NOVELSUncategorized

KWARATA 75

???? —— 73
      Zaune suke ƙofar gida a saman dakali yana korawa Baba Ƙarami bayani cewa Dikko ne ya anshi sammacin daya kaiwa Sultana , gyara zama Baba ƙarami yayi tare da cewa ko shi gwamnan ne da kanshi ya ansa bai shafeshi ba shidai Sultana yake ƙara kuma koshi gwamnan ai yasan gaskiya in banda yarinyar nan ta gaji iskanci har tasan ta
yadda zata haɗa wani da wata yayi iskanci ? Duk wannan bai isheta ba gidan da ni kaina ban sanshi ba amma ita taje ta ganoshi ta tattara kaf kuɗaɗen gado kuma tayi ruf da ciki dasu !

      Amma kai waye yace maka ta anshi kuɗin gadon naku ne ? Jikar gidanmu ana ce mata Hafsa itace suka zo da wata yarinya ana ce mata Amisty , a saman wannan dakalin suka sameni cewa idan naga Sultana dan girman Allah inyi mata magana tasa a sako mata Dadynta , dana tambayeta abinda ya haɗa Babanta da Sultana sai ta koramin bayani ta kuma ƙara da cewa kuma ta anshi kuɗin amma har yanzu ba’a sako Dadyn ba shin saini in zura mata ido ta cinye duk wa’annan yawan kuɗin a cikinta ?

      Kuma iskancin Sultana bai tsaya nan ba saida tabi hanyar da aka lalatamin tarbiyar yarinya , ita kaɗai taji tana ra’ayin iskancinta taje tayi babu wanda ya hanata amma akan me zata gurɓatawa wata da bataji bata gani rayuwa ba ? Abokin firar nashi dai bai sake wata magana ba saidai sauƙi daya nema tare dayi ma Baba ƙarami sallama ya tashi , Baba ƙarami kuma yaci gaba da bunbunai shi ɗaya.

      A kwance na samu Inna tana waya da zani ɗaurin ƙirji da alama wanka tayi , gefenta na zauna ina tunanin rayuwar da zanyi a gidan Dikko idan har Allah ya ƙaddara na zama matarshi , zama dani da Jiddah ? Matar data zo har ƙofar gidan ubana suka ɗaukeni sukaje dani sukaci zarafi na ? Mahaifiyar Dikko ta tsaneni babu gaira babu dalili ga Al ‘ Ameen kuma tunda har mahaifiyar Dikko bata so na tou kuwa taya su “yan uwanshi zasu so ni ne ? Wace irin rayuwa zan fuskata ? Ya za’ayi idan har Jiddah tamin wani abu shin na iya ramawa ? Idan kuma na rama ta faɗawa Dikko ya goyi bayan matarshi ni ina zan saka tawa rayuwar ne ? Tunda dai nayi imani bazai goyi bayan ni bare ba ya yage bayan “yar uwarshi da sukayi auren zuminchie da mahaifiyar Jidda data Dikko uwa ɗaya uba ɗaya shin ya zanyi ne…………?


2gnovel

4medicals

Smidris


       Maganar Inna naji tana cewa ina kikaje ? Nan baya na zagaya na bata amsa dan bana san ina tunanin Dikko ana min magana wallahi , Inna tace ai kin kyauta ni tashi akwai ƙullun koko a palo nima yanzun nan aka kawomin shi yau da maitar koko na tashi a rayuwata saida na samu ƙullun nan hankalina ya kwanta kije ki dama min shi.

      Inna ina zan dama miki wani koko ? Nan gidan mana , kinga karmu tsaya ba shari’a wahala ni ban iya ba Allah ya sani kuma Dikko yace yana gaisheki na faɗa mishi baki lafiya yace zai dawo anjima kuma a ajiye mishi abun daɗi….. Ya zo ne ? Eh , shine nace ina kikaje kika cemin kin zagaya baya ? Tayi maganar tana murmushi , nima murmushin nayi mata amma banyi magana ba.

