irin yaro ne mara jin magana, ba na raba ka da Sa’a ba, me kuma kaje kana ce mata? tun wuri ka daina kula yarinyar nan kafin nayi maka baki” shi dai shiru naji yayi mata bai ce komai ba ni kuwa a xuciyata nace “yau na janyowa ya salim faɗa” Ni kaina ina so na daina saurar shi idan ya kula ni, sai dai baxan iya yin hakan ba saboda yadda yake bani kulawa da yadda yake damuwa da dukkan abinda ya dame ni.
Muna a wannan halin muka ji sallamar innah da sauri na tashi na rungume ta ina yi mata oyoyo ita ma Rukayya sannu da zuwa tayi mata, sai dai abinda ya bani mamaki tare da kakarta gwaggo Abu suke tafe, da alama ita ce ta rakota gaisheta muka yi da sakin fuska ta amsa mana, bin su muka yi gaba daya muka shiga ciki, ƙoƙarin bude dakin nake yi xamu shiga, muna gama buɗe musu dakin gwaggo Abu ta dakatar da mu “ku tsaya a nan na fito sai ku shiga” bin umarninta muka yi muka zauna a bakin kofa, abinda na fahimta akwai maganar da zasu yi wacce basa so mu ji.

Cikin siririyar murya take yiwa innah magana “kiyi hakuri mero, wannan dakin shi ne sutturar ki duk abinda za a yi miki ki kawar da kai kiyi hakuri, idan kika ce kin yi fushi ki tafi kin bar gidan nan wane hali kike so ‘yarki ta samu kanta, kin san dai halin malam Salisu sarai baxai bari ki tafar masa da ‘ya ba, dan Allah kiyi hakuri da dukkan abinda zaki ji ko ki gani wata rana sai labari, basu isa su yi muku abinda Allah bai muku ba, komai kika ga ya samu bawa mukaddari ne sannan ki manta da Maganar mutumin nan zamu yi iya bakin kokarinmu wajen hana abin sai dai idan kuma ya fi karfinmu” 

Godiya innah tayi mata, sai da ta raka gwaggo Abu har bakin kofa sannan ta dawo, abinda na fahimta a Maganar da suke yi kamar yaji innah tayi aka dawo da ita.
Daki muka shiga tambayarta na fara yi “Innah ina kika tafi kika barni ina ta tunani duk duniya tayi min zafi” ƙoƙarin mayar da damuwarta tayi don kada na gane halin da take ciki amma hakan ya gagara don kallo daya xaka yi mata ka gane akwai damuwa mai yawa a tattare da ita. “Yau na sha yawo ne a garin nan Sa’adatu shi yasa na dade ban dawo ba, kin san na dade ban fita ba to akwai gaishe-gaishen marasa lafiya da naje da gaisuwar mutuwa da yan barke-barke shi yasa na dade”
Sannu da zuwa muka yi mata, har na bude baki xan tambayeta dalilin rakiyar da gwaggo Abu tayi mata sai kuma na fasa, saboda bana so na ƙara tayar mata da wani tabo a xuciyarta, sai bayan sallar isha’i Rukayya ta tafi gida yau da wuri muka kwanta bacci saboda mu yi yaƙi da damuwar da ta addabe mu.

Yau ya kama Alhamis ba makaranta don haka ban tashi da wuri ba sai da rana ta ɗaga sosai kasancewar garin akwai dan sanyi, ita ma Innah baccinta take yi, daga gidansu Rukayya aka aiko mana da abin karin kumallo sai da muka watstsake sosai muka karya. Muna cikin cin abincin na jefawa innah tambaya “innah wai me Baba yake nufi dani? naje makaranta ne jiya sai malam jibo yace naxo na tambayi Baba a kan maganar da yaje masa da ita, da na dawo na tambaye shi ya nuna min cewa duk hukuncin da ya yanke a kaina ya yanku sai dai nayi hakuri dan Allah me yake nufi da hakan, na tambayi kaina na kasa gane amsar abinda suke nufi, na san duk abinda yake faruwa zaki iya sani kuma baxa ki boye min ba”?
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ina kallon idanun innah kamar xasu xubar da hawaye, hadiye miyan takaici tayi gami da cewa “Babu komai Sa’adatu kawai xance ne irin nasa so yake ya tayar mana da hankali”

