FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 1-20

Zani ta dora akan towel din ta dauko hijab ta saka sann ta yaye towel din ta ciki ta ajeshi akan gado,kafin nan harya shimfida mata sallaya
Yana tsaye harta kammala sallan ta raka’a biyu,sallan safiya,.
tanayin sallama suka hade ido yace na baki minti biyu kisaka kaya kizo yanzun nan ki same abakin tanki.

Yana juya baya ta mike tsaye cikin gaggawa wani irin rawa jikinta yakeyi tsabar axaban tsoron sa datakeji acikin zcyarta ,agaggauce ta shafa mai ta saka wankakken pants dinta tabita zura doguwar rigan atamfa A shape,snn ta kwaso kayan fitsarinta da zanin gadon a gurguje taje wajen ta same shi.

Samu tayi harya karkada omo acikin ruwa yana zaune yana jiranta,koda ta iso wajen ko kallanta baiyi ba ,jikinta a mugun sanyaye ta karaso gaban sa ta ajiye mishi kayan fitsarin ahankli ..”

“Jeki can ki tsaya, ya
Mata nuni da can gefe inda rana yasoma haskawa da kadan kadan

Tsaye ya mike yana kallon ta harta isa wajen snn yace
“Ki saka yatsarki daya a kasa sann ki daga kafarki daya sama inkika yadda kika fadi kasa saina zaneki.

Babu musu wasime ta aikata hakan jikinta sai rawa rawa yakeyi tanajin kamar zata fado kasa, ga tsamin da kafarta yake mata na jiya bai gama warwarewa ba..Ko kallanta baiyayi bare halinda take ciki ya damesa,earpice ya jona da kunnenshi yahau wanke kayan fitsarinta ya wanke su tasss..kafin nan wasime taci kuka tayi kuka kamar zata cire ranta amma tsoro bai iya barinta ta saɓa dokansa ba..saida ya kammala wankinsa tass ya shanya sannan yay releasing dinta ta wuce cikin gida tana matse ido cikin kuka tana tafiyarta a hankli.

A fannin bilti kuwa shararta kawai takeyi bata ko lura da yadda malam musa yafito ya rakube a bayan windown sa ya zuba ma bayan ta idanunsa ba.

Gabaki daya ya shagalta zuciyarsa tayi nisa da abunda shedan din jikinshi yake tunzirasa akan dayayi..

Yasan labarin bilti kuma yasan bazaurace wanda mijinta ya rasu aka laka mata sharrin wai ita mayyace ita ta cinye shi danta mallake arzikin shi shiyasa ma taki haihuwa dashi,haka aka taru aka mata taron dangi aka kulla mata sharri kala kala,she went tru hectic emotional trauma, dan hatta uwar rikonta data aurar da ita bayan iyayenta sun mutu juya mata baya tayi a wancan lokacin..

Adan dole bilti ta gudu ta shiga uwa duniya da goyon bayan wani dan uwan mahaifyarta wanda shine ma yay sanadiyar sama mata aiki agidan su taheer lokacin mahaifiyar taheer tana shan wahala da laulayin cikinshi bata da wani lpya sosai sai aka kawo bilti ta zauna da ita tana kulawa da ita sosai

Kamar yar uwanta na jini haka ta zage ta kula da maman taher har cikin ta ya girma suka saba da juna sosai,kowa yay trusting din bilti dake tunda suke bata taba cin amanansu ko ta nuna musu wani mummunan halinta ba.

Ita tay renon taher tun yana jaririn sa harya girma,iyayen are alwys on the run yau suna nan gobe suna can dukansu babu mai takammmen lokacin kansa acikinsu bare na dansu.

Da zuciya daya bilti take zamanta agidan kuma sosai suke kyautata mata suna kkri wajen girmama ta..tana da ilimin ta daidai gwargwado dan tayi karatun NCE a garinsu kafin tay aure.

Tun zuwan malam musa gidan ya kyallara ido ya saka ranshi akanta, gani yake kamar mace bazata taɓa iya zama hakanan cikin kwanciyar hankli babu wani namiji a kunkutirinta ba.

Amma saiya sha mamakin ganin bilti da yadda take rayuwarta gaba daya,namiji ko shaawar yin aure baya gabanta.. aikin da takeyi na kulawa da taheer sune abunda sukafi saka ta farinciki da kwanciyar hankli.

Sann kuma taki sam ta sake musu fuska musamman ma tolu
Shiyasa Yana fara mata wargi sai tace zata hadashi da taheer.

