BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 60

60

…….Cikin nasa idanun suka shiga, sakamakon kallonta yake shima. A karan farko taji hakan babban abune a gareta kallon tsakkiyar idonsa tai masa koda harara ne. Janyewa tai a kasalance ta maida ga Aysha dake kallonta fuska da damuwa duk da bata san mike damu ƴar uwar tata ba. Dan ita dai tana gida ya kirata a waya wai ta ɗakko kaya kala ɗata ta fito ta samesa an kwantar da Anaam asibiti. Ya kuma mata gargaɗin karta sanarma kowa, Mommy ma tace mata zataje waje Fadwa ne. Hakaɗin tayi shine ta sami damar fitowa dan itama Mommyn na buƙatar aje mata gidan Shareff ɗin duk da tasan ba lallai ta sami abinda take so ga Ayshan ba. Amma tasan ta inda zata dinga binta tana jin koma ai. Amma sai ta kasa kallon aunty Mimi da itama kallonta take duk da bata san mike damunta ba, ya sanar mata dai kawai Anaam babu lafiya, sai dai bai son su Mamie su sani.

    Matsowa Aysha tai suka rungume juna, idon Anaam cike da ƙwalla. 

 “Blood mike damunki?”.

Ɗan satar kallonsa tai shi da aunty mimi, idanunsa ƙyam a kansu, Hawayenta ta share da girgiza mata kai kawai alamar babu komai. 

    “Blood ba’a zuwa asibiti ai babu komai, dan ALLAH ki faɗamin”.

   Katse Ayshan yay da faɗin, “Idan kinji maganin mi haka zai miki?, malama tashi ki bata abinci ban son surutu mara amfani”.

   Badan Aysha taso ba dole tai shiru. Aunty Mimi ta ƙaraso ta zauna saman kujera, gaba ɗaya Anaam ta kasa kallonta, idanunta a rissine tace “Ummi good afternoon”.

   “How are you feeling?”.

  Kasa amsawa tai sai hawaye data matso. Aunty mimi tai murmushi, “Mamana har yanzu baki san kin girma ba, shagwaɓa dai shagwaɓa dai why?” nanma batace komai ba, aunty mimi da zuciyarta ke ɗan hasko mata wani abu ta kalla Shareff, shima kansa yay saurin kaudawa gefe yana shafo bayan ƙeyarsa da hannu. “Humm” tace kawai. Itace ta taimaka mata ta koma saman gadon. Aysha kuma ta fara zuba mata abinci. Takowa yay daga inda yake tsaye ya zauna kusa da ita a gefen gadon. Jitai kamar ta makesa sai dai babu dama. Koda Aysha ta gama zuba abincin shine ya amsa, sake gyara zamansa yay yana fuskantarta da ƙyau, sai dai taƙi yarda koda wasa su haɗa ido. 

  “Ko zaki sha tea ne kafin kici abincin?”. Ya faɗa idonsa a kanta. Girgiza masa nata kan tayi, murya a shaƙe tace, “Bazanci komai ba na ƙoshi”. 

     Komai baice mata ba, ya ɗibo abincin zuwa bakinta yana faɗin, “Hahh!”. 

Sosai ta ƙwaɓe fuska, ta ɗan ɗago cikin marairaicewa tana kallonsa, sai kuma ta saci kallon gefen aunty mimi. Ganin basu take kallo ba ta ɗanji sassauci kaɗan. Kanta ta girgiza masa “Banajin cin komai ALLAH”.

   Ƙasa-ƙasa yace, “Gashi kuma dole sai kin ci! In ba haka ba kuma…..” ya ɗage mata gira ɗaya batare daya ƙarasa faɗaba. Dole badan taso ba ta buɗe bakin ya fara bata abincin da tun a ɗanɗanon farko ta gane girkin Mamienta ne. Kasa ɓoyewa tai. 

   “Yaya wajen Mamie ka amso min abinci?”.

  Kansa ya jinjina mata da kai babban yatsansa ya goge mata mai daya taɓa gefen bakinta. Sai taji kunya ta kamata kasancewar Aunty mimi da Aysha a ɗakin. Shiko babu alamar hakan ya damesa ma ya sake miƙa mata wani daya ɗibo a spoon. A haka Dr Bilkisu ta shigo ta samesu yana bata abincin, a ranta ta ayyana (Maza ga zaƙi ga harbi kenan). A zahiri kam idonta akan Anaam tana murmushi. “Masha ALLAH my patient jiki yayi daɗi”.

   Cikowa idanun Anaam sukai da hawaye, ta girguzama Doctor kanta. “Har yanzu inajin ciwo a wajen”.