       Tashi tayi ta saka kayanta aka ɗan matsa turare aka kashe ɗauri ta fita palo , tashi nayi nabi bayanta a saman kujera nasameta zaune tana waya da mijinta , bedroom in na koma na kwanta nasan dai kafin in tashi bacci tasan “yar dibarar da zatayi wanda zamu ci ma cikinmu !

        Biye yake da bayan Bello saf da ƙafa har cikin tsakiyar filin tsakar gidanshi , dakel Bello yake tafiya kamar zai kife Ashiru na biye dashi har cikin ɗakinshi , gaban wani ƙato bedsite Bello ya durƙusa a gajiye sannan ya fara ƙoƙarin turashi gefe ɗaya , Ashiru yasa hannu ɗaya ya janyeshi gefe Ashiru na janyewa Bello ya ɗafe wani bargo sai ya janye wani katako wani zurmemen rami ya bayyana mai tsananin duhu da matsakaicin zurfi.

      Kwanciya Bello yayi ya zura hannunshi a cikin ramin ya jawo kwalbar kallo ɗaya Ashiru yayiwa kwalbar ya fara kakarin amai saboda yadda zuciyarshi ke tashi da tsikar jikinshi , bayan ya ɗauko ya miƙowa Ashiru yace kai kaci uwaka riƙeta muje , rungume kwalbar Bello yayi suka fita daga gidan…..

      Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un ta faɗa da wata irin ƙara mai tayar da hankali tare da tashi zaune saman tsakiyar gado tana sauke wani irin numfashin wahala , da gudu Inna ta shigo tana lafiya ? Wai , wai , wai tayi tare da goge zufar goshinta tana numfashi a wahalce , ke Sultana lafiya ? Har yanzu numfashin ta bai daidaita ba , Inna tace wai mene ne ? A tsora ce nace wani ne ya biyoni a bacci wai zai kasheni kuma idan inajin wasa idan na tashi naje Qerau yau zanga karuwa ɗaya ta mutu sanadin kwakwale mata idanuwa da yayi kamar yadda ya kwakwale idanuwan Mamy , cikin faɗa da ɗaga murya Inna tace ki koma baccin ki faɗa masa baki kasuwa kuma babu wanda ya isa ya kasheki , ta ƙarasa maganar tana kwantar dani ta lulluɓeni da bargo.

     Wayyo Allah Inna da Allah bana so wallahi banayin bacci , cikin hayani tace duk abinda ya cimmiki nasara a bacci a zahiri sai yayi nasara a kanki babu wani maiyi sai Allah haka babu mai rayawa da kashewa idan bashi ba ki faɗa masa baki mutuwa sai kwananki ya ƙare……………………..!

      Saukowa nayi daga saman gadon jiki a sanyaye nace nidai banajin wani bacci , toilet na shiga na watso ruwa dan inɗanji ƙwarin jikina , ina fitowa ko mai ban shafa ba na zura kayana ina gama sakawa na wuce wurin Inna mukaci abinci tare…

Duk wani mahaluƙin dake anguwar Qerau yau kam yana cikin tashin hankali abu ba’a magana anguwar ta cika faful sakamakon alhinin safkar idanuwan wata matar aure duk inda ka leƙa gida ko bisa santa labarin akeyi bayan an cire idanuwanta aka zo aka yadda ita a saman santa….

      Tun asuba aka tsinceta mutanen da suka fito domin zuwa masallaci sallar asuba sune suka fara ganinta dan haka a hankali labari ya fara zagawa cikin anguwa kafin wani lokaci kuma gaba ɗaya gari ya ɗauka ba’a kaiga kaita asibiti ba tace ga garinku nan ,

       Wannan tashin hankali ya zama baƙon al’amari ga mutanen wannan anguwa anyi mutuwa maimakon addu’a ga mamaciyar sai zaƙule²n abinda ya kaita ga afkawa bariki akeyi , ita dai mamaciyar tana da aure da yaranta biyu kuma tana zaman lafiya da mijinta , bakin abinda Allah ya rufa mishi asiri yana riƙe da gidanshi bakin iya gwargwadon karfinshi.

