TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAKA 18

 

*_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_MACE SAI DA GYARA_*????????????????

_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_

    *YERWA INCENSE AND MORE*

 *Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*

_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_

*_Muna da haɗin_*

_Turaren wuta kala kala na gidah_

_khumrahs_

_Kullaccham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_

_Turaren wanki_

_turaren mopping_

_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_

_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_

_Muna Gyaran jiki_ 

_Na amare_ 

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_

_Turaren tsugunno_

_zumar goran tula_

_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_

_Akwaisu kujeran tsugunno

_Dilke and halwa set_

_Burners da igniters da tong_

_turaren fesawa dana ruwa._

_wardrobe balls_

_scented pebbles_

_cotton wooly oudi incense_

_kabbasas_

_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_

_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_

_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan ????????_*

 _EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_

_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.

100% TESTED AND TRUSTED_

••••••••••••••••••••••••••••••••

*_Chapter Eighteen_*

…………..Tashin hankalin wannan magana yasa na yanke jiki na faɗi, dan ko sanda akai na Muhammad da sauƙi inada garkuwata Aliyu. Amma wannan ni kaɗai ce naketa ƙoƙarin kare kaina sai malam da Halilu da bansan miye manufarsa na bani kariyar ba. Kamar na Muhammad wannan ma malam yace sai a jira na haihu. Haka kuwa akai, na cigaba da rainon ciki Halilu nata hidima dani da ƴaƴa na. Abin na bani mamaki yana sakani a ruɗani., ya kuma bani tsoro Dan sam na kasa hango manufarsa a kan hakan har takai ALLAH ya saukeni lafiya na haifo ɗiyata mace a karon farko. Itama dai tunda ta diro duniya kowa ya shaida jinin Aliyu ce. Dan kamanni sak ta ɗebo nasa dana ƴan uwanta harma taso ta fisu ɗebo komai nashi, sai dai kawai dan ita mace ce. Bakin kowa ya mutu kam, dan ko tari ba’a sakeba akan batun na cigaba da shayar da ɗiyata da taci sunan mahaifiya Muhibbat. Bakowa bane da wannan aikin sai malam. Ya tabbatarmin da wasiyya ya cika shima. Mahaifina ne ya roƙesa dan ALLAH inhar ALLAH yasa na sami miji nai aure na haifi ɗiya mace duk rintsi yana son a saka mata suna Muhibbat sunan mahaifiyata. Sai ko gashi ALLAH yaja da ran malam ya cika wannan wasiya. Sakama Tanee sunan mahaifiyata shine abu na farko daya jawo mata baƙin jini itama a wajensu. Dan anata ƙananun magana Halilu ne kawai ke karewa. Haka dai sukayi suka gama har ƙura ta lafa. Bayan na yaye Tanee aka raba gadon ku, sai dai malam ya kirani gefe mukai maganar da kunyarsa bazata barni na bijire masa ba. Dan yamin hallaci irin wanda bai kamata ni na saka mishi da butulci ba.”