Harta kammala sharanta ta kwashe ta shiga cikin gida bata lura da shi ba..shedan sai ingiza zcyrsa yakeyi akan kawai ya denajin tsoro ya tunkareta hala itama a matse take zata iya biye mishi harma ya aureta

Wucewa yay dakin tolu waidan ya bashi shawara ya same tolu yana waya da wata budurwa, waje ya nema ya zauna yana jiranshi ya kammala ya saurare shi.,tolu yana karkare wayar suka haura ma juna gaugau

Malam musa cikin mamaki yana cewa Kai
Tolu baka gajiya ne?toh wallh yaukam bazan bude ma wata shegiya gate ba,tolu ya dinga lallabrsa ahaka har shima ya shigo masa da zancen bilti dake tolun ma wawa ne zigashi kawai ya dadayi yana ingiza shi akan daya fara nuna ma bilti alamar cewa yana sonta.

Bilti tana kitchen tana kkrin hada breakfast taheer ya sace jikinshi yabar musu gidan ya wuce wajen karatunsa daganan kuma wajen training zaije.

Dukansu basu san baya gidan ba harsanda bti ta kammala girkin ta je ta daki dubo wasime dataga yau bata sauko ba a tunaninta tsorone ya hanata saukowa,ashe tunda ta shiga dakin kuka kawai takeyi da tunanin saheeb cike acikin zuciyarta

She missed him alots,ji take kamar an sakata a prison kwana biyu musamman ma da taheer ya soma shiga cikin rayuwarta yana tsorata ta.

Rarrashin duniyan nan bilti tayi mata kafin nan tayi shiru ta dena kuka, duk tabi ta damu ta cusa tunani kala kala aranta sai tambayar bilti takeyi ko yaushe ne saheeb zaizo,bilti har tagaji da boye mata ta fito mata karara ta nuna mata cewa ta dena tunanin zata kara ganinsa saboda taher ya hana afkuwar hakan…

Tagumi tayi da bakin cikin taher aranta,yau abinci ma kadan ta taba ta tashi tahaura sama ta dinga kuka,sai da tay me isarta snn ta debo kayan wasanta tazo tanayi harta dan somajin dama dama acikin ranta.

A fannin saheeb kuwa zuciyansa ta kasa iya daurewa,sam baya zanne baya tsaye akan tunanin wasime,zuciya yasa har yagama shirin tattaro thugs din baban sa don suyi mobbing taher su masa mummunan dukan daga baya kuma sai yaji yafasa yin hakan kawai

In bakin ciki ya damesa sai dai ya sha giya ya kira zeee yay mata cin hauka,Ita kuwa duk ta dauka so ne yake kawo haka bata fahimci cewa amfani da ita yakeyi kawai danya saukaka ma zuyarsa bakincikin rashin ganin wasime ba.

Abu kamar wasa sai gashi saheeb ya cusa wani mummunan qudiri akan taheer…

Ji yake ya tsane sa,baya son ganinsa badon komi ba sabida wasime…

Haka rayuwarsu ta kasance,karfin addu’a da ikon Allah yasaka duk wani mummunan sharri da saheeb yake kullawa akan taheer domin daukar fansa bata yuwa ko yay ma haka kawai saiyaji ya fasa ku kuma abunyazo baiyu ba

Rayuwar wasime ya kasance a mugun takure
Saboda yadda taheer ya mugun saka ido akanta yanamai saka mata daci akan ibada,girmama na gaba, da kuma fitsarin kwance datakeyi.

Purnishment kala kala bawanda batasha shi ba,tayi pimping tayi frog jump tayi jumping tayi smell ur nyash babu azaban da bai bata ba.
Duk da sanyin A.C tsoro saida yasaka wasime ta dena fitsarin kwance.

Ranar da tayi by mistake zokaga tashin hankli,gashi bata isa ta je ta wanke kafin ya sani ba da asubahin fari yake ‘lekowa ya tasheta tayi sallah…hartazo ta dena kwanciya da kaya ajikinta,sabida kotay fitsarin karyajika kayan ta amma duk da haka asirinta baya rufuwa daga zarar anyi ruwan sama bata iya controling kanta dole ne saita tsula.

Da kyar yazo ya fahimci cewa Sanyin A.c na daya daga cikin abunda yake assasa mata jin fitsari,..

saboda hakan ya daure ya sauko da fushin dayakeyi ya soma yin magana da bilti,zama yay sukayi magana cikin son ya fahimtar da ita cewa yana so adena kunna ma wasime A c musamman acikin dare in zatay bacci.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button