     Wannan matar aure dai ta samu damar antayawa a harkar bariki ne sakamakon gurɓatacciyar ƙawa data tsinta a saman yanar giza gizo , mamaciyar ta shiga harkar bariki ne a sakamakon ƙorafi wa ƙawar tata ta hanyar nuna gazawar mijinta a wurin riƙon gidanshi.

      Bayan ta tsinci wannan ƙawa a saman iska sun ƙulla alaƙa mai girma ta yadda kowa baya iya ɓoyewa kowa sirrinsa , wani zamani ne wanda Allah ya kawomu wai sai kaga mace a duniyar nan duk abinda taci ko tasha saita ɗaukeshi hoto ta turawa wata , duk ƙawar da kike tare da ita ta fara miki wannan tsire²n na ɗaukar abinci ta turo miki shi ta waya wannan ba ƙawa bace ba maza kija mata layi ba abokiyar tarayya bace ba idan har tanajin ita mai kirkice to ta zobo abinci a kwano ta bada a kawo miki bawai ta turo miki ta waya ki gani ba , kina gani miyanki ya fara tsinkewa saidai ki kalla ki ƙara kallo kina aimu ansha damu mukam mata muka rako wasu sun more duniya muko dai gamu nan rayuwa har yanzu bata canja ba.

     Abota ta ƙulle mai girma kowa yana ziyarta ɗan uwansa , yayin da suka shawartar junansu ta hanyar tura saƙo wa junansu ta whatsapp , ita dai mamaciyar tana tura ƙorafin mijinta ne idan yayi mata abu kaɗan , yake “yar uwata ki kwantar da hankalinki yatsun hannunki kawai kika kalla kinsan ba tsawonsu ɗaya ba wani yafi wani wani kuma bai kai wani ba , ita rayuwa bata yuwuwa ace kullum ke abinda kake so shi zaka samu dole , ita rayuwa juyawa takeyi wata rana asha zuma wata rana a lashi maɗaci haka rayuwar take tafiya duk wanda kika gani yana da tashi damuwar idan mai haƙuri ne ya ɓoye sirrin shi wa rayuwarshi da zuciyarshi ke kuma mai surutu jira kike a tara taron sabga biki ko suna duk inda kika zauna harshenki ake ji ke sarki matsalar gidan aure kullum an miki , kuɗin cefanenki bai kai ba , waya aikeki ? Waya sa ki ? Duk namijin da kika gani duniya babu namijin da yake so afi matarshi wanda duk baima iyalinshi ba baya da iko ne , idan ko maƙetacin namiji ne yana dashi ya ƙuntata miki barshi da Allah ja bakinki kiyi shiru ki lulluɓe aibin mijinki sai Allah ya lulluɓe miki naki….

     Bayan ƙawance yayi girma ta waya sai aka fara ziyartar juna , mai mutuwa itace ta fara zuwa gidan rayayya tare da yaranta dan sada zuminci an tareta da shagali mai girma ta hanyar tara mata abubuwan motsa baki na zamani irin wanda bata taɓa ci ko sha a rayuwarta ba , an yini ana fira kowa yana faɗar irin rayuwar da yakeyi a gidan aure , yayin da ita wacce akaje gidanta take faɗo nata nasarorin rayuwar , mai mutuwa kuma ta hankaɗe zuciyarta taci gaba da tona asirin mijinta ta hanyar nuna gazawarshi wurin riƙon gida , bayan ta tashi tafiya ita wacce akaje gidanta ta shiga store ta ɗan tattaro mata kayan abinci ɗanye , irinsu shinkafa , taliya , makaroni , cuscus da dai sauransu ta haɗa mata da ɗan kuɗi bayan ta haɗa mata da kwancen kayan sawa….