       “A wancan lokacin bayan na samesa ya fara da faɗin, (Asiya ke ɗin ɗiyace ɗaya tamkar da dubu. Kuma ɗiya kamar sauran ƴaƴa. Dan baki da banbanci da su kamar yanda wasu suke gani. Baki da laifin komai dan bakece kika aikata laifinba. Ita kanta mahaifiyarki ƙaddara ce ta afka mata har aka sameki. Kiyi haƙuri na ɗakko miki wannan zancen ne saboda abinda nake hangowa da zaije ya dawo game da zuri’arki da wannan dukiyar tasu. Nasan baki wuce aure ba. Dan haka manema yanzu zasu fito gareki tako ina. Sai dai bai zama lallai su kasance dan ALLAH zasuzo ba ko dansu riƙe waɗan nan marayun. Banason bayan babu raina ki shiga gararin rayuwa. Dan mahaifinki kafin yabar duniya yayi matuƙar nadama ya duƙufa neman gafarar ALLAH, ya duƙufa neman ilimin addini a wajena batare da kowa ya sani ba. Shiyyasa ya danƙa amanarki a gareni. Kuma insha ALLAHU zan yi iya bakin ƙoƙarina naga na tsare wannan amanar har zuwa sanda nima ta ALLAH zata kasance. Asiya babu wanda yafi cancanta ya adana dukiyar ƴaƴanki sai ke da kanki, amma dole sai da taimakon namiji. Ni kuma gashi ƙarfina ya ƙare, dan bani da isashshiyar lafiyar nima tun bayan rasuwar Zaki (da yake haka yake kiransa). Amma inata nazari har zuciyata ta yanke min wata shawara da nake fatan zata zama mafita agaremu baki ɗaya. Halilu ɗan uwane ga zaki, duk da halayyarsu ta banbanta. Amma shima idan kin lura ya jima da dawowa hankalinsa. Rasuwar ɗan uwansa kuma ta sake lausasar dashi ko mahaifiyarsu baya son yaji ta aibantaki. Shiyyasa nake ganin mizai haka ki amince ki auresa ku haɗu ku riƙe wannan amanar da ALLAH ya bar mana ta yaran nan da dukiyarsu har sanda zasu kai girma. Na tabbatar hakan zai sakaki nutsuwa da kwanciyar hankali Asiya. duk runtsi babu mai rabaki da ƴaƴanki kema kina gidan mijinki tare da su. Ko sake haihuwa kikai dai duk zasu zama da ga tsatson jini ɗaya ba zaki rarraba kan zuri’arki ba. Amma bawai dole bane fa. Na baki dama kije kiyi nazari daga nan har wata guda. Hukuncin da kikaji ya kwanta miki a rai sai kizo min da shi. ALLAH yayi miki albarka, yayama yaranki albarka. ya baku kariya a dukkan motsinku da numfashinku). Cikin kuka na amsa masa da amin”.

