NOVELSUncategorized

NAJEEB 42

AISHA taci gaba da fad’in Wlh zarah inda yayanki zai yarda ya aureni….. Hmmm da naji dad’in rayuwa, ni aida na more da nafi ko wace mace Sa’a….. 


hauwa ta Katseta da fad’in nidai Ina son ganin wannan guy din da kike ta wasa wa haka Wlh 

Aisha tace uhm, Aini tsoran ki ganshi ma nake wlh, baki ga yanda ya had’u ba 
Pls Kuna mana click na ads


Hauwa tace yakai zarah kyau??

Tsaki Aisha taja, tace ina itafa Zarah ba’ka ce, wannan sak Balarabe, baki ji zarah tace mamansu ya d’auko ba, Kai Wlh ya had’u namiji iya namiji, Kinga Wlh zaiyi kwazo….. 

Dariya suka saki tare da shewa 

Ibtisam gaba d’aya ji tayi ranta na baci, jin bazata iya sauraransu ba yasa ta tashi tayi waje abunta, koda ta fita tsaki taja tare da fad’in aikin Banza dana hofi, waima NAJEEB suke wani kuzantawa, tsaki taja tare da fad’in inda Sun San halinshi da basu bata lokacin suba, Wlh, gaba d’aya ranta taji babu dad’i. 

Gaba tayi tana tafiya, ranta gaba d’aya a jagule yake 

mota ce ta tsaya a gabanta, wanda hasken motar ya kashe mata ido, tsaki taja tare da fad’in duba yanda suke wani haska mutum saboda iskanci 

Har zata gota wajan motar taji muryan Dr jibril yana fad’in am so sorry plz, na kashe miki ido, sai Ina haka?? 

Ibtisam tsayawa tayi cak tare da fad’in ina wuni sir 

Yace lafiya, tare da kallonta lokaci d’aya kuma ya fito daka cikin motar ya nufi inda take 

Murmushi ya sakar mata tare da fad’in Amina dare yayi ina zaki?? 

Tace sir na fito insha iska ne 

Yace Ok, ya exam din?? 

Tace Alhmdlh 

Yace Bari in gudu, so Kema ki koma ciki, domin bai kamata kina yawo ke d’aya yanzu ba, domin lokaci ne da yara marasa ji ke zanyar fita 

Ibtisam tace toh tare da fad’in saida safe
Pls Kuna mana click na ads

Yace OK motarshi ya nufa tare da barin skul din 

Itama hanyar komawa tayi, domin gaskiya ya fad’a mata, domin taga irin motocin dake shigowa suna d’iban y’an Mata, ga kuma y’an Mata sai fita ake, Allah dai ya kyauta ya kuma shirya…. 

Ta kusa zuwa kofar d’akinsu ta hango zarah Tana tawowa, tsayawa tayi har Zarah ta k’araso inda take 

Ibtisam tace sai Ina?? 

Zarah tace ke nazo nema, ina kika je???  Kodai duk kishin najeeb dinne yasa kika fita 

Tsaki taja tare da fad’in Allah ya kiyaye akan mai zanyi kishin shi. Wlh kina bani haushi Idan kina fad’in haka, saifa kana son mutum kake kishin shi, in baka son mutum kishin Mai zakayi nashi?? 

Zarah tace toh mai yasa kika fita sanda ake maganan najeeb?? 

Ibtisam shuru tayi kaman tana tunanin abunda zata ce, can tace saboda haka nayi ra’ayi, keda kanki kin San bana son yayanki Mai zanyi dashi?  Kinga dan Allah ki barni haka inji da abunda ke damuna na exam d’ina, gashi gobe zan Gama paper amma gaba d’aya na kasa zama inyi karatu nidai wannan semester din gaba d’aya sai a hankali Wlh 

