GOJE

GOJE 3 and 4

       FREE PEGE

3&4
Tuntun’be tayi da wani girkakken icce tayi mummunar faduwa kanta ya bugu da tsinin iccen, lokaci guda jini ya fara tsartuwa, hannu tasa ta dafe gurin, murya ta bud’e sosai ta kwarma ihu! wanda ya tashi dabbobin dake dajin. lokaci guda suka fara koke-koke, wasu daga ciki har sun fara fitowa daga ramukansu.

Hakan ya sanyasu tsayawa a gurin kwakkwaran motsi babu wanda yayi a cikinsu, da ido yayi musu magana cewa suyi lamfu a kada wanda yayi motsi wanda zai dauki hankalin dabbobin da suka fara fitowa, hakan sukayi, dajin! yayi tsit! sai kukan dabbobin ne kawai ke tashi.

Wani irin juwa da hajijiya ta dinga yi a gurin kafin ta yanke jiki ta fad’i kan ciyayi, jini kuwa duk ya jika mata fuska da gaban rigarta.

Cike da jarumta ya daidaita kwari da bakar dake hannunsa, yanayi yana waiwayen bayansa yana hasashen ta inda wata dabbar zata fito, da baya da baya ya dinga tafiya har ya cimma inda take kwance, yana yunk’urin d’aukarta yaji hucin wucewarsa zurrrrrrr! cikin zafin nama yayi wani irin tsalle ya zaro kaifaffar wukar dake rataye a bayansa ya fille masa kai! tsayin macijin ya kai in taha.!

Fitilar dake hannunsa ya kunna ya haske mata fuska yana kallonta, yayi mamakin yanda akayi ma har ya dawo da baya domin taimaka mata, wai kamarshi, GOJE! yarinya ‘kank’anuwa irin wannan tayi yunkurin marin fuskarsa.

Tsaki! yaja yana gyada kanshi, da alama hakan ya zame masa jiki, tsumman dake d’aure a k’ugunta ya fizge, ya yagi rabi ya daure mata kan dashi, tsam ya matse jinin ya daina zuba, ya dauketa kacokan ya goya a bayansa yasa tsumman ya daureta, yanayin tafiyarsa sam be sanja ba cike da jarumta yake taka itacuwan gurin tunda ya fahimci a sume take burinshi ya samu inda ruwa yake domin ceton rayuwarta.

Yaran ya kira suka fito, daga mab’oyarsu da yawa daga cikinsu sun farauci k’ananun dabbobi irin wanda suka firfito, ya basu umarnin zuwa su nannad’o macijin da ya sare masa kai, yana gama basu umarni yayi gaba bai tsaya ba har sai da ya cimma inda ruwa yake,
Kwantar da ita yayi kan rairaiyi, yasa hannunsa cikin ruwan yana debowa yana watsa mata a ko’ina na jikinta.

Sai da jikinta ya jike jagab da ruwa sannan Allah ya bata ikon sauke ajiyar zuciya, gashin idonta ya fara motsi tana so ta bude idon amma sunyi mata nauyi ga wani irin ciwo da kanta yake mata, hannu ta dora saman kanta bakinta sai motsi yake, Tashi yayi ya bar gurin.

Ta jima tana ganin dishi-dishi a idonta kafin su bude sosai, da yake garin ya soma haske can nesa ta hangoshi tsaye amma bayanshi kawai take gani, cikin mugun tsamin jiki da azabar qunar data tashi tai jawur! ta mike zaune tana bin ilahirin jikinta da kallo, wasu zafafan hawaye suka kwace mata, lebe ta ciza tana furzar da wani irin huci! wai kamar ita Gimbiya gaba da baya itace a wulakance a yashe a bakin kogi, wani kazami bagidaje yana ganin sassan jikinta, wannan abun yayi mata mugun ciwo a rai.

Yana daga inda yake tsaye ya dinga jin shashshekar kukanta na tashi. Ya juyo tare da da zuba mata jajayen idanuwansa.

Itama shi take kallo tana kisma irin hukuncin da za tayi masa mutukar ya kusanto inda take.

Be saurareta ba, bakin kogin ya nufa ya tsuguna yana daura alwala.

Jin sawun tafiya da haushin karnuka yasa da sauri ta waiwaya, yaran shi ne tare da karnukansu da kuma abunda suka farauto.

