KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 21 to 30

Ad

_____

Tun farkon aurensu salma take fuskantan matsala wajan dangin mahmud, gashi baban abun tashin hankali shine yau shekaran salma uku da aure amma shuru babu haiyuwa, nan hjy binta tace Sam bazai yiwu ba, mahmud ya zama dole ya kara aure domin tana son ganin jikoki, bazai yiwu kaita zama da juya ba, badan ranshi yaso ba ya amince dan yabi umarnin mahaifiyarshi dan baya so ya saba mata, Amma shi a nashi ra’ayin baya sha’awan tara mata shi salman shi ta isheshi kawai,amma babu yanda ya iya matsalanshi kawai yanda zai gayama salma zai kara aure yake damunshi dan baya San bacin ranta, kaman yanda bata san nashi, duk wani abu da zaisa shi farin ciki shi take so, bata san bacin ranshi sai yasa shima yake gujema abun da zaisa ta bacin rai ko zargi duk da yasan ba halinta bane tana da hakuri,amma babu yanda zaiyi dole ya fad’a mata dan yafi so taji abakinshi akan taji a wajan wasu, ya yanke yau Zai fada mata. 

A lokacin da mahmud yaje gida, salma ta tarbeshi kaman yanda ta saba,yaci abinci suna fira amma gaba daya yana tunanin yanda za’ayi ya fada mata, haka dai ya daure yayi na maza ya sanar da ita, amma abun da yayi zata sai bai gani bah, tace alhamdulillah Allah ya sanya alkairi yasa abokiyar zama ce ya baka ikon yi mana adalci, ya amsa da ameen tare da kara son salma, haka aka shirya biki hjy binta ta nemo mai wata yarinyar mai suna bilkisu yar masu kudin gaske anyi biki an kashe naira, amarya ta tare cikin gidanta, suna zaman lafiya ita da salma abun su, tun lokacin da hjy zaliha tazo gidan taga irin yanda suke zama ta kitsa ma bilkisu abubuwa iri2 aiko Tun daka ranan ta canza ta fara yima salma bakaken magana da zagi salma bata taba kulata ba, sai dai ma tace bilkisu mai na miki naga kin canza dan Allah in laifi nayi ya kamata ki fadamin ta daga hannu ta mari salma dallah yimin shuru munafuka, jin muryan mahmud sukai yana fadin bilkisu kije na sakeki saki uku, da sauri salma ta juya tana fadin innalillahi wa inna’ilahira jiun, mahmud wannan wani irin abune haka mai tama zaka mata wannan hukuncin, yace salma bazan zauna da macen da zata ci mutuncin kiba, domin ke nake so bazan bari a wulakanta min ke ba, harga Allah salma bata ji dadin sakin da mahmud yama bilkisu ba, a lokacin da hjy binta ta samu labari tazo tama salma ta tas tace kuma wlh aure nan da sati biyu zai kara, aiko hakan akayi aka aura mishi wata shima dai akan salma din suka kara rabuwa tun daka lokacin suke fadin salma ta mallake shi, tana koran duk wanda ya aura, wannan kenan 

MUN DAWO KAN LABARIN

yau aka daura aure, Mutane sun taru domin hjy binta tayi gayya sosai, ango dai kwata2 baya cikin nishad’i, zai iya cewa yau itace ranan bakin cika a rayuwanshi domin an daura mishi mara tarbiya shi yama rasa mai yasa mama ta yarda ta bashi fauziya ba,

Ita kuma gefen amarya tana cikin farin ciki, yau itace matar mahmud abun da take ta burin samu shekara da shekaru yau ya zama nata, ta lumshe ido tare da fadin yau zan nuna maka nawa fagen soyayyar, yau zaka sha zumata, ji take kaman azo a tafi da ita yanzu, ta tashi ta dauko maganin da boka ya bata tayi matsi dashi, tayi murmushi tare da tuna abun da bokan ya fada mata indai ki kai amfani da wannan maganin ya sadu dake toh daka ranan sai yanda kikayi da mahmud, domin duk macen daya sadu da ita zai jita kaman dusa, tace salma saina rabaki da mahmud har abada domin nawa neshi. 

Salma anci kwalliya sosai tayi kyau, tasa wani tsadaddan material wanda mahmud ya kuma siyo mata tasa da bikin, gefen ta kuma kanwarta ce hauwa, wanda tazo taya ta zama har a kawo amarya ta wuce, suna dan fira jefi2 hauwa tace niko salma mai yasa kika bar mahmud ya kara aure bayan nasan ba zaki barta ta zauna ba, salma tace hauwa mai kike nufi? Tace naga duk wanda mahmud ya aura kin koresu itama nasan wannan ba barinta za kiyi ba, salma tayi murmushin takaici tace hauwa kenan, kina bani mamaki wlh, tace name ai gaskiya ne abun da yake a zahiri mahmud fah akan ki zai iya komai inba wani abu kika mai ba toh mai yasa zai dinga miki haka, salma tace bana tsafi bana shirka, bana makirci, hauwa tayi dariya tare da fadin toh sai me? Tace KISSA hauwa ta kafeta da ido tare da kuma nanata kalman da salma ta fada kissa, tace ya ake ita kissan hala naki na daban ne, tace a’a kaman na kowa ne, hauwa tace toh koya min mana nima inji ko zan gamsu ita kikeyi, salma tace zan fada miki nan gaba hauwa tace dan Allah ki fadamin yanzu dan na matsu inji, tace na miki alkawari dakai na zanzo gidan ki in fada miki, hauwa tace toh shi kenan, nasan bakya karya alkawari ai, sukayi dariya a dai2 nan mahmud ya shigo salma ta tashi da sauri tare da fadin wlcm my dear dana iya guda da nama, yayi dan murmushi yace toh Ina binki bashi tayi dariya dan ta fahimci abun da yake nufi yayi gefenshi itama ta bishi anan suka bar hauwa tana shs’awar irin rayuwar su, sai dai salma taki fada mata sirrin yayin da ita nata mijin suke yawan samun matsala wannan kenan 

Anzo daukan amarya an jera motoci masu tsadan gaske, nan fauziya ta tashi cikin murna da zumudi, aka fita, kai tsaye aka wuce da ita gidan ta, suna shiga suka fara guda da habaice2 suna fadin an kawo wacce zata haifa mana y’ay’a Allah ya rabamu da juya sai ci ana zubarwa, salma dai tana d’aki bata fito ba,. 

Ad

_____

1 2 3 4 5Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button