Zarah tace ai dole, tunda kin d’auki Abu kinsa ma ranki, ibtisam karki ce zanyi miki wannan maganan dan najeeb yayana ne, karki manta Kema y’ar uwata ce, sannan kuma abokiyar shawarata, Nasan a baya bakya son NAJEEB, amma a yanzu na tabbata kina sonshi, domin kuwa a da yanda kike yawan nuna tsananshi k’arara a ranki yanzu ba haka bane, gaba d’aya tsanar da kike Mai ya ragu, kibar yaudaran kanki, ki amshi mijinki hannu bibbiyu…… 

ibtisam wani harara ta sakar ma Zarah tare da fad’in baki da hankali sannan tayi gaba cikin fushi tana fad’in akan me Zata ce tana son NAJEEB, ai koda zanso mutum bazan so wanda ya tsaneni ba, mutumin da baya so na shine zanso??  Allah ya kyauta, mai zanyi dashi, mutumin da yake zina, tare dashan giya wanda baya tsoran Allah, aini har abada bazan taba sonshi ba, yaje can ya zauna da matanshi Wanda ya saba dasu, domin zama da irinshi wata rana saiya kwaso ma mutum cuta ya manna Mai, tunda shi neman Mata yasa gaba, d’aki ta shiga, tana shiga daga su Aisha Anata surutu da HAUWA, ko kallonsu batayi ba, domin gaba d’aya ji tayi haushi suke bata, nufa gadonta tayi wanda kubra ke kwance tana jin karatu bacci ya d’auketa, kashe karatun tayi domin su Aisha Nata surutu ga karatu, itama kwanciya tayi a kusa da kubra, amma gaba d’aya ta kasa bacci, har yau abunda najeeb yayi ya tsaya mata a rai yanda ta kamashi da Najwa suna sex, wani hawaye Mai zafi taji yana zubar mata, lallai najeeb ba mijin zama bane, har yau abun ya tsaya mata a rai ta kasa Manta abun kuma wani abun mamaki ta kasa fad’ama kowa, daga tazo fad’a saita fasa, ta rasa dalili, ita dai ranta yana bata ta rufa Mai asiri…..

Hawaye take da yake ba kuka bane, kuma akwai huta ga k’aran fanka yasa su Aisha basu San mai takeyi ba, balle su Fara mata tambaya ko lafiya 

Ido ta lumshe tana ganin yanda najeeb din ke fucking din Najwa, da sauri ta bud’e ido tare da tashi ta zauna tana sauke wani nishi, sama sama, lokaci d’aya kuma ta fita taje ta dauraye fuskanta, inda ta hango zarah Tana waya 

Bayan ta dauraye fuskan Nata, ciki ta koma inda tahau gado ta kwanta, still tunanin nedai ya kuma dawo mata, duk yanda takai danta cire Abun a rai ta kasa gaba d’aya tunanin abun ne a ranta

Haka taita juyi akan gadon har zarah ta shigo d’akin Itama ta kwanta, ibtisam ta kasa bacci har su Aisha masu fira suma sukai bacci 

Washe gari ibtisam idonta duk ya kumbura ga ciwon kai, domin batai bacci ba, ga exam 8 haka ta shirya ta nufi exam, Bayan sun fito daga exam dinne ta dawo dak’i inda ta samu kubra na zaune ta manne waje d’aya alaman zazzabi ke damunta 

Ibtisam tace kubra bakya jin dad’i ne?? 

Kubra tace eh wlh fever ke damuna Sosai, plz ki bani paracetamol insha, ko zanji dama dama 

Ibtisam tace Kai Wlh banda paracetamol, amma inaga ki tashi muje hspt sai a dubaki, a baki magani, Kinga is very risk kisha magani baki San maike damunki ba 

Kubra tace hakane, bari muje, tashi kubra tayi ta d’auki babban hijab tasa suka fita ita da ibtisam, inda sukai cikin Shika domin taga Dr 

Bayan taga Dr inda aka bata gwaji inda aka ga Malaria ne, nan aka rubuta Mata magani, suka biyo ta wajan emergency, inda suna tsaye domin wata mota ta wuce, aka faka wata mota kusa dasu, nan aka bud’e wani matashi ne wanda kallo d’aya zaka mishi kace lafiyanshi kalau, domin ko motsi bayayi amma sai wanda suka kawo shi sukace bazai iya tafiya ba, nan aka d’auko Keken guragu domin a sashi, nurse din na tabashi tace ai ya rasu…… 

Kubra wani irin ihu tasa yanda kuka san ta san yaron, kuka take tana fad’in ibtisam kalla kiga, wlh kaman kice ya tashi, kalla kiga ikon Allah Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, wayyo kai Allah yaji k’anka 