         “Tunda malam ya tafi ya barni ban huta ba dare da rana akan tunani da nazarin wannan tayi nasa nake. Na hanga na hango naga zancensa shine kawai mafita a gareni da ku kanku. Sai dai har cikin raina ina matuƙar tsoron abinda zaije ya dawo akan Halilu. Dan gaba ɗaya yanzu ba iya gane inda ya dosa nake ba kai tsaye. Ya riga yayma kansa lulluɓin biri da fatar kura. Ta wani gefe kuma ina kallon kima da darajar malam. ALLAH ne ya zaɓa min Aliyu matsayin miji shine ya zama sila kuma. Bai duba ni ɗin wacece ba, bai ƙyamaceni kamar yanda kowa ke ƙyamata ta ba. Ɗansa ya karɓeni da hannu biyu babu musu, ya nunamin dukkan soyayya da ƙauna. Ya bani farin ciki a ƙarƙashin igiyar aurensa. Koda suɓutar baki bai taɓa gorantamin akan asalina ba. Idan ma na faɗa ƙwaɓata yake ya nunamin ɓacin ransa. To nikan inba butulci ba mizai sa na bijirema zaɓinsa a karo na biyu. Ina ganin koda Halilu mutumin banza ne zanyi fatan dawo da shi hanya. Yanda mahaifinsa da ɗan uwansa basu ƙyamaceni ba shima bazan ƙyamacesa ba. Da waɗan nan kalolin tunanin na gama yankema kaina shawara, a ƙarshen watan da malam yazo ziyararmu tamkar yanda ya saba a kowane wata sai na nuna masa kawai na amince. Ya matuƙar nunamin farin cikinsa da jin daɗi. Yayta sakamin albarka da sakama ƴaƴana. Indai ta ƙaice muku zance da ga ƙarshe an ɗaura aurena da Halilu, auren da ya bama kowa mamaki, musamman da akaga Hajiya mama ko tari batai akansa ba balle asan bata so ko tana so. A farkon auren nan a kunyace nake da lamarin Halilu kota wane fanni, amma ina iya bakin ƙoƙarina na sauke haƙƙokinsa a kaina. Shima kuma yana bani kulawa da respecting ɗina. Hakama ƴaƴana ƙauna yake nuna muku tamkar mahaifinku. Hankalina ya sake kwanciya da shi, na saki jikina sosai tare da ɗaukar duka dukiyarmu na danƙa a hannunsa akan cewar sai kun girma za’a bama kowa nashi. Da farko ya nunamin bazai amsaba. Sai da naita roƙonsa da nuna masa muhimmancin zaman komai a hannunsa saɓanin ni mace. Da ga ƙarshe dai ya amsa da ƙyar. Sati biyu kacal da yin haka ALLAH yayma malam rasuwa. Ƙwarai da gaske na shiga ruɗani fiye da rasuwar mahaifina. Dan malam ya taka matukar rawar gani a rayuwata wadda baki bazai musalta ba. A wannan lokacin naje ƙauye rasuwar malam, duk da a ɗarare nake da kowa ban samu matsi kamar sanda ina rayuwa a ciki ba. Sai ma abin kallo da na zama ni da ƴaƴana saboda da kaina naja mota ta har can. Kwanan malam huɗu da rasuwa kakana ma ya rasu, mahaifin babana kenan. Ban wani ji tasa rasuwar ba. Dan da shi da babu a gareni duk ɗaya dai. Satina guda a kauye muka dawo tare da Halilu, inda tun shigowarmu na fara ganin sabbin al’amura da ga garesa da suka nema rikita mani tunani. Cikin ƙanƙanin lokaci komai ya canja. Hajiya mama ta dawo nan da zama, hakama matar Halilu da ƴaƴansa. Ya cireku da ga makarantar da kukeyi ya maidaku ta gwamnati, nima ya haramtamin tuƙa mota. Al’amarin ya matuƙar gigitani da sani a tashin hankali, amma saina daurema zuciyata saboda halaccin mutane biyu da nake tunawa a koda yaushe. Kawu na da mijina. Komai ya sauya da ga salonsa. duk wata cusgunawa ita Halilu da Hajiya mama kemin harma da matarsa da yaransa. Ku kanku baku da sukuni a gidan koda nayin wasa ne. Abubuwa da yawa kullum cikin gorantamin su yake, tare da neman komai gareni ta ƙarfi (uwa ta gari kenan, maimakon tace yana mata fyaɗe saita sirranta domin mutunta kanta????). Ɗawainiyarku duk ta dawo hannuna. Komai baya mana ya bari. sai ma filin garden ɗinmu da Aliyu ya kashe kuɗi sosai yayisa saboda mutumne mai tsananin son furanni da ƴayan itatuwa Halilu ya bajesa ya kafa wancan ginin, part ɗinsa da matarsa, sai part ɗin hajiya mama. Bayan an kammala suka koma can da zamam babu ruwansu damu balle yaya mukaci, sai tarin masifa da hantara a garemu. Gidan da Aliyu ya sai min da kuɗin hayarsa na cigaba da ɗaukar nauyin karatunku, sai taimakon Sheikh Aliyu Maina abokinsa. Dan ya matuƙar taka rawar gani akan rayuwarmu shima. kullum nunamin yake nayi haƙuri na cigaba da rayuwa da Halilu har kukai girma dukiyarku ta dawo hannunku sannan na rabu da shi. Wannan yana cikin dalili na na karshe bayan tuna halacci da ƙauna da mahaifinku da Malam suka nunamin a rayuwa, yayinda kowa ya gujeni har ƙannen mahaifiyata. Shiyyasa kukaga ina cigaba da jure komai har kawo iyanzu da insha ALLAHU komai yazo ƙarshe, zamu bar musu gidan duk da kuwa haƙƙinmu ne. Dukiyarku kuma idan ma bai baku ba ku barsa da ALLAH kawai tunda ya rufa mana asiri bamu rasa ci ba balle sha da suturar sakawa. Fatana kar wannan labarin ya sakaku tunanin ɗaukar wani mataki akan hajiya mama da Halilu. Ku barsu ALLAH zai muku maganinsu ta hanyar da bakuyi zato ko tsammani ba. Dan banason ya cutarmin daku. Dan ALLAH na roƙeku ku barsu mu rabu lafiya salin alin”.

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button