Kuka na fara yi “Allah innah da gaske yake, lokacin da yake Maganar babu wasa a fuskar shi, shima malam din haka sannan malam Jibo yana magana yana murmushi, a jiyan kuma naji innah salamatu tana habaici maganganunta sun yi kama da abinda malam da Baba suka fada min kada fa a ce shi Baba xai aura min”
Saurin dakatar da ni tayi ” ya kike irin wannan maganar Sa’adatu bana so na sake jin irin wannan daga gare ki, kin san haka baxai faru ba insha Allah”

Sosai nake kuka “wlh Innah indai shi aka ce za a  aura min baxan xauna ba kuma sai yaga salo salo na rashin mutunci, saboda an raina mu duk ya’yan gidan nan ni kadai aka tsana wa aka taɓa yiwa irin abinda ake mana, wannan karon baxan iya yiwa Baba biyayya ba sai dai idan a kore mu”
Shiru Innah tayi tana saurarona nasan bata taba tunanin fitowar wadannan xantukan daga gare ni ba. Rarrashina ta shiga yi har sai da xuciyata tayi sanyi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Yau muka yi da Izuddeen xai kawo min ziyara tun yamma na fara shiryawa saboda na kosa yazo a yi duk wacce za a yi yanxu tsoron kowa ya fita a xuciyata, Bayan sallar magariba na cigaba da jira shiru bai zo ba, sai daf da isha’i aka aiko yaro ana kirana, ban ja lokaci ba na fita shimfida nayi masa a inda ya xauna ran nan, gaisawa muka yi muka fara hirar mu ta masoya, cike da nishadi muke maganar mu kamar babu wata damuwa a raina, sai da hirar mu tayi nisa sannan ya miko min wata leda, “karbi wannan Sa’adatu” makale kafada nayi alamar baxan karba ba sake miko min yayi “ki karba kiga abinda ke ciki” ban yi masa gardama ba na karba ina budewa waya na gani sabuwa fil a kwalinta kirar infinex, da sauri na bude ido ” wannan wayar ta min girma ka barta idan kana da karama ka bani” a xuciyata nace idan ka bani wannan ai sai a ce karuwancin nake yi da gaske, muna cikin duba wayar muka ji mutum a kanmu.

Daga idon da zamu yi naga Baba yana mana wani kallo, cike da ladabi Izuddeen ya gaishe shi, harara ya kwada masa bai kuma amsa gaisuwar ba.

 Cikin fushi ya nuna Izuddeen da hannu “Dan ubanka dama kaina kake zuwa har gida kana lalata min yarinya”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Kallon mamaki Izuddeen ya bi shi da shi saboda bai san me yake nufi da abinda yake fada ba, cikin ladabi ya sunkuya “wlh Baba ba da niyyar yaudarar Sa’adatu naxo ba naxo ne don na aureta” nuna shi yayi da hannu aurenta xaka yi amma kaxo kana lalata ta da Abin duniya salon ta bijirewa iyayenta ko? Irinku ne masu hurewa yaran Mutane kunne har gida, ashi ka fita ka bar min gida kafin ranka ya ɓaci kada na sake ganinka a nan, ke kuma xaki zo ki same ni”

Wucewa yayi ya barni a tsugunne ina sharar hawaye har Izuddeen ya fita yana waiwaye na.



Idan an yi comment na saki page 8 Idan ba a yi ba na rike kayana sai gobe



Kada a manta a rika sharing don yan uwa su karanta


*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button