Bakar InuwaBAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELSUncategorized

BAKAR WASIKA 4

Page -4️⃣

“So yanzu ka yarda zaka bata hakuri kenan”

Talba ta girgiza kai.

“Kai no never ni fa ba zan taba ba wanda yake kasa da ni hakuri ba”

Ali ya kalleshi.

“Amman ka ce Daddy yace laifinka ne, kuma kaje ka bata hakuri”

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa ya sauke numfashi a hankali.

“Yeah ba wai yana nufin na ce tai hakuri ba, ni yanzu so nake ka kirata ka bata hakuri kuma ka dauke ta ku je yawo ta wayance Shikenan komai ya wuce, amman karka ce ni na ce ka bata hakuri fa”

Ali ya rausayar da kai yana kallon abokin nasa cike da mamaki.

“Miye a ciki dan kace tai hakuri? Ko kuma ka dauke ta kuje yawo, faduwa kai?”

Sai Talba ya amsa masa kai tsaye.

“Yes, taya zaka bawa mace hakuri macen ma wanda take kasa da kai, ni me fa Ali”

“To wai idan kuka yi aure kuka samu matsala, kuma kai kake da laifi…”

Kamin Ali ya karasa Talba ya tari numfashinsa.

“Sai ta ba ni hakuri”

Ta fada da iyakancin gaskiyarta, domin har ga Allah be ga dalilin da zai saka shi bawa wanda ke kasa da shi hakuri ba, kuma mace sai dai shi a ba shi. Ali yayi murmushi.

“Yanzu dai for the sake of Daddy zaka yi”

“For the sake of him na zo har ina rokonka da kai, idan ba haka ba babu abun da zai saka na roke ka ma”

“Look Talba I’m not her boyfriend, ban san kalaman da zan mata ba, kuma ba ni nai mata laifin nan ba”

Talba ya mike, ganin hakan yasa Ali ma ya mike tsaye.

“Fine, amman tare za mu je, kana driving ina baya”

Talba be ce masa uffan ba ya nufi kofar fita, wanda hakan ya tabbatarwa Ali cewar ya yarda kenan. Sai da Ali ya shiga yai sallama da Samira sannan ya fito ya samu Talba a cikin motarsa. A hankali Talba yake tukin har suka fita daga cikin gidan suka hau titi.

“Kirata ka tambaye ta tana ina”

Ali ya masa wani kallo.

“Kiran ma? Talba wai kai zaka bata hakuri ko ni? Just ka kirata ka tambayi tana ina ma you can’t?”

Ko kallon gefen Ali Talba be yi ba balle ya tanka masa.

“Fine”

Ali ya fada sannan ya zaro wayarsa ya shiga contact dinsa ya nemo number Amal, domin baya son batawa kansa lokaci tambayar Talba number ta zai iya ce masa baya da ita ma. Ringing biyu ta dauka.

“Hello”

“Hello Lil Sis ya kike?”

Ta yi murmushi jin ya kiranta da sunan da Talba yake kiranta.

“Na’am Ya Ali ina lafiya”

“Good number Leila nake so”

“Okay zan turo maka yanzu”

“Thank You”

Ya aje wayar yana kallon abokinsa tare da mamakin halinsa. In few minutes Amal ta turo masa number, a take ya kira Leila, abun ka da mai jin kai sai da wayar ta yi ringing ta katse bata daga ba, har sai da ya sake kira, wannan karon ma sai da ta kusan yankewa sannan ta daga kuma tai shiru tana sauraren mai kiran, daman can haka take babu yadda za’ayi ka kirata kuma ka yi expecting ita zata fara maka magana, sai da Ali ya saka wayar a speaker sannan ya fara magana.

“Kanwata Leila kina lafiya?”

Jin muryar Ali yasa ta dan sake domin ta san waye shi.

“Ali ya weekend?”

“Alhamdulillah kina ina?”

“Ina gida dari gidansu Madina”

“Okay gani nan zuwa”

Be jira abun da zata ce ba, ya aje wayar ya kalli Talba.

“Idan munje ta fito kai zan bata hakuri sannan na baku guri ku yi magana”

Talba ya masa wani kallo irin really!

*** *** ***

Leila ta aje wayar tana tabe baki.

“Waye?”

Madina ta tambaya tana gyara kwanciyarta.

“Ali wai gashi nan zuwa?”

“To ko ya san abun da ya faru tsakaninku ne?”

“Maybe ai Talba baya boye masa komai”

“Kin gani na fada ya damu fa”

“Ya damu amman be kira ni ya bani hakuri ko ya aiko min da sako ba? Ni I don’t think Talba yana so Madina”

“Yana son ki mana Leila”

Madina ta fada sannan ta sauka saman gadon ta kama hannun Leila.

“Zo nan let me show you something”

Gaban madaubin dakin ta nufa da ita ta tsayar da ita gaban madubin.

“Kalli kanki da kyau Leila ki fada min abun da kika rasa”

Leila ta kurawa kanta ido a madabin tana kallon irin baiwar da Allah yai mata ta kyau daidai gwargwadon.