Nan y’an uwan yaron suka bita da ido, domin ganin yanda ta nuna damuwa akan dan uwan nasu

Nan ibtisam ta jata sukai gaba 

Kubra na hawaye tana fad’in ibtisam wannan kukan Inayi ne tare da tausaya ma kaina, wlh ibtisam tunani Nayi inda nice na mutu, mai zance ma Allah?? Gaba d’aya na bata rayuwa ta, na bijire ma Abun da ubangiji yace Ayi, nabi hudubar shaidan, amma yanzu na gode Allah daya ganar dani tun lokaci bai k’ure Ba, wlh gaba d’aya komai na duniya ya fitar min a kai, ina matukar jin tsoran in aikata Sabo yanzu, lallai ibtisam idan kana son ka k’ara jin tsoran Allah imani ya Kama ka kazo asibti ziyara, na tabbata inda mun shiga accident and emergency da munga abubuwa wanda tayu wani in muka gani bazamu iya bacci ba, saboda tausayi, ibtisam kalla wannan saurayin, jikinshi fresh kaman bai mutu ba, kaman kice Mai ya tashi, ya kuma tashi din, lallai duniya ba komai bace

Ibtisam tace hakane nima mutuwar shi ta tsaya min a rai tasa gaba d’aya jikina yayi sanyi….. Allah yaji k’anshi tare da sauran musulmai 

Kubra ta amsa da Ameen, tare da fad’in Wlh ibtisam ke Kinji dad’i kina da aure, rayuwarki Abun sha’awa, baki da wani fargaba, amma mu gashi babu aure ga sabon Allah, gashi karatun bama bashi muhimmanci tunda yawon mu kawai muke, in mun dawo mubi lecturer su kwanta damu, dan karsu fadar damu, kai Wlh babu komai cikin raina sai tarin dana sani, gobe zan koma Gida tunda na Gama paper, ina son koda na koma Kafin hutu ya Kare zamu dinga waya ina tambayarki abunda ya shige min duhu 

Ibtisam tace karki damu kubra, insha Allah, duk sanda kike da tambaya ki kirani kawai

Nan sukai gaba, inda suka koma cikin skul 

Koda suka shiga d’akinsu a kwance suka tarar da zarah 

Ganin Sun shigo yasa Zarah fad’in Ina kukayi 

Ibtisam tace hspt na raka kubra ganin Dr, ya paper din?? 

Zarah tace hmm, Alhmdlh, tare da kallon kubra tace bakya jin dad’i ne? Ko duk maganan mutumin nan ne??  Kubra tace a’a kawai zazzabi naji Inayi 

Zarah tace Allah ya sawake 

Washe gari duka suka watse sukai gida, Zarah taso ibtisam ta bita suyi abuja amma ta’ki, dole ta hakura ta tafi abuja ibtisam tayi Kano 

Ibtisam ta isa Gida wajan 1 Tana shiga ta iske Ummi bata nan sai granny dake sallah, Dan haka itama alwala taje tayi inda ta Fara sallah 

Bayan ta idar, ta kalli Granny dake zaune tace ina ummi?? 

Granny tace ta tafi anguwa, ya naga kin dawo, ko baki da lafiya ne? Naga duk kin rame 

Ibtisam tace Hmmm granny ba dole ba, exam babu dad’i Wlh, munyi hutu ne sai yasa na dawo

Granny tace auwo tare da gatsan goranta tana ci tana gurus gurus 

Ibtisam tace wai ba zaki daina cin wannan goran ba??  An fad’a miki yana da Illa, Amma kin k’i, wlh Granny ki shafa mana lafiya ki daina, kar kije kici abunda zaisa Musha wuya, gwara ki mutu cikin salama ba tare da wahalan jinya ba…… 

Granny tace dallah Rufamin baki, AI sai a kasheni, naga bakan mutum nake ba, in naci goro ya kashe ni, jiki na ko naki, haba yara sai iyayi komai ace yana da Illa shi kenan mutum kar yaji dad’in rayuwa, haba ni ban taba jin inda akace goro nada Illa ba 

Ibtisam tace ai sai kiyi taci tunda an fad’a miki kin dage, nidai in ciwo ya kama ki bazanyi jinya ba, tunda na fad’a 

Granny ta tsuke baki tare da fad’in shirmen banza da hofi, dama wake bukatar ki? AI na tabbata babu abun arzikin da zaki iya, Aini da kiyi jinyata gwara in zauna ni d’aya yafi min, wannan ba’kar zuciya taki, gashi mijin naki kin kasa hakuri dashi….. 