    Bayan an kwana biyu ƙawa tace itama zata zo , dan haka mai mutuwa ta hana ma kanta zaman lafiya ta faɗa maƙota neman rancen kuɗi wai ƙawarta zata zo bata so tazo ta raina mata , haka dai tayi ta faɗawa maƙota tana neman rance harta samo tazo itama ta haɗa irin tata ƙaryar , bayan ƙawa tazo ana fira ne tace mata amma yadda kike faɗar talaucin mijin naki kamar bai kai ba gashi komai na gani babu dai wata damuwa , hmmm “yar maular saita buɗe baki taci gaba da sana’ar nata tunda taga idan ta faɗi damuwarta kuɗi ake bata dan haka tace tou duk wannan da kika gani bashi na ciwo kuɗin a maƙota dan in fita kunyarki kindai san hausawa sunce abokin cin mushe ba’a nuna mishi wuƙa , taci gaba da ɗimi faɗi ba’a tambayeta ba , amma ni a gani na wasu matan sunayin “yar sana’a haka a gida dan su taimakawa mazajensu da abinda suka gagara yi musu.

     Da ƙawa ta tashi tafiya taba mamaciya kuɗin da suka gigita mata lissafi tace ta biya bashin da ake binta ita kuma tayi ta zabga , haka dai akaci gaba da abota rayayya tana taimakon matacciya sosai , ganin ana yi mata hauka da kuɗi yasa ta gaji ta tambayeta kodai tana kasuwanci ne ? Tace bata kasuwanci bata siyar da fari ko baƙi tana da abokai ne dai masu taimakonta a waje , ta nemi ƙarin bayani aka bata sirrin abun dan haka babu wani tunani ko hangen abinda zaije ya dawo itama ta yanki kati ta faɗa harkar bariki yanzu yau wa gari ya waya………?

      Bello rungume yake da kwalba har suka iso inda aka ajiyesu ake basu horo , Ashiru kasa taɓa kwalbar yayi ya barta a hannun Bello yadai faɗawa mai gida sunje sun dawo , mai gida yace kawai yaje abunshi…..

     Bayan sati ɗaya

     Dikko yazo gidanmu a ranar da yace zai dawo kuma ciki ya shiga Inna da kanta ta lallaɓa ta nema masa abun daɗi kamar yadda ya faɗamin kuma yaci naji daɗi , daya zo kuma ya tanbayeni akan yadda akayi na saka Safiyya karuwanci nace ni babu ruwana kawai dai naji haushi ne sunamin gori na zama karuwa ranar da na rabu dashi a hanyarmu ta komawa makaranta mukayi faɗa na dawo gida ranar da suka ganni shine sukayi ta tura yaransu gida wai ga karuwa nan karna ɓata musu tarbiyar yara abin yamin ciwo shine na faɗawa Aunty Mamy daga nan bansan yadda akayi ba ,

     Dikko yamin faɗa sosai kamar zai dakeni dan harsai da Inna ta kirani a waya dan a palo muke tana bedroom , ta tambayeni abinda ya haɗamu ban faɗa mata ba dan har Dikko yazo ya tafi Inna bata fito ba ,

    A ranar ya sauke hidima wa Inna yayi jib da kwano na kuɗin da wallahi saida Inna ta ruɗe data gansu danni dama kyauta ta da Dikko biyu ce daga kuɗin daya bani a makaranta sai wanda ya sakomin a mota nasha mai da Umar ya kawomin wacce Al ‘ ameen ya ansa aka bawa Jiddah ita take hawa , sai kuɗin daya bani a ƙofar gidanmu ban ansa ba , ranar kam saida ya gigita Inna yasa mata mantuwar dole da manya kuɗaɗe a palo ya ɓaresu saman kujera ni kuma yayi fushi dani yai tafiyarshi saboda na haɗa Safiyya anyi iskanci da ita da baban Mardiyya duk da nace bani bace yace ba abinda ya dameshi bashi naci zamu bayan aure.