“Kyau?”

Madina ta tambaya sai Leila ta girgiza kai.

“Kudi? Lafiya? Kima, gata ko kuma me?”

“Ba ko daya”

Leila ta amsa.

“Kina da kyau da babu namijin da zaki yi tayin kanki ya ce miki aa ko waye shi kuwa, mahaifinki na da arziki da zai iya siya miki rai idan ana saidawa Leila, kina da kima, ga gata ta ko’ina, kuma duk wannan tarin baiwar da take tare da ke sai zuciyarki ta raya miki Talba baya son ki?”

Leila ta juyo tana kallon Madina

“Za ki iya fada min dalilin da ya saka yake min haka?”

Madina ta yi murmushi ta koma saman gadon ta zauna.

“Saboda Talba, na daya daga cikin irin mazajen nan masu matukar tsada da wahalar samu, kin ga duk wannan abubuwan da kike da su, Talba na da damar da zai iya cewa ba ya son ki idan har baya son ki, kuma ta zauna, domin kin san mutun ne da baya boye abu a ransa idan be masa ba, kuma babu wanda ya isa ya cilastashi, idan har baya son ki kai tsaye zai fada, amman be amsa cewar baya son ki ba ya amince”

Leila ta dan yi sama da ido.

“Haka ne but…”

Madina ta tari numfashinta.

“But Talba yana da matukar tsada Leila, Talba wani irin murdadden mutum ne mai wahala sha’ani, yadda kike takama da kyau yana da kyau, yana da dukiya, yana da duk wani abu da ake so a jikin namiji, yana da arzikin da yake jin zai iya tankwara komai yadda yake so, yana ganin tun da yana da komai dole a bi shi”

“Shi ne matsalarsa ai”

Leila ta fada tana zaunawa kusa da kawarta.

“Yeah ya kasa yarda cewar akwai abun da kudi basa siye, a nan ne kawai yai kuskure”

Leila ta yi murmushi.

“Ni kuma zan gyara masa wannan kuskuren, sai na nuna masa banbanci da sauran mata, dole ne ya san cewar ina da kima da daraja, kuma dole ya koyi yadda zai yi rayuwa da ni, all those four years of dating, ni nake bashi hakuri ko da ni ce da gaskiya, ina binsa kamar wani sarki da baiwa, all those years ni nake masa text how are you, so so so this, idan ya bar kasar nan ni zan kira shi na tambayi lafiyarsa, ko na masa sako, amman ko da rana daya Talba be taba daga waya ya tambayi ya nake ba! Idan na yi kwaliya be taba ce min kyau ba, be taba replied sakona ba, be san yai min kyauta irin ta masoya ba, balle har ya dauke ni muje yawo, ba zan taba yarda na aure shi a haka ba, now it’s my turn, dole ne ya canja”

Ta karasa yana yawo da idonta a dakin. Madina ta kama hannunta.

“No Leila mutane irin Talba suna da wahalar sha’ani, kuma suna da shaukin kai ga wanda ya iya zama da su, kar garin gyara ki ballo wata barnar, idan kin bashi hakuri a inda kike da gaskiya ai ba laifi ba ne”

“No dole ne ya gyara, yana son soyayya amman be san yadda zai nuna ta ba? Be san yadda zai biya ta ba? Ban taba kiran sunansa a gaban idonsa ba sai na sakaya, amman shi be taba gwada kirana da suna mai dadi ba”

Ta karasa tana murmushi.

“I’m such a fool”

Ta kai dubanta gurin wayarta da ta soma ringing. Hannu ta kai ta dauki wayar sannan tai picking.

“Hello?”

“Kanwata ga mu harabar gidan”

“Okay”

Ya mike tsaye ba tare da tunanin komai ba ta nufi kofar fita.

“Talba ne?”

“Ali dai Uhm Talba zai zo nan?”

Ta fada tana mere baki sannan ta fice, hango Motar Talba harabar gidan ba karamin mamaki ya bata ba, domin ko a mafarki bata taba saka ran zai zo ba, kuma bata zaton Ali ya aro motarsa ne. Tun kamin ta sauko entrance din ta canja tafiya, kamar wata hawainiya haka ta rika takawa kamar bata son karasawa kusa da motar.
Da gangan tai haka domin ta san a cikin abubuwan da Talba ya tsaya akwai jira, ko bata masa lokaci for nothing, mutum ne da yake daukar lokacinsa da muhimmanci sosai, dakika daya ko biyu idan ka kara, zai iya rushe ko miye a tsakaninku, hakan yasa yana girmama lokacin wani da ra’ayinsa.
Kamin ta iso Talba ya cika har ya kusan fashewa, ba karamin jihadi yai ba na bawa zuciyarsa hakuri har ta iso. Ali dake front seat ne ya sauke gilashin motar yana murmushi, Talba kam ko inda take be kallo ba sai taba wayarsa yake kamar his life depends on it. Kallo daya Leila tai masa ta dauke kai tana amsa gaisuwar da Ali yake mika mata.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button