Granny jin ibtisam tayi shuru yasa ta kalleta, ganinta tayi tana hawaye…. 

Granny tace miye haka kuma?? Haba takwarata maiya faru? cikin sigar rarrashi take tambayarta 

Ibtisam kallon Granny tayi tare da fad’in yanzu Granny komai najeeb yayi ba’a ga laifinshi ba sai nawa???

Granny tace ba haka nake nufi ba, abunda nake nufi kin kasa hakuri dashi….. 

Ibtisam tace taya zanyi hakuri dashi?? Granny karki manta ni mace ce, an d’aura min najeeb ba tare da sanina ba, infact ma ban taba tunanin zan aureshi ba, gaba d’aya nasa rai za muyi aure da kabir sai naji an d’aura da wani, yau najeeb Koba dan uwana bane shi, dole yanda naji babu dad’i hakan zanyi, anyi min wannan a matsayina na mace, wanda ya zama dole in hakura in zauna dashi, Wanda nasan igiyar auren shine keda ikon tsinkata, sannan shi namiji ne, Ance in za suyi adalci su Fara daga Biyu….. 

Kinga Mata biyu akace ba d’aya ba, kinga yana da ikon k’ara auren wacce yake so, amma nifa??  Bani dashi, dole shi dinnan dai zan zauna mawa, ba wani ba, granny inda kin San zafin rabuwa da wanda kake so da ance Nayi hakuri, da yawa mutane basa gane wani abu, yau Indai Abu ba’a kansu yake ba, koya fad’a musu ba, toh basa gane irin zafin abun da kuma rad’adinsa

Nasan ni mace ce, kuma Aljanna ta tana k’asan kafar mijina, Nasan dole nayi masa biyayya, dole nayi masa abunda yayi umarni da inyi masa Indai bai saba ma sha’ria ba……

Duk Nasan wannan, toh amma shi najeeb din yana bin abunda ubangiji yace?? 

Baya bi, mutumin daya kauce ma mahaliccin shi taya wani zai bishi….. 

Kuka ta saki mai cin rai sannan tace Granny, Koba alakan aure najeeb jinina ne, duk da tun Farko bama jituwa haka koda mukai aure babu wata magana Mai dad’i data taba shiga tsakanin mu, yau Koba najeeb dake jinina ba, ko wani naga yana shan giya Wlh zan tsaneshi, amma da yake najeeb akwai ala’kan jini sannan aure ya had’amu dole haka na hakura, kuma na tabbata inda najeeb ba jinina bane kuda kanku zaku ce saiya rabu dani, tun a lokacin da yayi min sharri yace wannan cikin ba nasa bane 

Ya kamata inda kuna sona a lokacin da kun raba wannan auren, amma daga karshe sai kuka barni a wajansa, duk da ya nuna baya bukatar in zauna a tafi dani amma sai lokacin kika ce dole in zauna,  haka kuka tafi kuka barni dashi 

Granny Kun San irin abunda naji??  Kun san irin kuncin da naji??  Duk baku Sani ba, ku burinku in zauna dole a gidan miji, tunda ni mace ce banda wani zabi face inyi hakuri da duk irin abunda miji zaimin, ku matsalanku kar ace y’arku ta zama bazawara koh??  Koba shi bane matsalan?? 

