Labaran Kannywood

Tirkashi Rigima tayi Zafi, Bazai Yiwu ba Kana Matsayin dan Fim Kuma a Kiraka da Mumini Sheikh Idris Abdulazeez Yasa Yan Fim a gaba.

Tirkashi Rigima tayi Zafi, Bazai Yiwu ba Kana Matsayin dan Fim Kuma a Kiraka da Mumini Sheikh Idris Abdulazeez Yasa Yan Fim a gaba.

Fitaccen malamin Addinin Musulunci nan Watau Sheikh Idris Abdulazeez bauchi yaci gaba da sukar yan fim akan maganarsa da yayi na cewa kaf yan fim babu me Ilimin Addini Acikinsu duk jahilaine.

Wannan magana da malam yayi tayi matukar jawo cece kuce a shafukan sada Zumunta inda Da yawa daga cikin masoyan jaruman sukaita maida martani ga malamin a karshe kuma maganar ta Matukar batawa jaruman Kannywood rai.

Duk da cewa dama dai Jaruman na Kannywood sun saba jin irin wadannan maganganun da suka daga wajen Malamai da sauran Alumma. domin yawancin Malamai suna Kallon Jaruman Kannywood a matsayin masu bata Tarbiyyar al’umma.

Sai dai har yau jaruman Kannywood Sunki yarda da irin maganganun da malamai keyi akansu inda yawancinsu suke bayyana cewa Masana’antar su da Finafinan su suna fadakar da al’umma ba gurbata Tarbiyyar ba.

Wasu Tsofaffin jaruman Kannywood irinsu musbahu m ahmad da kuma al’amin chiroma sun fito sun maidawa malamin da martani Mai matuka zafi.

inda shi Musbahu yake cewa aiba kai ka hallicemu ba kuma ba zamanka mukeyi a duniya ba, Ko kuma dai jadadda mana kalamar shahada zakayi harma ya kira malamin da mahassadi maici da Addini.

Harwa yaude shehin malamin yana nan akan bakansa inda ya fada kuma ya jadadda cewa babu wani dan fim me addini idan kuma akwaishi to ya fito ya bayyana kansa, sannan ya kara da cewa Ba zai yiwu ba ace mutum yana matsayin dan Fim Kuma a Kiraka da Mumini.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button