  Idanu ya waro da sauri jin zatai masa fallasa, ya daura yatsansa akan lips ɗinsa alamar tai shiru, ta gefe kuma yana nuna mata aunty Mimi da ido. Sai dai kuma bai san sarai aunty mimin na kallonsu ba ita da doctor. Ta ƙunshe dariya da kyar, Dr Bilkisu dai kasa dannewa tai sai da tayi tata.

“Ayya karki damu insha ALLAHU zai daina, idan na sallameku zan baki dukkan dabarun da zasu taimaka miki har ki dawo normal a cigaba da amarci ko”.

   God forbid”.

Ta faɗa a hankali samman lips ɗinta. Da ɗan ɗagowa zata hararesa suka kuwa haɗa ido. Babu shiri ta mayar ta risinar. Har doctor ta gama ƙara duddubata bata sake yarda ta kalla sashen da yake ba dan tuni tace masa ta ƙoshi da abincin. Shima dai kunya ta hanashi sake wani motsi, dan ya san dai aunty mimi ta gama fahimtar komai kuma. Magungunnanta ya bata ta sha kamar yanda Doctor tace. Sai da ya tabbatar komai yayi normal sannan ya mike yana kallon agogon hanunsa. 

    “Small Mom ni zanje gida nai wanka bara na maidaki, inaga sai zuwa anjima zan dawo. Aysha ki kula da ita idan da buƙatar wani abu sai ki kirani a waya. Bana buƙatar wani yasan da zamanku anan, idan hakan ta faru ranki sai yafi nawa ɓaci”.

   Aysha ta amsa masa da to.

“Karka damu Babana jeka kawai harka dawo, bara naga likitar nan. Aunty Mimi ta faɗa kai tsaye tana miƙewa ta fita. (Shike nan na mutu) ya ayyana a ransa da bin aunty Mimin da kallo. Itako Anaam tuni tai kwanciyartama ta juya musu baya. Har tayi zaton ya fice sai ga saukar numfashinsa a cikin kunnenta, da sauri ta juyo dan ta tsorata, hakan ya bawa fuskarsu damar haɗuwa, ƙoƙarin jan tata tai baya ya hana hakan ta hanyar riƙota.

    “Ina alfahari da ke a wannan rana, alfahari irin wanda zuciya bazata iya ƙayyadewa ba, hannu bazai iya zanawa ba, ke ɗin zinariya ce, idan nace zinariya ina tabbatarwa duniya zinariya a tsakkiyar duhuwar jeji, amsar itace, Haskenki kaɗai za’a iya gani”. 

    Daburcewa tai, sakamakon saukar lips ɗinsa akan nata, ta shiga son ture masa fuska, amma yaƙi yarda da hakan har sai da yay yanda yake so da ita. Yana sakinta sashen da Aysha da aunty mimi suke ta fara kalla, sai dai wayam da alama ma duka basa a ɗakin. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke da saurin kauda kanta saboda ido da suka haɗa da shi. Murmushi ya saki mai faɗi da yalwa dan ya fahimci catake su Aysha na a ɗakin.

   Sake ranƙwafowa yay kanta har lokacin murmushi shimfiɗe a fuskar tasa. “A ƙara ko? Nima ban ƙoshiba”.

  Ture fuskarsa tai da sauri tana jan bedsheet ɗin dake a matsayin bargo ta ƙudundune kanta. Murmushinsa ne ya ƙara faɗaɗa, ya girgiza kansa kawai da juyawa ya fice a ɗakin.

   Sallamar Aysha ta sakata sakin ajiyar zuciya, sai da taji ta zauna a kusa da ita sannan ta buɗe kanta. “Da alama dai kin samu sauƙi tunda naga Yaya ya fita yana faman murmushi”.

  (Ba dole ya fita yana murmushi ba tunda ya gama yayyagani) a fili kam sai ta taɓe baki da yunƙurawa zata tashi zaune. Taimaka mata Ayshan tayi ta zauna cikin dauriya dan ƙasanta sosai yake mata zafi zamanma dai tayisane irin na kishingiɗa ɗin nan..

  Aysha ta sauke ajiyar zuya tana kallonta, “Dan ALLAH ki kwantar da hakainki na tabbatar zaki ji daɗin zama da Yaya Shareff insha ALLAHU Blood. Yanada ƙyawawan halaye da lokaci ne zai tabbatar miki da hakan kamar yanda nasan kema kina da su. Hatta Fadwa bana son ki biye mata dan ita kanta komai na ƙiyayyarki tanayine ba’a kan tunaninta ba, tunanin su Mommy shike sarrafata tun farko, amma wlhy inhar kika jajirce sai kin ƙwace komai kuma a hankali Mommy zata fahimceki halayen banzar da Gwaggo ta ɗorata a kai duk zata ajiyesu kodan son da takema Yaya”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button