KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 31 to 40

Driver gudu yake amma mahmud gani yake kaman baya tafiya, gaba daya ya tsorata da yana yin salma, suna isa asibitin aka kuma yin emergency da ita, nan Dr ya shiga ya fara dubata mahmud sai kaiwa da komowa yake, Dr ya dauki wajan 30mnt kafin ya fito, ya kalli mahmud yace saika godema Allah yanzu ta dawo haiyacinta, yace Dr cikin fah?? Hope babu abunda ya sameshi?? Dr yace eh babu abunda ya sami cikin sai dai tana bukatar bed rest, inba haka ba cikin zai iya fita, nan yayi ma Dr godiya sannan ya nufi d’akin da aka canza mata, ya sameta a kwance ga wata nurse tana gefenta, bayan ya shiga nurse din ta fita, ta sakar mishi murmushi, ya kamo hannunta tare da fadin ya jikin naki? Tace da sauki, yace kiyi hakuri babyna yana baki wahala koh? Yanda yayi maganan abun ya bata dariya, nan ya zauna tare da ita har wajan 10 tace yaje gida, ya mata wani irin kallo yace in tafi in barki dawa? Tace nurse zata dinga kula dani, yace a’a babu inda zani ina tare dake, tayi murmushi tace plz dear ka tafi kaga babu wani abu dake damuna, na warke kawai hutu nake bukata, yace shikenan amma sai dai in kira hauwa taxo ta kwana dake ban yarda ki kwana da nurse kawai ba, tayi dariya tace toh shikenan,

Kai tsaye gidan hauwa din suka nufa, dama ya kirata ya fada mata zasu zo su dauketa tace babu komai mijinta yana lagos ta fada mishi, bayan sun dauketa yace bari suje gida ta dauko ma salma kaya sai driver ya dawo da ita, hakan koh akayi sunje gidan babu kowa a falo hauwa taje d’akin salma ta kwaso mata kayan sawa da sauran abunda take bukata ciki harda wayarta, sannan suka koma asibiti ita da driver, driver ya taya ta diban kayan sukai ciki dashi sannan ya wuce, hauwa ta kalli salma tace wannan abun kaman wani almara kin tafi lafiya kuma kin dawo jiki babu dadi, salma tayi dariya tace ikon Allah kenan babu yanda bazai iya ba, jarabawa ne, hauwa tace hakane Allah dai ya sauke ki lafiya ta amsa da amin, da hauwa da nurse suka kwana da salma komai take so sai dai a mata basa bari tana wani motsi mai karfi domin har yanzu ruwan nan yana fita. 

Mahmud kwanciya yayi a falo, can ya tuna da wayoyinshi a dakin fauziya yayi tsaki sannan ya tashi ya nufi d’akin, tana nan daka ita sai wata riga na bacci iya cinyanta, suka hada ido ta sakar mishi murmushi, lokaci daya yaji komai nashi ya tsaya, shima ya mayar mata da martani, ganin haka yasa taji dadi domin abunda take so ta samu magani yayi aiki, matsawa yayi kusa da ita yayi hugging dinta, gaba daya ya gigice, ji yayi kaman ana tsungulinshi nan suka shiga soyayya, tun daka lokacin gaba daya yaji fauziya ta shiga ranshi har yake ganin ta fiye mishi salma, amma wani gefen na zuciyanshi na karyata hakan, washe gari har wajan 12 suna ta bacci abunsu gaba daya fauziya ta kashe wayanshi,. 

Salma ta tambayi hauwa mahmud yazo kuwa dan itama tasha bacci, tace a’a bai zo ba, abun ya bata mamaki tace anya lafiya kuwa? Har karfe daya tayi bai shigo ba, tace bani wayana in kirashi ta kira a kashe, tace anya lafiya, wayanshi a kashe mahmud kuma baya kashe waya, duk ta rude, tace hauwa dan Allah ko zaki gida kiji koh lafiya, tace salma ki kwantar da hankalinki dan Allah, ki kira driver dinshi kiji, nan ta doka ma driver kira, ya dauka tare da gaidata ta amsa tare da fadin oga fa Kuna tare ne? Yace yana cikin gida dazu na shiga naji shuru bai fito ba dan ko sallan asuba yau banga ya fito ba, sai madam tace min yana bacci yace wai ya gaji yana son ya huta, nan salma taji gabanta ya fadi ta kashe wayan, ta kalli hauwa tace hauwa ki kira min Dr ya sallameni, hauwa tace akan wani dalili salma? Tace hauwa barin fauziya da mahmud hatsari ne ki duba fah har yanzu bai zo ba kuma ko waya baiyi ba yaji ya jikina, na kira ance yana bacci wai ya gaji, hauwa tayi shuru tare da tausaya ma yar uwarta tace toh ko Kin je gidan mai zaki yi, ba gwara ki zauna a nan ba ki sami lafiya, tace hauwa baki San wacece fauziya ba, fauziya makira ce wlh ina tsoran makircinta, hauwa tayi dan murmushi tace salma kenan, har akwai macen da zata baki tsoro keda ake jin tsoranki kin mallake miji, ganin hauwa ba zata fahimce taba yasa tayi shuru, gaba daya ranan mahmud bai zo asibitin ba, hankalin salma yayi mugun tashi, ta tashi daka kan gadon nurse tace madam lafiya ina zaki ko toilet zaki shiga, tace mata eh, nan ta taya ta sauka a hankula sannan ta shiga toilet din, tayi alwala, taxo ta zauna tana sallah tana kuka tana rokan Allah ya kare mata mijinta tun wajan biyu ta fara sai da takai wajan uku tana yi, data sallame, nurse din tace madam sannu gaskiya kina burgeni yanda bakya wasa da sallah salma tayi dan murmushi, ta tashi ta koma gado ta taimakon nurse din ta kwanta tana ta Istigfari, bacci barawo yayi gaba da ita. 