     A ɓangarensu Bello kuma bai saki Dady ba amma tunda Momy tayi magana yasa aka sassauta bala’en da ake musu , an canja musu wurin zama ana basu abinci mai kyau shi Dady kuɗi kawai zai bayar ya kama gabanshi amma yace yana jiran wasu kuɗaɗe ne suzo saiya bayar ,

     Tun washe garin ranar da aka ɗauko kwalba Dikko yasa aka tara manyan malamai yayi musu bayanin abinda yake so na za’ayi masa saukar al’qur’ani sau goma a rana har tsawon kwanaki talatin , tou an buɗe kwalba kamar yadda Bello yace malamai kuma suka ci gaba da sauka kuma ragunann nan goma duk ranar duniya idan akayi sauka haka ake yankesu ana raba naman sadaka.

      Ranar da ya kama zuwa kotu banje ba lawyer Dikko ya tura bayan ya faɗa masa yadda kuɗi yake , idan kuma an gama shari’ar yana ƙarar baba ƙarami akan ƙazafin da yayi ma matarsa kuji wani neman rikici da rashin san zaman lafiya na Dikko kuma……..!

        Maganar Bello daya faɗa shine ya kashe Binna da kanshi nayi amfani da wata magana daya faɗamin a police station cewa , inji tsoron Allah in babu nan akwai ranar hisabi duk wanda yaci zalin wani dai² da ƙwayar zarra ubangiji bazai barshi ba , ki daina ganin kin samu dama ta taƙin lokaci yasa ki manta da rayuwar gaba , karki biyewa zuciya ki kafa abinda zaisa kiyi nadama wata rana , tunda har yayi imani da ranar hisabi bazan bar akashe Bello ba zamu haɗu ranar hisabin dani dashi da *BA BINNA* wannan shari’ar Allah kaɗai zaiyi ta…….

     Hafsa kuwa tana tsaye wurin ganin ta gano inda kakar Ba Binna take kuma ta faɗawa Hajiya cewa idan harta ganosu saita faɗa musu itace silar mutuwar “yar su kuma tana roƙo Allah yasa masu zuciyane su kasheta kowa ya huta mai baƙin halin masifa kamar zuciyar fir’auna.

      Tunda nayi mafarkin an kashe wata matar aure a Qerau ban sake ganin mutumin a bacci ba kuma ban faɗawa Dikko ba ,

       Dikko ya riƙo wuta sosai ya matse lamba wa Dady a tura gidansu An mata , Dady yace tou kadai ga yadda Mom inka take hawa da rana ɗaya bata sauko ba abun nata kullum gaba yakeyi akan bata yadda ka auri yarinyar nan ba , Dikko yace Dady nayi nisa fa za’a samu matsala Dady yace yanzu ya kake so ayi ? Ka tura “yan uwanka kawai su an somin auren ta babu wanda yaji babu wanda ya gani ,

       Idan kuma bayan anyi auren matsala ta shigo fa ? Babu damuwa Dady ni zanji da duk wata matsala , shiru Dady yayi yana nazari sannan yace daga neman aure idan abun ya warware ba’a ɗaura ba fa ? Dikko yace babu maganar neman aure kawai ɗaura aure za’ayi daga nan sai ayi duk wadda za’ayi , tou ina zaka ajiyeta Babana ? G R A tare da Jiddah , Babana yarinyar nan bata iya zama da Jiddah gaskiya , Dady nidai tare zasu zauna Allah ya bada sa’a kawai zakace , murmushi Dady yayi tare da cewa Allah ya tabbatar da alkairi Dikko ya ansa da amin tare da faɗa masa ranar juma’a ne , Dady yace Allah ya kaimu zai tafi da Momy ta rakashi ganin likita kafin su dawo anyi komai an gama………..

