KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 11 to 20

Ad

_____

Hajiya zaliha tace tashi muje d’aki mana muyi maganan a ciki, hajiya binta bata musa ba, ta tashi sukai d’aki, fauziya kuma ta shige ciki wai ita a dole kunya, hajiya binta tace su fauziya manya yanzu an fara yar buya kenan, suka saki dariya ita da hjy zaliha, nan hjy binta tace toh yanzu nidai nazo inji ne kun shirya dai koh dan nan da sati daya nake so ayi a wuce wajan, nan hjy zaliha ta dafe kirji tace sati daya, ni yanzu ina naga kudi, da zanyi siyayya, hjy binta tace haba zaliha siyayyan mai zaki yi, bana bukatan kisai koda tsintsiya ne, komai zansa mahmud yayi, tace anya ayi haka kuwa, hjy binta tace to miye a ciki aiko bashi Zai aureta ya kamata yayi mata kayan d’aki nan hjy zaliha ta hau godiya Amma na ciki na ciki, hjy binta ta zaro yan dubu daya2 bandir daya dubu dari kenan tace ga wannan ki fara hidima dashi kafin a kawo abunda za’a dafa ma yan biki, ta amsa tana washe baki cikin jin dadi tace Allah ya saka da alkairi, inba naka ba waye xaima haka, ta fada tare da kallon hjy binta wanda taji dadin godiyar data mata,. 

Hajiya binta tana ta shirye shiryen biki ba tare da mahmud yasan tana yiba, ta hada akwati cikin kwana biyu ansa kaya masu tsadan gaske, an kuma kai gidan su hjy zaliha, murna wajan fauziya ba’a magana zata zama matar mahmud zata kece sa’a wajan kawayenta, har tana ganin irin takun da zata dinga yi a gidan, sai dai ko da yaushe ta tuna da salma sai taji gabanta ya fadi dan tasan irin son da mahmud yake mata, sai dai itama ta dau alwashi indai akwai bokaye a gari da malaman tsubbu to tabbas sai tasa mahmud ya sota fiye da irin sonda yake ma salma wannan kenan. 

Salma tana kitchen tana hadama mahmud dinner kafin ya dawo daka office, taji kaman muryan hajiya binta nan ta fito da sauri tana fadin sannu da zuwa mama, ko kallo bata isheta ba balle tama san tana magana ta nemi waje ta zauna, tana sakar mata harara cikin tsana, ganin tayi banza da ita ta tashi tayi kitchen ta hado mata kayan motsa baki, bayan ta ajiye tace keee zo nan ki dauke wannan abun daka nan, wa kika kawo ma wa an gaya miki shiya kawo ni, wato nima inci ki mallake ni koh, toh wlh ni nafi karfin bokan ki wlh kije ki sake shiri, salma ta dauka tare da cewa kiyi hakuri mama, tace kaya ne ta bita da harara, yarinya kin shanye min yaro baya ganin kowa sai ke, wlh dubun ki ya kusa cika, a dai2 nan mahmud yayi sallama ya shigo yace a’ah mama yau kece a gidan, tace eh nice mana tunda kai an hanaka zuwa bah, yace haba mama waye zai hanani zuwa wajanki, tace matarka mana wacce ta shanye ka baka ganin kowa sai ita, yace mama kiyi hakuri wlh ba haka salma take ba yarinya ce mai biyayya sai……. Dakata malam bashi ya kawo niba, banzo kuma dan inji hakan ba, abun daya kawo ni shine in fada maka ran Friday daurin aurenka da fauziya nan salma take kitchen wani xazzafan hawaye na xuba mata a ido, koya zata zauna da fauziya a gidan nan a matsayin kishiya tirkashi ada ma ya aka kaya balle itama yanzu ta zama matar mahmud, mahmud din shima cikin rawan murya yace mama Friday kuma ai ya kamata a fadamin da wuri inyi shiri, tace karka damu na gama komai gobe za’a kawo kaya asa a kusa da d’akin matarka dan kar a riga cutanta, yace mama d’aki nane nan sai dai asa ana kasa tace wlh baka isa ba sai dai ita waccan mayyar ta dawo kasa amma ba yata ba, wato tun yanzu ka fara nunamin za kayi rashin adalci ko wlh ka shiga hankalinka, tun wuri yace to mama kiyi hakuri yanda kikace hakan za’ayi tace shine zaman lafiya, tace ni Zan wuce saika fara shiri kuma anjima ka shirya kaje gidan su fauziya din dan kaji mai take bukata, yace toh, ta tashi tare da fadin saura kuma kaki zuwa, yace zanje insha Allah, ta fita yabi bayanta dan ya rakata, 

Bayan ya dawo yaga salma a falo wanda ya tabbata taji abun daya faru, duk sai yaji babu dadi, ta sakar mishi murmushi tare da fadin sannu da zuwa bbyna, tace lafiya kuwa yau naga jarumin nawa kaman yana fushi, ta matsa kusa dashi tare da hugging dinshi tace plz kayi mun murmushi ko zanji dadi, ban san ganinka cikin wannan halin, my one, yayi dan murmushi tare da kara matseta a jikinshi tace naji duk abunda mama tace karka damu matar mutum kabarinshi kuma ina murna zan sami yar uwa, yace salma ke yar aljanna ce, tayi dariya nan ta shiga gaya mishi kalamai masu dadi taja hannunshi sukai toilet nan ta taya shi yayi wanka, sannan ya shirya cikin manyan kaya wanda ta xaba mai, ta kalleshi tace kayi kyau my, muje kaci abinci, bai musa ba suka nufi dinning, tuwan shinkafa ne miyan agusi yaji dry fish da ganda ga kuma nama, yaci ya koshi, har aka kira Isha’i Bayan ya dawo tace toh my sai ka nufi wajan kanwata dan ka ganta sannan in kaje ka gaida min da ita, wani irin kallo yake ma salma wanda itama da kanta sai da tayi mamaki…… 

Maryam obam😘

💭💭💭KISSA KO MAKIRCI👹👹👹

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  20to25

Ad

Yace kina tunanin zani wajan tane? Tace ban fahimta ba my, yace salma bazan iya zuwa wajan fauziya ba, tayi rau2 da ido tace haba babyna Mai kake fada haka, kar ka manta dazu kama hajiya alkawari kuma ni ban sanka da karya alkawari ba, kuma in baka jeba nima bazan ji dadi ba, sannan ita fauziya din zata ji wani iri, plz my muje in raka ka mota ka tafi, yayi hugging dinta tare da gadin “I love you salma u r my happiness, tayi dan murmushi tare da fadin I love you too my, ta danja baya daka rikon daya mata tace saika dawo, ya fita tare da fadin OK, tabi hanyar da yabi ya fita da kallo idonta ya ciko da kwalla mai zafi yanzu mahmud tad’i xaije wajan wata macen wanda zata shigo a matsayin kishiya ta, lokaci daya ta cire abun a ranta tare da fadin Allah kaban juriya da hakuri. 

Ad

_____

1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button