GOJE

GOJE 31 and 32

Maigirma governor da kansa ya ‘bukacin san ganin GOJE!! gani da ido domin tattauna wasu muhimman abubuwa.

Asp ne ya jagoranci tafiyar……..shigarsu government house din keda wuya Maigirma governor ya mike daga kan kujerarsa, Asp yayi mamakin hakan sosai! koda yake yaron ya kai kuma ya cancanta da girmamawa! Governor be zauna ba har sai da suka zauna sannan ya koma ya zauna kan kujerarsa.

Cikin mutumci da girmama juna suka gaisa kafin su shiga tattauna abinda ya tarasu a gurin.

Ya jima kanshi a sunkuye yana nazari da tunanin maganganun governor a kansa. ya sauke ajiyar zuciya, cikin nutsuwa ya kalleshi da fadin.” Wannan shine burina a duniya cewar na tabbatu gurin hidimtawa addinin Allah da kuma hidimtawa k’asata Najeria da al’ummar dake cikinta, amma ranka ya dad’e ya za’ayi nayi gogayya da manya-manyan ma’aikatan tsaro! bayan bani da cikkaken ilimi a kan hakan, ba zan boye maka cewa iyakaci na secondary skull ba shin dama hakan tana iya faruwa.”?

Maigirma governor yayi dariya irin ta manya kafin yace.” Malam bahaushe yace ta yaro kyau take bata k’arko! UMARU! ai bai cancata ka kira kanka da jahili ba, koda iyakacinka primary ka cancanta daka zauna a kujera irin ta Asp saboda jarumtarka, kayi abinda shi Asp din ya kasa dashi da wa’inda suke ‘karkashinsa, sun buga! sun buga! sunyi-sunyi! Allah bai basu nasara ba, wannan dalilin ya sanya na d’auko hayar sojoji daga libiya domin su taimaka musu, sai gashi kai d’aya ‘kwal kayi aikin mutum dubu! koda baka san (A) ba to ni na d’auke ‘ka aiki a’kar’kashin mulki na, kuma zan biya ka albashi mai kyau! sannan kuma na baka kyautar gida da motar hawa, domin ka zauna da iyalinka a ciki.”

Sai ya rasa bakin magana kawai ya zubawa Asp ido yana jimanta al’amarin, ganin ya rasa bakin magana ne yasa Asp din ya ari bakinsa domin yaci masa albasa.

Governor ya kalleshi da fadin.” Asp babu batun godiya UMARU ya cancanci abinda yafi haka, godiyar ta isa haka, kai dashi duk kuna aiki kan gaskiya gami da kishin ‘kasar ku, duka kun cancanci a baku lambar yabo.”

Asp ya mika masa sannu cike da farin ciki yace.” Mungode sosai da wannan karamci ranka ya dade Allah yasa ayi a gama lafiya.” Ya amsa da “ameen ya Allah, kuma Allah ya taimake ku akan aikinku.” gabadaya suka amsa da “ameen.”

Hotona sukayi sosai suka sanya shi a tsakiya, sai kuma wasu da maigirman governor ya rungumeshi bayan ya bashi lambar yabo da girmamawa!! sosai ya samu kyaututtuka na mussaman daga gurin manya manyan ‘yan siyasan dake gidan gwamnatin, su kansu sun jinjinawa kokarinsa,

Cike da tsantsar farin ciki da annushuwa suka fita daga gidan gwamnatin.


A daran ranar da al’amarin ya faru ZINATU da kyar ta iya runtsawa saboda ‘bakin ciki da takaicin ganin yanda lokaci guda Allah ya daukakashi, ganin hotonsa da governor a lokacin da ya bashi lambar yabo da girmamawa ya mugun daga mata hankali, haka kawai take so ta ganshi a tagaiyare! a wulakance! amma hakan bata samu ba, babban bakin cikinta yanda taga manya mutane na girmamshi tare da kambaba! darajarsa, bata damu da kyaututtukan da ya samu ba kamar yanda ta damu da taga ya k’askanta!

Washe gari da ‘kyar ta fito daga dakin domin breakfast, Asp din ya gidan be fita ba, ta gaisheshi kamar bata so, ya amsa yana nazarinta shi kansa d’abi’un yarinyar gabadaya basu bashi sha’awa, shiyasa yake so su shirya ranar da zasu kaita gaban mahaifinta kamar yanda yayi alkawari.

