FARHATAL-QALB 9
PG:9
××××××.
Da sallama Umma Hadiza ta shigaa cikin gidan . Bakinta na furta adduar shigaa gidah a hankali. Da Sa’adatu ta fara cin karo a zaure. Tabi ledar hannunta da kallo har tana lankwasar da kanta .
“Unguwa zaki? A dawo lapia.”
“Kiji ki da wata tambayar banza. Dama idan zan fita ina sanar miki ne? Sabon salon kinibibi. To aniyar ki ta bi ki idan ma da wata kullalliyar kika dawo.”
“Ya SubhanAllah! Haba Sa’adatu “
“Atoh ai gaskia ne. “
“To Allah ya baki hakuri.”
“Matsalar ki ce.”
Umma hadiza bata sake cewa komai ba. Tayi hanyar dakin Marka kai tsaye tana sallama a hankali. Shiru ba amsawa . Ta dan zura kanta kofar dakin Markan. Bata nan sai yar rediyon ta da keyi ita kadai. Nan da nan kuwa Umma Hadiza ta saka hannu ta kashe gudun kar battery din yayi sanyi.
Sannan ta fito daga ciki tayi dakin su Kamal. Sai Najib shi kadai yana fiffita da mahuci. Tayi sallama ya amsa yana dan gyara kwanciyar sa.
“Sannu da zuwa Umma…”
“Kai zan wa sannu Najib. Ina yayan na ku?”
“Bai jima da yin wanka ba ya fita. Yace na ce miki ya dan ji dadi jikin sa ya tafi kasuwa “
“Masha Allahu! Allah ya kara muku lapia . Amin”
“Amin Ummah. Nima daman jiran dawowar ku nake . Ko ke ko Waheedah “
“Ai ga ni na dawo. Wani abun ne Najib?”
“Ah babu komai wallahi. Nima so nake na fita na dan zauna ko a bakin titi ne.”
“Alhamdulillah! Jiki ya yi sauki. Allah ubangiji ya kara muku lapia mai dorewa. Allah ya takaita wahala, Aamin Yaa rabbi.”
“Aamin Aamin Umma. Bari na dan watsa ruwan ni ma.”
“Toh Najibu. Akwai ruwa ai. Na kwallan yafi dumi.”
“Tohm Umma.”
Fuskarta cike da farin cikin jin dadin ganin ciwon nasu ya dan lapa. Gashi har daya ya futa ma daya kuma zai fita yanzu. Bayan dogon zangon da suka dauka suna fama da jinya. Dama haka cutar sickler/ amosanin jini yake. Ya lapa ya tashi. Sai fatan samun lapia ga dukkanin masu fama da ciwon. Allah kuma yasa hakan ya zamto musu samun rahamar Allah , Aamin. (Our warriors !! Allah ya baku lapia mai dorewa. Da dukkanin marasa lapia na gidah dana asibiti.) Aamin.
“Ummah ya naga kinata murmushi ne? Allah yasa murmushin alkhairi ne.” Cewar Najib daya gama wanka ya zura kayan sa.
Umma hadiza ta sake murmusawa kafin tace,
“Murmushin farin ciki ne Najib. Babban murmushin da nake yanzu bai wuce na ganin warwarewar jikin ku yayi ba wallahi. Har a raina baka ji dadin da nake ji yana ratsa ni ba.”
“Allah sarki Ummah.. Allah ya kara mana lapia ya yaye mana dukkanin matsalolin mu. Ya azurta mu muma muyi miki iyakar kokarin mu. Dan har mu koma ga Allah ba zamu iya biyan ki abunda kike mana ba Ummah. Allah ya kara miki lapia da nisan kwana…”
“Da imanin Allah.”
“Ai kuwa dai da imanin Allah. Allahumma Aamin Umma.”
“Sai abu na biyu. Idan kun dawo baki daya an jima na gaya muku. Amma kafin sannan dubi abun arzikin da ke gabana. Gidan da Najaatu ta sama mun aiki ne suka babba mu. “
“Masha Allah. Allah ya saka musu da mafificin alkhairin sa . Gaskia mutanen arziki ne. Yanzu du wannan abubuwan haka ? Masha Allah .”
“Wallahi kuwa Najib. Amin Aamin. Sun san abun arziki. Mutanen kirki ne.”
“Toh umma me zan tayaki da shi kafin na fita?”
“Ba abunda zaka tayani dashi Najib. Kayi ficewar ka. Yanzun nan zan hada komai “
“Toh shikenan Umma. Sai mun dawo.”
“Sai kun dawo Najib. Allah yayi albarka .”
Nan da nan Umma Hadiza ta shigaa harhada kayan girkin da zatayi. Ta dake kayan kamshinta waje daya saboda qarnin kajin. Ta wanke su tas bayan ta yayyanka su tsoka da yawa.
