FARHATAL-QALB 17
PG:17_
Akan yan makarantar dake wucewa. Wasu na tafe suna ciye ciye. Wasu suna hirarrakin su yayinda wasu ke tafiya kawai.
Ya kifa kansa akan sitiyarin motar yayin da fuskar sa ke kallon waje. Tamkar almara yana sake bude idanun yaga tamkar yarinyar nan ta dazu. Suna tafe su uku. Biyu na hira, Ya yin da ita kuma kawai tafiya take. Amman daka gansu kasan atare suke.
Hannunta daya ta saka ta na gyara zaman gilashin idanunta da suka kara mata kyau. Ya sake bude idanu. Wata zuciyar na ingiza shi. Da shi kansa ya kasa gane menene dalilin?
Ya sake matse idanu ya bude. Wannan karon kuma ba ita yagani ba. Wasu ne daban yan makarantar su ma su uku suna tafe.
Girgiza kai yayi kawai. Kenan yarinyar nan gizo ta fara masa.? Har idanun sa ke nuna masa hotanta bayan ba ita din ba ce.
Ya sauke zucia . Hade da kunna rediyon motan. Labarai akeyi na kasa da yadda ruwa ya yi gyara awasu guraren.
Wayar sa ce ta shiga kara. Mahaifin sa ne ke kiran sa. Nan da nan ya dauka ya dauka.
“Hello Abiey. Na’am, Wallahi Abiey ban karasa ba. Wani hold off ne ya tsare ni. No! Mota ce ta lalace. Amma suna gyarawa. Alright insha Allah.”
Dakyar aka iya gyara babbar motar data lalace. Aka samu aka mayar da ita gefe yayin da motoci suka shiga wucewa hanyar su .
Zayn yaja dogon tsaki yana waiwayar motar. Banda rashin bin kaidar tuki na garin kano. Taya babbar gingimari zata biyo hanyar kananun motoci?
Da takaicin hakan ya karasa gidah. Tun daga nesa masu gadi suka wangale masa gate ya shige,
Kai tsaye ya wuce sashen da su Ummimi ke zama idan sun zo. Hannun sa dauke da notepad da pen.
Ya shiga zagaye parlukan sashen da dakunan ciki. Harta bandakuna da duk wasu sockets na gidan sai daya dudduba komai. Ya rubuta abubuwan da suke bukatar a canza da wadanda babu a kawo.
Yana gama rubutawa ya shiga mota ya koma office. Kai tsaye ya wuce babban ofishin mahaifin su dake cikin kamfanin. Dankareren ofishin mai dauke da manyan rubutun: Professor Adams Nasser.
Sai daya fara knocking kafin ya bude kofar ya shiga bakinsa dauke da sallama.
Mahaifin nasa na zaune akan wata kujera mai cin mutane uku. Center table na gabansa yana cike wasu takardu.
Tsugunna wa yayi har kasa ya gayshe da mahaifin na su. Kafin ya miqa masa takardar da yayi rubuce rubuce ajiki.
Mahaifin nasa ya karba yana dubawa. Hade da gyara zaman gilashin da ke jikin fuskar sa.
Take Waheedah ta sake fado masa a zuciar sa. Ya runtse idanun sa da sauri. Kamshin turaren ta na dawainiya a kofofin hancin sa.
Mahaifin nasa ya daga kai ya dube shi.
“Ya akai Zayn?”
Ya bude idanu da saurin sa yana girgiza kai hade da soso kasan keyar sa.
“Bakomai Abiey….”
“To masha Allahu. Kana ji ko?”
“Eh Abiey.”
“Zan turawa su Simon list dinnan. Sai su kai komai gidan. Yanzu ka biya wajen Lajawa kace gobe idan Allah ya kai mu yazo gida “
“Tohm Abiey. Insha Allahu “
“Yauwa Allahumma bareek.”
“Aamin…”
“Zaka iya tafiya.”
“Tou Abiey . A huta lapia “
Ya bude kofa ya fice zuwa inda suke buga snooker shi da abokan sa, A bakin wani pool site
Ko da yaje ma kasa tabuka komai yayi. Ya koma kan kujera ya zauna kawai .
Useey abokin sa dake gefen sa da wayar sa a hannu yace dashi,
“Maza ya ne?”
“Steady oga.”
“Nagan ka yau pale. Akwai damuwa ne?”
“Bakomai fa. Kawai nagaji ne.”
“Toh Allah yabamu saa. “
“Aamin.”
Cikin haka sai ga wasu yan mata su biyu sunje wucewa, sunci ado cikin dogayen riguna fitted. Mayafan su shara shara kamar na tatar koko.
Lameen dake buga snooker da Awais ya riqe bakin sa. Karasawa wajen su Useey dake zaune shi da Zayn
“Wow woah, wawwww”
“Meye hakan sekace ambulance. Haba kaman wasu yan kwana kwana.”
“Wasu masu zafi na hango mana. .”
“Suna Ina?”
“Gasu can zasu tsarar da me napep.”
Useey ya miqe yana hango su. Tsayawa sukayi su na kallon su banda Awais da Zayn.
“Kallo daya bisa ka’ida dai akace.” Cewar Zayn da ke zaune yana duba wayar sa. Don shi ko tashi bai yi ba.
Ussey da Lameen suka tsallaka har inda suke a tsaye sunata tsara su. Kowanen su ya karbo number wadda tayi masa. Useey ya zaro sabuwar dari biyar ya mikawa mai napep din. Yaja suna masu daga musu hannu
Suka tsallaka sunata dariya. Awais yace dasu,
“Ba dai kyau wallahi. Zaku batawa yaran mutane lokaci. Soo not fair. “
“Sai mu zauna mata su bace mana? Ga dama agaban mu?” Lameen ya amsa shi yana daria.
“Rabu dashi. Kasan meyasa yace haka lameen?”
“A’ah.”
“Saboda already an hadashi da matar aure.”
“Dan an hadani da wadda zan aura sai akace bani da damar kara wasu ukun? “
“Eh dukda hakan kasan dai baka isa ka auro wata nan kusa ba. Sai ka fara aurar sury..”
“Kyale su aboki na. Tunda sunada hankali sukayi fatali da sanin hakan.” Cewar Zayn . Fuskar sa a hade.
Ussey ya tuntsire da dariya har yana riqe ciki,
“Banda kai da abun ka abokina. Kai da shi ai du kanwar ja ce. Kai har gwara gwara shi ma, A iya cewa yana da damar karo uku. Kai fa you can’t marry any other girl da bata cikin naku family . Dole sai yarinya yar cikin dangin ku. Jinin ku, Kuma tsatson ku daya . Na yan uwan ku The Adams family..”
“Ku inda ake nuna muku a har kullum ba shi kuke hanga ba. “
“Rabu dasu maza, Su je suci gaba da yaudarar yaran mutane. At the very end su zo su auri wadanda basu taba tsammani ba.”
“Kai de banza ne Awais. Ji wani mugun fata.”
Dariya suka kyalkyale baki daya. Kafin su cigaba da yin snooker din su.
“Ni yunwa ma nake ji.”
“To ina zamu je.?”
“Okay I’m out. Later.” Zayn yace dasu. Domin shi gaba daya baya cin abokcin eateries ko roadside ko na ordering. Harta na masu aiki bayaci sai wanda Maa ta dafa masa da hannun ta …
❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????