         Dikko da kanshi yazo ya samu Inna sukayi magana yau duk laɓe²nta saida ya ganta kuma ya faɗa mata cewa ya tsaida ranar aurenshi da An mata ranar juma’a saura kwana 8 daga yau kenan , Inna tace ita gaskiya kwana 8 yayi mata kusa² tana da hidima sosai , Dikko yace shi baya buƙatar wuce wannan lokacin , kuma wane hidima gareta ta manta da yanzu An mata tayi aure da Sultan ? Ko sai nashi ne za’ace yazo da wuri ? Kodai har yanzu bata daina fushi dashi ba ? Shiru Inna tayi bata bashi ansa ba , saida ya ƙari maganarshi ya tashi yauma kuɗi ya safke mata na mamaki mai nuni da ko rashin kuɗi yasa kwana 8 yayi mata kusa² , baima saurareni ba kuma dana gaishi bai ansa ba.

     Bayan tafiyar Dikko Inna ta shige ɗaki ta kira ƙawarta suka tattauna dan ita Inna kallon ɗan duniya take ma Dikko shi yasa ta fara neman hanyar da zata gyara “yarta gani take wannan hanyar itace mafita….

      Da mijinta yazo ta rattafa mishi auren Sultana yau saura kwana 8 aurenta , waishi ba’a kyauta mishi ba ya za’ayi masa haka abu babu notice tace yayi haƙuri , kuma daya tambayeta wanda Sultana zata aura aure haka kwatsam , cewa tayi sunanshi Muhammadu , waye ubanshi kuma sun bincika halinsa har zata ɗauki Sultana ga baƙon fuska ta bayar tayi mata aure haka kamar ta gaji da ita ? Inna tace sanin ubanshi halinshi da komai nashi sa fuskanci juna idan anyi auren ,

        Inna ranar jinta takeyi kamar ba ita ba , tana cikin farin ciki mara musultuwa cikin ƙanƙanin lokaci gidanta ya cika da taron ƙawayenta ƙasaitattun mata masuji da kansu a gidan aure tou wai ita Inna ina ma ta samu wa’anan ƙwanƙwasashin mata ? Suke ta huɗɗinsu Inna ta faɗa musu Sultana Dikko zata aura , amma bansan abinda yasa ta ɓoyewa mijinta ba ,

         Bayan kwana biyu yadda Dikko yasa aka haukata gidanshi yasa Jiddah ta gane aure zaiyi dan haka ta fara ɓarin kaya tana ta hauka tana zage² gaba ɗaya ta tashi hankalin duk wani wanda yake da dalilin sanin Dikko zai aure , tou ai babu mai iya tunkarar Dikko da zancen dakatar da aure sai Momy kuma bata nan Dady yajata sunyi tafiya dan Dikko yayi hidimarshi ya gama saida tazo ta samu amarya ,

       Jiddah bata gama tabbatar da Dikko zaiyi aure ba saida taga katin ɗaurin aure kuma Umar ne ya kawo mata shi , Dikko yana kwance yana bacci ta shigo ɗakin da gudu bayan Mardiyya ta tunzurota ta shigo tana ta ɓarke²n zagi tana aibata shi san ranta bai mata magana ba yayi kamar bacci yake dan yasan zafin da raɗaɗin da mata keji yayin da za’a musu abiyar zama , ya gani yadda Yayarshi tayi da akayi mata abiyar zama aurenta kamar zai rabu dan Momy ɗaure mata ƙugu tayi ta dawo gida , ba abinda zaice ma Jiddah tayi duk haukanta kila haka zaisa ta samu natsuwa idan kuma tayi ƙoƙarin keta iyaka zai nuna mata nashi haukan sai yayi mata dukan da har ya gama auren tana saman gadon asibiti saboda shi abu ƙalilin ke ƙufular dashi…….!

pls click

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button