Granny da yawa a k’asar Hausa Anfi samun irin wannan matsalan, kiga namiji shine dukan mace, cin zarafin ta, ya hanata haiyuwa, saboda baya bukata, ya tauye Mata hakkinta, etc 

Kinga duk irin wannan matsalolin ba zasu gyaru ba, har sai iyaye sun daina jin tsoran kar y’ay’ansu su dawo gida su Zame musu nauyi ko kuma kar ace suna da bazawara 

Granny shifa aure sunna ne, ba farillah bane, sannan shi aure daka ranan da mace tayi komai kikayi lada ake baki, bauta ne

Ni a nawa ganin Nasan duk abunda akace bauta ne sai an jure, amma da mace ta zauna miji ya dinga kuntata Mata, ita kuma tana masa abunda zaiji baya so, gwara a raba auren, domin anyi aure Dan samun lada sannan yakai mutum da Aljanna, amma babu farin ciki kuna kai kanku hanyar halaka, ku jefa kanku wuta, Indai irin wannan ne miye amfanin auren??  Kinga babu shi 

Namiji zai bugi mace, ya mata mummunan duka, inta dawo gida sai a bata hakuri ace ta koma aure d’an hakuri ne shi dama bauta sai an jure, aita bata hakuri ana fad’in kiyi ta hakuri wata rana sai labari….. 

Toh Kunga tun daga nan kun ba mijin daman ci gaba da dukanta kenan, domin yaga yayi na Farko ba’a d’auki mataki ba, an k’ara tura mishi ita, kinga zaiga baki da wani gata, wani namijin ma sai yaga kaman Turaki akeyi wajansa, kinga ba’a Fata a haka sai kiji ana fad’in ya kasheta wata rana, ko ita ta kashe shi, domin ita zuciya bata da k’ashi. Bawai Ina nufin Idan namiji ya bugi mace a raba auren bane a’a, but ya kamata a nemo shi aji dalili da zai bugeta, in Abun ta Kama a nemo har waliyansa ayi magana akan Karya k’ara dukanta, in Abun bazaiyi ba ko babu Mai fad’a mishi yaji zaku iya zuwa kotu, alkali ya bashi takarda yayi signing akan inya K’ara dukanki akwai hukunci akansa.

Indai aka d’auki wannan matakin bazai k’ara ba, shine ake kira da kwatan y’anci 

Idan ana haka za’a rage irin abubuwan dake faruwa a gidajan aure musamman…… 

Granny ta dakatar da ita da fad’in ya isa haka ibtisam, na fahimta, amma ina son ki sani, shi aure dace ne, kuma ko wace mace tana da nata jarabawan, Mai hakuri yana tare da Allah, eh abunda kika fad’a gaskiya ne, yana dakyau a kwatan ma mutum yancinshi , amma ina son ki san wani abu guda d’aya akan najeeb, sannan ina son ki sama ranki wani abu, ki d’auka duk abunda yayi miki yayi miki ne cikin rashin sani, ba tare da yasan yayi ba…… Ibtisam na k’okarin magana Granny ta Katseta da fad’in kiyi shuru in Gama magana sai kiyi 

Granny taci gaba da fad’in yanzu kinga NAJEEB yana Abu ne ba tare da sanin ilimin addini ba, kinga baiyi karatun addini ba, duk wasu abu da zaki ga yanayi Ina son ki d’auka cewa bai sani bane, abunda muke k’okarin yanzu mu d’aura shi a hanya kenan, muna son yasan addini ta yanda zai bauta ma mahaliccin sa, duk wannan Abun laifin mahaifinshi ne daya fifita boko akan karatun addini, wanda shi yake d’auka yama d’ansa gata ne, bai san ba gata ya masa ba, domin inda yana sonsa yana son nuna mishi gata shine ya koya Mai ilimin addini, wanda shine zai kaishi ga tsira ranan lahira,.

Granny kamo hannun ibtisam tayi tana fad’in dan Allah takwara ta, Ina son ki zauna da najeeb, ki ceto Dan uwanki daga fad’awa halaka, ina son ki zauna dashi matsayin mata Mai biyayya, domin ke y’ar uwarsa ce, Kece zaki fi kowa sanin darajansa, Koba dangantakar aure akwai na jini, ina son ki duba girman Allah kiyi hakuri ki koma wajan mijinki……….

Ibtisam kuka ya kubce mata sosai gaba d’aya ta kasa magana, ta rasa mai yasa Granny take ganin kaman itace take gudun zama dashi, shine fah yace ya saketa, Bayan haka kuma ance Mai sakin baiyi ba, amma ya tafi ba tare da yace komai ba, sannan tunda ya tafi bai kuma waiwayo waba, amma granny tazo tana d’aura mata laifi……..




2gnovel

4medicals

Smidris


Related Articles

Leave a Reply

Back to top button