Ya kalleta sai kumbure-kumbure take alhalin babu abunda akai mata, da kulawa a maganarsa yace.”ZINATU Ina fatan dai kina jin dadin zama damu ko.”

Da ‘kyar tace.” Um ina jin dadin karamcinku a gareni nagode amma yaushe ne za’a sallame ni haka, tunda dai duk bukatunku sun biya.”

Ya kalleta da mamakin maganarta yace.” Kamar akwai abunda yake cikin ranki duba da yanayin maganarki.”

Murmushi takaici tayi da fadin.” Ranka shi dad’e wannan mutumin fa da kuka d’auki son duniya kuka d’ora masa bai da kirki ko kad’an! mugu! ne azzalimi! ni har yanzu ban yarda da gaskiyarsa ba.”

Asp ransa ya baci da jin maganarta sai kawai ya rufeta da fad’a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, yace.” Ban san wace irin kiyayya kike wa Umaru ba, shin me kike so muyi masa bayan wanda yafi haka? mutumin nan ya taimakeki a lokacin da kike bukatar taimako amma duk sanda za kiyi magana a kansa ba mai kyau bace! shin wai me yayi miki da zafi da kika tsaneshi haka.”!

Cikin ‘Kunci da takaici tace.” Ranka ya dade mu bar maganar kawai domin duk abinda zan fada maka a kansa ba zaka yarda ba duba da ganin yanda zuciyarka ta hasala! kawai saboda na kiraye shi da macuci alhalin sunan daya cancanta dashi kenan.”

Yace.”Kin san Allah ba zan matsa daga gurin nan ba har sai kin sheda min irin cutar da yayi miki da har kike kiran sa da wannan sunan.”

Ganin yanda ya kafe ta da idanuwansa yasa jikinta mutuwa, me zata ce yayi mata bayan alkairi, ta san ya taka muhimmiyar rawa a kanta amma haka kawai take jin haushinsa! a yanzu duk abinda zata fada a kansa sharri ne!

Ya katse tunaninta da fadin.” Ke nake sauraro na fada miki ba zan bar gurin nan ba har sai naji dalilin da yasa kike tsaneshi.”

Bakinta ya sub’ce gurin fadin”Saboda ya keta min haddi sakamakon kad’aicewar mu a dajin.”

Ya zuba mata ido da so ya tabbatar da maganarta…….”Ya keta miki haddi kamar yaya.”?

Ko kunya ta sake lailayo wani sharrin……”Fyad’e yayi min.” Tafad’a babu nadama a cikin maganarta.

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta kafin ya girgiza kai da fadin.” Wannan shaci fad’i ne ban yarda zai aikata hakan ba.”

Murmushin takaici tayi da fadin.” Ai dama ba zaka yarda ba saboda jarumtarsa tana burgeka a matsayinka na babban mutumin mai rik’e da mu’kamin Asp bai kamata ace kana mubaya ga wannan k’azamin mutumin ba.”

Maganarta sai ta bashi dariya, ya tsaya ya dara kafin ya mike yana duba agogon dake daure a hannunsa yace.” Lallai yarinyar nan da gaske kike amma babu damuwa, wannan maganar kuma ba zan barta ba sai mun tattaunata da mutumin naki.” Shuru tayi ba tace komai ba, har ya bar gurin, tana zaune a gurin suka fito tare da madam d’inshi dirarriyar mace kyakykawa da kyawun jiki sam ba za kace ta haifi ‘yar shekara ashirin ba, hannunta rike da ‘yar jakarshi ta rakashi bakin mota ta nayi masa fatan alkairi.
Koda ta dawo a falon ta zauna suna hira jefi-jefi ta d’an saki jikinta sakamakon mutunci da karamcin matar wanda ya janyo mata ‘kima da mutunci a idonta……Sai dai kwata-kwata jininta bai had’u da Nabila ba, haka kawai ta tsani yarinyar alhalin babu wani abu da tayi mata na laifi……..daidai gwargwado tana bata girma tunda ta fahimci cewa ta d’an girme mata sai take kiranta da Auntyna. hakan yana sake sanyawa kanta ya kara girma domin akwai ta da son girma, gata dai a gidan ubanta amma mulkar yarinyar take, da yake ita din mai saukin kai ce bata damuwa, domin bata mance ingantaccen hadisin nan da yake cewa “ka girmama bakon ka, wannan dalilin yasa take mata duk abinda take so, wanda ita kuma anata ‘bangaran take ganin kamar ta isa ne! shiyasa take mata biyayya…..!

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button