Mahmud harga Allah ya manta da salma, gaba daya baya ganin kowa sai fauziya ta hanashi fita ko nan da can, salma ta kira ta kira amma sai dai fauziya taita danna mata busy, harta hjy binta itama ta kirashi amma fauziya taki bari ya gani balle ya dauka, ta zauna dashi daka tace kaza yace mata toh an gama,

Yau satin salma daya a asibiti, babu mahmud babu dalilinshi, koda yaushe salma na gayama Allah kukanta, cikin ikon Allah wannan ruwan ya daina zuba, duk ta rame, hjy binta tazo asibiti da kanta ta sami salma a zaune ita da hauwa, ta mata tatas tace kin shanye min d’a inna kirashi baya dauka baya zuwa waje na, to wlh baki isa ba, babu abunda salma take sai kuka, nan hauwa tace hjy kiyi hakuri wlh itama rabonta da mahmud yau wajan kwana bakwai kenan, nan hjy binta tayi shuru, can tace karyan banza muna fukai wlh zanyi maganinki, ta fita fuuuu, tana mota tana tunani ko dai gaskiya aka fada mata domin inta kira fauziya itama bata dauka, sai rannan data dauka tace tana gidansu ta tambaye ta mahmud fa tace yana gida, da haka har driver ya karasa da ita gida, mahmud ko ya koma saniyar tatsa dan fauziya ansan kudi take a hannunshi kaman hauka, har gida ta gani tace tana so ya bata kudin ta siya, 

Yau salma ta cika kwana goma sha daya a asibiti, Dr ya bata sallama, yace ta dinga kiyaye wa, tace toh, ta kira wayan mahmud a kashe nan tace suje su hau taxi, hauwa ta fita ta samo mai taxi suka kwashe kayansu suka sa a ciki, kai tsaye gidan suka nufa, babu kowa a falo, har yanzu tana jin kalan abun da taji ranan data shigo falon, tana ta furta innalillahi wa inna’ilahira jiun…… 

Maryam obam????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  60to65

Har suka haura sama sai data shiga dakinta taji dai2, nan hauwa tace bari inje in hada miki wani abu kici, tace toh, nan ta sauka tayi kitchen, bayan hauwa ta fita salma ta zauna tana kuka tare da tambayan kanta mai tama mahmud, wata zuciyar tace baki masa komai ba, aikin fauziya ne, nan tayi sauri ta kawar da tunanin dan bata son ta gasganta abunda zuciyarta take fada mata,lokaci daya ta share hawayenta tare da fadin koma mai nene addu’a shine magani, 

Mahmud ya shigo gida dan yau ya fita suna da meeting, yaji motsi a kitchen ga kamshi dake tashi, nan yayi kitchen din amma sai yaga ba fauziya bace, yace hauwa, yaushe kika zo? Ranta a bace tace dazu, tace salma fa? Tace tana d’aki, nan yayi sama, har hauwa ta gama ta dauka takai mata farfesun kayan ciki ne, da teba miyan ogbono, tace tashi kici, salma ta tashi tare da daukan kayan cikin ta fara ci, tace kaman Kin san abunda nake so inci gashi yayi yaji, hauwa tayi dariya tace mai ciki an bani da kwadayi yanzu wannan ne yayi yaji, tace eh sosai yajin yamin dadi, nan suka fara fira can hauwa tace mahmud ya shigo kuwa? Tayi shuru tare da kallon hauwa taci gaba da cewa dazu ya shigo kitchen nace kina d’aki, salma ta ‘kago murmushi tace eh ya shigo yace min bari ya dawo, shuru tayi tare da tunanin toh mai yasa mahmud bai zoba bayan ta fada mai ina d’aki, ganin shurun yayi yawa hauwa tace bari inzo in wuce gida, salma tace kai mai yakon ki bari in dan kara warkewa tace ai kin warke yau gida zani, nan ta tashi ta dauki kayanta tace toh sai min yi waya, Allah ya kara sauki ta fita,

1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button