Labaran Kannywood

Gaskiyar Magana Akan Mutuwar Dan Azumi Baba Kamaye na Dadin Kowa…

A safiyar yau dinnan ne wani labari ya karade shafukan sada zumunta ana fadin cewa Allah yayiwa fitaccen Marubucin nan kuma darakta haka kuma a lokaci daya jarumi a masana’antar kannywood Dan Azumi Baba wanda akafi sani da Kamaye rasuwa.

Jaruman Kannywood da dama sun wallafa hakan,wasun su sun karyata kansu daga baya,yayin da wasu kuma suka cire wallafar ba tare da dadin wani ba’asi ba.

Bayan mun gudanar da bincike ne muka tabbatar muku da cewa yana nan a raye cikin koshin Lafiya.

Haka kuma shima jarumin da kansa ya fito ya karyata hakan a shafinsa na Instagram,ga bidiyon nan.

Haka kuma shafin nan na Kannywood Celebrities ya fito ya karyata Jaruman da suka fara wallafa sanarwar mutuwar ba tare da bincikawa ba.

 

Muna rokon Allah yajikansa idan lokaci yayi har damu baki daya.

 

Kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button