Ta hada wuta ta fara tafashen kazar da kayan kamshi. Dayan murhun kuma ta dora ruwan taliya. Tanata aikinta ita daya agidan du ba kowa. Har Allah yasa ta kammala komai ta soye naman ta zuba komai a muhallin sa tukun sannan ta kai cikin daki bayan ta kakkasafce na kowa a faranti. Taliyar da miyaar ma nanma ta zuzzuba ta ajiye.
An kira sallah kenan. Bayan tayo alwala ta tada sallar ta idar. Tana zaune tana addu’oi. Waheedah ta dawo daga makaranta ita da Zainab . Can sai ga shigowar Marka. Ba jimawa tamkar hadin baki sai ga Sa’adatu itama ta dawo. Sai malam NaLado daya dawo a karshe.
“Kamshin meye wannan haka?” Cewar malam NaLado hadi da fara dauke murafan kwanuka. Yana sake bude kofofin hancin sa.
“Marka kamshin me nake ji haka.?”
“Kai wanene ya kashe mun yar radio di ta iyye?” Cewar Marka. Ta fito daga cikin dakinta tana huci tamkar zakanya.
Sai da Umma hadiza ta shafa adduar da ta daga hannuwa sama tukun sannan ta mike ta nannade sallayar ta ajiye ta a bakin gefen katifa.
“Ni ce marka. Naga tana tayi ita kadai kada batirin yayi sanyi.”
“Mts! Dama na san sai ke wallahi. Tsugudidi kashin o’o. Yanzu banda nemawa kai magana. Akan wani dalilin zaki kashemun radio bayan sarai kinsan ba kida hurumin kashewar? Tukun nama akan wane dalilin zaki ketare ki shigaa cikin daki na iyye? Nace akan wane dalili. Kuma na rantse da rantsuwar ba fashi sai kin gyaro mun radio ta. Yanzu gashi nan kinsa ta denayi baki daya. Dama joganeta nake ahankali na kunna amma saboda tsabar mugunta shine zaki lalata mun. To wallahi sai kin gyaro mun kinji Allah kuwa.” Marka ta karasa fada , Hadi da ajiye rediyo din agaban Umma Hadiza dake tsaye tana sauraron Marka ta karasa abunda zata fada.
Doguwar ajiyar zuciyar ta sauke .kafin cikin muryar lallashi da ban girma tace,
“Kiyi hakuri Marka. . Wallahi ba da sani nayi miki haka ba. Wai dan kada batirin suyi sanyi tanata yi ita kadai shi yasa na kashe. Abunda yasa na shigaa tsakar dakin ki kuma dana dawo ne zan gayda ke ba kowa agidan sai Sa’adatu da na hadu da ita a zaure zata fita. Abunda ya saka na kashe kenan wallahi. . kiyi hakuri dan Allah, ki gafarce ni.”
“Kinibibin banza dana wofi.” Marka ta shigaa mita a kasan makoshi.
“Nace marka kamshin ..”
“Dan Allah mai sunan Malam ka kyale ni. Kamshi da kakeji haka nima nake jinsa. Haba.”
“Kiyi hakuri Marka. Kamshi kuma gidan dana samu aikatau ne matar gidan zatayi tafiya shine ta bamu kayan miya da taliya da kaji guda biyu. Shine ina dawowa na fara aikin su ban jima da karasawa ba. Ga sunan na zubawa kowa a mazubi.”
“Wanne ne nawa?” Cewar Malam NaLado sai wulkita idanu yake yana hangen inda zai gano nasa.
“Gashi Malam naka. Marka ga naki kema. Sa’adatu ga naki ke da yaran. Ke ma Waheedah ga na ku nan.”
Malam NaLado ya karba da sauri ya koma kan turmi ya zauna yana ci. Sai gyada kai yake yana lumshe idanu
Hakama marka data karbu nata sai baza hanci take tana shakar kamshin miyar dataji komai ta hadu da dadi. Dama umma hadiza akwai iya girki idan ta samu kayan abinci
Inna Sa’adatu ma data karaci hura hancin ta. Daga karshe bajewa tayi tana ci. Sai taunar kashi kake ji. Kunnuwa na motsawa.
Kamal ne ya fara dawowa. Sai Najibu daga karshe. Umma hadiza ta basu nasu abincin. Tukun sannan itama ta zuba nata tanaci.
Daga ita sai su waheedah dake gefe tana taune kashin cinyar kaza. Alokacin umma Hadiza ke sanar dasu yadda sukayi da Hajia Hameedah. Bata boye musu komai ba. Kwarai matuka sun taya Umman ta su murna. Sai farin ciki ya kara ninkuwa da annushuwa a fuskokin su da zukatan su.
Bayan sun gama cin abincin. Umma hadiza ta dakko dubu daya ta bawa Najibu kan ya siyo sabuwar rediyo ya kaiwa marka. Hakan kuwa akayi ya sayo ya kai mata. Mai makon tayi murna sai ta zo tayi wa Umma Hadizan tatas akan saboda taga ta samu aiki ne zata fara daga kai da nuna isa da izza. Dakyar ta karbi rediyon dan sai da aminiyar ta lawuri ta tausashe ta. Dakyar ta karba