Suka samu wani fili suka zube kayansu da yake duk inda zasu shiga sukan tafi da guzurinsu, wata katuwar dadduma suka shimfida, kafin su hura wuta, sannan suka nufi bakin kogin domin daura alwala kamar yanda suka ga ogansu yayi
Shine ya jasu jam’i, duk tana zaune tana kallonsu, suka idar ya daga hannu sama yana addua suna amsawa mamaki sosai ya lullubeta ganin yanda yake azkar masu zafi da adduoin da takasa tantance mai yake fada tunda wasu da labarci yake, tayi mamakin hakan daga gurinsa a ganinta rikakken d’an daba d’an ta’addah! irinsa bai kamata a samu ilimin addini a tare dashi ba.

A nutse ya juyo yayi wani irin zama tamkar basarake! ya kashingida tare da tankwashe kafa daya ya dogare dayar tare da dora hannunsa akai.

A maimakon musabaha kamar yanda Annabi ya koyar sai kawai suka dinga dukan hannunwasu da sunan gaisuwa a gareshi, wasu daga cikinsu suka fara bushe-bushe irin nasu suka hada baki gurin fadin.” A lafiya Goje! Cauuu!! Uban mafarauta! Sa’a dai mai maganin wuka da kaho Dawa dai!! Umarul-Faruku muna mika gaisuwa a gareka.”

Ya dinga girgiza kansa yana jin tsigar jikinsa na wani irin tashi, numfashi ya shiga saukewa yana furzar da wani irin huci, Shisha ya kaiwa raruma yasa a baki ya fara tada hayaki a gurin.

Ganin haka sai suka tashi suka bar gurin, rabuwa sukayi wasu suka fara aikin gashe-gashen irin dabbobin da suke farauto, wasu kuma suka kutsa cikin dajika domin samun abun da zasu ci.

Tana nan zaune a inda take k’aik’ayi duk ya isheta, rana ta kwalle a gurin, so take ta tashi ta sauya guri kunya da tarin takaici sunyi mata dabaibayi, yanda Allah ya taimake ta ma ta lura sam ita din bata gaba gabansu, domin dik wanda yazo wucewa ta kusa da ita ba yayi mata kyakykyawan kallo.

Kafafunta ta motsa, domin mikewa tsaye, aikuwa qunar ta kwaile ta fara fitar da ruwa da jini, tsananin azabar zafi ya sanyata tayi saurin mikar da kafar cikin tsautsayi ta danne kunama! lokacin ta d’ana! wani irin ‘kara tayi jikinta ya dinga rawa! da rarrafe ta matsa daga gurin, idonta kan kunamar tana kokarin bin gefen kogin domin shiga wani rami………..Kafarsa yasa ya murjeta! yana cire kafar taga yanda tabi kasa tayi daga-daga a gurin!!

Inuwarsa ta dinga kallo yayi mata rumfa gata tayi goho tamkar mai shirin haihuwa, gabadaya duwawunta a waje wando ne kawai ya taimaketa.

Duk da tana jin tsoron sake zama a gurin hakan nan ta hakura ta zauna jikinta har yanzu rawa yake ga zufa sai ketowa take da sassan jikinta.

Tsugunawa yayi kusa da ita har tana jin hucin numfashinsa, ta kalleshi, beyi aune ba yaji saukar kakkauran yawun bakinta a fuskarsa, yasa hannu ya sharce yawun yana me cigaba da watsa mata kwala-kwalan idanuwansa,

Cikin zafin nama ta ciko hannunta da kasar gurin zata watsa masa ya kautar da fuskarsa, kasar ta zube a jikinsa, hannu yasa ya buge, ya kalleta fuskarsa a murtuke yace.” Meye sunanki a wane gari kike.”?

Tana kuka me cike da azabar data rasa wace iri ce tace.” Ni kake tambaya garinmu kaje ka daukoni a gaban iyayenta amma saboda rainin hankali kazo kana tambayata.”

Ya girgiza kai da fadin.” Ni taimaka miki zanyi amma ban san abinda ya shafeki b……….”Karya kake.”! ta katse shi da karfin gaske sai huci take! tana jira ya sake wata magana ta kaiwa fuskarsa mari!

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta, tunda ya taso a lokacin yarinta da girma babu wanda ya ta’ba karyatashi cikin abokai da sauran jama’ar gari sai wannan karamar yarinyar, Sa’arta ta sameshi mai tsananin tausayin mace amma ba don hakaba da yau ta gane kuranta a hannunsa.

Cinyoyinta ya zubawa ido yana kallon yanda qunar ta ruruce! tana ruwa da jini gashi har ta fara cin jikinta, ba tare da tayi aune ba taji saukar hannunsa, fittt ya d’aye fatar data qone! jiki na karkarwa ta rike hannunsa, tana aika masa da Allah ya isa.

Be saurareta ba ya hade duka hannuwanta ya rike da hannunsa daya, ya sake bin d’aya cinyar ya d’aye fatar qunar! kawai sai ta zube a gurin tana makyarkyata.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button